Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 74

12K to 15K   out of 220.3K words

yayan abokina ne muna gaisawa da shi sosai gaskiya bazanji dad'iba idan har baka tsaya mashiba.
B'ata fuska Faruk yayi yace Dad kasan bazan iya bin bayan rashin gaskiya ba, kuma shi Alhaji Mani baida gaskiya, gidan wasu marayu ne yakeso intsaya mashi ya amsa.
A'a Son ban tunanin haka baka saniba ko gidanshi ne.
Allah Dad dagaske nayi bincike ba nashi bane, na bashi hak'uri dan ni aikina babu Magud'i a ciki gaskiya kawai nake goya ma baya, marairaicewa yayi yace please Dad katayani da addu'a Allah yashige min gaba akan wannan aikin nawa banda buri a rayuwata da yawuce intaimaka ma masu gaskiya wajen ganin na kwato masu hak'k'insu dan daman wannan dalilin ne yasa naje nakaranci law.
Cikin sanyin jiki Dad yace Hakane Son insha Allahu zan ci gaba da tayaka addu'a kamar yadda nakeyi a kullum.
cikin jin dad'i yace nagode sosai Daddyna.

Suna shiga gida direct part d'inshi yawuce a saman kujera 3 seater yakwanta tare da d'age kanshi sama tunaninshi d'aya yadda shara'a kusan biyar suka tasoshi a gaba acikin wata biyu ko'ina k'ok'ari yake wajen samun bayanan da suka dace saidai shara'ar jawahir itace kad'ai matsalar shi har yau baisamu jin komai daga wajenta ba.


*BARRISTER UMAR FARUK.*
Alhaji Sani Maishadda da Hajiya Nuratu haifaffun garin Daura ne dake cikin jihar katsina sun fito daga family d'aya na wani babban Alk'ali Nasir mai shadda, 'ya 'yanshi ukku a duniya Alhaji Abdul'aziz ne babba sai Alhaji Umar sannan autarsu Hajiya Kilima, Hajiya Nuratu diyace ga Alhaji Umar shikuma Alhaji Sani Maishadda d'a ne ga Alhaji Abdul'aziz su biyu iyayenshi suka haifa shi da k'anenshi kasancewar iyayensu masu son junansu ne yasa suka had'a ya'yansu auren zumunci, shi da d'iyar k'anen babanshi Hajiya Nuratu bayan bikkinsu ne Allah yayi ma mahaifinta rasuwa yarage daga kakanninta sai yan uwan babanta biyu suka rage mata dan dama mahaifiyarta wajen haihuwarta Allah yayi mata cikawa.

Alhaji Sani Maishadda babban d'an kasuwa ne yana da manyan shagunan shi a cikin garin katsina da plaza wannan dalilin ne yasa bai zauna a Daura garin iyayenshi ba yazauna a cikin garin katsina.


Hajiya Kilima a chan garinsu take auren wani kansilan garin tana da yaranta biyar




Shekararsu Alhaji Sani Maishadda hud'u da aure sannan Allah yabasu haihuwa suka haifi Umar Faruk sunan Mahaifin Mom da yarasu aka sa mashi, bayan shi sun haifi ya'ya biyu ammah duk sun rasu tun daga nan kuma basu sake haihuwa ba, duk son duniya suka d'auka suka d'aura ma d'annan nasu tilo, ya yi primary da secondary school a makarantu masu tsada a cikin garin katsina inda daga gefe d'aya ya samu iliminshi na islamiyya bakin gwalgwado, koda Faruk yake d'an masu kud'i wanda yakeda gata gaba da baya ammah hakan baisa yatashi sargataccen yaroba yana da hankali da tausayi sosai dan tun yana k'arami Indai yaga almajiri to duk kud'in da suke hannunshi sai ya bashi inma babu to wajen mahaifinshi yake zuwa ya amso yabada.
Wata rana lokacin yana ajin k'arshe a secondary school yana kallon wani film yaga yadda ake shara'a ana fafatawa sai abun yaburgeshi sosai yaji yana son aikin dan haka yaje gidan wani makwabcinsu abokin Daddynshi dayake lauya ne yamatsa mashi saida yaje da shi kotu yaga anyi shara'a a gabanshi wata taburgeshi wata kuma batayi mashi dad'iba ganin yadda wasu da gaskiyarsu ammah ake masu fin k'arfi dan haka ne yace shiko baida karatun da zaiyi sai na law.
Iyayenshi ma suka amince da hakan dan duk abinda yakeso su ma shi suke so.
Yana gama secondary school d'inshi suka tura shi chan USA a chan yayi karatun Law d'inshi tsawon shekaru shidda yazama babban Lauya yadawo, lokacin da yadawo ana gwagwata wata Shari'a wanda makwabcinsu ne yake yinta kusan shekara d'aya nan yadamk'a mashi ita kuma yai nasarar lashewa, haka yatsaya da wani justice Samir suka kara a wata Shari'a nan ma yalashe, hatta shi kanshi Barr Muhsin sunyi wata shara'a da shi.

Nan Dadynshi yafara cukucukun sama mashi aiki dayake abu ga masu kud'i aka bashi a Shari'a court.
Barr Faruk baya tsaya ma duk Wanda bai da gaskiya ko da bai saniba yatsaya maka daga inda yagano kaine ba akan gaskiya ba zai barka yace kacanza lauya, ahaka yafara yin suna yana a cikin wata na takwas da fara aikinshi Barr Muhsin yarasu nan aka d'aukoshi aka maida shi a High court aka bashi muk'amin shi, a ranar da yafara zuwa court d'in ya amshi Shari'a guda biyu da Barr muhsin yafara bai idaba na wasu bayin Allah,
Watanshi biyu a court d'in yazo sukayi wata shara'a bayan sun gama tasu ne a ranar akazo akayi ta jawahir yaganta tabashi tausayi yaji yana da gurin tsaya mata.


Nasiba d'iya ce ga wani chairman nagarin katsina Alhaji Sufyan abokin Dad d'inshi ne itama maminta k'awar mommynshi ce, bayan gama karatunshi ne da yadawo suka had'u da ita ta zo gidan, sannan shima momcy tana aikenshi a gidansu wajen Hajiyarta, momcy ce tayi mashi sha'awar ya auri Nasiba shima dayake ya lura da nutsuwarta sai ya amince suka fara soyayya har zuwa yanzu da ake shirin tsaida maganar aurensu degree d'inta kawai ake jira ta ida had'awa.

**** ****

Wayarshi ce da tafara ringing yasa yatashi zaune daga kwancen da yake yad'auko wayar ganin Nasiba ce yasa yayi murmushi tare da yin picking yace sahibata y kk?
Daga chan 6angaren amsawa tayi da lafiya kaima dafatan haka Habibyna.
Nima Lafiya nake saidai....shuru yayi
Saidai me??? Cewar Nasiba.
Ahankali yace saidai tunaninki da nake yawan yi.
Dariya tayi cikin jin dad'i tace wallahi nima haka nake fama da tunaninka wai bazakayi ma su Daddy magana ba suzo sunema maka aurena nifa hankalina ba zai kwantaba indai banga anyi aurenmu ba dan ina tsoron yan matan nan nasan suna sa maka ido saisa na kasa samun nutsuwa.

Dariya Barr Faruk yayi sosai yace lallai Nasiba da alama zakiyi kishi.
Ta6e baki tayi kamar tana a gabanshi tace inma kaji ance kishi to kad'an kenan dan hauka ma zan iya yi akanka.
Cikin jin dad'i yace nagode sosai My wife to be insha Allah.
Lumshe idanunta tayi tace kaifa me zaka iya yi akaina idan akace wani yana sona.
Murmushi yayi cike da k'asaita yace bana ma tunanin akwai wanda zai iya jayayya da soyayyar da nikeyi maki dan nasan na riga da na mallake zuciyarki.
Uhm Allah lovely hakane fa nidai fatana kakasance tare da ni har abada.
"wannan ba matsala bane sweetheart dan nima fatan da nake kenan a rayuwata,,,kallon agogon bango yayi ganin biyar tayi yasa yace Sweety zan kiraki da anjima yanzu zan fita wani d'an aiki da zanyi.
'Bata fuska tayi tace nifa wallahi aikin nan ya fara isata duk shi yake cinye min lokaci na.
Murmushi yayi yace kar kidamu zamuyi waya kikular min da kanki.
Ahankali tace Uhm hmm,, nan sukayi sallama yakashe wayar, mik'ewa yayi yad'auko key d'in motarshi yafito yabar gidan.

Hanyar unguwar yari yakama yana zuwa saida yabiya wajen Ogan prison d'in suka gaisa yafad'a mashi zai he yaga Jawahir nan yakira wani ma'aikacin gidan suka tafi tare suna shiga saidai suka gaisa da megadi nan yabud'e masu wajen Jawahir daga bakin k'ofa ma'aikacin yatsaya inda Barr Faruk yashiga ciki yasameta tsaye wajen yar k'aramar tagar da take a d'akin ta juya baya, matsawa yayi ahankali, muryar Jawahir yaji cikin sanyinta tace akowane lokaci gargad'i nikeyi maka akan kanisantar da kanka daga gareni ammah akowane lokaci k'ara kusanto kanka kakeyi shin wai ka gaji da rayuwarka ne?
Dan guntun murmushi yayi yace kusan haka Indai akan aikinane toh ban damu da rayuwartaba, jawahir ya kamata ki fahimceni nifa banzo da niyar incutar da rayuwarkiba.
Cikin muryar kuka tace haka su ma sauran suka fad'a, nidai shawarar da zan baka shine kafita hanyata kabarni inmutu dan mutuwar itace tadace da rayuwata.
Cike da mamaki yace meyasa kikace haka jawahir?
Batare da ta juyoba tace saboda itace sakamakon abinda na aikata.
Girgiza kai yayi yace bazan yarda da maganarkiba jawahir dan bakiyi kama da wadda tayi kisan ba, nidai dama nakeso kibani intaimakeki tahanyar fad'a min dukkan abinda yafaru ta hakane kawai zan iya taimaka maki.
Girgiza kai tayi batare da ta juyoba tace babu abinda zaka iya sani a game da ni, ina k'ara baka shawara kayi baya da ni inko ba hakaba zakayi da kasani a rayuwarka dan kaima baza'a ta'ba barinkaba.

Matsowa yayi yace jawahir suwanene bazasu ta'ba barina ba?
Juyowa tayi taimashi wani irin kallo sannan tajuya takoma tazauna.
Biyota Barr Faruk yayi yace Jawahir kinyi shuru kiban amsa.
Maimakon tayi magana sai ma had'e kai da gwiwa datayi tacigaba da kuka.

Barr Faruk ya yi juyin duniyar nan tayi magana ammah tak'i kan dole yajuya yatafi yabarta cike da jin haushin rashin maganar da takeyi mashi.


_*Free Page*_


_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_

_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_



_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_




_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/9, 14:43] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967347683033/?substory_index=0&sfnsn=mo

*......FANSAR RAI.......*



_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_



*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]


*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*



*PAGE SEVEN*

Gudu yake sosai yana neman ma6oye cike da tashin hankali yawaiga yakalli wata tsohuwa tukuf saman iska tana biye da shi gashin kanta me tsawo sosai wuta tana kamawa ta bisa shi wata yar bukka ce da yahango cikin sauri yanufi wajen bukkar dan yasamu mafaka k'ark'ashin wasu tulin ciyawu yashiga yaboye zufa take kwarara a jikinshi ta ko'ina, yana kallon matar tashigo tatsaya tana kalle kalle chan kuma sai yaga ta fara nad'ewa siffar jikinta tana komawa ta macizzai, wani irin k'aton maciji takoma wanda saboda girmanshi sai ahad'a kusan mutane k'attai ukku sannan ayi fad'in macijin ahankali yake tafowa yanufo wajen ciyawar, k'arshen tashin hankali ya shigeshi dan ya san yau kwananshi sun k'are duk yadda yaso yatashi yagudu ammah yakasa dan ya san ko da ya tashi baida wajen tsira,,,,k'arar fad'uwar wani abu ne yasa yafarka firgit daga baccin da yake gabad'aya ya yi zufa jikinshi sai 6ari yake waige waige yafara yi a d'akin tare da kunna makunnin fitila ajiyar zuciya yasafke tare da furta Alhamdulillah da yaga ba dagaske bane mafarki yayi, glass cup ne yagani a tsakiyar d'akin afashe tabbas k'ararshi ne yatadashi daga baccin da yake yi, mamaki yafara taya cup d'in yashigo d'akin shi har yafashe, kallon agogo yayi ganin k'arfe d'ayan dare yasa cikin sanyin jiki yakoma yakwanta batare da ya kashe bedside lamp d'inba kasa komawa bacci yayi dan mafarkin da yayi ya bashi tsoro sosai dan ko a film bai ta6a ganin maciji mai girman wanda yagani a mafarkin ba, saidai tsohuwar da yagani tana binshi tabbas ya ta6a ganin fuskarta ammah kuma a ina?
Tunowa yayi da tsohuwar da yagani ya kusa bugewa lokacin yana tuk'in mota, Zumbur yatashi zaune yana k'ara tuno fuskarta tabbas itace to kodai ba mutum bace? Girgiza kai yayi yace wannan nasan sharrin mafarki ne ba komai ba nan yakoma yakwanta tare da sake yin wata addu'a har wajen k'arfe ukku idanunshi biyu yana tunanin mafarkin da yayi kafin daga bisani bacci yad'aukeshi.

Har yatashi dasafe jikinshi babu k'wari tun daga ranar kusan kullum sai ya yi mafarki da tsohuwar nan kowace rana da irin mafarkin da zaiyi na tsoro akanta, kwana ukku bai samu yaje wajen Jawahir ba saboda wata Shari'a da suka shiga tsawon kwanakin a chan garin Kano saida sukayi nasara sannan yadawo gida saidai duk da haka jawahir tana a ranshi ya ce Barr Bilal yadinga kwatanta zuwa wajenta ko a dace shi tafad'a mashi wani abu akanta ammah kullum sukayi waya Barr Bilal cewa yake bata ma kallonshi bare tayi mashi magana, shidai Barr Faruk ba dan ya yardaba dan yasan dakyar ne idan yana zuwa saboda ya lura kamar tsoronta yakeji.

Ranar da yadawo ganin dare ya yi yasa baijeba yai zamanshi gida dan yahuta amsa waya ko har yagaji da masu kira suna tayasu murnar nasarar da sukayi.


Washe gari koda yaje aiki yalek'a yan ayyukan da suka dace yayi sannan yatashi yana shirin fita Barr Bilal yashigo office d'inshi kallonshi yayi yace barrister fita ma zakayi ko?
Eh zanje Chan priso.
Barr Bilal yace Allah kau Barrister da zaka bi ta shawarata da ka kyale yarinyar nan k'ila ma ba mutum bace.
Kaidai kasani matsoracin kawai nidai sai na je daman koda kace min ka je ban yarda da kaiba.
Murmushi Barr Bilal yayi yace k'ara da kagane hakan dan tabbas banjeba.
Wucewa Barr Faruk yayi yace ni kaga tafiyata kar ka6ata min lokaci, nan yawuce yafita yashiga motarshi yatafi.

Yana shiga zaune yasameta ta Jingine kanta a jikin bango tana kallon sama, tsayawa yayi daga gefenta yace Jawahir lokaci yana k'urewa duka fa yanzu kwana hud'u yarage azauna kotu banda wata kwakkwarar hujja da zan kareki da ita, murmushi tayi batare da tad'ago kantaba tace Barrister ya kamata ace abubuwan da kake gani a mafarkinka ya sa ka janye daga tsaya min da kakeso kayi bazan gaji da fad'a maka kafita daga rayuwata ba,
Cike da mamaki yake kallonta yace mafarki kuma? Wane irin mafarki kike magana inayi?
Batare da ta kalleshiba tace na san ka sani tun daga tsohuwar da kagani ta gifta maka ta gaban mota zuwa ga mafarken da kakeyi da ita, shawarar da zan baka kawai itace kazare hannunka daga cikin wannan shara'ar.
Mamaki ne ya ida kashe Barr Faruk yace jawahir ya akayi kikasan tsohuwar da mafarkan da nakeyi? Waye yafad'a maki bayan nasan babu wanda yasani inba niba kuma ban fad'a ma kowaba anya kuwa zargin da akeyi ba gaskiya bane ke ba mutum bace?
'Dan guntun murmushi tayi lokaci guda kuma hawaye suka gangaro mata tace wannan amsar ce nima nakasa ganewa a yanzu saisa nafi buk'atar mutuwa akan rayuwata.
Idanu yazuba mata yana kallonta ba k'aramin firgita yayi da maganartaba nan yafara tunani akan matum ko aljan ce? Bai ida tabbatarwa ba saida yaji ta ce nasan dole kayi tunani akan hakan ammah ni abinda nasani shine ni mutum ce kamar kowa.
Girgiza kai yayi yace ban yadda da hakan ba, idan ke mutum ce ya akayi kikasan tsohuwar da nakusa bugewa har da mafarken da nikeyi.
Had'e kanta tayi da gwiwa tafara rusa kuka tace Barrister bakada hali irin na su Barr Muhsin bazan gaji da cemaka kazare hannunka ba dan banso kashiga wahalalliyar rayuwa.
Cikin sanyin jiki yace na ji haka ammah idan kinsan banda hali irin nasu toh me zai hana kifad'a min tarihinki, sannan su Barr muhsin wane irin haline garesu? Shuru tayi nan yasake maimaita mata Numfashin da yaji ta fara safkewa ne yasa yai saurin k'ara matsawa kusa da ita da mamakinshi sai yaga har ta yi bacci, cikin sauri yaja da baya yace anya kuwa yarinyar nan mutum ce? Juyawa yayi yafita yaje yasamu megadi zaune a wajen da yake zama tare da ma'aikacin prison d'in da sukazo tare da shi, cikin sanyin jiki yace Baba inaso inmaka tambaya akan jawahir in bazaka damuba.
Murmushi megadi yayi yace nikuma insha Allahu zan fad'a maka abinda nasani.
Zama yayi daga gefen megadin yace Baba inaso kafad'a min a iya saninka shin jawahir tana wasu abubuwa na mamaki masu kama da na aljannu?
Murmushi yayi yace tabbas nima kaina abinda nakeso insani kenan dan wasu lokuttan inji tana wasu irin surutai tana kuka, a da duk ayyukan da ake fitar da ita tanayi ammah hannunta babu kanta ko kad'an da zaka gani kace tana cikin wahala ko aikin aka fita da ita baka ganin alamar gajiya atare da ita,,kai abubuwa da dama dai inkaga tayi sai ka dasa alamar tambaya saidai gaskiya nafi tunanin mutum ce saboda akwaita da kula da addini dan da lokacin sallah ya yi zakaga tayi alwallah tayi Sallah inma babu ruwa zata rok'eni insanmata ruwa tayi alwallah ammah nima fa ina yawan kokwanto akanta har yau na kasa gane gaskiya akanta.
Ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke yace shikenan baba Nagode sosai da bayaninka.


Yana fita a mota tafiya kawai yakeyi ammah tunaninshi yana ga jawahir duk ya rasa ya ma zaiyi dan yakasa gane kanta.

Yana isa court direct office d'in Barr Bilal yawuce Barr Bilal yana ganinshi yace Allah yasa ba maganar jawahir kazo min da itaba dan wallahi da na ganka gabana har fad'uwa yakeyi.
Murmushi Barr Faruk yayi tare da zama yace kaidai ka cika tsoro ni ba wannan yakawoni ba nazo inmaka tambaya agame da aikin su Barr muhsin.
Idanu Barr Bilal yazuba mashi yana kallonshi nan Barr Faruk yacigaba da cewa inaso kafad'a min agame da aikinsu waye yasasu suka tsaya ma jawahir? Dan d'azu take wata irin magana tace min wai taga ni ba irin su Barr Muhsin bane banda irin halayyarsu.

Girgiza kai yayi yace kamar yadda nafad'a maka banda masaniya akai saidai gaskiya Barr Muhsin yana kar6ar cin hanci Indai har zai tsaya ma mutum a matsayin lauya sannan akwai wata rana da nazo zan kawo mashi wasu files lokacin yana tsaye a gaban office d'inshi da alama bud'ewa zaiyi aka kirashi a waya na ji yana magana yana cewa kar sudamu shi zai kar6i k'arar yatsaya mata sannan za'a turo mashi 5 millons abarmashi aikin a hannunshi shi ya san yadda zaiyi komai, koda yajuyo yaganni duk sai yacanza fuska alamun baiji dad'iba nan yace ma Wanda suke wayan yabari zai kirashi su ida magana,,,tun daga lokacin da naga ya tsaya a matsayin lauyan jawahir yasa raina yaban tabbas akanta ake maganar kuma ya amshi cin hanci dan yatsaya

5 / 74