Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
sukace 'Dallabai gata Oga yace akawota.
Kallon matan yayi yace wacece wannan? Jawahir fa nace akawo min?
wannan ai itace jawahir din",,cewar d'aya daga cikin matan.
Kallonshi yamaida ga yarinyar da aka shigo da ita take tsaye kanta sunkuye a kasa doguwa ce kalarta farace ko ma ace me haske sosai daga gani wahala ce tadisar da ita fuskarta me round ce hancinta dogo ne ba chan ba bakinta madaidaici koda tana cikin yanayi na wahala ammah hakan bai hana agane kyaunta, Jinjina kai yayi yace shikenan zaku iya bamu waje.
Tsawa suka daka mata sukace bazaki tsugunna ba?
Ahankali tazame k'asa ta tsugunna still dai kanta na sunkuye a kasa bata d'agoba, juyawa matan sukayi suka fita Inda wani ma'aikaci yatsaya daga bakin k'ofar yadda yana hangensu.
Barr Faruk zuba mata idanu yayi yana kallonta tana kallon ankwar da take hannunta Ahankali yakira sunanta.
D'ago kai tayi tana mashi kallon mamaki batare da ta amsaba.
Numfasawa yayi yace Jawahir sunana Barr Faruk Sani Maishadda.
Wani irin kallo tayi mashi cikin dasashiyar murya tamaimaita Sani Maishadda!
Da mamaki yake kallonta yace kin sanshi ne?
Wani irin murmushi tayi mai wuyar fassarawa sannan tace menene yakawo ka wajena?
Ta6e baki yayi yace ba komai bane yakawo ni sai dan inaso intaimaka maki idan kika bani duk wani bayani da yadace zanyi k'ok'ari wajen ganin na fitar da ke daga cikin gidan nan.
Lokaci guda fuskarta tacanza takoma kwata-kwata babu annuri tace bana buk'atar taimakon ka,
Baki buk'atar taimako na saboda wane dalili nifa so nake intaimaka maki kifita daga gidan nan ammah idan har kika ban damar haka.
Idanu tak'ura mashi tana kallonshi sai kuma chan tajuyar da kanta gefe d'aya tace bazaka iya taimaka min ba kabarni kawai ink'arasa rayuwata ahaka kar kajefa rayuwarka cikin hatsari dan shiga rayuwata daidai yake da ruguza duk wani farin cikin rayuwarka.
No Jawahir kidaina cewa haka akowane lokaci ni me tsayawa ne bayan gaskiya kuma nasan ke bakida hannu a cikin kisan nan.
Fashewa tayi da wani irin firgitaccen kuka tace wannan ba gaskiya bane Barrister kar kasaki kayi gigin shiga rayuwata gudun kar kayi silar rasa taka rayuwarka.
Mik'ewa yayi tsaye yamatso kusa da ita yace ban damu da rayuwataba Indai akan gaskiya zanyi aikina.
Cikin wata irin razanannar murya tace tabbas zaka aikata babban kuskure idan har kanemi kataimaka min zaka iya rasa rayuwarka kamar yadda lauyoyi biyu suka rasa tasu rayuwar.
Cike da mamaki yake kallonta ganin yadda lokaci guda tahargitse yace jawahir kodai kina da hannu acikin mutuwar su Barr muhsin?
K'ara sautin kukanta tayi tace ina gargad'inka kar kayi gigin shiga rayuwata katafi kawai.
Matso da kujerarshi yayi yazauna a gabanta yace na ji zan tafi ammah inaso kifad'a min gaskiyar lamari akan kisan da akayi shin kina da hannu a ciki?
Hannuwanta biyu masu d'aure da ankwana tasa tadafe kanta da su dataji ya fara sara mata k'ara tafasa da dukkan k'arfinta wanda yasa saida gabad'aya d'akin ya amshi shi kanshi Barr Faruk saida yada d'e kunnuwanshi har tagama k'arar idanuwanta yaga lokaci guda sun juye sun canza ta yi wata kala da ita.
Barr Faruk d'auko wata Newspaper yayi ya ajiye a gabanta yace me zakice a nan?
Ido tazuba ma hoton da yake manne jikin newspaper d'in kafin daga baya tajanye idanunta daga kallonta.
Barr Faruk yace shin gaskiya ne wannan bayanin da akayi na hotonki da aka buga akan kin kashe mutane bakwai ciki har da nakusa da ke?
Zumbur Jawahir tamik'e tsaye tare da ja baya kad'an tace ina sake gargad'inka kar kayi gigin shiga rayuwata kabari kawai ayanke min hukuncin kisa domin hakan shine kawai zai kasance *FANSAR RAI* kagaugauta zare hannunka acikin lamurra na banso kaima kajefa kanka cikin wahalalliyar rayuwa, dan taimakona daidai yake da barazana da rayuwarka,,,saurin dafe kanta tayi da taji ya sara mata.
Daidai lokacin matan suka shigo sukace 'Dallabai 20 minutes d'in da aka baku ta cika.
D'aga kai yayi cikin sanyin jiki yace kutafi da ita.
D'ago kai Jawahir tayi takalleshi sannan tajuya suka riketa suka tafi.
Ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke tare da mik'ewa tsaye yafara zagaye d'akin maganganunta suka dinga tariyo mashi a k'walwa cikin ranshi yace kenan tana nufin da hannunta acikin kisan nan duk da akayi? Saidai taya hakan zai kasance bayan ita me k'ananun shekaru ce? Tunowa yayi da irin kallon da tayi mashi lokacin da za'a tafi da ita sai yaga gabad'aya idanuwanta sun canza sunyo waje, ahankali yace anya yarinyar nan mutum ce?
Wayarshi ce da tafara ringing takatseshi daga tunanin da yakeyi dan haka yad'auki key d'in motarshi yaficce cikin sauri saboda wannan Kiran ya san cewa Alk'ali ne yake nemanshi a court.
_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_
_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_
_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/6, 15:07] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo
*......FANSAN RAI.......*
_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_
*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]
*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*
*PAGE FOUR*
Suna janye da jawahir suka maida ta d'akinta suka wullar da ita ciki suka maida k'ofar suka gark'ame, Jawahir had'e kai da gwiwa tayi tafara fitar da kuka Marar sauti wata irin k'ara tafara ji me kama da kukan hadari saurin mik'ewa tsaye tayi tafara waige waige jin k'arar daga saman d'aki take yasa tayi saurin d'aga kanta sama wata irin razanannar k'ara tasaki tare da sulalewa k'asa tafad'i a sume.
Barr Faruk bayan ya je wajen Alk'ali sun sake tattaunawa akan case d'in Jawahir nan ya amshi file d'inta yaduba akan dai laifin kisan ake zarginta list d'in mutanen da takashe yabi.
Yana gama dubawa wasu information yad'auka akan mutanen sannan yatashi yatafi koda yakoma office d'in shi kiran Barr Bilal yayi a waya yace yanaso yaje yasamo mashi hotunan wad'anda ake zargin Jawahir ta kashe, Jim Barr Bilal yayi cikin ranshi ko baisoba dan a rayuwarshi bayason abinda zaisa yashiga Case d'in Jawahir, ba dan ya soba ya amsa mashi da toh zaiyi k'ok'arin hakan.
Barr Faruk yace yatabbatar koma me ake kar yawuce zuwa gobe da safe.
Barr Bilal ya amsa da insha Allahu.
Suna gama wayar yatashi yakama hanyar gida yana isa a parlour yasamu Hajiya Nuratu zaune a main parlor tana ganinshi tayi murmushi tare da cewa sannu da dawowa Son
Shima murmushin yayi yamatso yabata peck a goshi yace yauwa first love dafatan na dawo na sameki lafiya?
Lafiya lau ya aikin?
Alhamdulillah Momcy muna ta fama.
"ai na gani Son dan yanzu kullum busy kake Allah ubangiji dai yataimaka"
Barr Faruk yace Ameen First love
Wai son ka je gidansu Nasiba kuwa?
Murmushi yayi yace a'a Momcy yau dai nakeson zuwa.
Shikenan son ya dai kamata kaje dan Allah kadaina wannan zurfin cikin naka kana son Nasiba ammah sai kadinga basarwa kadinga bata kulawarka ta hakane zata gane kana sonta.
Murmushi yayi yace Toh Momxy insha Allah zanci gaba da k'ok'arin hakan.
Allah yayarda dan wallahi idan har kayi wasa da damarka karasa Nasiba babu ruwana.
Dariya yayi yace insha Allahu ma bazan rasataba Momcy kema nasan ai bazaki bari inrasata ba.
Toh ya zanyi tunda kana ta ja mata aji ai sai inzare hannuna aciki.
Marairaicewa yayi yace kai momcy keda zakiyi min fatan insameta yanzu ma bari inshiga ciki inshirya inzo inyi lunch zuwa anjima sai inje ingano Masoyiyata.
Momcy cikin jin dad'i tace toh shikenan Son idan zakaje sai kayi min magana zan baka sak'o kakai mata Barr Faruk ya amsa da toh momcy nan wuce yanufi hanyar part d'inshi da kallo Hajiya Nuratu tabi d'an nata cike da so kafin daga bisani tamik'e itama tanufi part d'inta.
Barr Faruk bayan ya shiga part d'inshi wanka yayi yashirya yafito yayi lunch bayan sallar la'asar ne yad'auki key d'in motarshi yabiya part d'in Momcy yafad'a mata zai tafi gidansu Nasiba wata Leda tad'auko dank'are da kaya tabashi tace yakaimata.
Murmushi yayi ya amsa yace toh momcy mun gode Allah yak'ara girma da bud'i.
Itama murmushin tayi cikin jin dad'i tace Ameen son.
Yana fita motarshi yabud'e yasaka kayan a bayan mota sannan yabud'e mazaunin megadi yashiga yaja motar driver yahangeme mashi gate yabar gidan dagudu.
Cikin k'ank'anin lokaci ya isa Malali Quarters a daidai k'ofar gidan Alhaji Sufyan Mai Nasara yayi horn nan megadi yataso cikin sauri yalek'o ganin motarshi yasa yai saurin hangame mashi tankamemen gate d'in gidan yashiga.
A daidai inda ake parking d'in motocin gidan yai parking yad'auko wayarshi yayi dialing d'in wata number, saida takusan tsinkewa sannan akayi picking tare da yin sallama akace Hello Lovely.
Lumshe idanunshi yayi dan sosai yakejin dad'in sunan da take kiranshi da shi yace Sweetheart kifito ganinan nazo.
Daga chan 6angaren Nasiba tace ohk ina zuwa.
Katse wayar yayi tare da Jingine kanshi jikin kujerar yana jiranta tafito.
Tayi kusan minti biyar sannan tafito tana tafiya tana yauk'i, Nasiba chocolate colour ce bak'inta mekyau ne batada tsawo sosai saidai yar duma duma ce idan tana tafiya jikinta gabad'aya yake motsawa koda take bak'a ammah tana da kyaunta daidai ita idanuwanta dara dara ne, a nutse take takowa sanye cikin gown din material red da bak'in veil har ta iso wajenshi baisan ta zoba knocking tayi ma glass d'in motarshi nan yabud'e idanunshi tare da bud'e mata gaba fuskarta d'auke da murmushi tashigo tare da yin sallama.
Shima murmushin yayi yana binta da kallo dan sosai tayi mashi kyau.
Kallonshi tayi cike da shauk'in so tace lovely kallon fa?
Lumshe idanunshi yayi yabud'e yace Sweetheart kinyi kyau sosai.
Uhm nagode ammah fa fushi nake da kai.
Zaro ido yayi yace da nayi maki mi?
Juyawa tayi takalli window tace Komai ma kayi yau kusan kwana ukku baka kirani a wayaba kuma rannan munje gidan shine ko kafito mugaisa.
Cikin kwantar da murya yace Ayya sorry sweetheart kinsan yanayin aikin namu yanzu kullum busy nake fara aikin nan da nayi a High Court natarar da aiki dayawa yana jirana yanzu haka shara'ar da na amsa zan tsaya ma mutane sun kai goma banda ma wad'anda namaida nace bazanyi ba saisa kusan kullum banda lokacin kaina cikin research nake.
6ata fuska tayi tace gaskiya lovely tun bakayi nisa da aikin nan ba ya fara fita a raina dan ko munyi aure nasan sai ka fi ba aikinka muhimmanci akaina.
Girgiza kai yayi yace wannan ba hujja bace Nasiba shi aiki daban haka shima aure daban yake ina sonki Kamar yadda nasan kema kina sona kar kidinga sa damuwa a ranki akan haka koda bayan aurenmu ni nasan yadda zan kula da ke batare da nashiga hak'k'in kiba.
Ajiyar zuciya tasafke tace hakane lovely saisa a kullum nake k'ara jinka acikin raina dan Allah kar karabu da ni komin daren dad'ewa.
Murmushi yayi yace kar kidamu insha Allahu muna tare babu abinda zaya rabamu.
Allah yasa, bismillah kazo mushiga cikin gida.
Girgiza kai yayi yace a'a muyi hirarmu a nan.
Kai lovely narasa meyasa bakason shigowa cikin gida kai wai kunyar Ummi ita babu ruwanta tana d'akinta ma.
Ni bazan fa shigaba sweetheart nan dai nakeso muyi hirarmu.
Shikenan lovely duk yadda kakeso haka za'ayi.
Nan suka zauna suka dinga hira cike da k'aunar juna kafin daga bisani sukayi sallama kamar kar su rabu sukeji yad'auko kayan da Mom tabada yabata yamik'a mata nan tayi mashi godiya takoma cikin gida shikuma yafizgi mota yakama hanyar gida tuk'i yake a nutse yana tafiya nan yafara jin motsi a bayan motarshi ta mirror yakalla ammah baiga kowaba ji yayi kamar anwane glass d'in bayan motar dan haka yayi saurin waigawa ganin ba kowa yasa yajuyo k'iiiiittttt yataka burki cikin sauri yatsayar da motar a lokacin da yaga wata tsohuwa tukuf rik'e da sanda ta zo ta gifta mashi ta gaban motar ajiyar zuciya yasafke ganin saura kad'an yabigeta Allah yataimakeshi yatsayar da motar da idanu yabita yana kallonta d'ago kai tayi takalleshi saida gabanshi yafad'i wanda yasa baisan dalilin fad'uwar gaban ba cikin sauri yajanye idanunshi daga kallonta dan idanuwanta sun tsorata shi wasu ficificin idanu ne k'wayar Idanun blue ce ba kalar ta mutane ba saddar da kanta tayi tana rik'e da yar sandarta tawuce batare da ya sake kallon inda takeba yaja motarshi yatafi cikin ranshi yana cewa Allah ya taimakeni da na bugeta,,,tuk'i yake ammah gabad'aya kamannin tsohuwar suke fad'o mashi a rai ahaka har ya isa gida.
Da dare bayan ya dawo daga masallaci sallar isha'i dinner d'inshi yaci sannan yaima momcy sallama yatafi part d'inshi system d'inshi yad'auko yafara searching kamar yadda yasabayi kusan kullum kafin yakwanta bacci, sai wajen k'arfe goma yagama yaje yai wanka yayi shirin kwanciya saida yakwanta yakira Nasiba a waya sukasha hirarsu har wajen 12 sannan sukayi sallama suka kwanta bacci.
Baccinshi yake a nutse hankali kwance ahankali yafara jin taku a cikin d'akinshi ana k'was k'was k'was k'ara gyara kwanciyarshi yayi cike da jin dad'in baccinshi wani irin iska yaji fuuuuuu ta gefen kanshi ta wuce firgit yafarka daga baccin tare da tashi zaune yalalubo makunnin fitila yakunna yana bin d'akin da kallo ammah baiga komai ba kallon agogo yayi yaga k'arfe biyu da rabi na dare dan haka yad'auka acikin mafarkine yaji hakan nan yakoma yakwanta tare da kashe fitilar d'akin.
Washe gari wajen k'arfe goma yagama shirinshi na zuwa wajen aiki yafito part d'in Momcy yaje ganin har lokacin bacci take yasa yawuce dining yayi breakfast d'inshi sama sama ganin yana shirin yin late yasa yawuce yanufi wajen aiki yana shiga secretary yashigo yakawo mashi wasu files yace inji Oga yabada yace abashi.
Amsa yayi yafara dubawa nan yabud'e system d'inshi yafara aiki a ciki.
Barr Bilal ne yaturo k'ofar yashigo Barr Faruk yana ganinshi yajanye files d'in da suke gabanshi tare da rufe system d'inshi.
Hannu Barr Bilal yamik'a mashi sukayi musabaha sannan yazauna yana kallon files d'in da Barr Faruk yajanye yace Barrister wad'annan fa?
Murmushi Barr Faruk yayi yace ina wani aiki ne agame da shara'ar da zamu zauna ta gidan marayun nan da ake son k'wacewa.
Ayya Allah sarki gaskiya Barrister kana k'ok'ari sosai samun irinka a yanzu sai antona dan bakowa bane za'a iya kawo ma mak'udan kud'in da Alhaji Mani yakawo maka ba yak'i kar6a dan kawai yad'aure ma k'arya gindi.
Murmushi Barr Faruk yayi yace ya maganar hotunan ina fata dai ansamo min?
Murmushi shima yayi yace Eh na samo wajen registrar saidai me abin da mamaki yanayin da aka d'auko hotunan.
Mamaki kuma?
Barr Bilal bud'e briefcase d'inshi yayi yafiddo wani d'an envelop yamik'a ma Barr Faruk batare da ya yi maganaba shima yakar6a yabud'e yafara dubawa hotunan mutane bakwai ne yagani dukkansu hotunan anja masu layi da jini cike da mamaki yake kallon hotunan dukansu duk na manyan mutane ne biyu daga cikinsu ma suna da mulki acikin garin katsina, Barr Bilal ne yace kaga wannan jinin da ake sawa a hoton shine dalilin da yasa akace itace tayi kisan saboda ko lokacin da aka kashe babban me kud'in nan Alhaji Nalaraba shima anyi amfani da jinin a hotonshi sannan duk mutanen nan da aka kashe tana da alak'a da su wasu dan duk abokan mahaifinta ne.
Ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke yace ta wace hanya tabi tayi kisan shin da wuk'a aka kashesu ko da bindiga?
Girgiza kai yayi yace babu d'aya daga ciki saidai ta hanyar rataya aka kashe wasu wasu kuma anshak'e masu wuya.
Hotunan mutum ukku yaware waje guda yace wad'annan da kake gani mahaifi ne da 'ya'yanshi saidai bamusan dalilinta na kashesu ba.
Kar6an hotunan yayi yana dubawa kafin daga bisani yace nagode sosai Barr Bilal da wannan k'ok'arin da kayi min Zanyi k'ok'arin zuwa inji daga gareta kafin inje ga dangin mamatan.
Barr Bilal mik'ewa yayi tsaye yace ba damuwa Barrister saidai kakula da kanka.
Kar kadamu a kowane lokaci natashi neman wani taimakon zan nemeka ina fata hakan ba matsala.
Murmushi Barr Bilal yayi yace Eh babu matsala sai naji daga gareka,,Shima mik'ewa yayi yamik'a mashi hannu sukayi musabaha sannan barrister Bilal yatafi.
Yana barin office d'in komawa Barr Faruk yayi yazauna bisa kujerarshi tare da d'auko hotunan yana sake dubawa kowane d'aya anyi mashi mark da jini, kwashewa yayi yasaka cikin envelop d'in sannan yamik'e yad'auki suit d'inshi yasaka sannan yawuce yafita.
Motarshi yashiga yabar Kotun yanufi gidan yari tun a mota yak'ara Shugaban prison din yasanar da shi zuwanshi dan haka yana isa wani ma'aikacin gidan yatarbeshi yayi mashi jagora zuwa d'akin da Jawahir take a rufe, suna gaisawa da megadin da yake kula da gate din da su Jawahir suke nan yatashi yabude masu k'ofar d'an kurkukun da take ciki ana budewa yawuce yashiga d'akin duhu gareshi kasancewar tagar da take ciki yar k'arama ce dan hasken da ke akwai babu yawa ammah duk da haka zaka iya ganin wanda yake ciki, ganinta yayi chan k'arshen bango ta takure duk ta baje gashinta a fuskarta ta juya baya, daga bakin k'ofar me aiki prison d'in yatsaya inda Barr Faruk yashiga ciki fara takawa yayi ahankali ya isa wajen da take zaune ta sadda kanta a k'asa gashinta baya bari aga fuskarta.....
_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_
_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_
_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai