Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 74

102K to 105K   out of 220.3K words

yafaru, yayyen Nasiba kusan kullum sai sunzo gidan saboda mahaifiyarsu da tafi kowa sa damuwa a ranta dan har jininta saida yahau kwana biyu tad'an kwanta ciwo.


Nasiba ko abu goma da ishirin suka taru sukayi mata yawa bayan tashin hankalin da tashiga ta rashin mahaifi ga kuma soyayyar Faruk da take d'awainiya da ita saidai a yanzu tana tunanin kamar bazai sake saurarenta ba.

Yau ma dai tana zaune a d'akinta ita kad'ai ta buga tagumi tana tunanin masoyin nata, Aunty Sadiya ce tashigo tana mata magana ammah Nasiba bata ma san tana yi ba har saida tad'an ta'bata sannan tadawo hayyacinta saurin goge k'wallan da suka cika mata idanu tayi tace Yaya Sadiya yaushe kika shigo?

Zama tayi gefenta cike da jin tausayinta tace haba Nasiba wane irin abune kike haka kina ganin hankalin kowa ba'a kwance yakeba duk muna k'ok'arin danne damuwarmu saboda mahaifiyarmu yanzu da ace ta shigo ta ganki me kike tunani kinsan dai dole hankalinta yasake tashi, kinsan dai ciwonta.

Girgiza kai tayi tace Yaya Sadiya bazaku fahimceni ba, ba wai ina kuka akan Daddy bane a'a kawai ina kuka akan Faruk da nariga namallaka ma gabad'aya zuciyata wallahi yaya sadiya ina mashi son da ni kaina bazan iya misulta shi ba, ammah a yanzu Faruk ya tsaneni na san bazai ta'ba aurena ba saboda abinda mahaifina ya aikata wannan wace irin jaraba ce ya zanyi? Kifad'a min Yaya Sadiya ya zanyi Faruk yasoni?
Hannunta tajanyo tad'aura saman k'irjinta tace ji kiji yadda zuciyata take bugawa akan sonshi.

Tausayinta ne yakama Sadiya tajanye hannunta tare da zuba ma k'anwartata idanu da soyayya take nema tazautata.
Ganin haka yasa Nasiba tafashe da kuka tace kice wani abu Yaya Sadiya dan Allah kifahimceni na san Mummy ce kawai tasan irin halin da nake ciki gashi batada isassar lafiya bare yanzu intunkareta da maganar.

Dafata Sadiya tayi tace kikwantar da hankalinki Nasiba zan taimakeki nima na fahimceki kibani hankalinki gabad'aya zan fad'a maki yadda zakiyi kisamu Faruk.
Saurin goge hawayenta tayi tare da tattara hankalinta gaba'aya ga yayartata dan jin abinda zata fad'a mata.



_______

Mom ce zaune a Parlor tana kallo nan tafara jin sallama a wajen k'ofa.
Amsawa tayi tare da bada izinin shigowa.
Nasiba ce tashigo cikin ado kanta sadde a k'asa cike da jin kunya.
Mom na ganinta nan cikin fara'a tace a'ah wai Nasiba ce bismillah kishigo man.
Shigowa tayi a nutse taduk'a k'asa Mom tace miye haka zaki zauna k'asa kihau kujera man.
Girgiza kai tayi tace a'a Mom nan ma ya yi, ina wuni?
Amsawa Mom tayi sannan tatambayeta Mummynta tace tana nan lafiya lau.
Daga nan kuma duk sukayi shuru Nasiba duk tarasa me ma zatace ita kuma Mom duk sai taji ba dad'i da bata jajanta masu abinda yafaru ba koda ta san Alhaji Sufyan ya yi masu laifi.
Mom mik'ewa tayi tace bari inkawo maki ruwa kitashi kikoma saman kujera Nasiba.
Har ta bud'e baki zatayi magana sai muryar Faruk tajiyo yana waya saurin d'ago kai tayi takalli hanyar part d'inshi da tajuyo muryar daidai lokacin da yake safkowa saman step karaf suka had'a idanu tsaye Faruk yayi a wajen yana kallonta cike da mamakin ganinta, inda itama Nasiba tazuba mashi idanu lokaci guda k'wallah suka cika mata ido, Mom tsaye tayi tana kallonsu sai chan tace Faruk ka fito ne?
Jin muryar Mom yasa yayi saurin d'auke idanunshi daga kan Nasiba tare da ida safkowa yanufi wajen Mom yana cewa Eh Mom yanzu zan d'an fita ne.
Ganin yadda yabasar yasa tace ga Nasiba baku gaisaba ko baka ganta ba?
Batare da ya kalli inda take ba yace sannu Nasiba ya gida?
Wani irin k'ululun bak'in ciki ne yatsaya mata a mak'ogoro cikin ranta tace lallai ma Faruk watau dagaske yanzu ya daina sona.
Mom tace jirani Faruk inkawo ma Nasiba ruwa zan d'akko maka sak'o.
Bai musaba yatsaya batare da ya ce komai ba, maida kallonta tayi ga Nasiba tace ina zuwa sannan tawuce tafita.

Kamar jira suke tana fita nan duk suka zuba ma juna idanu, Nasiba saurin mik'ewa tayi tsaye tamatso inda yake cikin muryar kuka tace dan Allah Faruk kar ka azabtar da zuciyata bazan iya jure rashinka ba abubuwa biyu sun taru sun min yawa dan Allah kasafsafta min kayi hak'uri kar ka kamani da laifin da ba nawa ba.

Har lokacin idanunshi suna a kanta duk ta d'an fad'a da kaga yanayinta ka san tana cikin damuwa, kauda idanunshi yayi gefe yace Nasiba ni me nayi maki? Ina ce kece da kanki kikace baki sona toh minene nawa a ciki ko ance maki ni marar zuciya ne da zanta bibiyarki.

Tun kan yarufe baki tafashe da kuka tace Faruk wallahi rashin fahimta ne yasa nafad'i haka dan duk tunanina kana so katozarta mahaifina ashe ba haka bane daga baya na fahimci haka, tabbas su Dad sun kasance azzalumai da har suka aikata haka ga abokinsu saboda dukiyarshi, ni kaina ina da na sani akan kasancewata d'iya ga Alhaji Sufyan domin bai cancanci kasancewa uba agareni ba, dan Allah Faruk kayi hak'uri da abinda su Daddy suka aikata maka sannan kuma na gane kuskurena dan Allah kayi hak'uri kayafe min Faruk.

Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace koma me kikayi daidai ne Nasiba ni ban rik'eki ba akan abinda yafaru kije kawai.

Tun kan yarufe baki tace ammah kana nufin ka daina sona?
Ta'be baki yayi yace tun lokacin da kika nemi indaina sonki ni kuma nadaina dan haka a yanzu babu sonki a raina.

Saurin ja da baya tafara yi tare da k'ara sautin kukanta tace shikenan Faruk nagode ashe har zaka iya daina sona a lokaci guda? Meyasa haka Faruk? Miyasa bazaka fahimceni ba?
Shuru yayi yak'yaleta jin motsin Mom yasa tayi saurin tsaida kukanta tare da sa hannu tagoge fuskarta kallon Faruk tayi da yake kallon gefe sannan tajuya cikin sauri tafita daidai lokacin da Mom zata shigo da tray a hannunta tsayawa tayi tana kallon Nasiba tace ah-ah Nasiba ina kuma zakije?

Duk'ar da kanta tayi k'asa tace Mom zanje gidane.
Ammah ai da kin bari kinsha ko ruwane nan fa ba bak'on waje bane Nasiba gida ne.
Ahankali tace kiyi hak'uri Mom wani lokacin zan sha yanzu sauri nake su Yaya Sadiya suna jirana nagode sosai Mom,,, tana fad'in haka tawuce cikin sauri tafita.

Mom mamakine yacikata tayi saurin shiga parlorn tasamu Faruk a tsaye yana dannar waya cikin 'bacin rai tace Faruk me kayi ma Nasiba?
'Dagowa yayi yakalli Mahaifiyartashi yace ni kuma Mom? Banyi mata komai ba.
Ajiye tray d'in hannunta tayi tace na tabbata akwai abinda kayi mata tunda har tafita tana kuka, haba Faruk bai dace kakasance butulu ba ko bakomai Nasiba ba ita tayi maka laifi ba mahaifinta ne dan su basusan ma ya yi ba, duk wannan zaman jajen da mukayi duk da ita mukayi shi ta shiga tashin hankali sosai dan ko abinci bata iya ci sannan bata barin gidan nan sai dare shima sai su Dad d'inka sun sa ta tatafi gida, shin wannan ba k'auna bace? wallahi Faruk ba baki zan maka ba ammah na tabbata mawuyacine kasamu me sonka kamar Nasiba domin ita da zuciyata d'aya take k'aunarka.


Shuru yayi duk sai yaji jikinshi ya yi sanyi dan tabbas ya san Nasiba tana k'aunarshi shima kanshi yana sonta ya yi mata haka ne kawai saboda abinda tayi mashi.

Mom cigaba tayi da cewa Faruk baka isa kacanza ma zuciyarka abinda take k'auna ba a lokaci guda ammah shikenan kayi abinda kake gani daidai ne a wajenka,
tana fad'in haka tawuce tabarshi wajen tsaye, runtse idanunshi yayi ahankali yace inko hakane banyi ma Nasiba adalci ba, saurin zama yayi tare da dafe kanshi yana tunanin yanayin da Nasiba tafita lokaci guda yayi saurin mik'ewa yad'auki wayarshi yafita cikin zuciyarshi yana addu'a Allah yasa Nasiba ta isa gida lafiya.



Mom direct d'akin Dad ta isa tasameshi zaune yana karanta Newspaper ganin yadda tashigo yasa yace lafiya Hajiya naga duk ranki a 'bace?
Zama tayi gefenshi tace dole raina ya'baci Alhaji wallahi Faruk baya kyautawa wai menene laifin Nasiba a ciki da har zai rabu da ita?
Nuratu wani abun yafaru?
Kwashe komai tayi game da zuwan Nasiba tasanar da shi, girgiza kai Dad yayi yace Faruk kenan kirabu da shi Hajiya ni nasan yana son Nasiba kawai dai yana dannewane, kinsan halin d'an naki ammah ina nan da ke dakanshi zai koma wajenta.
Cikin sanyin jiki tace Allah yasa haka Alhaji.
Ameen Nuratu kar ma kisa damuwa a ranki, yauwa daman ke naje jira ad'an kawo min coffee d'innan me dad'i wanda kika saba had'a min.
Mik'ewa tayi tana murmushi tace toh Alhaji yanzu ko.



Nasiba da taimakon Allah ta samu ta isa gida lafiya tana shiga a parlor tasamu mahaifiyarta da 'yan uwanta zaune k'ok'arin 'boye damuwarta tayi tamatsa kusa da Mummynta tace sannu Mummy ya jikin naki?

Hajiya Maijidda ajiye ruwan da tasha magani da shi tayi idanunta suna akan d'iyartata tace Nasiba lafiya naganki haka me yafaru dan idanunki sun nuna kinyi kuka?
Saurin duk'ar da kanta tayi tace bakomai Mummy ba kuka nayi ba.

Haj Maijidda kallon Yaya Sadiya tayi tace wannan k'anwartaku bansan irinta ba ita akowane lokaci tana son 'boye damuwarta.
Yaya Sadiya tace hakane Mummy saidai k'ila kuma ko wani abun tatuna yasata kuka.
Murmushi Haj Maijidda tayi tace na san d'iyata babu abinda tatuna kawai dai soyayyar Faruk ce take d'awainiya da ita saidai Faruk bana tunanin zai cigaba da sonta saboda abinda mahaifinta ya aikata ya kamata kubata shawara tahak'ura da shi.

Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata cikin sauri tajuya tashige d'akinta tamaida tarufe saman gado tafad'a nan tashiga rusa kuka da k'arfi.

Su Yaya Sadiya da Yaya Na'ima sunyi juyin duniya akan tabud'e k'ofar ammah tak'i kan dole suka rabu da ita.


Saida tayi kuka me isarta sannan tayi shuru idanunta duk sun kumbura kanta taji ya fara mata ciwo nan tamaida idanunta taruntse.


Faruk motarshi yashiga yakife kanshi a kan steering yana jin babu dad'i akan abinda yayi ma Nasiba, sun had'a mata tension biyu ga nashi ga na mahaifinta ya san dole ta shiga damuwa sosai ba abinda yafi tada mashi hankali sai fitar da tayi cikin 'bacin rai baisan yanayin da zata isa gida ba, saurin d'ago kai yayi yad'auko wayarshi yakirata ammah har tagama ringing ba'a d'agaba sake kiran yayi nan ma ba'a d'aga ba dan haka yatada motarshi yatafi cikin ranshi yana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya.

Nasiba ko tana kwance lokacin da yayi mata 2 missed tana ji ammah takasa bud'e idanunta taduba me kiran dan gabad'aya taji komai ma ya fita ranta batason jin muryar kowa a yanayin da take ciki.


Bayan kamar minti goma wani kiran yasake shigowa a wayarki tsaki taja tare da bud'e idanunta tajawo wayar zata kashe nan idanunta suka safka ga sunan me kiranta wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tamaida wayar ta aje har tatsinke wani kiran yasake shigowa ji tayi bazata iya k'in d'agawaba dan haka tayi picking tare da mannawa a kunnenta, muryar Faruk taji ya ce please Nasiba kifito gani a waje ina jiranki, ahankali ta amsa da toh sannan takashe wayar.


Su Yaya Sadiya suna zaune sukaga ta fito sanye da hijab, mummy ce tace ina kuma zakije?
Batare da ta juyoba tace ina nan waje sannan cikin sauri tawuce tatafi.

Yaya Na'ima tace oh ni lallai Nasiba soyayya ta rufe mata idanu lallai tana son guy d'innan sosai.

Hmmm kece daman baki saniba ammah Nasiba k'aunar da take ma Faruk ni har mamaki take bani daman zata taimaka tacireshi a ranta dan bana tunanin zai aureta.

Mummy da take saurarensu tace a'a kudaina cewa haka ku dai kutayata da addu'a Allah yaza'ba mata abinda zaifi zama alkhairi.
Su duka suka amsa da Ameen.



Kanta sunkuye a k'asa tafito a harabar gidansu taganshi tsaye a jikin motarshi ammah ko da sau d'aya bata d'ago takalleshi ba har ta iso wajen, shi ko idanu yakafeta da su yana kallon yadda take tafiya a nutse dan Nasiba ba bayaba wajen nutsuwa, har ta iso wajen idanunshi suna a kanta.

Tana zuwa ja tayi tatsaya sai a lokacin tad'ago idanunta da sukayi ja saboda kuka tace gani.
Cikin idanunta yakalle cike da nuna damuwa yace yanzu Hearty duk akaina aka zubar da wad'annan hawayen?.
Harara tawurga mashi tace kaga kafad'a min abinda yakawoka inma biyoni kayi kaimin wani wulak'ancin toh babu damuwa bismillah kayi zan iya jurewa saboda duk abinda yafaru laifina ne nice namallaka zuciyata ga wanda bai damu da ita ba, zan iya hak'ura Faruk ko da ace zan rasa rayuwata bazan sake matsa maka ba domin na san bakada laifi a ciki duk abinda yafaru na san mahaifinane yaja min.

Jikin Faruk sanyi yayi sosai yace Nasiba ko d'aya banzo dan inci mutuncinki ba saidai na zone dan inbaki hak'uri sannan inmaido martabar soyayyata.
Da mamaki take kallonshi tana so tayi magana ammah takasa.

Ganin haka yasa Faruk yayi murmushi yace inbanda abun Nasiba taya za'ayi tayi tunanin Faruk zai iya daina sonta bayan ya riga da ya mallaka mata zuciyarshi, Nasiba ina sonki da zuciya d'aya kamar yadda kike sona wallahi nayi maki hakane dan kema kid'and'ani bak'in cikin da kika d'and'ana min a lokacin da kika nisantar da kanki agareni, bana ji zan iya daina sonki Nasiba domin kece Rayuwata.


Wasu irin hawaye ne suka gangaro a fuskarta muryarta tana rawa tace dagaske kake Faruk? Dagaske kana sona zaka aureni?
'Daga kai yayi yace sosai ma indai ba kece kika daina sona ba, ammah a yanzu haka a shirye nake idan kikace inturo sai inturo ayi maganar aurenmu.
'Daga hannunta tayi sama tace Allah nagode maka da kamaido min masoyina, kallonta tamaida ga Faruk tace wallahi bazan iya daina sonka ba Faruk na riga na gama mallaka maka zuciyata idan nabarka taya zan iya son wani.

Ajiyar zuciya yasafke tare da furta Alhamdulillah na yi farin ciki da jin haka daga gareki Nasiba, nima bazan iya son wata ba dan kin riga kin mamaye gabad'aya zuciyata, yanzu dai ina fatan za'a yafe min sannan acigaba da bani kulawa kamar da, komai yawuce mucigaba da nuna ma juna soyayya har zuwa aurenmu.

Murmushi tayi cikin jin dad'in maganarshi tace insha Allahu Faruk na yi maka alk'awalin haka zan cigaba da baka kulawa har k'arshen rayuwata wallahi bakaji farin cikin da kasaka ni ba a yau ji nake kamar a mafarki kadawo gareni.

Su duka dariya sukayi Faruk yace duk farin cikin da zaki shiga na fiki Nasiba yanzu dai kiyi min iso wajen Mummy inshiga mugaisa yau dai zan cire kunya in nemi aurenki dakaina inyaso idan nakoma gida sai insanar da su Dad su kuma su ida nasu.

Wayyoo kar kuso kuga farin ciki wajen Nasiba rasa inda zata sa kanta tayi, haka tanufi hanyar cikin gida tana shiga da gudu ta isa parlor tana k'wala ma Mummy kira, su duka suka d'ago suna kallonta.
Kusa da mummy tazauna cike da farin ciki tace Mummy Faruk ne yazo ya ce zai shigo yanzu kugaisa.

Su duka farin ciki suka nuna nan Mummy tace taje tace yashigo.
Mik'ewa tayi tafita cikin sauri suka bita da idanu, mummy tace kungani ko ai nasan suna k'aunar junansu sosai shima bazai iya barinta ba sai ya biyota.

Su Aunty Sadiya sukace lallai kam ga alama nan mungani.


Tana fita tasanar da shi sak'on Mummy sannan tafad'a mashi batada lafiya, a tare suka jero suka shigo gidan bakinshi d'auke da sallama yashiga parlorn suka amsa mashi har zai zauna a k'asa Mummy tace a'a kar yasaki yazauna yahau kujera dan haka yazauna saman kujera d'an zamowa yayi yagaisheta ta amsa nan yayi mata ya jiki sannan suka gaisa da su Yaya Sadiya da suke zaune gefenta.

Nasiba ko baki k'in rufuwa yayi haka tafita tafara had'a mashi kayan motsa baki.

Mummy ce cikin k'arfin hali tace dan Allah Faruk kayi hak'uri da abinda yafaru wallahi ba da saninmu bane Alhaji yake aikata wad'annan mugayen halayyar daga ni har 'ya'yana babu wanda yasan haka sai daga baya ashe su ne suka saceka dan Allah kayi hak'uri kar kadubemu da laifin da bamu muka aikata ba.

'Dago kai yayi yakalleta cike da girmamawa yace kod'aya Mummy bana kalkonku da laifin da ba naku bane ai laifin wani baya ta'ba shafar wani nima kaina banyi hakan dan in tozartasu ba saidai nayi ne dan intseratar da yarinyar da aka zalunta sannan daga baya ake shirin ganin anrabata da rayuwarta.

Mummy tace hakane na san haka Faruk wannan dalilin ne yasa na k'ara son Nasiba takasance mata ga miji irinka domin ka cancanci asoka ko dan saboda gaskiyarka.

Su yaya Sadiya sukace hakane muma muna k'ara bada hak'uri Faruk.
Murmushin jin dad'i yayi yace bakomai nagode sosai, daidai lokacin Nasiba tashigo d'auke da k'aton tray ta ajiye gabanshi nan duk suka mik'e zasu bar wajen yace Mummy daman magana nakeso muyi da ke.
Toh Faruk kagama sannan sai muyi maganar.
Kanshi sadde k'asa yace wallahi mummy Alhamdulillah daga gida nake.
Komawa tayi tazauna tace nan ma gidan ne ban yarda ba sai ka ci.
Kallon Nasiba yayi da tatsiyaya mashi lemu a cup tamik'o mashi nan ya amsa tare da sakar mata lallausan murmushi itama tamaida mashi da martani.

Kur'ba yayi ya ajiye sannan yaduk'ar da kanshi k'asa yace daman Mummy akan maganar auren Nasiba ne idan anban dama sai insanar da su Dad inyaso cikin satin nan atsaida rana.

Mummy kallon Nasiba tayi nan Nasiba tamik'e cikin jin kunya tawuce sumi sumi tabar wajen tana ji kamar tanutse saboda kunya.

Murmushi Mummy tayi tace haba Faruk wannan ai abun farin ciki ne agaremu ba damuwa kasanar da su Alhaji kawai akowane lokaci mu ai ashirye muke.
Godiya yayi mata tace bakomai Faruk ai mune da godiya dan kai d'in mutum ne wallahi, dan Allah katayamu godiya a wajen Jawahir akan taimakon da tayi mana kaduba kaga yadda tamaido mana gidan da yake mallakinta da dukiya.
Murmushi yayi yace ai cancanta ce tasa haka mummy kuma ku ai bakuda laifi a ciki saisa itama ta ga dacewar maido maku kayanku.
Jinjina kai tayi tace Allah dai yasaka da alkgairi.
Amsawa yayi da Ameen sannan yamik'e yace Mummy bari inwuce.
Tun yanzu? Baka dai ci komai ba.
Allah mummy a k'oshe nake ne.
Toh shikenan Faruk mungode sosai Allah yasaka da alkhairi dan Allah kagaishe min da Hajiya Nuratu kafin ink'ara samun k'arfin jiki inshigo.
Toh Mummy insha Allahu zata ji.


Yana fita tak'wala ma Nasiba kira nan tafito tabishi a wajen mota tasameshi nan sukayi bankwana kasancewar magrib ta yi nan yaimata alk'awalin kiranta

35 / 74