Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
sosai dan bata ta'ba tunanin hakan daga gareshiba musamman yadda yake nuna mata so ta d'auka ba wani case ba hatta aikinshi zai iya hak'ura da shi saboda ita sai gashi taga ba hakaba, ammah meyasa su Daddy sukace dole sai ya janye ya tsame hannunshi daga case d'in sannan zasu amince subashi ita? Miye had'in aurensu da aikinshi?,,, buga steering d'in motar tayi tare da girgiza kai a fili tace sam hakan bai daceba.
Wajen k'arfe biyar motocin police ukku suka tsaya a harabar gidan yarin inda police d'in suka fito wasu suka tsaya a nan wasu kuma suka shiga ciki tare da ogansu direct office d'in shugaban gidan suka je inda DPO yashiga ciki su kuma suka ja suka tsaya bakin k'ofa.
Bayan sun gaisa da Alhaji Mahadi ne DPO yake ce mashi mun dai dawo akan case d'in yarinyar chan.
'Dan guntun yawu Alhaji Mahadi yagad'e yace toh 'yallabai dafatan dai ba wani abu yasake faruwa ba?
No bakomai saidai akan kisan Alhaji Sa'idu Nepa wallahi ka yi sakaci da kayarje aka fita da ita alhali ka san hakan baya daga cikin aikinku abar me laifi lauyanshi yafita da shi koma za'a fita ai kyau a had'a da su da police bare ma wannan yarinyar da take da had'ari.
Cikin sanyin jiki yace hakane d'alla'bai nima sai daga baya naga rashin dacewar hakan ammah Barr Faruk mutum ne me amana na sanshi sosai wannan yana daga cikin dalilin da yasa na amince mashi.
Shuru DPO yayi na d'an lokaci sai chan yace ai bata a nan duk yadda kad'auki mutum bai zama dole hakaba, inma haka ne taya zasu iya fita su kad'ai ai zata ma iya guduwa kaima kanka ka san iya dad'ewarmu muna bincike akan case d'innan kafin mugane itace take kisan, shikenan dai kakiyaye yanzu bari inje inganta dan akwai wasu tambayoyi da nakeso inyi maka.
Alhaji Mahadi yace toh shikenan babu damuwa, nan yad'auko wayarshi yakira wani ma'aikaci yazo yayi ma su DPO jagora har d'akin da aka gark'ame jawahir.
Suna isa suka sameta zaune ta jingine kanta da bango tana kallon gefe d'aya har suka shiga bata d'aga kai takallesu ba.
DPO ne yamatsa kusa da ita tare da d'an tsugunnawa a gabanta yace sannu ko jawahir.
'Dago kai tayi takalleshi sai kuma tamaida kallonta a gefe d'aya.
Jinjina kai yayi sannan yace nasan ko ban fad'a ba kinsan abinda yakawoni inaso ki amsa laifinki na kashe Alhaji Sa'idu Nepa kamar yadda kika kashe sauran.
Ahankali tabud'e baki tace banda masaniya akan mutuwarshi.
'Dan guntun murmushi yayi yace ko kina da hujjar da zaki iya kare kanki da ita bayan bincikenmu ya nuna mana kece? Shin abun tambaya ko kina layar zana ko wani siddabaru ne?.
Shuru tayi kamar bataji abinda yaceba.
Juyawa yayi yakalli wata police mace yace tambayar min ita.
Cikin sauri tazo wajen jawahir sai ji tayi anja mata gashi dak'arfi wanda hakan yasa saida tasaki 'yar k'ara, muryar macen taji ta ce bazaki amsa tambayar da akayi maki ba.
Runtse idanunta tayi tare da kai hannunta zata rik'e hannun police d'in sai ji tayi ta sa mata wani abu me kamar k'arfe a wuyanta wanda yataimaka wajen d'ago kanta sama, ji tayi abun ya shak'eta sosai muryar police d'in taji ta ce bazaki amsa tambayar da akayi makiba.
Dak'yar tabud'e baki muryarta tana rawa tace ni bansan komai akan hakaba.
Taya zamu yadda da hakan bayan jiya kun fita tare da Barr Faruk.
Tsananin azabar da takeji ne yasa tafara safke numfashi kad'an kad'an dak'yar tace na fad'a maku bani ba....k'ara matse mata wuya da akayi da k'arfen yasa takasa k'arasa fad'in abinda yake bakinta nan idanuwanta sukayo waje.
Ganin haja yasa DPO yace ak'yaleta.
Ana janye mata k'arfen daga wuyanta nan taduk'e tana tari tare da rik'e wuyanta.
Muryar DPO taji yana cewa jawahir idan har kika cigaba da 'boye min gaskiya fiye da wannan zansa ayi maki, inaso kifad'a min gaskiya game da mutuwar Alhaji Sa'idu ko shima bazaki amsa laifinba kamar yadda kika k'i amsa na sauran?
'Dago kai tayi a galabaice takalleshi tana nishi tace bai zama dole in iya amsa abinda banda masaniya a kai.
Murmushi yayi yace matsalata da ke taurin kai ammah da sannu zan safke maki shi, zanje incigaba da bincike idan har na ida tabbatar da kece kikayi kisan to nayi maki alk'awalin zaki fuskanci hukunci me tsauri akan k'aryar da kikayi min, yana fad'in haka yamik'e tsaye yace a kowane lokaci zaki iya ganina na dawo gareki a duk lokacin da kika ganni to ki tabbata asirinki ya gama tonuwa kuma zaki fuskanci hukuncin daidai da abinda kika aikata,,, yana fad'in haka yajuya yatafi inda sauran police suka take mashi ba.
Jawahir da idanu tabishi hannunta yana rik'e da wuyanta har lokacin numfashinta bai ida komawa daidai ba dan idanuwanta ko gabad'aya suka birkice, kwanciya tayi a wajen tana safke numfashi sama sama kafin daga bisani tafara motsa bakinta ahankali kamar me karanto wani abu chan sai ga wani haske ya bayyana a chan k'arshen bangon d'akin jawahir tashi tayi zaune tana tari sama sama nan tayi yunk'urin mik'ewa tsaye ammah takasa lokaci guda takoma takwanta tare da runtse idanunta ahankali hasken yabayyana a wajen da take yashiga jikinta,,, nan bacci yayi awon gaba da ita.
Alhaji Sufyan da Hajiya maijidda daidai lokacin da suka fito daga d'aki zata raka mijinta da zai fita suka jiyo k'ara a d'akin Nasiba cikin sauri su dukansu suka nufi d'akin, suna zuwa suka tura k'ofar suka shiga, su dukansu ja sukayi suka tsaya lokacin da suka ganta tana watse d'akin duk kayan kwalliyar da suke saman mirror ta zubar da su tana kuka, cikin sauri Hajiya Maijidda tanufi wajenta tarik'eta tana cewa lafiya Nasiba me yake faruwa?
Fad'awa tayi jikin mahaifiyartata tare da fashewa da sabon kuka tana cewa Mummy meyasa su Daddy zasuyi min haka bayan sun san inason Faruk, miye had'in aurenmu da aikinshi? meyasa zasuce dole sai ya yanje daga wani case sannan zasu bashi ni? Hakan da sukayi sun kyauta mana kenan?
Hajiya Maijidda juyawa tayi takalli mijin nata da yake tsaye sannan tamaida kallonta ga d'iyarta da take rungume jikinta tace yanzu Nasiba akan haka ne kike nema kimaida kanki mahaukaciya?.
Cikin kuka tace fiye da haka ma zanyi mummy indai akan son Faruk ne, saboda haka ya daina kulani d'azu na je gidansu ya shareni.
Alhaji Sufyan takowa yayi yamatso wajen da suke tsaye yace haba Nasiba minene abun damuwa ni fa taimakonki nayi domin naji labarin cewa case d'in da faruk yad'aukar ma kanshi yana da had'ari sosai dan yarinyar kisa tayi ba mutum d'aya ba ta kashe mutane dadama ke hatta lauyoyinta bata bariba, tana abu saikace ba mutum ba duk wanda yanemi yara'beta sai taga bayanshi, shi kanshi Faruk ya san da haka ammah bansan dalilin da yasa yanace sai ya tsaya mataba taya kike gani zan d'auki 'yata inba lauya irin faruk.
Cikin kuka tace Daddy,,, sai kuma tayi shuru.
Cigaba yayi da cewa ki kwantar da hankalinki indai har Faruk dagaske yake sonki na tabbata zai janye game da wannan case d'in sannan zai zo yanemi aurenki, ina jin tsoro kar wani abu yashafeki game da case d'in nan Nasiba kiyi tunani a kai ni mahaifinki ne me son farin cikinki.
Janyewa tayi daga cikin Hajiya maijidda tawuce dagudu tafita tabar d'akin tana cigaba da kukanta.
Su duka da idanu suka bita sai chan Hajiya Maijidda tace kar kadamu Alhaji katafi kawai kabarni da ita zan fahimtar da ita yadda zata gane.
Ajiyar zuciya yasafke yace to shikenan maijidda dan Allah kiyi k'ok'arin hakan.
Toh Alhaji insha Allahu, sai ka dawo.
Toh Allah yasa nan yawuce yatafi ita kuma tanufi part d'inta dan tasan chan ne kawai Nasiba zataje.
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
_~GORON SALLAH Last page~_
*PAGE 3*
Wajen k'arfe taran dare Barr Faruk yabaro gidanshi tunda yafito daga cikin gidan zai shiga mota yadinga ji kamar ana bin bayanshi sai ya waiga sai yaga ba kowa cikin ranshi yace inma aljannu ne to na fi k'arfinsu.
Mota yashiga yabar gidan tuk'inshi yake a nutse har ya isa gida, direct part d'inshi yawuce yai wanka yashirya, yana cikin saka kaya Dad yakirashi a waya yace yasameshi a parlor, amsawa yayi da toh.
Saida yagama shirinshi sannan yafita yasamesu zaune shi da Mom.
Gaishe da iyayenshi yayi sannan yazauna yace Dad gani.
Dad yace na ganka Faruk tambayarka nakeso inyi mi yahad'a ka da Nasiba?
'Dago kai yayi yakalleshi yace Dad wani abu tace na yi mata?
Mom harararshi tayi tace ba a saniba ana tambayarka kana tambayar mutane.
Kwantar da murya yayi yace ba haka bane Mom kiyi hak'uri.
"Kaine dai zaka ba kanka hak'uri, wallahi Faruk baka kyauta ba d'azu yarinyar nan tashigo tana kuka kuma nasan fitarka da kuka had'u kayi mata wani abun, kawai dan kaga tana sonka shine zaka dinga wulak'antata, wai ma me tayi maka?
Ganin yadda Mom take fad'a yasa jikinshi yayi sanyi yace Mom kuyi hak'uri babu abinda nayi mata.
Dad yace anya kuwa Faruk, toh menene dalilinka na k'in amincewa ayi baikonku bayan iyayenta sun amince da hakan, faruk ko dai so kake kawatsa mana k'asa a idanu kasa muji kunya.
Kallon Dad d'in nashi yayi cikin sanyin jiki yace ko d'aya ba haka bane Dad nima kaina ina son Nasiba saidai kawai saboda mahaifinta da yakeso yamaida min soyayya kamar kasuwanci, yadda nakeson Nasiba haka ma aikina ina sonshi.
Su dukansu idanu suka zuba mashi cikin rashin fahimtar maganarshi Dad yace me kake nufi da hakan? Watau kana nufin ba wai saboda karatunta kak'i amincewa ba kana da wani dalili naka?
" Eh Dad nasan koda ban fad'a makuba dole wata rana kusani, akan wani case ne shine mahaifinta da abokinshi suka nuna bazasu bani itaba har sai na janye nikuma naga ba zan iyaba dan baidace ace maganar aurenmu ta shafi aikina ba"
Tsaki Mom taja tace toh menene ba sai ka amince kajanye ba.
A'a Mom kod'aya yin hakan bai daceba domin wannan shara'ar itace tafiye min komai a rayuwata ban da burin da yawuce inga ina taimaka ma mutane musamman ma wad'anda aka zalunta aka tauye ma hak'k'insu, idan har shi mahaifin Nasiba bai kasance wanda zai iya taimaka ma wanda aka zalunta ba toh bai dace yahana wani yataimaka ba, janyewata a shara'ar nan daidai yake da salwantar rayuwar jawahir wanda hakan zai iya sa akasheta.
Dad da Mom lokaci guda sukace Jawahir kuma? Wacece hakan?
Shuru Faruk yayi saida Mom tace tambayarka muke sannan yajuyo yakalleta yace Mom ta kasance yarinya ce wadda aka salwantar da ran iyayenta dan aci dukiyar da mahaifinta yatara wannan duk bai isaba saida akayi silar zuwanta gidan yari,, ganin yadda jikin iyayenshi yayi sanyi yasa yace dan Allah na rok'eku kar ku hanani yin wannan taimakon indai akan aurena da Nasiba ne na hak'ura ko da ace sonta zai kasheni dan bazan iya kasuwanci da soyayyata ba idan har mahaifinta zai iya bani ita ahaka to inkuma bazai iyaba shikenan na hak'ura ammah kugafarce ni idan har maganata ta 'bata maku rai iyayena hak'ik'a ban fad'i haka ba dan in 'bata maku,,, yana fad'in haka yamik'e cikin sauri yawuce yanufi part d'inshi.
Su dukansu da kallo suka bi shi suna jin wani iri a cikin ransu musamman ma Mom da tasan halin d'anta ta tabbata tunda har d'anta yafurta haka to zai iya hak'ura ko da ace zai rasa rayuwarshi akan soyayyar Nasiba.
Dad ne yajuyo yakalleta yace Nuratu kinji abinda Faruk yace.
Cikin sanyin jiki tace babu yadda zamuyi tunda har yafurta ammah me zai hana kasamu shi mahaifin Nasiba kafahimtar da shi wannan shara'ar da Faruk zaiyi ai batada wani aibu tunda akan gaskiya zaiyi ta inyaso sai yajanye k'udurunshi ya amince yabashi auren Nasiba.
Shuru Dad yayi yana nazarin maganarta na d'an wani lokaci sannan yace shikenan zan kwatanta hakan kikwantar da hankalinki.
Murmushi tayi tace bakomai Alhaji nagode, yanzu muje mukwanta dare ya yi.
Kallon agogo yayi yace hakane sannan yamik'e suka nufi part d'insu.
Faruk yana shiga part d'inshi fridge gabud'e yad'auko ruwa yatsiyaya acikin cup yad'aga kai yashanye sannan yawuce yanufi wajen kujera yazauna tare da d'auko wayarshi chan kuma yayi wurgi da ita yadafe kanshi da dukkan hannuwanshi, ahankali yafara jiyo k'ara kamar ruwa yana zuba a toilet lokaci guda yamik'e yanufi bedroom yana shiga yawuce toilet yamurd'a k'ofar yashiga fanfo ne yagani a bud'e ruwa suna ta tsiyaya, wajen fanfon yaje yad'ibi ruwan yazuba ma fuskarshi bud'e idanun da zaiyi tare da d'ago kai ta cikin madubi yaga kamar wannan tsohuwar tsaye a bayanshi gashin nan ya baje mata fuska saurin waigawa yayi ammah baiga kowaba yasake juyowa yakalli madubi nan ma ba kowa ajiyar zuciya yasafke tare da kashe famfon yafito yarufe toilet d'in yawuce yanufi gadonshi yazauna saida yayi addu'a sannan yakashe haske yakwanta
Duk yadda yaso yayi bacci ammah ya kasa babu abinda yake tunani sai labarin da yake cikin diary d'in jawahir, ammah toh wacece wannan aljannar miye had'inta da jawahir? Taya za'a ce mahaifiyarta ce tayi fatalwa bayan bai ta'ba jin haka ba saidai aljannu sudinga siffa irin ta mutane, Ba ma wannan ba ina k'anen babanta da mijinta Umar meyasa bai ta'ba ganin sun zo dubata ba koda akayi zama a kotu baigansu ba? Shin meyasa bazatayi min bayani yadda zan fahimta ba? Runtse idanunshi yayi ahankali yace Jawahir ya kamata kice wani abu,,,
Juyawa yayi d'ayan 'barin yakwanta yana ta tunane tunanenshi ahaka har bacci yai awon gaba da shi.
Washe gari yana wajen aiki wajen k'arfe sha d'aya yana ta fama da ayyukanshi na kwana biyu da bai samu yazauna ba ga wata shara'a da zasu zauna a jibi duk abin ya taru ya yi mashi yawa, knocking d'in k'ofa yaji anyi tun kan yabada izini aka turo k'ofar aka shigo.
'Dago kai yayi dan ganin wanene yashigo batare da izininshi ba sai ido hud'u sukayi da Nasiba, ajiyar zuciya yasafke tare da jingine kanshi a jikin kujerar da yake zaune.
Takowa tayi ta iso taja kujera tazauna tana me kallonshi.
Jin shuru yasa yad'ago kai yakalleta nan suka had'a ido a karo na biyu, d'an guntun murmushi yayi yace Nasiba kece da kanki maimakon kiyo min waya?
Ajiye jakkarta tayi a saman table d'in tazare bak'in space d'in da yake manne a idanunta, ganin idanunta yayi sunyi ja alamun ta ci kuka har zaiyi magana nan tatari numfashinshi tace babu abinda zakace min Faruk ni kawulak'anta narasa me kake nufi da hakan ashe bazaka iya salwantar da komai ba akaina.
Kinga Nasiba ba haka bane kawai dai.......
Kawai dai me? Wai ma shin wacece wannan yarinyar da saboda ita kasalwantar da soyayyarmu wacece ita a wajenka?,,, tafad'a tare da fashewa da kuka.
Faruk duk sai yaji wani iri ganin Nasiba tana kuka duk sai yama rasa me zaiyi, chan yayi k'arfin hali yace Nasiba duk yadda kike tunani ba haka bane ke kanki shedace banda wata wadda nakeso bayanki kawai dai abinda mahaifinki yazo min da shi ne naji kwatakwata bazan iyaba idan har sun amince zasu bani aurenki a haka ashirye nake muyi aure ammah bazan ta'ba yin baya akan case d'in Jawahir ba domin ya zama dole intaimaka mata.
'Dagowa tayi takalleshi tare da rage sautin kukanta tace ammah ai ka san rayuwarta tana da had'ari wannan dalilin ne yasa su Daddy sukeso kajanye dan kar wani abu yashafemu, na ji labari ta kashe mutane dadama daga ciki har da lauyoyin da suka nemi sutsaya mata ammah Faruk ahaka kake ik'irarin zaka tsaya mata? Toh nifa soyayyata kana nufin ka hak'ura da ni?
Shuru Faruk yayi tare da rintse idanunshi yana jin wani iri a ranshi wanda yakasa misulta hakan.
Mik'ewa Nasiba tayi tace tunda bana da amsa shikenan nagode Faruk ni zan tafi.
Saurin bud'e idanunshi yayi yakalleta nan tad'auki jakkarta tajuya zata tafi ahankali yakira sunanta.
Tsayawa tayi batare da ta juyoba tace bana son jin komai daga wajenka Faruk indai har baka janye k'udurunka ba zan tafi zanyi jinyar zuciyata akan tabon da kayi mata saidai ban saniba ko zata iya warkewa,,, tana fad'in haka tawuce cikin sauri zata fita.
Saurin mik'ewa tsaye yayi yace Nasiba dan Allah kitsaya kisaurareni,,, bata ko tsayaba taficce tare da rufe mashi k'ofa.
Buga table d'in da yake gabanshi yayi sannan yakoma yazauna tare da dafe kanshi cikin ranshi yace meyasa zaki min haka Nasiba?
Duk yadda yaso yacigaba da aikin da yake kasawa yayi nan yai zaune zugum abubuwa sun taru sunyi mashi yawa.
Daga k'arshe yai shirin tashi sai ga Barr Bilal ya shigo dan haka yafasa suka zauna suka cigaba da aiki tare har wajen k'arfe d'aya sannan suka tashi sukaje masallaci daga chan barr faruk yaimashi bankwana yawuce gida.
Tunda yakoma gida bai sake fitaba nan yazauna yacigaba da aikinshi yana ji wayoyinshi suna ta ruri ammah yashare su bai d'aga kiran kowaba daga k'arshe ma yakashe wayoyin.
Alhaji Sufyan kallon Abokin nashi yayi yace Alhaji kaga har yanzu babu wani bayani daga yaron chan ya faye taurin kai ban saniba ko hakan yana nufin ya hak'ura da auren Nasiba.
Shuru Alhaji Mansur yayi yana nazarin maganar sai chan yace gaskiya ne nima na fahimci hakan, watau yana nufin abinda yasa gaba sai ya cimmashi bai saniba shi zai kwana a ciki domin bana tunanin yarinyar chan tana barin duk wanda yara'beta wallahi ina bak'in cikin barinta a raye da akayi har zuwa wannan lokacin batare da an d'auki fansar rayukan da takashe ba, taya za'ayi ace wanda yai kisa irin haka anbarshi har tsawon wannan lokacin a raye, miye amfanin hakan bayan kowa ya shaida itace,,, yafad'a cike da nuna damuwa.
Jinjina kai Alhaji Sufyan yayi yace hakane shi kanshi Faruk bansan dalilin tsaya mata da yayi ba kodai akwai wanda yabashi cin hanci?
Ohon mashi koma me kenan insha Allahu bai isa yahana hukunci zartuwaba akanta ya zama dole yadda takashe itama