Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
fad'a makaba cigaba da rayuwata a doron k'asa hadarine, muje kamaidani kafin tazo inba hakaba kaima rayuwarka zata iya salwanta.
Mik'ewa yayi cikin rashin fahimtar maganarta yace jawahir wacece zatazo?
Lokaci guda jawahir tarikid'e Idanuwan nan sukayi jajir cikin d'aga murya tace na ce muje kamaida ni!
Barr Faruk bai musaba yad'auki system da wayoyinshi yawuce gaba jawahir tana dafe da kanta ahaka take binshi har suka fito yarufe d'akin yaje yabasu key d'insu sannan suka wuce wajen motarshi.
Suna shiga tura kanta tayi tsakanin cinyiyonta wani irin sautin kuka takeyi, gabad'aya kan Barr Faruk ya d'aure yarasa dalilin damuwarta a lokaci guda ahaka har suka isa gidan yarin suna isa tana shirin bud'e mota tafita yakira sunanta juyowa tayi takalleshi yace sai yaushe zaki ida min labarin?
Girgiza kai tayi tace bazan iyaba Barrister akwai had'ari sosai acikin rayuwata, Barr Faruk yace duk da haka jawahir ya kamata kidaure.
Bud'e motar tayi tafita shima nan yabud'e yafito nan yawuce gaba wasu 'yan sanda sukazo suka rik'eta wata irin tafiya takeyi tana rangaji har office d'in shugabansu.
Da mamaki yake kallonsu yace Barrister lafiya?
Murmushi Barr Faruk yayi yace lafiya lau na maidota kamar yadda nayi Alk'awali.
Murmushi yayi yace aiko ka kyauta dan ina nan hankalina a tashe na kasa zaune da tsaye saboda gangancin barinka da nayi kuka fita da ita dan na karya dokat aikina, ammah kamar ta yi kuka ko?
Kallonta Barr Faruk yayi yaga yadda idanunta sukayi jajir.
Alhaji Mahadi sawa yayi 'yan sanda sumaidata d'akinta dakyar take tafiya tana yin baya kamar zata fad'i.
Bayan tafiyarsu Barr Faruk yace kasan duk wanda yake cikin gidan nan yatuna rayuwarshi tabaya dole yaji wani iri.
Hakane ammah in kayi rayuwa mekyau ba.
Murmushi yayi yana shirin yin magana wayarshi tafara ringing d'aukowa yayi yai picking tare da yin sallama yace Daddy.
Daga chan 'bangaren dady yace Faruk kazo gida yanzu zakaje Daura.
Daura kuma Daddy? A wannan lokacin?
Daddy tsinke wayarshi yayi Barr Faruk yayi murmushi yace Alhaji Mahadi bari intashi intafi ana nemana a gida ammah kafin intafi zan d'anyi magana da jawahir.
Alhaji Mahadi shuru yayi sai chan yace shikenan Barrister babu damuwa bari insa arakaka.
'Daya daga cikin ma'aikatan gidan yakira nan Barr Faruk yamike suka tafi suna zuwa yasamu jawahir kwance a k'asa idanuwanta a rufe daga gefenta yatsugunna yace jawahir.
Zumbur tatashi zaune hawaye na fita daga idanunta bakinta yana rawa tace Faruk kabar wajen nan kawuce katafi kar taganka.
Da mamaki yace wai jawahir wacece zata ganni? Kukan me kike haka? Wai me yake faruwa da rayuwarki?
Cikin kuka tace Faruk kaje kawai,
Faruk yace babu inda zanje jawahir sai kin fad'a min abinda yake faruwa.
Juyawa tayi cikin sauri tafara waige waige sai kuma chan tamik'e tsaye dakyar tana kyangasa k'afa tanufi wajen da dutsin nan yake ajiye tana zuwa tad'agashi dakyar tajawo d'an k'aramin littafinta jinginewa tayi jikin bango cikin sauri Barr Faruk yataso yazo inda take a tsaye yace lafiya jawahir?
Kallonshi tayi da idanuwanta da suka fara lunshewa cikin jigata tace Barrister ga wannan duk wani bayani da kake nema zaka samu a ciki, katafi.
Amsa yayi yarik'e, yace jawahir yakamata akaiki asibiti ko bakida lafiya.
Girgiza kai tayi tace kaidai katafi.
Barr Faruk har ya bud'e baki zaiyi magana tace dan Allah kar kace komai katafi kawai.
Juyawa yayi cikin sanyin jiki yafita.
Yana fita jawahir tafad'i k'asa a sume.
Tausayinta duk yacika Barr Faruk haka yawuce yatafi cikin sauri dan amsa kiran Dadynshi.
Yana isa a parlour yasamu Daddy yana jiranshi ko zama baiyiba Daddy yace Faruk d'azu Malam ya kirani ya ce yana ta Kiran wayarka bai samuba lafiya dai ko?
Zama yayi sannan yace Daddy ina tunanin network ne.
Toh shikenan yanzu kaje kashirya kaje Daura ya ce yau yau d'innan yana son ganinka.
Yau kuma Daddy me yake faruwa?
Nima ban saniba Faruk kaidai kaje kashirya inkaje sai kaji dan tun d'azu yake kirana a waya yana tambayata ka tafo.
Mik'ewa Barr Faruk yayi yace shikenan Daddy bari inje inyi wanka inyi sallar la'asar sai intafi.
Daddy yace toh shikenan haka yakamata.
Har yagama shiri yana tunanin dalilin kiran gaugawa da kakan nashi yakeyi mashi koda zai tafi Daddy tsaraba yabashi sosai yace yakaima Mahaifin nashi, bayan ya yi sallama da iyayenshi yakama hanyar Daura gudu yake sosai.
Bayan tafiyar Barr Faruk da minti talatin aka kira Alhaji Mahadi shugaban prison a waya yana yin picking daga chan 'bangaren akace masu kula da bincike ne.
Alhaji Mahadi yace toh Lafiya dai ko?
"Eh toh kana da labarin mutuwar babban d'an kasuwar nan Alhaji Saidu Nepa?
Da mamaki Alhaji Mahadi yace banda labari yaushe yarasu?
Daga chan 6angaren akace baifi awa d'aya da rasuwa ba shine muke bincike akan mutuwarshi mun tsinci hoto irin Wanda aka kashe su Alhaji Saminu shine mukeso muji shin wannan yarinyar jawahir tana prison d'innan?
Eh Eh tana nan a rufe,,,,cewar Alhaji Mahadi.
Daga chan 'bangaren akace babu inda taje yau? Ba aje da ita ko kotu ko asibiti ba?
Shuru yayi sai chan yace am a'a d'azu Barr Faruk ya fita da ita ya yi bincike akan aikinshi.
Wanene kuma Barr Faruk?
Lauyanta da yake kareta ammah sun dawo tun d'azu.
Shikenan zamu nemeshi.
Cikin 50 minutes Barr Faruk ya isa daura saboda gudun da yake da motar yana isa a k'ofar gidan kakannin nashi yaga malam zaune yana ba wasu darasi dan haka yatsugunna yagaishesu bayan sun gaisa yashiga cikin gida yasamu yar tsohuwar tashi suka gaisa nan takawo mashi hura damamma yana sha suna hira yana janta ahaka har yagama yace bari yaje yaga ko malam ya gama dan lokacin biyar da rabi tayi tace Eh gaskiya zuwa yanzu ya gama.
Yana fita yasameshi zaune yana jan carbi daga gefen d'an buzunshi yazauna suka sake gaisawa yatambayeshi mutanen gida yace kowa yana lafiya,
Malam yace ai mahaifinka ya kirani d'azu ya ce wai iyayen yarinyar da zaka aura sunce ad'aga sa ranar sai zuwa jibi ayi baikon.
Faruk yana shirin yin magana nan wayarshi tafara ringing fiddowa yayi yai picking tare da yin sallama.
Daga chan 6angaren akace Barr Faruk muna buk'atar ganinka a yanzu dan samun cikakkun bayanai daga wajenka saboda munsan kana da labari awa biyu da suka wuce ankashe babban dan kasuwa Alhaji Saidu nepa, da mamaki yake saurarenshi yace ankashe shi kuma?
Eh saisa mukeso muji daga gareka dan antabbatar mana ka fita da jawahir daga prison yau.
Cikin sanyin jiki yace ammah koda nafita da ita ai babu inda taje hotel kawai muka safka.
Barrister koma menene inkazo sai muyi magana dan yanzu haka muna a cikin bincike.
Barr Faruk yace shikenan sai na shigo, yana gama wayar kallon malam yayi da yatsareshi da idanu yace wacece jawahir kuma?
Barr Faruk yace wata baiwar Allah ce da nake tsaya mawa a shara'arta shine wai suke zarginta da kisa.
Jinjina kai Malam yayi yace kusan abinda yasa nace kazo kenan akan yawan mugun mafarkin da nake akanka.
Mafarkina kuma? Yafad'a cike da mamaki.
Eh mafarkinka kuma duk akan wannan aikin naka ne, Faruk ya kamata ka ajiyeshi dan ina tsoron wani abu yafaru da rayuwarka.
Gabanshi wani irin mummunan fad'uwa yayi yace ajiye aiki kuma malam? Kar kayi duba da abinda kagani acikin mafarki dan duk wannan sharrin mafarki ne.
Eh Faruk zai iya zama haka ammah ni ina tsoron abinda zai faru da rayuwarka ko ga wani naka......
_Shin wane irin mafarkine Malam yayi da har yakeso Barr Faruk ya ajiye aikinshi?_
_Shin Barr Faruk yana da yadda zaiyi yakare jawahir akan zargin kisa da akeyi mata?_
_Anya kuwa ba jawahir bace take kisan nan ba? inko ba ita bace toh wanene?_
_Wane dalili ne yasa aka d'aga baikon Barr Faruk kodai akwai wata k'ullaliya a k'asa da akeson yi?_
_Shin minene cikin wannan littafin (diary) da jawahir taba Barr Faruk?_
_Tofa laifin dad'i k'arewa, wad'annan amsoshin naku duk suna acikin cigaban *FANSAR RAI* kar kumance har yanzu bamuyi komai ba acikin labarin d'and'ana labarin kawai mukayi_
_Ga duk me buk'atar cigaba da karantawa cikin aminci zai biya d'ari biyu (200) dan kasancewa da SIS NERJA'ART_
_Akowane lokaci muna maraba da masoya nagaskiya Sis Nerja'art takuce_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-Nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
PART TWO
_~GORON SALLAH~_
*PAGE 1*
Kwance yake saman makeken gadonshi yad'age kanshi sama yana kallon Ceiling tare da lumshe idanunshi kamar me bacci ammah azahiri tunani yake rayuwar jawahir kawai yake tunani akan irin gwagwarmayar da tasha, tambayar kanshi yafara yi daman ashe tana da aure? Toh ina mijin nata? Meyasa bai ta'ba ganinshi ya je wajenta ba??tambayoyin da suka dinga mashi yawo kenan a k'walwa saidai me a gefe d'aya Allah Allah yake yi gari ya ida wayewa yayi wanka yatafi gidan kaso na mata dan yagana da ita dan ya fi so ya ida samun full details kafin yafara aikinshi,,,, yana cikin wannan tunani bacci 'barawo yasace shi.
Wajen k'arfe bakwai kiran da yashigo wayarshi ne yatashe shi dakyar yabud'e idanunshi da sukayi mashi nauyi saboda rashin samun isashen bacci, d'auko wayar yayi yaduba yana ganin me kiranshi sai ma yamaida ta silent sannan yamik'e yashiga wanka.
Bayan ya fito ya shirya cikin shirinshi na tafiya aiki jikkar laptop d'inshi da wayoyinshi yad'auko yafito parlor daidai da Momcy ta shigo parlorn d'auke da plask tsayawa tayi tana kallonshi.
Murmishi Faruk yasakar mata tare da gaisheta.
Amsawa tayi sannan tace Son ka dai san babu inda zakaje sai ka yi breakfast ko?
'Bata fuska yayi yace Momcy bana jin yunwa.
Batace mashi komai ba tawuce dining area.
Ajiye kayan da suke hannunshi yayi yabi bayanta yana zuwa yaja kujera yazauna, fara serving d'inshi tayi sannan tace d'azu Nasiba ta kirani a waya ta ce tana ta kiran wayarka baka d'auka ba.
Yi yayi kamar baiji ba yafara breakfast d'inshi.
Kallonshi Momcy tayi tace Faruk magana fa nake maka ka min shuru.
'Dagowa yayi yakalleta yasakar mata murmushi sannan yace momcy time d'in bacci nake kuma ko da natashi ban bi ta kan wayarba saboda naga zanyi late ban tafi aiki ba.
Momcy kallonshi kawai tayi tawuce tatafi cikin ranta tana mamakin halin d'an nata.
Sama sama yayi breakfast d'in yamik'e yad'auki kayanshi yaficce yabar gidan.
Yana cikin mota yana tuk'inshi a nutse nan wayarshi tafara ringing kallon wayar yayi ganin sunan da yabayyana a jikin screen d'in wayar yasa yai saurin yin picking tare da yin sallama,,, yanayin yadda yake maganar kawai zaka gani kagane cewa akan wajen aiki ne suke tattaunawa sun dad'e suna wayar kafin daga bisani suyi sallama.
Suna gama wayar d'an guntun tsaki yaja tare da canza hanya yanufi wajen aikinsu.
Yana isa yai parking a daidai inda yasaba yin parking yad'auko bakin space d'inshi yadad'e fuskarshi sannan yafito daga cikin motar yazagaya yabud'e mazaunin me zaman banza yad'auko jakkar laptop d'inshi.
Tafiya yake cikin takunshi me burgewa duk inda yagifta sai mutane sun mashi barka da safiya saidai kawai yad'aga masu hannu, wad'anda suka yi mashi farin sani ne kawai zasuce daman haka yake dan Barr Faruk ba mutum bane me yawan son hayani.
Yana zaune a office d'inshi akayi mashi knocking izini yabada ashigo nan aka turo k'ofa.
'Daga kai yayi yakalli me shigowa sai kuma yamaida kallonshi ga system d'in shi.
Sacratery takowa yayi ya iso wajen Barr Faruk daga gaban table d'inshi yatsaya yace Barrister barka da aiki.
Batare da ya d'agoba yace yauwa barka.
File d'in da yake hannunshi yamik'a mashi yace gashi oga yace akawo maka.
Ohk ajiye nan.
Ajiyewa yayi saman table d'in yace atashi lafiya sannan yajuya yafita.
Barr Faruk d'auko file d'in yayi yabud'e yafara dubawa chan sai yamik'e tare da d'aukar file d'in da key d'in motarshi yafita.
Saida yafara biyawa a office d'in ogansu suka tattauna sannan yatafi.
Yana barin nan direct gidan yari yawuce yana isa kamar yadda yasaba office d'in abokin nashi yafara safka bayan sun gaisa ne yanuna yanaso yaje yagana da jawahir.
Alhaji Nasibi yanuna ba matsala nan yakira wani ma'aikacin gidan kamar yadda yasaba yahad'a shi da Barr Faruk suka je.
Suna zuwa suka sameta zaune ta had'e kai da gwiwa, daga bakin k'ofa ma'aikacin yatsaya inda shi kuma Barr Faruk yashiga ciki ko kad'an bata motsa ba daga inda take da alama kamar bata ma san da shigowarshi ba.
Barr Faruk matsawa yayi yatsugunna a gabanta tare da kiran sunanta ahankali.
Bud'e rinannun idanuwanta tayi tare da d'ago kanta tasafke idanunta a fuskarshi inda fuskarta take a d'aure.
Cike da jin tausayinta yake binta da kallo inda itama take kallonshi babu ko k'yaftawa.
Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir insha Allahu zan taimaka maki zan wanke ki daga zargin da akeyi maki.
Lokaci guda tamik'e tsaye tare da sakar mashi murmushi sannan tawuce tafara taku d'aya biyu sai taja tatsaya batare da ta juyo ta kalleshi ba cikin dashewar murya tace zargi kuma? Wanene yafad'a maka zargina akeyi? Duk abinda kaji ance na aikata to dagaske ne.
Mik'ewa yayi daga inda yake yatsaya yace idan har abinda kika rubuta a kan labarinki gaskiya ne toh tabbas zanyi k'ok'ari wajen wanke ki.
Murmushi tayi a karo na biyu tare da sake jefa mashi tambaya tace labarina kuma?
'Dan matsowa yayi kad'an yace Eh saidai inaso insan k'arshen shi dan samun cikakkar hujja.
Shuru tayi kamar bataji abinda yaceba ganin haka yasa Barr Faruk yace shin ina Umar?
Lokaci guda tajuyo takalleshi cikin sauri tatako ta iso wajen da yake tsaye tare da cacimo wuyar rigarshi muryarta tana rawa tace wanene yafad'a maka shi? Ina kasan yaya umar d'ina?,, tafad'a tare da fashewa da kuka.
K'wacewa yayi daga rik'on da tayi mashi yad'an ja baya kad'an yace ban san umar ba saidai na karanta acikin labarin da kika rubuta.
Hannu tamik'a mashi muryarta tana rawa tace ina diary na.
Cikin nuna rashin damuwa yace yana wajena zanyi wani aiki ne akanshi ammah jawahir ya kamata kisanar da ni ina umar da su Abba shin suna raye?
Sulalewa tayi a lokaci guda tazauna k'asa tare da rushewa da kuka tace nima ban saniba bansan me yasa babu wani wanda yazo gareniba meyasa zasuyi min haka?
Takowa yayi yamatso wajen da take yace kenan suna a raye jawahir?
Wani irin kallo tayi mashi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa.
Ganin haka yasa yacigaba da cewa jawahir dole sai kin daure kin sanar da ni komai domin ta haka ne zamu samu mafita wad'annan mutanen da suka kashe maki iyaye, sannan ita wannan aljanar ta wace hanya takebi tana d'aukar maki fansa akansu, kuma idan har itace take yin kisan ai inaga bai dace ace ankama ki akan laifin da bake kika aikata ba ammah me yasa tun lokacin da akayi abun baki sanar da hukuma ba? Inaga da ace kin sanar da......wata irin k'ara jawahir tayi tare da toshe kunnuwanta cikin d'aga murya tace ya isa haka barrister! ya isaaa!!!
Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanunta tace taya kake tunanin hukuma zata taimaka min bayan Ammina ita kanta ta je ma hukuma ammah babu wanda yakulata bare har yataimaka mata, wannan dalilin ne yasa nad'auki fansa dakaina ban damu da abinda zai faru da niba bana buk'atar cigaba da rayuwata ina so akasheni saidai kafin nan nafiso incika burina a rayuwa sai na ida kashe wad'anda suke da hannu a mutuwar iyayena daga nan nima zanyi farin ciki sosai idan na mutu dan daman mutuwar itace nafi buk'ata,,,,, juyawa tayi takalli gefe guda sannan tace rayuwata batada sauran amfani ban ta'ba bak'in ciki ba akan zaman da nayi a nan na tsawon wata goma zanyi farin ciki ace daga nan gidan sai k'abarina zan shiga.....
Katseta Barr Faruk yayi yace jawahir wannan wace irin magana ce kikeyi kidaina cewa haka insha Allahu zaki rayu ni zan taimaka maki kifita daga gidan nan saidai ta ina zan fara bi, shin ya za'ayi in iya sanar da kotu cewa aljanah ce take wannan kisan?
"Wannan ba gaskiya bane nice nan nayi kisan Barrister kar kasaka kanka acikin lamurra na domin gudun kar kajefa rayuwarka acikin had'ari, duk wanda yanemi yajawo jikinshi agareni yana shiga matsala yakamata kafahimci hakan.
Kallonta yake gabad'aya ta hargitse yace ban damu da wannan ba jawahir kawai dai akwai wasu tambayoyi da nakeso inyi maki shin ina lauyan mahaifinki wanene shi? Sannan dagaske kina da hannu acikin mutuwar Alhaji....
Bata bari yak'arasaba takatseshi tace ya isa haka barrister na fad'a maka babu abinda zaka samu daga gareni wannan duk ba gaskiya bane,,,, tana fad'in haka tamik'e taje chan wajen 'yar k'aramar tagar nan da tasaba tsayawa wajenta tatsaya tajuya mashi baya ahankali tace wannan duk shirina ne ya kamata katashi katafi.
Idanu Faruk yazuba mata yana kallonta har ya bud'e baki zaiyi magana tatari numfashinshi tace banason jin komai daga gareka dan Allah kabarni haka bansan ya zanyi ba tambayoyinka sun min yawa!.
Mik'ewa Barr Faruk yayi yace shikenan jawahir zan tafi ammah inaso kisani zan dawo agareki bamuda isashen lokaci ya kamata kisan haka sai anjima,,,, yana fad'in haka yajuya zai tafi sai jin muryarta yayi ta ce katabbatar ka maido min diary d'ina.
'Dan guntun murmushi yayi yajuya yafita.
yana fita yajiyota ta fashe da kuka d'an ja yayi yatsaya sai kuma chan yawuce yatafi.
Saida yabiya ta office d'in Alhaji Mahadi sukayi sallama sannan yawuce yatafi yana a mota DPO yakira shi a waya yace suna son ganinshi yanzu, amsa masu yayi da toh gashinan zuwa sannan yakashe wayar.
Lokacin da ya isa station d'in direct office d'in DPO yawuce lokacin yana ciki suna ganawa da wani dan haka yajira sugama.
Kusan minti shidda sai ga mutumin ya fito juyowar da Barr Faruk zaiyi nan sukayi ido hud'u da Alhaji Mansur wani shu'umin murmushi Alhaji Mansur yasakar mashi tare da cewa Barr Faruk barka da rana.
Kallo d'aya Barr Faruk yayi mashi batare da ya tanka shi ba yawuce zai shige sai jiyo muryarshi yayi daga baya yana cewa har yanzu kana da damar da zaka mallaki Nasiba but in kana da buk'atar hakan.
Ja yayi yatsaya har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa yawuce yashige.
Dariya Alhaji Mansur yayi yace nasan dai zaka amince da hakan.
Yana shiga hannu yamik'a ma DPO suka