Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
yarinyar nan tashigo tana kuka kuma nasan fitarka da kuka had'u kayi mata wani abun, kawai dan kaga tana sonka shine zaka dinga wulak'antata, wai ma me tayi maka?
Ganin yadda Mom take fad'a yasa jikinshi yayi sanyi yace Mom kuyi hak'uri babu abinda nayi mata.
Dad yace anya kuwa Faruk, toh menene dalilinka na k'in amincewa ayi baikonku bayan iyayenta sun amince da hakan, faruk ko dai so kake kawatsa mana k'asa a idanu kasa muji kunya.
Kallon Dad d'in nashi yayi cikin sanyin jiki yace ko d'aya ba haka bane Dad nima kaina ina son Nasiba saidai kawai saboda mahaifinta da yakeso yamaida min soyayya kamar kasuwanci, yadda nakeson Nasiba haka ma aikina ina sonshi.
Su dukansu idanu suka zuba mashi cikin rashin fahimtar maganarshi Dad yace me kake nufi da hakan? Watau kana nufin ba wai saboda karatunta kak'i amincewa ba kana da wani dalili naka?
" Eh Dad nasan koda ban fad'a makuba dole wata rana kusani, akan wani case ne shine mahaifinta da abokinshi suka nuna bazasu bani itaba har sai na janye nikuma naga ba zan iyaba dan baidace ace maganar aurenmu ta shafi aikina ba"
Tsaki Mom taja tace toh menene ba sai ka amince kajanye ba.
A'a Mom kod'aya yin hakan bai daceba domin wannan shara'ar itace tafiye min komai a rayuwata ban da burin da yawuce inga ina taimaka ma mutane musamman ma wad'anda aka zalunta aka tauye ma hak'k'insu, idan har shi mahaifin Nasiba bai kasance wanda zai iya taimaka ma wanda aka zalunta ba toh bai dace yahana wani yataimaka ba, janyewata a shara'ar nan daidai yake da salwantar rayuwar jawahir wanda hakan zai iya sa akasheta.
Dad da Mom lokaci guda sukace Jawahir kuma? Wacece hakan?
Shuru Faruk yayi saida Mom tace tambayarka muke sannan yajuyo yakalleta yace Mom ta kasance yarinya ce wadda aka salwantar da ran iyayenta dan aci dukiyar da mahaifinta yatara wannan duk bai isaba saida akayi silar zuwanta gidan yari,, ganin yadda jikin iyayenshi yayi sanyi yasa yace dan Allah na rok'eku kar ku hanani yin wannan taimakon indai akan aurena da Nasiba ne na hak'ura ko da ace sonta zai kasheni dan bazan iya kasuwanci da soyayyata ba idan har mahaifinta zai iya bani ita ahaka to inkuma bazai iyaba shikenan na hak'ura ammah kugafarce ni idan har maganata ta 'bata maku rai iyayena hak'ik'a ban fad'i haka ba dan in 'bata maku,,, yana fad'in haka yamik'e cikin sauri yawuce yanufi part d'inshi.
Su dukansu da kallo suka bi shi suna jin wani iri a cikin ransu musamman ma Mom da tasan halin d'anta ta tabbata tunda har d'anta yafurta haka to zai iya hak'ura ko da ace zai rasa rayuwarshi akan soyayyar Nasiba.
Dad ne yajuyo yakalleta yace Nuratu kinji abinda Faruk yace.
Cikin sanyin jiki tace babu yadda zamuyi tunda har yafurta ammah me zai hana kasamu shi mahaifin Nasiba kafahimtar da shi wannan shara'ar da Faruk zaiyi ai batada wani aibu tunda akan gaskiya zaiyi ta inyaso sai yajanye k'udurunshi ya amince yabashi auren Nasiba.
Shuru Dad yayi yana nazarin maganarta na d'an wani lokaci sannan yace shikenan zan kwatanta hakan kikwantar da hankalinki.
Murmushi tayi tace bakomai Alhaji nagode, yanzu muje mukwanta dare ya yi.
Kallon agogo yayi yace hakane sannan yamik'e suka nufi part d'insu.
Faruk yana shiga part d'inshi fridge gabud'e yad'auko ruwa yatsiyaya acikin cup yad'aga kai yashanye sannan yawuce yanufi wajen kujera yazauna tare da d'auko wayarshi chan kuma yayi wurgi da ita yadafe kanshi da dukkan hannuwanshi, ahankali yafara jiyo k'ara kamar ruwa yana zuba a toilet lokaci guda yamik'e yanufi bedroom yana shiga yawuce toilet yamurd'a k'ofar yashiga fanfo ne yagani a bud'e ruwa suna ta tsiyaya, wajen fanfon yaje yad'ibi ruwan yazuba ma fuskarshi bud'e idanun da zaiyi tare da d'ago kai ta cikin madubi yaga kamar wannan tsohuwar tsaye a bayanshi gashin nan ya baje mata fuska saurin waigawa yayi ammah baiga kowaba yasake juyowa yakalli madubi nan ma ba kowa ajiyar zuciya yasafke tare da kashe famfon yafito yarufe toilet d'in yawuce yanufi gadonshi yazauna saida yayi addu'a sannan yakashe haske yakwanta
Duk yadda yaso yayi bacci ammah ya kasa babu abinda yake tunani sai labarin da yake cikin diary d'in jawahir, ammah toh wacece wannan aljannar miye had'inta da jawahir? Taya za'a ce mahaifiyarta ce tayi fatalwa bayan bai ta'ba jin haka ba saidai aljannu sudinga siffa irin ta mutane, Ba ma wannan ba ina k'anen babanta da mijinta Umar meyasa bai ta'ba ganin sun zo dubata ba koda akayi zama a kotu baigansu ba? Shin meyasa bazatayi min bayani yadda zan fahimta ba? Runtse idanunshi yayi ahankali yace Jawahir ya kamata kice wani abu,,,
Juyawa yayi d'ayan 'barin yakwanta yana ta tunane tunanenshi ahaka har bacci yai awon gaba da shi.
Washe gari yana wajen aiki wajen k'arfe sha d'aya yana ta fama da ayyukanshi na kwana biyu da bai samu yazauna ba ga wata shara'a da zasu zauna a jibi duk abin ya taru ya yi mashi yawa, knocking d'in k'ofa yaji anyi tun kan yabada izini aka turo k'ofar aka shigo.
'Dago kai yayi dan ganin wanene yashigo batare da izininshi ba sai ido hud'u sukayi da Nasiba, ajiyar zuciya yasafke tare da jingine kanshi a jikin kujerar da yake zaune.
Takowa tayi ta iso taja kujera tazauna tana me kallonshi.
Jin shuru yasa yad'ago kai yakalleta nan suka had'a ido a karo na biyu, d'an guntun murmushi yayi yace Nasiba kece da kanki maimakon kiyo min waya?
Ajiye jakkarta tayi a saman table d'in tazare bak'in space d'in da yake manne a idanunta, ganin idanunta yayi sunyi ja alamun ta ci kuka har zaiyi magana nan tatari numfashinshi tace babu abinda zakace min Faruk ni kawulak'anta narasa me kake nufi da hakan ashe bazaka iya salwantar da komai ba akaina.
Kinga Nasiba ba haka bane kawai dai.......
Kawai dai me? Wai ma shin wacece wannan yarinyar da saboda ita kasalwantar da soyayyarmu wacece ita a wajenka?,,, tafad'a tare da fashewa da kuka.
Faruk duk sai yaji wani iri ganin Nasiba tana kuka duk sai yama rasa me zaiyi, chan yayi k'arfin hali yace Nasiba duk yadda kike tunani ba haka bane ke kanki shedace banda wata wadda nakeso bayanki kawai dai abinda mahaifinki yazo min da shi ne naji kwatakwata bazan iyaba idan har sun amince zasu bani aurenki a haka ashirye nake muyi aure ammah bazan ta'ba yin baya akan case d'in Jawahir ba domin ya zama dole intaimaka mata.
'Dagowa tayi takalleshi tare da rage sautin kukanta tace ammah ai ka san rayuwarta tana da had'ari wannan dalilin ne yasa su Daddy sukeso kajanye dan kar wani abu yashafemu, na ji labari ta kashe mutane dadama daga ciki har da lauyoyin da suka nemi sutsaya mata ammah Faruk ahaka kake ik'irarin zaka tsaya mata? Toh nifa soyayyata kana nufin ka hak'ura da ni?
Shuru Faruk yayi tare da rintse idanunshi yana jin wani iri a ranshi wanda yakasa misulta hakan.
Mik'ewa Nasiba tayi tace tunda bana da amsa shikenan nagode Faruk ni zan tafi.
Saurin bud'e idanunshi yayi yakalleta nan tad'auki jakkarta tajuya zata tafi ahankali yakira sunanta.
Tsayawa tayi batare da ta juyoba tace bana son jin komai daga wajenka Faruk indai har baka janye k'udurunka ba zan tafi zanyi jinyar zuciyata akan tabon da kayi mata saidai ban saniba ko zata iya warkewa,,, tana fad'in haka tawuce cikin sauri zata fita.
Saurin mik'ewa tsaye yayi yace Nasiba dan Allah kitsaya kisaurareni,,, bata ko tsayaba taficce tare da rufe mashi k'ofa.
Buga table d'in da yake gabanshi yayi sannan yakoma yazauna tare da dafe kanshi cikin ranshi yace meyasa zaki min haka Nasiba?
Duk yadda yaso yacigaba da aikin da yake kasawa yayi nan yai zaune zugum abubuwa sun taru sunyi mashi yawa.
Daga k'arshe yai shirin tashi sai ga Barr Bilal ya shigo dan haka yafasa suka zauna suka cigaba da aiki tare har wajen k'arfe d'aya sannan suka tashi sukaje masallaci daga chan barr faruk yaimashi bankwana yawuce gida.
Tunda yakoma gida bai sake fitaba nan yazauna yacigaba da aikinshi yana ji wayoyinshi suna ta ruri ammah yashare su bai d'aga kiran kowaba daga k'arshe ma yakashe wayoyin.
Alhaji Sufyan kallon Abokin nashi yayi yace Alhaji kaga har yanzu babu wani bayani daga yaron chan ya faye taurin kai ban saniba ko hakan yana nufin ya hak'ura da auren Nasiba.
Shuru Alhaji Mansur yayi yana nazarin maganar sai chan yace gaskiya ne nima na fahimci hakan, watau yana nufin abinda yasa gaba sai ya cimmashi bai saniba shi zai kwana a ciki domin bana tunanin yarinyar chan tana barin duk wanda yara'beta wallahi ina bak'in cikin barinta a raye da akayi har zuwa wannan lokacin batare da an d'auki fansar rayukan da takashe ba, taya za'ayi ace wanda yai kisa irin haka anbarshi har tsawon wannan lokacin a raye, miye amfanin hakan bayan kowa ya shaida itace,,, yafad'a cike da nuna damuwa.
Jinjina kai Alhaji Sufyan yayi yace hakane shi kanshi Faruk bansan dalilin tsaya mata da yayi ba kodai akwai wanda yabashi cin hanci?
Ohon mashi koma me kenan insha Allahu bai isa yahana hukunci zartuwaba akanta ya zama dole yadda takashe itama akasheta.
Hakane Alhaji Allah dai yashige mana gaba.
Ameen.
*BAYAN SATI 'DAYA*
Jawahir tana zaune d'an kurkukun d'akinta ita kad'ai kanta sadde a k'asa hannunta rik'e da wani d'an tsinke tana rubutu a k'asa koda rubutun ba fitowa yakeba ammah ahaka takeyi tana zubar da hawaye, kawai sai ji tayi an bud'e k'ofa anshigo saurin runtse idanunta tayi tare da tsayawa da abinda takeyi.
Barr Faruk ne yatsaya yana kallonta sai kuma chan yatako ya iso inda take, saurin mik'ewa tsaye tayi tare da matsawa gaba tajuya mashi baya cikin dashewar murya tace menene dalilinka nadawo wa wajena shin ba na ce kadaina zuwa ba?
Wani irin haushi ne yakama Faruk yana ji kamar yajuya yai tafiyarshi sai kuma yadake yace ammah ai kinsan bamuda isashen lokaci ya kamata ki fahimci hakan jawahir.
Cikin muryar kuka tace ban damu da hakan ba.
Jinjina kai yayi yace hakane ammah dai ya kamata ki k'arashe min labarinki,,
Shuru tayi tak'yaleshi kamar bataji abinda yace ba dan hakane Faruk yamatso kusa da ita yace Jawahir shin wai ina mijinki Umar meyasa ban ta'ba ganinshi ya zo nan ba?
Tun kan yarufe baki tafashe da kuka, dafe k'irjinta tayi da hannunta cikin kuka tace Yaya Umar d'ina? Taya zaizo inda nake alhali kowa yana fushi da ni, ko kad'an banyi nadamar abinda na aikata ba,, juyowa tayi takalleshi fuska sha'be sha'be da hawaye tace shin zaka taimaka min in ida cika burina inyaso akashe ni daga baya?
Kallonta yake cike da mamaki, d'an guntun murmushi tayi tace ban damu da cigaba da rayuwa ba domin rayuwata batada sauran amfani saidai ina burin inje inda iyayena sukaje.
Saurin katseta yayi yace ba haka ba jawahir yakamata ki ida min labarinki domin musan ta yadda zamu 'bullo ma lamarin ko da ace kina so in taimaka maki ki cika burinki dole ne in ida sanin komai shin kina da hannu a cikin mutuwar su Barr Muhsin? Shin dagaske ku ne kuka kashe Alhaji Sa'idu Nepa?
Murmushi tayi cikin nuna rashin damuwa kamar ba itace take kuka ba tace ni kaina bansan abinda zan iya cewa ba, saidai abu guda nasani Alhaji Sa'idu nice nakasheshi da hannuna.
Saurin ja da baya yayi cike da mamakk yake kallonta yace kece kika kashe shi? Garin ya bayan muna tare a hotel kuma baki fitaba?
Girgiza kai tayi tace ba wai dole sai na fitaba sannan nake samun damar kisa na san ka karanta diary na yakamata ace ka fahimci komai akan haka, taya zan iya barin wanda yake da gurin rabani da rayuwata batare da na cika nawa gurin ba.
Matsowa yayi kusa da ita yace kenan jawahir kina nufin yana cikin mutanen da suka kashe iyayenki?
Girgiza kai tayi a karo na biyu sannan tace baya ciki kawai dai d'an uwanshi ne yaturoshi daga chan Europe yazo yaga bayana kafin yadawo k'asar nikuma naga idan nabarshi zai iya samun galaba akaina, shi d'in abokin Abba ne shima saidai d'an uwane na jini ga Alhaji Tanimu sunaso suga bayana ammah kuma bansan me yasa hakaba.
Jawahir wannan ba wani abu bane da ace zaki min cikakken bayani da na taimaka miki na maki alk'awali zan tura ma Alhaji Tanimu takardar gaiyata domin muzauna kotu da shi da ma sauran duk wanda yake da hannu akan kisan iyayenki yakamata ki fahimci bana da burin da yawuce inwanke ki daga zargin da ake maki.
Ahankali tace zargi kuma? Wanene yace maka zargi ne na fad'a maka gaskiya ne nice nake kisan da taimakon wadda takasance masoyiya a gareni.
Shuru Faruk yayi cikin ranshi yace yarinyar nan ta cika taurin kai dayawa,,, muryarta yaji tana cewa iyayena sun sha suce ina da taurin kai tun ina k'arama musamman ma Ammina a duk lokacin da tayi min wanka tad'auko min kaya zan saka sai in nuna bana son su duk yadda zata so insa bana yarda har sai ta canza min wasu wannan dalilin ne yasa take cemin jawahir kin cika taurin kai,, d'an guntun murmushi tayi tare da kallonshi tace ammah wannan ba shine dalilin da yasa nake da taurin kai ba wani lokacin ina duba ne da abinda yadace da rayuwata.
Mamakine yacika Faruk ganin a zuci yayi magana ammah har ta san abinda yace cikin ranshi yace anya itama ba aljanar bace, ajiyar zuciya yasafke sannan yace hakane jawahir kin faye taurin kai nima kaina kiduba tsawon lokacin da nad'auka ina bibiyarki akan kifad'a min komai game da rayuwarki ammah kin k'i...
Katseshi tayi tace ba wai haka ba kawai dai banaso had'arin da yake tare da ni yashafeka dan baka cancanci hakan ba.
Jawahir kar kiyi duba da hakan insha Allahu babu abinda zai sameni dan Allah na rok'eki ki ida sanar da ni komai a game da rayuwarki, shin a lokacin da Abba yazo da malamin nan me yafaru da lokacin da Umar yagano kina da hannu a cikin kisan da akeyi?
Dafe kanta tayi da yasara mata lokaci guda tayi tace a'a bazan ce ga abinda yafaru ba nima kaina kawai dai duk abinda yafaru yana cikin.....bata k'arasa fad'in abinda yake bakinta ba sai gani yayi kamar an fizgeta da k'arfin ta je ta bugi bango, wata irin razanannar k'ara tasaki tare da sulalewa k'asa a sume.
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:10 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 4*
Mummyn Nasiba ce tashiga d'akin d'iyarta ta tasameta zaune ta buga tagumi girgiza kai tayi sannan taje gefenta tazauna cike da jin tausayinta tace Nasiba ya kamata kikwantar da hankalinki kidaina saka damuwa a ranki kiduba kiga a 'yan kwanakin nan yadda duk kika bi kika rame.
'Dago kai tayi takalli mahaifiyarta idanunta cike da hawaye tace bazan iyaba mummy bansan me yasa Faruk zaiyi min haka ba duk son da nake mashi ammah shine zai saka min da haka, shin wai ma wacece wannan yarinyar da yafifitata akan soyayyata.
Shafa kan d'iyartata tayi cike da jin tausayinta tace Nasiba saisa nace maki Faruk baida kirki kicire tunaninshi a ranki dan shi dama kike tunaninshi baisan kina yi ba da ace ya damu dake da bai fifita aikinshi akankiba.
Mik'ewa tayi tsaye tare da fashewa da kuka tace Mummy duk su Daddyne suka ja min hakan da ace sun barshi da aikinshi ai da bazai za'bi aikin akaina ba, koma menene yasamemu ai daga ubangiji ne ni inason faruk a hakan.
Yi shuru Nasiba kar insake jin haka kinsan dai kowane iyaye bazasu so 'ya'yansu susha wahala ba, taya kike tunani zamu amince ki auri Faruk a wannan yanayin ko ma ince akan wannan bala'in da yaratumo ma kanshi, ya kamata kigane cewa mahaifinki gatane yayi maki domin bayason duk abinda zai ta'ba lafiyarki.
Komawa tayi takwanta saman gadonta tajuma ma mahaifiyartata baya tare da fashewa da wani sabon kukan.
Hajiya Maijidda nan tadinga lallashinta tare da k'ok'arin kwatanta mata har tasamu tasafko daga fushin tadaina kukan.
Washe gari Faruk bai samu yakoma wajen jawahir ba saboda shara'ar da zasu shiga haka sukaje suna ta fafatawa har Allah yabasu nasara suka gama.
Bayan kwana biyu koda yaje gidan kaso bai samu ganawa da jawahir ba dan lokacin tana bacci koda yatambayi me gadi yashaida mashi tun baccin da takwanta shekaran jiya ne ammah tana yi tana d'an farkawa tayi sallah sai kuma idan ankawo mata abinci shine ake tashinta, haka yajuya yatafi batare da ya samu yadda yakeso ba abun ya d'aure mashi kai sosai dan bai ta'ba ganin irin haka ba.
A rana ta biyu ce da yakoma yasamu su DPO sunje wajenta sun tsareta da tambayoyi abun ya bashi mamaki sosai dan duk atunaninshi angama case d'in hakanan, DPO yana ganinshi yace Barr Faruk mun sake had'ewa kenan.
Murmushi Faruk yayi yace ai na d'auka tuni angama da wannan case d'in.
Taya za'a gama bayan ta k'i ta amsa laifinta, tana da taurin kai sosai.
Ta'be baki Faruk yayi yace bai zama dole mutum ya amsa laifin da bai aikata ba, yakamata ace ka gamsu da ba ita tayi kisan ba tunda bakada k'wak'warar shaidar da tanuna maka ita duk binciken da zakayi ka yi ammah baka samu ba, da ace ka yi wani tunanin watak'il zaka samu wani nadaban da yayi kisan.
Mik'ewa DPO yayi yamatso kusa da inda Barr Faruk yake tsaye yace har ni zaka fad'a ma haka bayan nasan itace tayi wannan kisan? Ni ko nake da k'wak'warar shaida ko da ace a yanzu nayi niyar kamata akan wannan laifin sai ta kamu saboda duk alamomi sun nuna itace, ya kamata kasan abinda kake fad'a musamman ga babban d'an sanda wanda yasan makamar aikinshi, juyawa yayi yakalli jawahir da kanta yake sadde k'asa yace tana da k'arancin shekaru sannan tana da fuska biyu zan iya amfani da damata insa ta amsa laifin nan ta k'arfin tsiya tunda ta k'i amsawa