Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   48 / 74

141K to 144K   out of 220.3K words

ka sai da rabonka_


*PAGE 7*

Bayan ya bar gidan yarin tun a mota yakira Barr Bilal a waya yatambayeshi inda zai sameshi yafad'a mashi yana gida dan haka direct yawuce gidan Barr Bilal yana isa yakirashi a waya yafito bayan sun gaisa ne yace Barr Bilal wani taimako ne nake nema a wajenka.

Barr Bilal yace toh Barrister Allah dai yasa ba akan case d'in jawahir bane.
Murmushi yayi sannan yace kaidai ka cika tsoro kuma anyi sa'a akanshi ne.
"Toh fa ka ji irinta nidai gaskiya Barrister kayi hak'uri wallahi ina tsoron case d'in yarinyar chan ban shirya mutuwa yanzu ba".
Dariya Barr Faruk yayi yace toh ai mutuwa tana kan kowa kaga kakwantar da hankalinka yanzu bari muyi maganar da takawo ni.

Barr Bilal cikin sanyin jiki yace toh shikenan oga ai dole abi abinda kakeso.

Jingine jikinshi yayi a motarshi sannan yace Barr Bilal shin ko zaka iya rakani gidan su jawahir? Sannan idan akwai wani abu da kasani agame da 'yan gidansu inaso kasanar da ni.

Shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toh gidansu dai na sanshi saidai a rufe yake a yanzu sannan mutanen gidansu a yadda naji duk sun mutu ko ma ince suna cikin wad'anda takashe.

Da mamaki Barr Faruk yake kallonshi yace dagaske ta kashesu har da Umar?

Cikin rashin fahimtar abinda yake nufi yace wanene kuma shi?

Shuru Barr Faruk yayi cikin ranshi yace Jawahit mi yasa kika aikata wannan kuskuren? Chan kuma yaja numfashi yace shikenan zanje muyi magana da Alk'ali zan san yadda zanyi in samo makullin gidansu muje dan akwai abinda nakeson d'aukowa zuwa gobe.
Toh nidai zan dai rakaka intsaya nesa da gidan ammah babu abinda zaisa inshiga dan inason raina.
Murmushi Barr Faruk yayi yace toh shikenan babu damuwa hakan ma nagode yanzu bari inje inga Alk'ali.
Barr Bilal yace toh Barrister koma me kenan sai kata'boni a waya.
Toh shikenan sai ka ji ni suna yin sallama yashiga motarshi yatafi.


Ya yi niyar zuwa wajen alk'ali sai kuma yayi tunani key d'in wajen DPO kawai zai iya samunshi dan haka daga nan yawuce chan station wajen DPO yai mashi bayanin abinda yakeso, tambayarshi DPO yayi me zaya d'auko a cikin gidan?.
Barr Faruk yace akwai bincike me muhimmanci ne da yakeson yi a cikin gidan.
Wannan ba hujja bace babu abinda zaka samu akan bincikenka kadai tsaya bincikenka akan jawahir.
Murmushi Barr Faruk yayi yace ammah ai ina akan aikina ne kuma aikina ya bani dama zan iya kowane irin bincike a matsayina na lauya.
Jinjina kai DPO yayi yace shikenan idan har aikinka ya baka dama sai kayi yadda kaga ya dace ammah ni bazan bada key d'in gidanba saboda bai dace ashigaba tunda ba kowa a ciki.
Shuru Barr Faruk yayi bai sake cewa komai ba dan ya san DPO ya fad'i hakane dan kawai yana jin haushinshi akan 'yar tsamar da sukayi, daga k'arshe ma yatashi yatafi yana tunanin yadda za'a yi yasamu key d'in gidansu jawahir.

Haka dai yakoma gida har sukayi lunch yana tunanin mafita Momcy ko ta yi mashi tambayoyi ba adadi akan ganin yadda yake ta tunane tunane tun da suka zauna yin lunch saidai yace mata bakomai daga k'arshe yace gajiya ce bacci kawai yakeson yi, yana gamawa tace yatafi yahuta dan haka yatafi part d'inshi a parlor yakwanta yana tunanin yadda zai 'bullo ma lamarin yana a haka bacci yayi awon gaba da shi.


Baifi baccin minti talatin ba yafarka saboda mafarkin da yayi saurin tashi zaune yayi cikin ranshi yana addu'a Allah yasa mafarkin shi yakasance gaskiya kallon agogo yayi yaga k'arfe hud'u ta gota dan haka yatashi yawatsa ruwa sannan yayi sallah yana gamawa yazari key d'in motarshi yaficce yabar gidan.

A karo na biyu yakoma gidan kaso nan yanemi buk'atar sake ganin Jawahir aka amince mashi yana shiga yasameta kwance tana ta bacci nan yatsaya yana tunanin ko yatasheta yatambayeta saidai kuma bayason tashinta, ya yi kusan minti goma a tsaye yana tunanin yadda zaiyi, gefe d'aya kuma yana tunanin mafarkin da yayi cikin ranshi yace wannan ai mafarkine bai zama dole yakasance gaskiya ba jawahir da take nan ciki a ina zata samu key d'in gidansu? Chan kuma yayi wani tunanin dan haka yawuce wajen dutsin nan nacikin d'akin yana dubawa bayanshi da mamaki sai ganin keys yayi guda biyu nan yad'auko mamaki duk ya ida cika shi cikin ranshi yace tabbas yarinyar nan akwai abubuwa masu rikitarwa a tare da ita taya za'a ce tana cikin gidan nan me tsaro ammah a tare da ita akwai wasu abubuwa batare da sanin kowa ba, toh ammah kodai aljanarta take kawo mata? Inko hakane mezaisa bazatayi k'ok'arin fitar da ita daga gidan ba?
Ganin ta motsa ne yasa yakatse tunaninshi yawuce yabar d'akin, k'arar rufe k'ofar da megadi yayi ne yasa tafarka daga baccin da take ahankali tabud'e idanunta tashi tayi zaune tajingine kanta a jikin bango kan kace mi hawaye sun fara wanke mata fuska wanda ita kad'ai tasan dalilin yin haka chan kuma sai tamik'e tanufi wajen 'yar k'aramar tagarnan da haske yake shigo mata ta nan tatsaya wata tsuntsuwa ce guda d'aya take ta shawagi a wajen nan jawahir tazuba mata idanu tana kallonta tana murmushi chan sai ganin tsuntsuwar tayi ta haye saman wani icce dake bayan d'akin ta girgiza ta zama k'aton maciji, tsaye jawahir tayi tana kallonshi nan taga ya tunkaro inda take ahankali tace Ammi.
Yana isowa wajen tagar tayi saurin ja da baya nan macijin yashigo dogo ne sosai dan saida yanannad'e jikinshi saboda tsawon d'akin bazai iya d'aukar ko rabinshi ba ahankali tace Ammi mi kikeso agareni?
Wani irin haske tagani ya fito daga bakin macijin sai gani tayi hasken ya kauraye d'akin lokaci guda macijin yazama siffar wannan tsohuwar, matsowa tayi a dudduk'e tatsaya gefen jawahir cikin shak'ak'ar murya wadda bata fita sosai tace kina ta aikata kuskure a karo na ba adadi jawahir kin cika taurin kai.
Kallon tsohuwar take chan kuma sai ta janye idanunta tace Ammi taya kike tunanin zaki cigaba da samuna cikin ruwan sanyi bayan laifin da kika aikata min?
Bushewa da dariya tsohuwar tayi tace a wajenki ne hakan yakasance laifi ammah ni a wajena ba haka bane.
Cikin d'aga murya tace saboda kin tsaneshi saisa kike ganin haka kinyi amfani da damarki kin rabani da farin cikina alhalin bai........maganar me gadi ce tajiyo yana cewa ke kuma dawa kike surutu haka?
Kallon Ammi tayi da take tsaye tana kallonta sannan tajuya takalli megadi batare da tayi maganaba dan ta san baiga Ammi ba.
Cikin fad'a yace ke baki iya nusuwa kamar yadda sauran sukeyi sai kullum kidinga damun mutane da surutu kar kibari insake jin bakinki.

Har yagama maganar yajuya yatafi jawahir batace mashi komai ba tamaida kallonta ga tsohuwar da take cigaba da kallonta har ta bud'e baki zatayi magana tsohuwar tatari numfashinta tace jawahir taurin kanki ne yasa kike cigaba da zama nan da ace zaki ajiyeshi da ni zan fitar da ke daga nan ammah wanchan barristern yana so yashiga sha'ani na kuma gab nake da inyi maganinshi...
Tun kan tarufe baki jawahir tace shin shima zaki kasheshi ne kamar yadda kika kashe sauran? Wane laifine ya aikata maki?
Bushewa tayi da dariya tace jawahir duk abinda naso shi nake aikatawa.
Cikin fad'a jawahir tace a wannan karon bazan ta'ba bari ki aikata abinda kika so ba.
Cigaba da dariya tsohuwar tayi nan jawahir tawuce takoma tazauna tana kallo tsohuwar ta'bace, tura hannuwanta duka biyun tayi cikin gashin kanta.






Bayan sallar isha'i yana kwance a d'akinshi ya d'age kanshi sama yana kallon ceiling Momcy tashigo d'akin baiji shigowarta ba sai ji yayi ana shafa mashi kai, lumshe idanunshi yayi tare da yin murmushi.
Faruk meyasa kake yawan damun kanka da tunani baka tsoron wani abu yasameka.
Tashi yayi zaune yana cigaba da murmushi yace momcy ba tunani nake ba.
Zama tayi gefenshi tace Faruk ni mahaifiyarka ce nafi kowa sanin halinka na san kana son Nasiba saidai zuciyarka bazata barka ba, naso ace ka yi masu yadda sukeso dan subaka aurenta.
Rik'o hannun mahaifiyar tashi yayi yace momcy kiyi hak'uri indai har Nasiba rabona ce zan sameta kicigaba da tayani da addu'a kawai, cikin sanyin jiki tace shikenan faruk insha Allahu zan cigaba, wata leda tamik'a mashi tace ga wannan Malam ya aiko maka dashi d'azu.
Amsa yayi yace nagode zan kirashi zuwa gobe tunda yanzu dare yayi.
Momcy tace toh shikenan bari intashi intafi Daddynka na chan na baro shi kad'ai.
Murmushi yayi yace toh Mom sai dasafe.
Allah yakaimu Son.




Washe gari wajen 11am barr faruk yakira Barr Bilal yafad'a mashi zai zo yarakashi gidansu Jawahir nan Barr bilal yace yanzu zasu shiga kotu ne saidai da anjima dan haka Barr Faruk yace shikenan zuwa anjiman sai muje.

Bayan sallar la'asar ne Barr Bilal dakanshi yazo gidan yad'auki Barr Faruk suka kama hanya tunda suka fara tafiya kowa shuru yayi chan Barr Faruk yaga shurun ya yi yawa duk surutun Bilal ammah yau ya yi shuru dan haka yajuyo yakalleshi yace ya dai Barr Bilal lafiya yau naga ka yi shuru?
Ta'be baki yayi yace taya kake tunanin zan iya magana bayan zaka kaini inda zan mutu wallahi Barrister da ace ba kai bane babu wanda zaice inje gidan in amince inje dan ina tsoron gidan kamar yadda nake tsoron yarinyar chan.
Murmushi Barr Faruk yayi yace kaifa ka ji matsalar ka tsoro wani abu ne akace ke akwai acikin gidan?
Ni ban saniba ammah tunda har yarinyar tafito daga gidan ai dole yakasance abun tsoro, kabarni incigaba da lazumina kawai.

Shuru Barr Faruk yayi cikin ranshi dariya yake ma Barr Bilal akan tsoron shi da yayi yawa ahaka har suka isa sai ji yayi ya ja mota ya tsaya a gaban wani gida.
Kallon gidan Barr Faruk yayi yace wannan shine gidan?
Girgiza kai yayi yace ga gidan chan gaba.
Da mamaki Barr Faruk yake kallon dank'areren gidan da Barr Bilal yanuna mashi wanda a cikin layin babu gida me girmanshi da kyaunshi koda gidajen wajen suna da kyau sosai yace kana nufin wanchan shine gidan?
Murmushi yayi yace eh ai ba abun mamaki bane ga wanda yasan kud'in megidan nidai ina daga nan bazan k'ara matsawa ko ina ba sai kafita ka ida takawa.
Murmushi Barr Faruk yayi yace shikenan ba damuwa daman nima banaso ka isa har k'ofar gidan saboda na fad'a maka ba da sanin hukuma nazo ba banaso asan na zo kajirani bari inshiga infito.
Cikin sanyin jiki yace toh shikenan Allah yasa kafito lafiya ammah dai kadinga addu'a.


Baice mashi komai ba yawuce yatunkari gidan fitowa Barr Faruk yayi daga cikin motar rik'e da 'yar brief case d'in Faruk dan ya yi tunanin zai tafi da ita sai kuma yaga ba haka ba dan haka yatsaya yana kallonshi cikin ranshi yana mamakin rashin tsoron Barr Faruk.
Yana zuwa k'ofar gidan tsayawa yayi saida yaga babu kowa gaba da baya sannan yad'auko makullen nan yabud'e k'ofar yashiga k'aton fili ne yafara cin karo da shi duk ganyaye suna ta yawo a tsakiyar filin hango k'ofar da zata sadaka cikin gidan yayi yaga rufe take nan yataka ya isa yana zuwa yasa gudan key d'in yabud'e duk ya'nah ce da k'ura shiga yayi yana bin part parts d'in gidan da kallo yana tunanin wane part yakamata yashiga tunowa yayi da mafarkin da yayi d'akin da yagani tabbas kamar parlor ne koda babu kaya a cikinshi toh ammah wane parlorn daga ciki? Tsaye yayi yarasa wanda zai shiga ya yi kusan minti biyar tsaye a wajen shi kad'ai sai chan yafara tunanin labarin jawahir a k'arshen inda tatsaya mashi murmushi yayi yace babban parlor zan shiga cikin sauri yanufi wajen parlorn yana zuwa yatura k'ofar yajita a rufe makullen da suke hannunshi yasa zai bud'e ammah yak'i bud'uwa daga chan gefe yajiyo k'ara kamar ansa key anbud'e wani d'aki waiwayawa yayi baiga kowaba dan haka yaje yafara tura k'ofofin d'akunan saidai dukkansu a rufe suke ta k'arshence yana turawa yaji a bud'e ajiyar zuciya yasafke tare da kallon k'ofar d'akin tabbas k'ofar ce yagani acikin mafarkinshi ahankali yafurta Alhamdulillah!
Tura k'ofar d'akin yayi yashiga ya'na ce tafara yi mashi sallama a fuska yayi saurin cireta nan yaja yana bin d'akin da kallo k'ura ce sosai aciki kasancewar gidan ya dad'e babu kowa a cikinshi tsaye yayi yana tunanin ta ina zai fara neman Memory Card d'in da zai taimaka mashi wajen samun k'wak'warar shedar da yake nema kuma tabbas yana cikin d'akin, saidai baisan ta inda zai faraba bayan duk tulin k'urar dake cikin d'akin runtse idanunshi yayi yana ji kamar yajuya yakoma baya saidai tabbas yasan sai ya samo Mcard d'in sannan zai iya samun abinda yake nema.

Maganar jawahir ce ta cikin mafarki tafara dawo mashi lokacin da yaga ta jawoshi ta shigo da shi cikin gidan ta nuna mashi wani d'aki mai jan k'ofa tace kashiga nan a nan cikine kawai zaka iya samun memory d'in daga farkon d'akin zuwa tsakiyar d'akin kar kawuce nan zaka sameshi tana fad'in haka ta'bace.

Bud'e idanunshi yayi cike da k'warin gwiwa yaduk'a yafara lalube a cikin tulin k'urar dake k'asan dakin a nutse yake lalube daga yad'auko dutsi sai yad'auko wasu abubuwan ahaka har saida yazo tsakiyar d'akin har zai cigaba sai yatsaya ganin ya zo tsakiyar d'akin dan haka yacigaba da lalube sannan yaji ya ta6o wani d'an abu k'arami cikin sauri yadauko goge shi yashiga yi chan yayi murmushi tare da furta Alhamdulillah tabbas shine cikin sauri yamik'e tsaye kawai sai ji yayi k'ofa ta maida kanta ta rufe dak'arfi, juyawa yayi yakalli k'ofar daga bayanshi yaji wata plastic chair da tasha k'ura tana motsi nan ma yayi saurin juyawa ammah baiga kowa samanta ba sai gani yayi kamar anjata tazo dagudu ta wuce fit tagabanshi
A karo nafarko da yaji gabanshi ya fad'i ammah cikin dakewa yace wanene?
Fitilun dake cikin d'akin ne suka fara d'aukewa suna kawowa nan yayi saurin juyawa zaije wajen k'ofa sai gani yayi hasken d'akin ya d'auke koda da rana ne ammah wani irin duhu yabayyana har baya ganin abinda yake gabanshi Memory Card din yayi saurin zurawa acikin aljihunshi yad'auko wayarshi dan yahaska sai ji yayi anfizge wayar ta fad'i k'asa wata irin dariya yaji anfara cikin wani irin amon murya gabad'aya d'akin yana amsawa, nan yai saurin runtse idanunshi yafara karanta duk addu'ar da tazo a bakinshi.

Murya me k'arfi ce yaji tana tashi tana cewa baka isa kashiga gonata ba bazan ta'ba barinka ba idan har kafita da wannan abun da kad'auka ni na ajiye shi ni nake tsaronshi babu wanda ya isa yad'aukeshi batare da izini na ba.

Hannu yasa cikin sauri yatoshe kunnuwanshi da yakeji kamar dodon kunnenshi zaiyi zillo yafad'o saboda k'arfin muryar cigaba yayi da karanto addu'o'i daga bakinshi wata irin k'ara yadinga ji yai saurin bud'e idanunshi sai ganin wani k'aton dutsi yayi wanda yahaske d'akin ya yo saitin inda yake tsaye cikin sauri yamatsa gefe guda ta gefenshi dutsin yawuce yafad'i rijim a bayanshin nan k'ura tabaje d'akin, tari yafarayi yana son yashak'i numfashi ammah babu ta inda zai ji iska saboda k'urar da tacika a d'akin, duk ya fita hayyacinshi ammah duk da haka bai daina addu'ar da yakeyi ba chan yaji wata irin iska me k'arfi ta taso chan kuma sai yaji iskar ta lafa nan haske yabayyana a d'akin, d'aukar wayarshi yayi da take k'asa yayi saurin fitowa daga cikin d'akin yana tari jawo k'ofar yayi yarufe.


A chan 'bangaren Barrister Bilal dake tsaye waje jikin mota a tsorace yana jiran fitowar Barr Faruk nan yahango wani irin duhu ya bayyana a gidan kallon inda yake yayi yaga haske ammah cikin gidan duhu ne zufa ce tafara kwararo mashi tsoro duk yabayyana a fuskarshi k'afafuwanshi rawa suka fara briefcase din dayake rik'e da ita hannunshi yasaki, bakinshi yana rawa yafara karanta wa'innahu sulaimana wa innahu bismillahirrahmanur rahim ssaids fitsari yakusa yakubce mashi saboda tsoro tunani yayi yashiga mota yagudu kawai dan baya tunanin Barrister Faruk zai fito da rai bare ma yasamu nasarar d'auko abinda yakaishi cikin gidan yana cikin tunanin yaga hasken gidan ya dawo, bud'e motar yayi zai shiga sai ganin Barr Faruk yayi ya fito yana atishawa da tari jikinshi duk ya yi farin k'ura cikin sauri yanufi wajenshi yana isa yace lafiya Barrister ya akayi naganka haka?
Mik'a mashi key d'in yayi alamun yarufe gidan, amsa yayi yarufe sannan yarik'eshi suka nufi wajen mota yana mashi sannu yana cewa saida nace kar kashiga gidan nan ammah kashiga.
Dafe k'irjinshi yayi da yake mashi zafi ahankali yace kawuce da ni gidana.
Amsawa yayi da toh nan yakama hanyar gidan Barr Faruk.









_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_



*PAGE 8*


Suna isa gidanshi a tare suka shiga ciki Barr Faruk bai tsaya sauraren surutun da Bilal yakeyi mashi ba yawuce toilet yana shiga yamaida k'ofa yarufe nan yatsaya a bakin k'ofa yana tunanin abinda yafaru da shi tabbas a yanzu ya ida gasgata maganar Jawahir akan aljanar nan, ya dad'e tsaye kafin daga bisani yasamu yayi wanka yafito, shiryawa yayi cikin kayan shi da yake da su a gidan sannan yafito parlor yasamu Barr Bilal zaune yana shan lemu, yana ganinshi murmushi yayi yace Barrister yanzu har ka fito fes ba kamar lokacin da muka zo ba wai me yafaru da kai?

Zama yayi saman kujera yai shuru kamar bai ji abinda yace ba sai chan har Barr Bilal ya fitar da rai da samun amsar shi sai ji yayi ya ce babu komai kawai dai gidan ne ya yi k'ura sosai saisa kaga na fito duk k'ura jikina.
Barr Bilal ba dan ya yarda ba yace ammah Barrister na hango gidan ya yi duhu babu haske wallahi na tsorata sosai da guduwa zanyi.
Murmushi Barr Faruk yayi yace ni banga hakan ba kaga

48 / 74