Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
wani yunk'uri ta shak'e mashi wuya da dukkan k'arfinta, k'ok'arin k'wacewa yafara ammah yakasa dan k'arfin ba na mutum d'aya bane, buga table yafara yi dak'arfi sai ga masu kula da ita sun shigo dan dama suna bakin k'ofa nan fa aka fara k'ok'arin k'waceshi, kuka jawahir tadinga yi cikin d'aga murya tana cewa bazan ta'ba bari hakan yafaru ba bazan barka ba barrister, saida kusan maza biyar suka taru sannan suka samu suka 'ban'bare hannunta daga wuyan barrister mubarak tari yafara yi, bugunta suka fara yi a wajen saida suka bugeta sosai har tasuma sannan aka jata aka maidata d'akinta.
Barr Mubarak ya dad'e a wajen tsaye rik'e da wuyanshi yana tari idanuwanshi sunyi jajir kafin daga baya yad'auki takardunshi yafita.
Yana barin nan wani makeken gida yaje a parlorn gidan yasamu su Alhaji Tanimu su ukku zaune suna ganinshi suka fara murmushi wani da yake zaune kusa da Alhaji Tanimu ne yace ya dai barrister muna fata dai angama komai.
Zama yayi tare da tsiyaya wani swan water da yake saman center table yasha saida yashanye kofi guda sannan ya ajiye kofin yace hmm ina fa hakan yasamu yarinyar chan saura kad'an takasheni..
Su duka idanu suka zuba mashi sukace garin ya?
Ajiyar zuciya yasafke yace yarinyar chan ina tunani aljannu gareta.
Dariya Alhaji Tanimu yayi yace muma ai Aljannun kanmu ne akan kud'i haba Barrister ya kamata kayi wani abu man kar fa kamance da mak'udan kud'ad'en da mukayi maka alk'awalin su kaga idan har kataimaka mana tayi signing shikenan zaka iya zare hannunka akan case d'in inyaso ma akasheta babu ruwan wani.
Shuru Barrister Mubarak yayi kamar me nazarin wani abu ya d'auki mintuna sosai yana nazari sai chan yace kubarni da ita na san yadda zanyi tasa hannu yau d'innan zanje wajen likitana yataimaka min da wata allura ce da na caka mata ita zata fita daga hayyacinta na san a lokacin zata amince tayi signing d'in batare da ta saniba.
Su dukansu dariya sukasa sukace lallai barister ashe k'walwarka tana ja sosai.
Dariya shima yayi yace yoh ba dole tajaba ai bazan ta'ba mancewa da rashin mutuncin da Alhaji Muhammad yayi min ba lokacin da nanemi yataimaka min da wasu kud'i zan biya bashi yace min baidasu bayan gabana aka kawo mashi wata leda cike da kud'i sai cewa yayi wai ba na shi bane na ajiya ne aka kawo mashi, saidai dubu d'ari yabani ni da nake neman million guda, koma menene kukasance cikin shiri gobe dan zan kawo maku takardun nan da signing d'in yarinyar chan.
Shewa suka dinga yi a wajen suna cigaba da tattaunawa sun d'au lokaci sosai suna tattaunawa kafin su rabu akan gobe zasu sake had'uwa.
Barr Mubarak bayan ya bar nan kamar yadda yayi alk'awali saida yabiya wajen wani likita amininshi yasamo allurar sannan yawuce gidanshi lokacin da yakoma iyalanshi duk basu nan yana shiga d'akinshi wanka yayi yafito parlor yana magana shi kad'ai yana cewa wato har wannan lokacin su madam basu dawoba su da nace kar suyi marece tsaki yaja tare da zama bisa 3 seater yad'auko remote yana canza channel sallama aka yi aka shigo ciki ciki ya amsa nan wata babbar mata tashigo da tray d'auke da abinci da lemu ta ajiye a gaban Barr Mubarak tace 'Dalla'bai ga abincinka Hajiya tace akawo maka idan ka dawo, tana fad'in haka tatashi cikin sauri tafita tabar d'akin, saida tafita sannan yajuyo yakalli tray d'in, a karo na biyu aka sake sallama matar ce yaga ta dawo kallo d'aya yayi mata yad'auke kai dan shi ya tsani 'yan aiki suna shigo mashi d'aki, zuwa tayi ta ajiye wani jug da tashigo da shi tatsiyaya mashi kunun aya tamik'a mashi tace Alhaji ga shi.
Juyowa yayi a wulak'ance yakalleta yace ni nasaki kizuba min?
Girgiza kai tayi tace a'a.
Toh bar nan wajen
A saman table d'in da yake gabanshi ta ajiye sannan tamik'e tafita.
Tsaki yaja tare da kallon cup d'in ganin had'ed'en lemun kankana ne yasa yad'auka yafara sha dan yana son shi sosai, saida yasha kusan kofi biyu sannan yabarshi.
Bayan magrib yana zaune yafara jin cikinshi ya fara ciwo tun yana d'aukar abun wasa sai gashi ya kwanta har akayi sallar isha'i yana murd'e murd'e matarshi koda tadawo taganshi a wannan halin hankalinta ya tashi sosai dan haka taje tad'auko wayarta dan takira family doctor d'insu tana fita yana kwance yana ta murd'e murd'e sai ganin wata irin mata me mummunan halitta yayi ta bayyana a gabanshi tana tsaye tana kallonshi koda yana cikin halin ciwo saida yatsorata yunk'urawa yayi zai tashi ammah yakasa, murmushi tayi wanda yasa hak'oranta suka bayyana waje,
Cikin zafin ciwo yace wacece ke? Me kikazo yi a nan.
Rikid'a tayi takoma siffar kamannin Jawahir, yunk'urin mik'ewa yayi nan tanuna shi da hannunta sai gashi ya koma ya kwanta a nan take duk kasala tarufeshi.
Zagaye gadon da yake kwance tayi tana dariya saida tayi me isarta sannan tace bazan baka damar magana ba saboda bana buk'atar jin komai daga bakinka tambayar da kayi min itace maganarka ta k'arshe a duniya, kamar yadda nayi alk'awali bazan ta'ba barinka ba bare har kasamu damar cutar da ni dan haka kafin ka kasheni ni zan fara shafe babin rayuwarka, idanu Barr Mubarak yazuba mata yana kallonta ko hannunshi yakasa motsawa, cigaba tayi da cewa kun zalunceni kun cuci abokantaka da kuka yaudari mahaifina kuka kasance me fuska biyu a wajenshi saboda dukiyarshi har saida kukayi silar barinshi duniya sannan wannan bai ishekuba kunaso kushafe duk wani tarihi na rayuwarshi toh inaso kasan cewa nasan lokacin da kaje wajen likita ka amso allurar nan nikuma nayi amfani da damata nakawo maka lemu me guba kasha na tabbata ko minti goma bazaka k'araba yanzu zaka mutu, zaka rigani zuwa inda kakeso kakaini dan haka na barka lafiya.....k'arar k'ofar da tajine alamun za'a bud'e yasa tayi saurin 'bacewa.
Barr Mubarak hawaye ne suka fara fita daga idanunshi yana kallon matarshi tana ta faman yi mashi sannu tana shaida mashi likita yana nan tafe zai dubashi, a lokacin ne yafara yunk'urin amai ammah yakasa tashi nan inda yake kwance yafara aman jini yana jin ciwon cikin yana k'ara tsananta a nan take yamutu kafin isowar likita dan lokacin da ya iso tuni ya bar duniya.
Hankalin mutane ya tashi sosai akan mutuwar Barr Mubarak musamman ma da likita yatabbatar da guba aka bashi yaci saidai anduba ba'a ga alamun ya ci wani abu me guba ba acikin abincin da aka kawo mashi ba nan aka rasa inda yasamo guba yaci.
Mutuwarshi tasa su Alhaji Tanimu suka shiga damuwa sosai inda suka fara tunanin jawahir tana da hannu akan mutuwarshi sune suka fara yad'a abun nan aka d'auka ana cewa itace tayi layar zana daga gidan yari taje takasheshi saidai hakan bai zama k'wak'warar sheda ba saidai duk da haka ana zarginta ammah babu wanda zai iya bada shedar cewa itace tayi kisan.
Mutuwarshi ta tada hankalin Alhaji Tanimu sosai saboda haka ne asatin da yamutu yatattara yagudu Europe dan ya tsorata sosai akan kisan da aka yi ma nakusa da shi......
Jawahir na kawowa nan juyowa tayi takalli Barr Faruk tace wannan dalilin ne yasa ake cewa na kashe lauyana me son kareni saidai mutane basu san cewa shi d'in me fuska biyu ne ni a wajena fuskar azzalumi gareshi,,, hawaye ne tafara yi nan takoma wajen zamanta tazauna.
Barr Faruk kasa cewa komai yayi ganin yadda take hawaye yasa yaje yalek'a waje yace ma ma'aikacin gidan yana buk'atar ruwan sha nan yatafi dan ya samo mashi.
Dawowa yayi yakalleta yace Tabbas Alhaji Tanimu ya kasance shed'ani ne idan har abinda kika fad'a akanshi gaskiya ne, ammah shi Barr Muhsin fa, ya akayi yatsaya maki kuma kina nufin shima yana da hannu a ciki saisa kika kasheshi?
Shuru tayi tazuba ma gefe d'aya idanu tana kallo, daidai lokacin ma'aikacin gidan yakawo mashi purewater me sanyi saman tray yad'auro cup a sama, amsa Barr Faruk yayi yai mashi godiya bayan ya fita ya basu waje ne yatsiyaya a cup d'in yamik'a ma jawahir.
Tsayawa tayi tana
Kallon cup d'in sai kuma chan ta amsa tare da yin murmushi tace nagode, nan takafa cup d'in a bakinta saida tashanye sannan tatsaya tana kallon cup d'in tana murmushi.
Shima kallonta yake ahankali yace ya burgeki ne cup d'in?
Girgiza kai tayi tare da mik'a mashi bayan ya amsa ne tace wannan cup d'in ankawo shi ne saboda kai ne zaka sha ruwan kuma kai mutum ne me daraja a wajensu mu ko k'ask'antattu ne a ko'ina.
Tarar numfashinta yayi yace a'a jawahir kidaina cewa haka kema mutum ce me daraja kuma insha Allahu zaki bar gidan nan rayuwarki zata koma irin wadda kikayi a da zaki cigaba da kasancewa a cikin farin ciki komai zai zama tarihi.
Murmushi tayi har saida hak'oranta suka bayyana sannan tagirgiza kai tace kaine kake tunanin haka barrister.
Shima murmushin yayi sannan yace ina saurarenki ya kamata ki ida sanar da ni abinda yafaru bayan mutuwar Barr Mubarak.
Ajiyar zuciya tasafke sannan tacigaba da cewa...........
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 10*
....Har lokacin zaman mu kotu yayi mukazo babu lauyan da zai tsaya min ana ta surutu akan na kashe lauyana, duk yadda akaso in amsa laifin kisan nan ammah nak'i amsawa saboda haka ne alk'ali yasake d'aga shara'ar nan da wata ukku masu zuwa inda yabada umurni da acigaba da sani aiki me tsanani a gidan yari.
Duk tsawon lokacin da nad'auka a gidan kaso muna zaune d'aki d'aya da wad'annan matan biyu watau Raliya da Rufaida har lokacin magana bata ta'ba had'ani da su ba koda daman suna nuna min tsana duk lokacin da za'a kawo mana abinci saidai sucinye har nawa, ahaka wata rana mukayi fad'a akan abincina da aka kawo min koda wannan fad'an ma Ammi ce sukayi da ita a lokacin tana jikina wanda yakaisu har suka dakeni a k'arshe ma suka yanke shawarar kasheni a cikin dare, ita kuma Ammi ganin haka yasa takashesu da daren dasafe aka tashi basu da rai,,wannan dalilin ne yasa aka maido ni wannan d'akin ni kad'ai ina cigaba da rayuwata, ana azabtar da ni aka hana adinga fita da ni aiki saidai batare da sanin shugaban gidan ba suke fita da ni suna sakani dan a ganinsu bazasu iya barina incigaba da zama haka ba kamar anmin gata ne.
Ana saura wata d'aya musake komawa kotu a lokacin ne Barr Muhsin yazo a matsayin lauyan da zai kareni ko kad'an banyi mamaki da ganinshi ba dan daman na sanshi a matsayinshi na lauyan mahaifina wanda yasan duk wani sirrin duniyarshi ta ciki da waje, tunda yazo ban ta'ba ce mashi uffan ba ya yi juyin duniya inyi mashi magana ammah na k'i har lokacin komawarmu kotu yayi muka koma haka aka gabatar da shara'a suka fafata shida Barr MB, yana k'ok'arin kareni saidai kawai inbisu da idanu har akayi aka gama inda aka k'ara d'aga shara'ar tamu zuwa wasu watanni biyu masu zuwa, nan aka maidoni gidan yari da alokacin yazame min gida idan da sabo na saba saidai duk lokacin da za'a fita da ni zuwa kotu ina jin wani irin yanayi a duk lokacin da muka fara tafiya cikin mota ina kallon mutane masu wucewa.
Haka dai Barr Muhsin yayi ta bina ammah bai samu yadda yakeso ba har aka sake wani zaman da yakasance na biyun k'arshe dan har lokacin baida k'wak'warar hujjar da zai kareni, a nan ma sake d'aga shara'ar akayi zuwa wasu watannin biyu masu zuwa a lokacin ne Barr Muhsin da aka maido ni gidan yari yazo yasameni kallona yake cike da mamaki yace Jawahir narasa meyasa kwatakwata kin kasa sakin jiki da ni nifa ba da niyar cutarwa nazo makiba taimakonki nakeson yi ammah kin kasa gane haka.
Murmushi nayi nace gane hakan abu ne mewuya domin mutane abun tsoro ne.
A cikin idanunshi naga mamaki k'arara koda mamakin bai nuna akan maganata ta farko da nayi agareshi ba saidai hakan ya faru ne saboda maganar da nayi bai zaci hakan ba, jinjina kai yayi yace hakane ammah jawahir ai kin sanni kinsan bazan zo da niyar cutar da ke ba.
Matsowa tayi kusa da shi sannan ahankali tace cutarwa ta nawa kuma? Shin ka mance lokacin da katsaya ma Abba akan kunaso kuk'wace kamfani na ta k'arfin tsiya? Ko baku bane kuka bugo jabun takardu akan kamfanin dan kawai kuga kun rabamu da su, hatta gidan Ammina kaine katsaya ma Abba wajen ganin ya k'waceshi ta karfin tsiya, idan ko haka ne cutarwa ta nawa zakayi min!....
Da mamaki yake kallonta har takai aya sannan yace jawahir duk wa yafad'a miki wannan? Wallahi ba gaskiya bane ko kad'an ban ta'ba tunanin cutar da ku ba.
Murmushi jawahir tayi a karo na biyu sannan tace ba ma wannan kad'ai ba hatta abinda kake da niyar aikatawa na sani.
Kasa cemata komai yayi yana binta da kallo kafin daga bisani yawuce yatafi.
Tun wannan zuwan bai sake dawowa ba sai bayan kwana ukku, koda yazo aka fiddo mashi ita dan sugana kallonshi tayi tace ashe zaka k'ara dawowa da ace zaka taimaka ma kanka da ka hak'ura da zuwa wajena dan bana buk'atar taimakonka.
Cikin ran Barr Muhsin yace wannan na rasa wace irin yarinya ce anya zata amince musamu abinda mukeso cikin ruwan sanyi? Chan kuma a fili yace zuwana shine daidai idan har ban taimaka makiba tabbas zan kasance acikin masu butulci mutanen gari zasu zageni a matsayina na lauyan mahaifinki ace na kasa kareki.
Cikin d'aga murya tace kaje kanuna tausayawarka ga wasu ba dai ga ni ba domin ni bana buk'atar hakan.
Jinjina kai yayi cike da mamakin maganganunta cikin ranshi yace lallai yarinyar nan da ace babu abinda nake nema a gareta da bazan ta'ba tsayawa tana min wannan wulak'ancin ba....
Jawahir tana zuwa nan a labarinta kallon Barr Faruk tayi da har lokacin yake tsaye ya tsareta da idanu d'an guntun murmushi tayi tace Barr muhsin tun bayan rasuwar Ammina baya k'asar zan iya cewa sai ma bayan mutuwar Barr Mubarak ne sannan yadawo kuma su Alh Tanimu ne suka turoshi ko ma ince Alhaji Tanimu ne yahad'a shi da sauran mutanen da sukeso suga sun mallake dukiyata koda yagane nice sukeson yin aiki a kaina ya yi farin ciki sosai domin shima akwai abinda yake buk'ata a wajena.
Wannan abun da mukayi da Barr Muhsin yasa sai bayan sati d'aya yasake dawowa bayan anfiddoni yad'auko wani Atm yanuna min yace wannan mallakin mahaifinkine yana da kud'ad'e a cikinshi kuma gab ake da arufe account d'in saboda ya kwana biyu ba'ayi amfani da shi ba kuma ba kowane yasan yana da wannan account d'inba tunda ya fi amfani da wanchan gudan, wannan ya bud'e shi ne saboda masu biyanshi bashi idan ya basu koda duk yarjejeniyar da suke akan bada bashi yana sanar da ni a matsayina na lauyanshi dan mahaifinki baya abu sai ya samu mesheda, wannan dalilin ne yasa nasan komai akan wannan Atm d'in da sabon account d'inshi.
Ta'be baki tayi tace nasan haka saidai bakasan Pin d'in da zaka ciro kud'in ba wannan dalilin ne yasa kasanar da ni?
Yanayin yadda take magana har mamaki take bashi dan tana da saurin fahimtar abu saidai bai nuna mata mamakinshi ba yace hakane inda zaki amince kisanar da ni da naje ancire kud'ad'en kafin arufe account d'in.
Kallonshi tayi a wulak'ance tace wannan ne bazai yuwu ba Barrister zanfi farin ciki ace sun rufe account d'in da dai ace kaine zaka ciro kud'in nan dan nasan kai zasu amfana.
Maganata ta 'bata mashi rai sosai ahaka yatafi yabarni.
Ya fad'a ma abokan nashi na k'i amincewa dan ina da wayo sosai koda k'arancin shekaru na, wanda yake jagoran su bayan tafiyar Alhaji Tanimu ne yazauna yatsara masu wata dubara inda suka samu wani k'wararre a wajen rubutu wanda yake da baiwa duk rubutun da yagani zai iya yin irinshi haka suka bashi irin rubutun mahaifina yayi masu, yarjejeniya ce suka rubuta akan wannan filayen da suke kawo min files d'insu insa hannu nak'i, sun kashe kud'ad'e sosai akan aikin inda Barr Muhsin yataimaka masu suka zauna har kotu akan cewa mahaifina ya siyar ma da Alhaji Tanimu filin kasancewar ansan Barr Muhsin shine lauyan mahaifina kuma ga sheda angani ta rubutu da komai yasa aka basu filayen sunyi farin ciki sosai da wannan nasarar da suka samu nan suka sanar da Alhaji Tanimu ta waya shi kuma yabasu dama da su saida ma gwamnati filayen biyu daman itace tabuk'aci hakan saboda filayen yana da girma sosai dan duk cikin filayen mahaifina babu me girmansu nan aka basu mak'udan kud'i sukaje suka raba a tsakaninsu.
Dalilin mutuwar Barr Muhsin kuma ganin bai ci nasarar samun Pin d'in a wajena ba yasa yashirya yaje wajen boka yai mashi bayanin duk abinda yakeso nan bokan yabashi wani kwalli yace da ya shafa yazo wajena duk abinda yakeso zanyi mashi nan yayi ta murna har yayanke shawarar hatta babban account d'in Abbu sai yasa nayi mashi signing ya fitar da kud'i, toh akan hanyar shine tadawowa Ammi takasheshi acikin motarshi aka tsinci gawarshi, shine dalilin da yasa ake cewa shima ni nakasheshi dan kawai ya tsaya min.....tana zuwa nan a labarin sai ganin wata irin guguwa sukayi me k'arfi tana shigowa cikin d'an kurkukun d'akin ta k'aramar tagar nan cikin sauri jawahir tamik'e tatsaya gaban Barr Faruk, su dukansu idanu suka zuba ma guguwar har tagama shigowa nan tahad'e waje guda sai ga wannan tsohuwar ta bayyana, tana bayyana tabushe da dariya.
Barr Faruk da mamaki yake kallonta tabbas itace wannan tsohuwar da yata'ba gani kuma itace yake yawan gani a mafarkin shi, muryar jawahir ce yaji ta ce Ammi menene dalilinki na zuwa nan a wannan lokacin?
Ci gaba tayi da dariyarta marar dad'in saurare me kama da haniniyar