Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   46 / 74

135K to 138K   out of 220.3K words

cike da k'osawa da maganar Junaid kamar ba zai ce komai ba sai kuma chan yad'ago yakalleshi yace a yanzu ba kowa bane zai iya fahimta ammah inaso kasani da sannu zan wanke jawahir daga zargin da akeyi mata.
'Yar dariya Barr Junaid yayi yace ka jika da wata irin magana da sannu dai asirinta zai tonu, wallahi Faruk ina baka shawara kafita daga harkar case d'in yarinyar nan dan kar kaji kunya..
Katseshi yayi ta hanyar cewa Junaid idan ka gama abinda yakawoka zaka iya tafiya domin ina aiki me muhimmanci.
Mik'ewa tsaye junaid yayi yace yi hak'uri oga yanzun nan ko, atashi lafiya.
'Daga kai kawai Faruk yayi batare da ya ce komai ba yajawo syatem d'inshi ganin haka yasa Junaid yawuce yafita yabar office d'in.



Wajen k'arfe biyar Faruk yagama shiri yafito zai fita a parlor yacikaro da Momcy tana zaune ta buga uban tagumi, zuwa yayi daga gefenta yazauna tare da rik'o mata hannu.
'Dago kai tayi takalleshi saida tasafke ajiyar zuciya sannan tace Faruk.
Marairaicewa yayi yace dan Allah Momcy kidaina tagumi.
Murmushi tayi tace ai dole inyi Faruk d'azu Hajiya Maijidda takirani tana min maganar Nasiba tana chan ta tashi hankalinta sosai, Faruk ya kamata kagane cewa Nasiba tana sonka sosai koma menene bata cancanci irin haka daga gareka ba.
Kwantar da kanshi yayi saman kafad'arta yace Momcy laifin mahaifinta ne ni banda matsala ko da a yanzu zai janye k'udurinshi ni kuma zan auri Nasiba.
Girgiza kai tayi tace Faruk ka fiye taurin kai watau kana nufin kai bazaka iya janye naka ba.
'Dago kanshi yayi yakalleta cikin sanyin jiki yace a'a Mom nawa bazai ta'ba janyuwa ba idan har nace zan janye toh tabbas banyi adalci ba domin Jawahir tana buk'atar taimako taya za'a zalunci mutum sannan akamashi a rufe, ta rasa me tsaya mata yak'wato mata hak'inta na tabbata daga inda najanye za'a iya kasheta inko nayi haka ban kasance me adalci ba akan aikina.
Cike da tausayin d'an nata take kallonshi tace hakane Faruk Allah ubangii yataimaka insha Allahu zaka auri Nasiba dayardar Allah ita rabonka ce.
Cikin jin dad'in kalaman mahaifiyar tashi yace nagode sosai Momcy.
Shafa kanshi tayi tace bakomai Babana.
Mik'ewa yayi yace Momcy bari inje akwai wani aiki da zanyi yanzu.
Toh shikenan Allah ubangiji yataimaka sai ka dawo.
Ameen Momcy.



Wajen k'arfe biyar da rabi ya isa gidan kaso direct office d'in Alhaji Mahadi yafara zuwa kamar yadda yasaba bayan sun gaisa ne mahadi yakalleshi yace wai Faruk minene yahad'aka da DPO ne?
Ta'be baki Faruk yayi yace me fa? Wani abu yace maka ya faru?
A'a ba wai haka ba.
'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace kabarni da shi kawai yanzu dai bari inje inga jawahir wallahi yarinyar nan ta k'i tabani had'in kai yadda yakamata.
Jinjina kai Alhaji Mahadi yayi yace kama gode ma Allah da bata shek'aka lahira ba.
Uhm kaidai kasani malam ni bari intashi inje.
Dariya Alhaji Mahadi yayi yace toh shikenan ba damuwa abokina bari insa arakaka.


Lokacin da suka isa tsaye yasameta wajen 'yar k'aramar tagar nan idanunta suna ga d'an hasken da yake shigowa tsaye yayi daga bakin k'ofar yana kallonta inda ma'aikacin gidan yake tsaye a waje yana jiranshi takowa yayi yamatso kusa da ita bai ankara ba sai jiyo muryarta yayi ta ce shin zaka taimaka min in cika burina?
Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir ya kamata kifahimta lokaci yana k'ure mana kidaure ki ida bani hujjojin da zasu taimaka wajen ganin na tseratar da ke daga gidan nan.
Cikin muryar kuka tace meyasa kafi damuwa da fitata akan d'aukar fansar abinda akayi min? Wa yafad'a maka na damu da incigaba da rayuwa? Nidai abu d'aya nakeso shine inga bayan duk wanda yarabani da iyayena.
Cikin sanyin jiki yace jawahir nasan haka kifahimceni idan har kika ban dama nayi aikina yadda yadace toh dole ne ingurfanar da su agaban hukuma ni zan taimaka maki da hakan.
Ahankali tace hukuma kuma? Ni bana buk'atar hukuma a ciki nafiso kowane d'a yad'and'ani irin rad'ad'in da naji a lokacin da narasa iyayena, nasan bazaka ta'ba taimaka min ba ammah ni zanyi komai dakaina.
Tsaye Barr Faruk yayi yana kallonta cikin ranshi yace meyasa jawahir take haka ko har yanzu bata yarda dani ba?
Juyowa tayi ahankali takalleshi idanun nan nata sunyi jajir kamar garwashin wuta duk sun k'ank'ance d'an guntun murmushi tayi tace kar kadamu ahakan ma nagode.
Amm jawahir ya kamata kifahimci kwana goma sha biyar fa yarage mana lokaci bazai ishemu ba kidaure muyi abinda yadace.
Dafe kanta tayi da hannu d'aya ahankali tace wannan shine abinda yadace Barrister a gobe zan kasance cikin farin ciki saboda akwai aikin da zan aiwatar wanda shine zai rage min rad'ad'in abinda nakeji.
Tun kan tarufe baki yace jawahir kisa zakiyi?
Takawa tayi dak'yar tana k'yangashi taje tazauna tare da jingine kai da bango sannan tace abinda yadace da rayuwata zanyi.
Matsowa yayi kusa da inda take zaune yatsaya yace jawahir na rok'eki ki taimaka kiban k'wak'warar hujja ni zan taimaka maki akan dukkan abinda yadace nayi maki wannan alk'awaline duk wanda yake da hannu akan mutuwar mahaifinki bazan ta'ba barinshi ba koma wanene shi.
Ahankali tamaimaita kalmar da yace koma wanene shi? sannan tad'anyi guntun murmushi tace kana nufin koda ace kana da dangantaka da shi idan har kagane yana da hannu a ciki zaka taimaka min?
Shuru Barr Faruk yayi sai chan yace ban damu da kusanci na da shi ba domin ina akan aikina ne zanyi k'ok'arin haka kiyarda da ni jawahir.
Hawaye ne suka gangaro mata tace bana so kajefa kanka acikin had'ari Barrister domin rayuwata babu komai a cikinta sai had'ari idan har kacigaba da bibiyata ahaka komai zai iya faruwa da kai wannan dalilin ne yasa nakeso kacire hannunka a ciki sannan saboda haka ne nakasa fad'a maka komai akan rayuwata.
Kidaina cewa haka jawahir ban damu da duk yanayin da zan shiga ba indai ina akan aikina nidai kawai taimako d'aya nakeso kiyi min.
Idanu tazuba mashi batare da tayi magana ba ganin haka yasa yace shin ina labarin su umar da d'an uwan mahaifinki? Ko zaki fad'a min inda suke saboda ina da tarin tambayoyi akansu sannan ya zama dole Abbanku yagurfana a gaban kotu.
Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanunta d'aya bayan d'aya chan tafara shashek'ar kuka lokaci guda tafashe da kuka tace bansan me zan ce maka ba barrister bansan ya akayi haka ba...hamma ce tafara yi chan kuma tayi murmushi cikin murya me kama da ta masu jin bacci tace koma menene zaka sani zanyi k'ok'arin haka ammah ya kamata yanzu katafi sai mun had'u a karo na gaba zan sanar da kai komai.
Sai a lokacin yalura da yadda gari yafara duhu yace kar kidamu jawahir ba wani abu bane zan iya zama a nan har lokacin da naso in fita.
'Dan guntun murmushi tayi tace saboda shugaban gidan ya kasance abokinka?
Da mamaki yake kallonta yace wanene yafad'a maki haka?
Janye idanunta tayi daga kallonshi.
Mik'ewa yayi yace zan tafi gobe dasafe zan dawo agareki.
Saurin cewa tayi a'a kar kadawo a lokacin saboda ina da aiki me muhimmacu da zanyi da k'arfe goma.
Aiki kuma? Wai wane irin aiki ne haka kike magana akai ban fahimceki ba?,, yafad'a fuskarshi d'auke da mamaki.
Cikin nuna rashin damuwa tace ba lallai ne kafahimci hakan ba katafi kawai.
Ta'be baki yayi yace shikenan zan tafi ammah goben dai zan dawo yakamata ki ida sanar da ni komai akanki.
A'a bazai yuwu ba saidai zuwa jibi.
Kallonta Barrister Faruk yayi nad'an lokaci sannan yace kin amince jibin zaki ida sanar da ni komai akan rayuwarki?
Saurin juya baya tayi cikin rawar murya tace ban saniba ko hakan zai yuwuba ya kamata kakula akan haka zaka iya jefa rayuwarka cikin matsala kafahimci hakan.
Kinga jawahir yanzu ba lokacin jayayya bane koma menene kishirya lokacin da duk nadawo zaki ida sanar da ni komai lokaci ya k'ure mana ammah kin kasa gane hakan, ni zan tafi.
Ko juyowa batayi takalleshi ba bare yasa ran zatayi mashi magana dan haka yawuce yayi tafiyarshi.

Tana jin an rufe d'akin hawaye suka gangaro mata tayi saurin runtse idanunta wata irin mahaukaciyar dariya da taji ne yasa tayi saurin bud'e idanun.
A saman iska taga matar zaune cikin mummunan siffa fuskarta fari tas babu alamun jini bakinta duk ya tsatstsage hak'ora sunyo waje, idanuwanta a d'inke suke da farin zare babu alamun k'waya a ciki gashin kan nan nata ya yi tsaitsaye saman iska sai juyawa yake, dariya tacigaba da yi cikin sauri jawahir tad'an ja baya tana cigaba da kallonta muryarta tana rawa tace me yamaidoki wajena?
Muryar matar taji kamar tartsatsin tsawa ta ce jawahir ya zama dole kiyi nadamar maganar da kika fad'a min idan dai har kina son ki tseratar da rayuwarki sannan baki isa kisanar da barrister komai ba.
Cikin d'aga murya tace bazan ta'ba nadama ba ban damuba ink'arashe rayuwata a nan cikin gidan nan daman rayuwar tawa batada sauran amfani a duk lokacin da kikaso zaki iya kasheni.
Matsowa matar tayi kusa da ita tana me cigaba da dariya sai kuma chan tatsagaita dariyar da take tace ke matsalarki d'aya kin cika taurin kai duk wahalar da nake baki ammah hakan ya kasa sawa ki aje makaman da suke saman kanki koma menene dai shikenan nasan dai kina sane da aikin da yake gabanmu gobe.
Wani irin kallo jawahir tayi mata tare da jan tsaki tajuya zata tafi, wani farin abu ne yafito daga cikin idanun matar jawahir bata ankara ba sai ji tayi an fizgeta da k'arfi anbuga da bango nan tasulale tafad'i a sume, matar na ganin haka tabushe da wata irin dariya nan ta isa wajen da jawahir take kwance a sume, wani irin abu tadinga karantawa wanda ba kowane zai gane abinda take cewa ba saboda yaren da take, wata 'yar kwalba ce tabayyana a hannunta k'arama tabud'e ta takarkata a wajen fuskar jawahir sai ga wani abu kamar jini yana zubowa har saida yak'are sannan tagirgiza ta'bace....










_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:10 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 5*

Sai bayan sallar isha'i sannan Barr Faruk yakoma gida saida sukayi dinner da iyayenshi sannan yawuce d'akin shi yayi wanka yai shirin bacci yana hawa saman gadonshi zai kwanta nan haske yad'auke gabad'aya duhu yabayyana a d'akin, tsaki yaja tare da mik'a hannunshi saman bedside zai d'auko wayarshi sai ji yayi wayam babu komai lalubawa yashigaa yi cike da mamaki ganin a sama ya ajiyeta ammah bai gantaba, ahankali yaji ana bud'e mashi k'ofar d'aki nan yai zaune yana jira yaji wanene yashigo, tafiya yafara ji anayi a tsakiyar d'akin, cikin rashin tsoro yace wanene? Momcy?.
Shuru yaji ba amsa sai ma k'arar tafiyar da aka cigaba da yi cikin d'aga murya yace koma wanene yayi magana man?
Nan ma shuru sai jin wata irin k'ara yayi shuuuuuu chan kuma yaji an datse d'akin daidai lokacin haske yadawo.
Mamaki yakamashi sosai yana juyawa yaga wayarshi ajiye inda ya aje ammah kuma duk ya laluba d'azu bai ji taba, ahankali yace watau wani yad'aukar min waya shine yanzu yamaido, mik'ewa yayi cikin sauri yafita yabar d'akin duddubawa yadinga yi ko zai ga wani ammah baiga kowaba har yasafko parlor su Dad ne yagani zaune shi da Mom suna ganinshi sukace ya dai Faruk lafiya kake ta sauri haka?
Murmushi yayi yatsaya daga saman step yace bakomai Dad ku ne kuka shigo d'akina?
Cike da mamaki sukace mu kuma?
Daman na ji an shigone lokacin da aka d'auke wuta kuma ina ta magana na ji shuru.
Dad kallon Mom yayi itama takalleshi sannan suka maida kallonsu ga Faruk sukace yaushe kuma aka d'auke nepa ba dai yanzu ba?
Da mamaki yake kallonsu yace bakuga an d'auke ba? Yanzu fa aka maidota.
Dad yace a'a Faruk akwai nepa gaskiya ba'a d'aukeba.
Cikin ranshi yace toh ya akayi haka? Me hakan yake nufi,,, ganin yadda iyayen nashi suke kallonshi yasa yai murmushi yace ina ji wutar d'akina ce tad'auke tadawo bari inje inkwanta.
Mom tace toh ammah kace ka ji kamar anshigo d'akin kuma bamuga kowa ya zo ya wuceba.
Cikin nuna rashin damuwa yace ina ji k'ofar ce tayi k'ara bari inje inkwanta sai dasafenku.
Basu kawo komai aransu ba sukace toh shikenan sai dasafe.

Juyawa yayi yakoma d'akin shi cikin ranshi yana tunanin toh kodai aljannu ne suke bibiyarshi? Addu'a yayi yahau gadonshi yakwanta bai kawo komai a ranshi ba, bai dad'e da kwanciya ba bacci yai awon gaba da shi.





Da asuba saida Dad yazo yatasheshi sannan yasamu yaje masallaci yasamu sallah cikin lokaci dan haka koda yadawo baccinshi yakoma.....

Wajen k'arfe tara yafarka daga baccin da yake a firgice yatashi saboda mummunan mafarkin da yayi dafe kai yayi tare da furta Alhamdulillah da yaga mafarki ne yake ba gaskiya bane dan mafarkin sosai yatsorata shi.
"Wata k'atuwar macijiya ce yagani tana binshi da gudu shi kuma yana ta gudu da dukkan k'arfinshi dan yasamu yatsira, a duk lokacin da zai waiga sai ya ga tana gab da taddoshi ga bakinta tana bud'ewa alamun zatayi mashi tsartuwa, k'ara gudu yake yana neman mafaka ahaka har ya iso wajen wani k'aton gida, wani irin dad'i yaji lokacin da akaron farko yayi tozali da gidan dan haka yana isa baiyi wata wata ba yashiga, daidai da ya shiga k'ofar gidan tamaida kanta tarufe sai gani yayi gidan ya koma mashi wani k'aton fili duk itace ne kawai a ciki, tsaye yayi yana bin filin da kallo chan yafara jiyo kuka ahankali yana tashi, waiwayawa yadinga yi yanaso yajiyo inda yakejin sautin kukan wata 'yar siririyar hanya ce yagani dan haka yabita yana tafiya chan bayan wani icce yahango mutum zaune, cikin sauri ya isa wajen sai ganin jawahir yayi tana ganinshi tabushe da dariya tare da mik'ewa tsaye nan take tayi girgiza sai komawa tayi wannan k'atuwar macijiyar.
Saurin ja da baya yafara kafin daga bisani yajuya yacigaba da gudu nan ko macijiyar tacigaba da binshi, daga nesa da shi yahango wasu d'ungozon mutane tsaye wani irin farin ciki yaji nan yai saurin isa wajensu yana cewa kutaimaka min ammah babu wanda yakalleshi har yashiga tsakiyarsu lokaci guda yaja yatsaya lokacin da yayi tozali da mutum kwance a k'asa alamun ya mutu murya yajiyo daga bayanshi an bushe da dariya wadda takusan rikita mashi dodon kunne saida yai saurin toshe kunnuwanshi da hannuwanshi har saida dariyar talafa sannan yajanye, kunnuwanshi ne suka jiyo ana cewa wannan shine aikin da zan yi a yau d'in nan!
saurin juyawa yayi sai baiga kowa ba dan haka ya ida isa wajen mutumin da yake kwance a k'asa har ya kai hannu zai janye abinda aka rufe mashi fuska da shi yaji wata irin murya ta yi mashi magana da k'arfi me kama da gargad'i ance kar kakuskura abud'e!!!! daidai nan yafarka daga baccin.

Sosai mafarkin yatsorata shi saidai abun ya tsaya mashi rai sosai wai jawahir ce take bibiyarshi tana son taga bayanshi ammah kuma ba wannan ba toh shi mutumin da yagani kwance wanene shi? Tunowa yayi da muryar da take dariya tace wannan shine aikin da zanyi yau,,, sai kuma jawahir tafad'o mashi a rai jiya da take fad'a mashi gobe akwai aikin da zatayi, ahankali yace toh me hakan yake nufi? Kenan tana nufin kisa zatayi?
Ture blanket d'in da yayi rufa da shi yayi cikin sauri yamik'e yafad'a toilet.
Bayan ya yo wanka a gurguje yashirya ko breakfast bai tsayaba ganin momcy bata fitoba yasa yaficce yabar gidan.
Motarshi yafizga cikin k'ank'anin lokaci ya isa gidan kaso, bai biya ta wajen Alhaji Mahadi ba shugaban gidan saidai yakirashi a waya yashaida mashi zuwanshi da son ganin jawahir da yake cikin sauri dan haka ya amince mashi yaturo wani ma'aikaci sukaje tare.

Suna isa cikin sauri yashiga d'akin kwance yasameta gashin nan duk ya baje mata fuska da alama bacci take, ajiyar zuciya yasafke cikin ranshi yace wannan duk yaye yayen mafarki ne, juyawa yayi zai tafi sai kuma yaja yatsaya ahankali yajuyo tare da tsugunnawa a gabanta wani farin abu yagani kamar Alli anyi rubutu da shi k'ananu a kusa da inda take kwance k'ura idanunshi yayi akan rubutun sai gani yayi ansa sunan Alhaji Tanimu Nepa 10:30am, gaban Faruk saida yafad'i a fili yasake maimaita sunan sannan yace me zatayi da sunanshi ko shima ta kasheshi?
Ammah kuma me lokacin yake nufi 10:30am, tsugunne yayi wajen yana tunani chan yatuno da yashiga mota ya ji a redio ana sanarwa a yau babban d'an kasuwa Alhaji Tanimu Nepa zai zo gaisuwar rasuwar d'an uwanshi da k'arfe goma jirginshi zai safka.
Saurin girgiza kai yayi yace a'a bai dace ba hakan, kiran sunan jawahir yafara yi ammah shuru bata ko motsa ba batada banbanci da matacce, ganin haka yasa yaduba agogon hannunshi sai gani yayi k'arfe goma da minti biyar, ahankali yace ya kamata inyi wani abu a yanzun nan, mik'ewa yayi cikin sauri yawuce yafita ko bankwana bai tsaya yi da megadi ba kamar yadda yasaba.


Motarshi yashiga yajata dagudu yabar gidan yarin, gudu yake sosai cike da tashin hankali yana cewa meyasa haka jawahir? Meyasa bazaki bari hukuma tad'auki mataki ba idan har yana da hannu a cikin mutuwar iyayenki, bazan bari kikasheshi ba yazama dole intseratar da shi dan ina son samun bayanai daga wajenshi, gudu yake sosai kamar wanda zai bar garin daidai da round d'in da zai sadashi da airport aka had'a wani irin go slow da yai sanadiyar tsaida duk wani abun hawa da yake wajen.
Hankalin Barr Faruk ba k'aramin tashi yayiba tsaki kawai yakeja yana duba agogo ji yake kamar yafito yabar motar yataka k'asa ya ida isa da k'afafunshi.




K'arfe goma daidai lokacin jirgin sama yasafka wanda ya iso daga k'asar Europe a filin jirgi mutane ne suke fitowa daga cikin shi chan sai ga Alhaji Tanimu ya fito cikin sauri driver d'inshi yaje ya amshi kayanshi yasaka a mota inda security suka take mashi baya dan yi mashi rakiya zuwa gidanshi kamar yadda yabuk'aci hakan dan

46 / 74