Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
mata saidai shi ma Barr Mubarak a yadda naji ance sai wane da wane yake tsaya mawa wannan ne kawai iya abinda nasani akan aikinsu.
Murmushi Barr Faruk yayi yace nagode sosai da bayaninka.
Shima murmushin yayi yace bakomai.
Bayan ya koma gida ma haka yawuni baida tunani sai na maganar jawahir akan mafarkinshi da tsohuwar da yakusa bankewa da mota, shin wai taya jawahir tasan duk wannan, yarasa meyasa har yanzu ta k'i tayi mashi wani kwakkwaran bayani ta barshi sai wahala yake,,wani irin haushi yaji yace anya bazan zare hannunaba akan shara'ar yarinyar nan inbari akashe ta ba? Saurin girgiza kai yayi yace hakan bai daceba yakamata inbari infara jin ta bakinta sai idan na tabbatar da tana da laifi sannan inzare hannuna.
Wasa wasa har kwana biyu yana zuwa yana ta fama da jawahir tayi mashi bayani ammah ta k'i ko kad'an ma bata damuba da hukuncin da za'a yanke mata na kisa,
Daren da zasu shiga court yazo yasameta ana shirin fita da ita za'a kaita wajen horo kallon ma'aikatan wajen yayi yace yanaso abarta zaiyi magana da ita dan haka suka kyaleta saboda sun san matsayinshi da kuma yadda yake a wajen shugaban gidan yarin.
Komawa tayi tazauna tare da kallonshi da mamakinshi sai yaga tayi mashi murmushi ta ce Barrister kaidai na lura baka gajiya kana da burin taimaka ma wadda rayuwarta batada sauran amfani.
Shima murmushin yayi yace kokad'an ba haka bane jawahir ina da burin taimaka makine dan bana tunani kina da hannu a kisan nan saboda bakiyi kama da muguwa ba.
Lokaci guda fara'ar fuskarta tagushe tace idan kuma ya kama ni me fuska biyu ce fa?
Murmushi yayi me k'ara ma fuskarshi kyau yace da ace haka ne da zan iya fahimta.
Girgiza kai tayi tace babu abinda zaka iya fahimta akaina barrister.
Haka dai kikace saidai kinsan gobe ne zamu zauna kotu ammah har yau bansamu kowane irin bayani akanki ba bansan me zanceba, ya kamata *KIYARDA DANI* bazan ta'ba cutar da rayuwarki ba inma wani abu su Barrister Muhsin sukayi maki Toh ni banzo da niyar cuta agareki ba.
Tun kan yarufe baki tace nasan da hakan dan da ace ba hakaba da bazaka ta'ba kai wannan lokacin ba kaima.
Cike da mamaki yace kenan zaki kasheni?
Shuru tayi tare da kauda kanta k'asa.
Barr Faruk yace shin dagaske ne akan zargin da akeyi na cewa kina da hannu akan mutuwar su Barr Muhsin?
Mik'ewa tayi tsaye tare da takawa tamatsa chan wajen yar tagar tatsaya d'an guntun murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo yace Barr Mubarak shine abokin mahaifina ya yi shirin taimaka min saboda wani guri nashi shine kad'ai abinda nasani ammah bansan game da mutuwarshi ba sannan Barr Muhsin lauyan mahaifina ne ya yi shirin taimaka min shima saboda wani dalili nashi nadaban ba wai dan ya ku'butar da ni ba, shin wai miye amfanin rayuwar mutanen da babu komai a ransu sai zalunci? Laifi ne mutuwarsu? Taya kake tunani zanso rayuwa bayan na rasa duk wani farin ciki nawa na rayuwa,,,,fashewa tayi da kuka tace rayuwarsu batada sauran amfani a duniya bana nadama akan mutuwar kowa a yanzu hatta ni kaina idan namutu bazan ta'ba nadama ba akan haka,,,, juyowa tayi takalleshi tahad'e hannuwanta biyu tace na rok'eka kataima kar kaje kotu gobe kabari kawai akasheni dan mutuwar ta fiye min rayuwata.
Barr Faruk bakinshi mutuwa yayi yarasa me ma zaice mata jin anfara kiran sallah ne yasa tawuce tashige wani d'an k'aramin kewaye da yake cikin Ceil din wanda girmanshi bai fi tak'i hud'u ba.
Ajiyar zuciya yasafke sannan shima yafita dan yaje yayi sallah, bayan ya dawo ne yasameta har ta kwanta tayi bacci dan haka yatafi yana mamakin yadda da ranta ya 'baci toh sai tayi bacci.
_*Free Page*_
_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_
_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_
_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/10, 20:03] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......*
_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_
*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]
*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*
*PAGE EIGHT*
Barr Faruk daga nan direct gidan Barr MB yawuce wanda yakasance lauya ne me kare masu k'ara babban lauya ne tun a Shari'ah court yasanshi da yafara aiki a chan kafin ayi mashi transfer amaidoshi High Court yana isa gidan a cikin mota yazauna yad'auko waya yakirashi yana yin picking yayi mashi sallama, bayan ya amsa ne yace dan Allah Barrister idan kana gida kafito gani a k'ofar gidanka.
Barr MB yace k'ofar gidana kuma Barr Faruk? ina fata dai babu wata matsala.
Murmushi yayi yace babu.
Ohk shikenan bari infito ganinan.
Amsawa yayi da toh sannan yakashe wayar.
Yana nan zaune ba'a fi minti biyar ba Barr MB yafito nan Barr Faruk yabud'e mashi gidan gaba dan yashigo cikin motar suyi magana bai kawo komai a ranshiba yazo yashiga tare da mik'a mashi hannu suka gaisa fuskarshi d'auke da murmushi yace ai da rabon ma zaka sameni dan ban dad'e da dawowa ba daga gidan wani Alhaji Mansur akan maganar kotu da zamu zauna gobe.
Murmushi Barr Faruk yayi yace Allah sarki akan shara'ar jawahir ko?
Barr MB yace Eh wallahi wannan shed'aniyar yarinyar idan kaganta baka ta6a cewa zata iya kisa.
Da mamaki yake kallonshi yace kai yanzu har ka yadda da ta yi kisan.
Kallonshi yayi yace a'a me zai hana in k'i yadda bayan mutanen da takashe hatta lauyoyinta ma bata barsuba saida takashesu mun fa dad'e muna fafatawa akan wannan shari'ar kusan wata goma kenan, na tabbata dan baka ta'ba zuwaba kaga shara'ar da kaima abun sai ya baka mamaki ai gobe nasan dole ayanke mata hukuncin kisa saboda batada lauyan da zai tsaya mata inma akwai to tabbas babu abinda zai iya yi.
Murmushi Barr Faruk yayi cike da jin dad'i dan yasan tabbas Barr MB baisan shine lauyan da zai tsaya mata ba, gyara zama yayi cike da jin dad'in bayanin da yake kora mashi yace ammah Barrister taya akayi ita yarinyar tabi manyan mutanen takashe su kuma har suka iya tsayawa?
Dariya Barr MB yayi yace toh nima dai abinda ban saniba kenan dan nidai anbiya ni kud'in aiki ankuma fad'a min itace tayi kisan tadinga binsu d'aya bayan d'aya tana kashewa kuma abinda zai baka mamaki daga danginta sai abokan mahaifinta takashe.
Barr Faruk idanu yazuba mashi yana kallonshi yace toh wanene yashigar da k'arar?
Shuru yayi sai chan yace mutane ukku ne kuma duk abokan mahaifinta ne d'aya daga cikinsu ya je gidan yatarar da ta yi kisa nan take gargad'inshi da shima yashirya tana nan zuwa gareshi shine yakira police aka kamata bayan ya koma gida daga nan yashigar da k'ara a kotu
Jinjina kai Barr Faruk yayi yace saidai har yanzu ban gamsu da hakan ba.
Murmushi Barr MB yayi a karo na biyu yace koma menene ni ban damuba tunda an lale min kud'ina yanzu jira nike agama shara'ar a ida cika min kud'ina.
Girgiza kai Barr Faruk yayi yace ammah hakan ba daidai bane.
Barr MB har ya bud'e baki zaiyi magana kome yatuno sai kuma yafasa yace ina saurarenka minene yake tafe da kai kayi min Kiran gaugawa haka.
'Dan yatsina fuska Barr Faruk yayi yace daman zuwa nayi mugaisa dan kwana dayawa rabon da muhad'u tunda nabar aiki a court d'inku.
Barr MB ba dan ya yardaba yace toh shikenan Nagode kasan yanayin aikin ne namu sai ahankali.
Hakane Allah ubangiji yataimaka mana.
Ya Amsa da Ameen nan sukayi sallama yafita daga motar shikuma yaja motarshi yatafi
Yana isa gida bai lura da su Dad da suke parlour zaune ba har zai haura saman step sai jin muryar Dad yayi ya ce Shalele.
Tsayawa yayi tare da juyawa yadawo yana murmushi yazauna yace Dad ashe kuna nan ban lura da ku ba.
Momcy ce tace taya zaka lura da mu ka shigo wani a birkice da kai.
Sosa k'eya yayi yace wallahi momcy gajiya ce nayi.
Uhm daman inba gajiya ba minene acikin aikin lauya aini da ka bi ta tawa da bakayi aikinba.
Daddy yace a'a Nuratu kidaina wannan maganar dan bata daceba albarka kawai yakamata musa mashi acikin aikinshi dan yana bakin k'ok'arin shi kuma ni abun alfahari na ne inga d'ana ya kasance jajirtacce.
Momcy cikn sanyin jiki tace hakane Alhaji.
Daddy yace yauwa,,sannan yamaida kallonshi ga Faruk da yasunkuyar da kanshi k'asa yace Son daman akan maganar sa ranar aurenka da Nasiba wata nawa kakeso asa?
'Dago kai yayi yakalleshi cike da jin dad'i yace Daddy ranar aurenmu za'a tsaida?
Murmushi Daddy yayi yace Eh haka nake buri Son dan yanzu auren ne yadace da kai tunda ka samu aiki sannan shi Alhaji Sufyan shi yakirani waya yace mufito atsaida ranar aurenku.
Sunkuyar da kai yayi cike da jin kunya yace Daddy duk lokacin da kuka tsaida ya yi min.
Momcy tace shegen gora ji yadda ya marairaice kamar duka ammah tunda yace haka kawai Alhaji asa shekara guda.
Saurin d'agowa yayi yace shekara kuma momcy?
Momcy da Daddy ko me zasuyi inba dariya ba, Faruk mik'ewa yayi cikin sauri yabar wajen.
Koda yashiga part d'inshi sosai yanuna farin cikin shi akan ranar aurensu da za'a tsaida nan yakira Nasiba yafad'a mata itama tayi ta murna.
Suna gama wayar tashi yayi yashiga wanka yana cikin wankan yaji kamar giftawar mutum ta wajen toilet din saurin waigawa yayi ammah baiga kowaba dan haka yad'auko towel yad'aura yafito yadudduba ba kowa cikin d'akin dan shi daman ya san dakanshi yarufe k'ofar da key nan yakoma ya ida wankanshi yafito yashirya yasafko parlorn k'asa yayi lunch d'inshi sannan yakoma part d'inshi yakashe wayoyinshi dan yasamu yayi aikinshi cikin nutsuwa.
File d'in jawahir da aka bashi yad'auko yasake dubawa tare da duba bayanan da yatattara akanta daga k'arshe yabud'e laptop d'inshi yacigaba da bincike sallah ce kawai take tadashi daga inda yake har k'arfe sha biyun dare yayi bai san tayiba yana nan yana aiki, momcy ma da taga bai fitoba saidai takawo mashi dinner d'inshi a nan d'aki.
Har wajen k'arfe d'aya yana nan yana aiki, hamma da yafara ne yasa ya ayyana a ranshi zai tashi yaje yakwanta ahankali yafara jiyo taku a chan k'asan bene kamar ana hawa step k'arar takalma masu tsini ana k'was k'was, shuru yayi yana saurare sai jin k'arar yake ta k'i k'arewa daga karshe yaji kamar anyo wajen d'akinshi cike da rashin tsoro yamik'e yaje yabud'e k'ofa sai ji yayi tsit k'arar ta daina lek'awa yayi baiga kowaba dan haka yamaida d'akin yarufe yazo yakashe laptop d'inshi yashige bedroom alwallah yayi yai sallah raka'a biyu sannan yahaye saman gadonshi saida yatofe jikinshi da addu'a sannan yakwanta bai dad'e da kwanciya ba bacci yakwashe shi.
Washe gari wajen k'arfe tara yagama shirinshi dan da k'arfe goma za'a fara gabatar da shara'a sama sama yayi breakfast nan iyayenshi sukayi mashi addu'ar samun nasara sannan yatafi lokacin da ya isa kotu ta cika makil Alk'ali kawai ake jira ya iso daga chan gaba yaje wajen da Barr Bilal yakama mashi yazauna nan suka gaisa da sauran lauyoyin suna a haka alk'ali ya iso nan kowa yamik'e tsaye har saida yaje yazauna sannan su ma suka koma suka zauna.
Me karanta k'ara ne yatashi yafara yin sallama sannan yace a yau 2 ga watan marich wanda yai daidai da 6 ga watan rajab... Shara'ar farko da zamu fara gabatarwa itace shara'ar indo wadda ake zargi da kashe d'an kishirta dan haka kotu tana buk'atar indo tabayyana a gabanta, wata mata ce tafito idanuwanta kumbure saboda tsananin kuka me gabatar da k'ara juyawa yayi yakalli Alk'ali yace Allah yagafarta malam wannan itace indo.
D'ago kai Alk'ali yayi yakalli wadda aka kira da indo sannan yasadda kai yayi yan rubuce rubuce yace kotu tanaso indo tabayyana mata yadda akayi takashe d'an kishiryata......
Haka aka gama shara'ar indo aka yanke mata hukuncin da yadace nan aka sake kiran wata shara'ar wani da yake zargin abokinshi da shigowa gidanshi cikin dare yayi mashi sata, and'auki lokaci ana tattaunawa kowa lauyanshi yana k'ok'arin kareshi inda daga k'arshe aka gane makwabcinshi ne yashiga yayi mashi satar.
Ana gama yanke hukunci nan me gabatar da k'ara yamik'e yace sai shara'a ta gaba wadda itace ta k'arshe a yau itace shara'ar Jawahir wadda ake zargi da kisan mutane bakwai, wadda iyalan mamatan suka shigar da k'ara wata goma da suka wuce.
Alk'ali d'ago kai yayi yace kotu tana buk'atar ganin wadda ake k'ara.
Me karanto k'ara ne yasake maimaita abinda Alk'ali yace.
Ma'aikatan gidan yari ne mata biyu suka tafo suna janye da ita har wajen da aka tanadar mata dan tatsaya.
Me karanto k'ara yace ga jawahir wadda ake k'ara nan ta bayyana.
Alk'ali yace kotu tana buk'atar ganin lauyan masu k'ara da na wadda ake k'ara.
Barr MB ne yamik'e yace Assaalamu Alaikum nine Barr Mahamud Bello lauyan da yake tsaya ma masu k'ara.
Jinjina kai Alk'ali yayi yaduk'a yayi yan rubuce rubuce nan Barr MB yazauna, me karanto k'ara yace kotu tana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara idan akwai.
Shuru kotu tayi ana jira aga wane me kasada ne wanda yagaji da rayuwarshi yatsaya ma jawahir.
Jawahir da take tsaye duk'ar da kanta tayi idanuwanta sun cika taf da k'wallah.
Barr Bilal ne yad'an ta6o Barr Faruk da yafad'a duniyar tunani daidai lokacin da aka sake maimaita ana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara, ahankali yamik'e tsaye yayi sallama yace nine Barr Faruk Sani Maishadda lauyan da yake kare wadda ake k'ara, gabad'aya kotun d'auka tayi da surutu, jawahir dakyar ta iya d'aga kai takalleshi lokacin shima ita yake kallo ko kad'an bataso hakaba taso ace ya bari anyanke mata hukunci,
'yan sanda ne suka shiga nutsar da mutanen da suke kallon shara'a, Barr MB da mamaki yake kallonshi yai mashi irin kallon nan na haka kayi min?
Alk'ali jinjina kai yayi nan Barr Faruk yakoma yazauna.
Alk'ali d'agowa yayi yace kotu ta ba lauyoyi dama idan da mai kwakkwarar shaida yatashi yagabatar da ita inkuma wadda ake tuhuma tana da abinda zata kare kanta akan tuhumar da akeyi mata na kisan kai akaro na hud'u da akayi zaman kotu toh bismillah
Shuru jawahir tayi still dai kanta yana sunkuye a k'asa.
Mai karanta k'ara ne yasake karanta abinda Alk'ali yace nan tayi shuru .
Mik'ewa Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a inaso kotu taban dama inma Jawahir wasu yan tambayoyi.
Alk'ali yace kotu ta baka dama.
Dan rissinawa yayi yace nagode sannan yataka ya isa inda jawahir take tsaye yace Malama jawahir shin ko zaki iya sanar da kotu dalilinki na kashe wad'annan bayin Allahn da kikayi?
D'ago kai tayi takalleshi da Idanuwanta da sukayi jajir tana so tabud'e baki tayi magana ammah ta kasa bakin nata taji kamar anrike mata shi.
K'ara maimaita mata tambayar yayi ammah shuru saidai kallonshi da takeyi.
Murmushi yayi yace idan wannan tambayar batada amsa toh ga tambaya ta biyu a lokacin da Alhaji Tanimu yashigo yasameki kinyi kisa kinyi mashi barazanar zaki kasheshi shima haka ne ko ba hakaba?
Still dai shuru jawahir tayi saidai hawayen da suke gangaro mata.
Murmushin mugunta yayi yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a yakamata kotu tagaugauta yanke ma jawahir kisa daidai da laifinta da tayi na kisa saboda batada amsar da zata iya badawa a wannan tambayoyin da nayi mata yakamata kotu tayadda da cewa jawahir itace wadda tayi kisa tayi amfani da mark ajikin hotunan wad'anda takashe, d'auko hotunan yayi yamik'a aka mik'a ma Alk'ali.
Duba hotunan Alk'ali yayi nan Barr MB yacigaba da cewa tabbas Jawahir ta shek'a wad'annan bayin Allahn lahira batare da ansan dalilinta na aikata hakan ba wanda daga k'arshe tahad'a da lauyoyin da suka kasance suna nema sukare ta.
Jawahir runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawaye suka gangaro mata.
Barr Faruk ne yai saurin mik'ewa tsaye yace ya me girma me shara'a ya kamata kotu tagargadi Barr Mahmud Bello akan munanan maganganun da yake jifar wadda ake k'ara da su.
Jinjina kai Alk'ali yayi yace kotu ta amshi k'orafinka dan haka kai barrister kagyara kalamanta.
Dan rissinawa Barr MB yayi yace nagode ya me girma me shara'a ina Neman afuwa
Sannan yajuya yakalli jawahir yace ko zaki iya kare kanki akan wannan laifin?
Shuru jawahir tayi tana mecigaba da kallonshi.
Juyawa yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a inaso kotu tagaugauta yanke ma Jawahir hukunci dan batada amsar da zata iya kare kanta da ita.
Mik'ewa Barr Faruk yayi yace ina da ja ya me girma me shara'a ina so kotu taban dama zan d'anyi wasu tambayoyi ga iyalan mamata.
'Yan rubuce rubuce yayi sannan yad'ago yace kotu ta baka dama.
'Dan rissinawa yayi yace nagode sannan yafito yatsaya nan Barr MB yakoma yazauna cike da jin haushi dan ba haka yasoba.
Me karanta k'ara ne yamik'e yace kotu tanason ganin iyalan masu k'ara sugurfana a gabanta.
Daga chan cikin jama'ar da suke zaune kallon shara'a wasu mutane goma suka fito sukazo gaba wajen da aka tanadar suka tsaya, matsowa Barr Faruk yayi kusa da su yace ku ne iyalan wad'anda suka rasu?
Dukansu d'aga kai sukayi alamun Eh.
Murmushi yayi yace ko zaku iya ma kotu bayani akan mutuwar mamatan shin akwai wanda yaga lokacin da jawahir tazo gidan takashe su?
Kame Kame suka fara suka rasa tayadda zasuyi bayani .
Barr Faruk sake jefo masu tambaya yayi yace munaso kuyi mana bayani yadda akayi kukasan itace tayi kisan nan ma sukayi shuru suna kallon gefe d'aya juyawa yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a inaso kotu tawanke jawahir daga laifin da ake zarginta da shi dan babu wanda zai iya bada shedar cewa Jawahir ce tayi kisan, saurin mik'ewa Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a yakamata