Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 74

9K to 12K   out of 220.3K words

domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_





_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/7, 20:57] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo

*......FANSAN RAI.......*



_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_



*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]


*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*



*PAGE FIVE*

Tsaye yayi yana kallonta nan yabud'e baki zaiyi magana sai ji yayi cikin wata irin murya ta ce minene yamaidoka wajena? Bance kafita daga harkata ba, ko kaima ka zo ne dan ka gaji da rayuwarka kamar yadda su Barr Muhsin suka gaji da tasu rayuwar? Ko turoka akayi wajena kaima?
Lokaci guda duk tajero mashi wad'annan tambayoyin idanu Barr Faruk yazuba ma gashinta da yabaje mata fuska kafin daga bisani yace jawahir ni banzo da niyar komai ba wajenki sai dan intaimaka maki kifita daga kurkukun nan fatana ki amsa min tambayoyin da zanyi maki.
Cikin murya me amo tace su ma ai da haka suka zo min, babu amsar da zaka samu daga wajena idan har kana son rayuwarka katafi kabar wajen nan.
Barr Faruk d'auko hotunan yayi yatsugunna a gabanta ya ajiyesu yace ina son kifad'a min gaskiyar al'amari akan kisan wad'annan mutanen.
Jawahir ta cikin gashin takalli hotunan da yabajesu a gabanta d'aya bayan d'aya tadinga kallonsu chan sai tafasa wata irin k'ara tare da fashewa da kuka cikin sauri takai hannunta yana rawa tad'auko d'aya daga cikin hotunan tamanna a k'irjinta tare da dagewa da dukkan k'arfinta tafasa wata irin razanannar k'ara wadda saida tasa gabad'aya d'akin ya amsa shi kanshi ma'aikacin prison d'in da me gadi cikin sauri suka matso wajen d'akin dan sugane ma idanunsu me yake faruwa,,cikin wani irin murya wadda ba irin ta dazu ba tace ku kasheni inhuta rayuwata bata da sauran amfani nice nakashe su nima kukashe ni,,yanayin yadda take maganar zaka gane bata cikin hayyacinta tana rungume da hoton tamik'e tsaye cikin k'araji tace na ce kukasheni na gaji da rayuwar me kuke jira da bazaku kasheni ba, Barr Faruk mik'ewa yayi yanufi inda take tsaye cikin sauri taja da baya tare da d'aga mashi hannu tace kar kayi gigin Matsowa kusa da ni jin haka yasa yaja yatsaya.
Jawahir zuwa tayi chan gefe tazauna tare da zuba ma hoton ido tana kallo tana me cigaba da kuka me shiga rai.

Me aiki gidan da yashigo shima tsaye yayi yana kallonta yace ma Barr Faruk anya kuwa babu wani abu a k'asa akan hoton nan da tarik'e.
Idanun Barr Faruk akanta yace nima ina tunanin haka ammah koma me kenan zanji daga gareta, tsaida kukan da take tayi idanuwanta suna a kan hoton kamar ba itace tagama kukaba tace kufita daga wajen nan.

Tsaye sukayi cirko-cirko suna kallonta.
D'ago kai tayi takallesu idanuwanta sunyo waje tazaresu duk jini ya kwanta cikin hargagi tace na ce kufita!!!
Megadi ne yai saurin zuwa yakwashe sauran hotunan da suke baje yace ma su Barr Faruk muje.

Tsaye Barr Faruk yayi yana kallonta nan tagalla mashi wata irin uwar harara tace me kake kallo katafi!

Bai musaba yajuya yafita yana fita megadi yamaida k'ofar yarufe tare da mik'a mashi hotunan yace Barrister yakamata kafita daga harkar yarinyar nan, Zaidu me aikin prison yace ka ji da kanta ta furta cewa itace tayi kisan kabari kawai akasheta.
Juyowa Barr Faruk yayi yakallesu yace ban tabbatar da hakan ba dole sai naji daga gareta kar kudamu zan barta yanzu tahuta saboda naga ganin hoton chan ya sa tashiga cikin wani irin yanayi,,,,yafad'a tare da kallon cikin Ceil din da jawahir take ciki ta kwanta a k'asa rungume da hoton tana me cigaba da kuka.
Shima megadin kallonta yayi cikin sanyin jiki yace shikenan Allah yakaimu goben.
Ameen yace tare da kar6ar hotunan yai masu sallama yajuya yatafi yana tunanin maganganunta musamman da tace shima anturoshi kamar yadda aka turo sauran lauyoyin cikin ranshi yace me take nufi da hakan? Su wane irin lauyoyi ne?Dole insamo amsar wannan tambayar.


Yana komawa court direct office d'in Barr junaid yawuce yasameshi zaune yana aiki waje Barr Junaid yabashi yazauna tare da mik'a mashi hannu suka gaisa sannan yace ya dai Barrister naganka haka?
Murmushi Barr Faruk yayi yace Barr Junaid inaso insan wanene Barr Muhsin inaso insan yanayin aikinshi da shida Barr Mubarak.

Juyawa Barr Junaid yayi a kujerar da yake zaune sannan yace su ma manyan lauyoyi ne kamar ka.
Girgiza kai yayi yace ba wannan nakeson ji ba inaso kafad'a min yanayin aikinsu sannan inaso insan ya akayi suka tsaya ma Jawahir a matsayin lauyoyinta shin wani ne yasasu ko su suka sa kansu kamar yadda nima nasa kaina?.
Shuru Barr Junaid yayi sai chan yace nidai abinda nasani akan Barr Mubarak shi babban lauya ne kuma abokin mahaifinta gaskiya banda masaniya idan wani yasashi ko shi yasa kanshi a matsayinshi na abokin mahaifinta lokacin da yake raye.
Ido Barr Faruk yazuba mashi yana kallonshi nan Barr Junaid yacigaba da cewa shikuma Barr Muhsin babban lauya ne kuma lauyan mahaifinta duk wani abu da mahaifinta zaiyi ko kwangila ko zai siya gida ko wani abu to barr Muhsin ne yakeda shaida akan haka dan shine lauyanshi bayan rasuwar Barr Mubarak ana shirin yanke mata hukuncin kisa nan shima yafito a matsayinshi na lauyan mahaifinta zai tsaya mata ammah bai samu nasarar hakan ba yarasu dan daga cikinsu babu wanda yasamu tattaunawa da ita dan Barr Muhsin ma ne yad'an samu wasu bayanai agareta har sun fara zama biyu a kotu ba'ayi zama na ukku ba yarasu.
Shiko Barr Mubarak koda sau d'aya bai samu wani bayani agaretaba a iya saniba saidai ban saniba a ranar da yayi zuwa nak'arshe a wajenta har tashakeshi ko yasamu wasu bayan daga gareta,,,wannan shine abinda nasani agame da wad'annan lauyoyin.
Murmushi Barr Faruk yayi yace nagode sosai abokina ni zan tafi idan wani taimakon yatashi zanzo innema.
Cikin sauri yace Karufan asiri wallahi ni ban gaji da rayuwataba kaida dai kasa kanka kayi ranka yadad'e.
Murmushi Barr Faruk yayi a karo nabiyu sannan yajuya yakoma office d'inshi yana shiga yamaida yarufe dan kar ma azo atakura mashi, kunna laptop d'inshi yayi yafara yan danne danne, chan kuma yad'ago yajingine kanshi a jikin kujerar da yake zaune idanunshi suna akan system d'in yana kallo kamar yana nazarin wani abu Ahankali yace yaushe zan samu wasu bayanai a wajen Jawahir har inyi bincike kafin kwanakin zama kotu suyi? Ajiyar zuciya yasafke yad'auko wayarshi yakira Barr Bilal yana yin picking ko sallama baiyi mashiba yace Barr Bilal inaso inbaka wani aiki.
Barr Bilal daga chan 6angaren yace ba damuwa barrister.
Mik'ewa Barrister Faruk yayi yace kabude datarka akwai abinda zan turo maka ina buk'atar asamo min ta kowane hali.
Daga chan 6angaren Barr Bilal yace ba damuwa bari inbud'e.
Kashe wayar yayi yakoma yazauna nan yatura mashi ta system d'inshi.




Jawahir da ke kwance rungume da hoto tana kuka lokaci guda d'akin yafara girgiza cikin sauri tatashi zaune tana ja da baya ahankali ahankali tana girgiza kai hoton yana manne a k'irjinta gam har tajingine jikin bangon d'akin baki tabud'e tanaso tayi magana ammah takasa sai rawa da bakinta yakeyi wata irin guguwa ce a nad'e tanufo inda take lokaci guda tayi sama da ita tafara juyata a saman iska k'ara Jawahir take da k'arfi ammah muryarta bata fita bare tayi tunanin za'aji, ji tayi iskar tana nema tafizge hoton nan tak'ara matseshi a jikinta gashinta taji anja da k'arfi, wuntsila k'afafu tashiga yi tana kware baki tayi k'ara ammah still muryar bata fita tun daga nan aka sakota tafad'o k'asa tabuge goshi lokaci guda taga guguwar ta 6ace dakyar ta iya maida idanunta tarufe hoton dai yana manne a jikinta.

Chan bayan sallar azuhur wata ma'aikaciyar wajen me suna Asabe tazo rik'e da d'an kwanon abinci a hannunta har lokacin jawahir tana nan wajen da take tana shigowa ajiye kwanon tayi tare da warware dorunar da take hannunta tashad'a ma Jawahir, dakyar ta iya bud'e idanunta cike da wahala takalleta babu alamar fara'a a fuskarta tace tashi zaune watau ke bacci kikeyi ko? K'ara shad'a mata bulalar tayi tace ance maki hutu ake a gidan yari idan akazo ke me laifi ce babu ke babu hutawa kitashi kici abinci za'a baki wani aiki.
Jawahir idanu tazuba mata tana a kwancen batare da ta tashi zaune ba,,a fusace tasake d'aga bulalar tak'ara shad'a mata cikin tsawa tace kitashi nace!!!
Jawahir dakyar ta iya tashi zaune tana rungume da hoton a k'irjinta.
Zaro ido matar tayi tace menene wannan nake gani a hannunki Kamar hoto? Waye yabaki shi?
Shuru Jawahir tayi tana cigaba da kallonta da rinannun idanunta.
Hannu matar tamik'a mata tace mik'o min shi nan.
Jawahir k'ara matseshi tayi a k'irjinta batare da tayi maganaba.
A fusace matar tad'aga bulalar tacigaba da zuba mata tana cewa na ce kibani ke daman bakida kunya sai anayi maki magana kidinga ma mutane shuru nice daidai dake dole ki ladabtu a cikin gidan nan,,ganin yadda take bugunta ammah ta k'i tamiko hoton yasa matar takai hannu da tsiya tana nema takwace shi jawahir ganin yana shirin 6arkewa yasa tasakar ma matar, matar harara tabanka mata tana nishi tace da baki sakiba da yau kinga yadda zanyi dake, nan tajuyo da hoton tana kallo tayi murmushi tace dakyau wannan had'ed'en guy d'in kike kallo ko shima kasheshin zakiyi?
Shuru Jawahir tayi tare da duk'ar da kanta k'asa.

Murmushi matar tayi a karo na biyu tace koma minene a cikin ranki kicireshi babu ke babu fita daga nan.

Ahankali jawahir tabud'e baki tace kibani hoton.
Harara matar tawurga mata tace bazan bayarba zuwa zanyi ink'onashi dan haka na baki minti biyar kici abincin kafin indawo infita da ke wajen aiki,,,tana fad'in haka tajuya zata fita.

Bata ji alamun tashin jawahir ba kawai sai ganinta tayi a tsaye a gabanta fuska a murtuk'e cikin k'araji tace na ce kiban hoton.
Matar ta tsorata da yanayin da taganta ammah tadake bata nuna ba tace bazan bayarba bari ma kiga ketashi zanyi tana d'ago hoton zata keta jawahir takai mata wata irin cacuma tahad'eta da jikin bango.
Da dukkan k'arfinta tashake mata wuya idanuwanta sukayo waje muryarta tana rawa tace idan har kikayi gigin 'barka hoton nan sai na kasheki, k'arshen tsorata Kande ta tsorata nan tayi saurin sakin hoton gabad'aya jikinta 6ari yakeyi, jawahir na ganin ta saki hoton tayi wurgi da ita gefe tafad'i, mik'ewa Kande tayi dagudu taficce a tsorace ko tsayawa rufe k'ofar batayiba saidai megadi yazo yarufe dan yana ta tambayarta lafiya ammah inaa bata tsaya saurareshiba bare tabashi amsa.

Jawahir ko d'aukar hoton tayi tana takawa dakyar ta isa wajen wannan dutsin da yake cikin d'akin tad'aga tad'auko dan cimimiyayyen littafinta tasaka hoton ciki tamaida ta ajiye ma'ajiyinta da bakowa yasan da shiba, tana ajiyewa tayi kwanciyarta a wajen tadage kanta sama tana kallon rufin d'akin.


Barr Faruk cigaba yayi da bincikenshi inda a gefe d'aya yake tunanin anya kuwa yarinyar nan tana da lafiya? Toh kodai mahaukaciya ce? Ammah meyasa maganganunta basuyi Kama da na marassa hankali ba?
Ganin baida amsar tambayoyinshi yasa yayi tsaki cike da takaici sannan yacigaba da aikinshi har wajen k'arfe ukku sannan yatashi yatafi gida.


Bayan sallar la'asar yana kwance a d'akinshi yana dannar waya Mom taturo k'ofa tashigo yana ganinta ajiye wayar yayi tare da yin murmushi.
Zuwa tayi tazauna bakin gadon tace son kana nan ashe ai na d'auka ka fita?
Eh Mom ina nan wallahi na gaji ne saisa ban fitaba.
Cike da jin tausayin d'an nata tace Allah sarki Son ai kana ma k'ok'ari da aikin nan Allah ubangiji dai yacigaba da rufa asiri.
Cikin jin dad'i yace Ameen Momcy.
Yauwa daman zuwa nayi inyi maka albishir da cewa Daddynka yana nan dawowa gobe.
Cike da jin dad'i yatashi zaune yace Momcy dagaske gobe Daddy zai dawo?
Murmushi tayi tace Eh haka yace min.
Kai Alhamdulillah gaskiya naji dad'i bari inkirashi intuna mashi da tsarabar da nace yasiyo min.
Momcy tace ai ya ma fad'a min ya siyo maka kaima kasan bazai iya mancewa da shalelenshi ba, ni yanzu burina idan yadawo atsaida maganar aurenku da Nasiba dan nidai na k'agara inga bikkinku.
Shafa kai yayi cike da jin kunya.
Ganin haka yasa momcy tamik'e tace bari inje in ida aikin da nake daman zuwa nayi in isar da sak'on da yabani yace infad'a maka dan ya kira wayoyinka d'azu bai samuba.
Murmushi yayi yace Allah sarki Daddyna aiko na gode bari ma yanzu zan kirashi waya.
Momcy tace hakan dai yakamata,,nan tawuce tafita
Barr Faruk wayarshi yad'auko cike da jin dad'i yakira Daddynshi.


_Free Page_


_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_

_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_


_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_




_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/8, 19:10] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967347683033/?substory_index=0&sfnsn=mo




*......FANSAR RAI.......*



_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_



*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]


*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*



*PAGE SIX*

Washe gari Barr Faruk bayan ya tashi cikin sauri yafara shiri dan 11 flight d'in su Daddy zai safka gashi har 10 ta yi, yana gama shirin yafito yasamu Momcy ta taimaka ma yan aikin gidan angyara ko'ina sai k'amshi yake tashi ga kwalliya da taca6a kasancewar ita macece me son gayu sosai, cikin jin dad'i Faruk ya k'arasa wajenta yana cewa momcy duk shirin tarbar Dad ne?
Murmushi tayi tace sosai ma kusan wata d'aya megida bai nan ai dole
Shima murmushin yayi yace Hakane momcy nan yagaisheta ta amsa tace muje kayi breakfast gashinan a dining, kallon agogon da take manne a tsintsiyar hannunshi yayi yace momcy zanje d'auko Dad fa.
Itama juyawa tayi takalli agogon da take manne a bangon d'akin tace ai dasauran lokaci kaje dai ko yayane kad'an yi dan nasan da yadawo bazaka zauna wani breakfast ba.
Faruk bai musaba yawuce yanufi dining Momcy tabishi tahad'a mashi nan yazauna yana yi, ya d'anci ba laifi yamik'e nan yace ma momcy zai tafi dan a lokacin baifi 10 minutes jirgin su Dad yasafka ba.

D'aya daga cikin maka-makan motocin da suke harabar gidan yashiga saida yakama hanyar airport sannan yakira a wajen aiki yasanar da su bazai samu damar shigowaba yau.


Yana isa daidai lokacin jirgin yasafka dan haka yafito yatsaya yana jira afara fitowa.

Idanu yazuba ma masu safkowa daga saman matattakalar har saida kusan rabinsu suka safka sannan yahango Dad d'inshi, cikin sauri yawuce yaje yatarboshi cike da farin ciki.
Shima kanshi Alhaji Sani Maishadda cikin jin dad'i yarungume d'an nashi d'aya tilo cike da jin sonshi a ranshi Faruk ne yace sannu da dawowa Daddyna ina farin ciki sosai da dawowarka.
Shafa kanshi yayi yace nima ina farin ciki da nadawo nasamu shalelena lafiya.
Murmushi Faruk yayi yace nagode Daddyna, muje ga motar chan, Faruk taya Dad d'aukar kayan sukayi suka nufi wajen motar da yazo da ita.

Tunda suka shigo mota suka kama hanyar gida hira kawai suke cike da farin cikin ganin juna ahaka har suka isa, a harabar gidan suka samu momcy tsaye tana jiran dawowar mijinta ai yana fitowa daga mota taje tarungumeshi bata damu da Faruk da yake tsaye a wajenba, shiko d'aukar babbar jakkar yayi yashiga da ita gida yabarsu nan tsaye suna Murnar ganin juna.

Yana ajiye jakkar yaje yad'auko sauran kayan lokacin su mommy har sun haye sama zata taimaka ma mijin nata yakimtsa.

Barr Faruk a nan parlor yazauna saman kujera yad'auki wayarshi yakira Barr Bilal yana yin picking yace ya dai Barr Bilal ansamu kuwa?
Daga chan 6angaren murmushi Barr Bilal yayi yace har yanzu dai saidai ina k'ok'arin ganin na samu saidai bari inturo maka wasu bayanan da nasamo.
Ohk ba damuwa katuro bari ind'auko system d'in,,kashe wayar yayi yamik'e yanufi part d'inshi yana shiga yajiyo shower akunne ruwa na ta tsiyaya wucewa yayi yanufi toilet din dan yakashe yana kashewa juyowar da zaiyi yaga kamar giftawar mutum cikin sauri yafito ammah baiga kowaba cikin ranshi yace maybe idanunshi ne sukayi mashi gizo dan haka yaje yad'auki laptop d'inshi yafita yakoma parlor har lokacin su momcy basu fitoba dan haka yazauna yacigaba da aikinshi.
Yana cikin yi su Dad suka fito suka sameshi Dad yace Shalele ana ta fama da aiki ko?
Murmushi yayi yace Eh Dad,,,nan yature system d'in yak'ara yi ma Dad din nashi sannu da hanya.
Zama Dad yayi gefen d'anshi yace son ina fata babu wata matsala ko?
Girgiza kai yayi yace babu.
Momcy ce tace kasan ma idan akwai bazaice maka akwaiba ni abinda yake bani mamaki da aikin nan kullum cikin aiki ake ba hutu.
Dad ne yace ai daman aikin lauya ya gaji haka saidai hak'uri fatanmu dai Allah ubangiji yataimaka mashi acikin aikinshi.
Nan suka amsa da Ameen.
Momcy zuwa tayi takawo ma Dad girkin da tasa aka shirya mashi nan yazauna yana ci Barr Faruk yana gama aikinshi janye laptop d'in yayi suka cigaba da hira da iyayenshi cike da nishad'i, Dad tsarabar da yayo yad'auko yaba kowa nashi hatta ma'aikatan gidan sannan yafitar da wata tsarabar yace ma Faruk ta Nasiba ba.
Cike da jin kunya ya amsa yace toh Dad mungode.

Sai wajen azuhur sannan suka tashi sukayi alwallah shi da Dad d'inshi suka tafi masallaci bayan sunyo sallah ne a hanyarsu ta dawoba Dad yace Son meyasa kak'i accepting d'in Alhaji Mani da yanemi kakasance lauyanshi da zai tsaya mashi ya amshi gidanshi?
Kallon Dad din yayi cike da mamaki yace Dad wa yafad'a maka?
Murmushi yayi yace ai kasan

4 / 74