Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
kai banza ne wanene yafad'a maka dagaske ne kawai dai so take taga ta kasheni saisa tayi wannan k'aryar ni bansan komai ba akan mutuwar d'an uwana, taya ma zan iya kashe shak'ik'ina bayan halarcin da yayi min a rayuwa idan har akace na kasheshi toh tabbas na zama butulu.
Cikin fushi yace toh shikenan saidai ni kuma ya zama dole inbi ran d'an uwana dan sai na d'auki *FANSAR RAI* kamar yadda takasheshi itama zan kasheta ban damu da aljannun k'aryarta ba!
Abba saurin girgiza kai yayi yace a'a Umar kar kayi haka kabar ma malam komai shi ya san yadda zaiyi da ita.
Malam zuwa yayi yabud'e jakkarshi yad'auko wata kwalba da wani abu cikin wata 'yar roba yanufo wajen da jawahir take a d'aure, bud'e idanunta tayi dakyar tana kallonsu a galabaice ahankali tabud'e baki tace me yasa zakuyi min haka, Abba nice dan Allah kukwance ni ummah, Abba murmushi yayi yace munafuka ai yau kema dole kimutu kamar yadda kikaso kikashe mu.
Ahankali tace kisa kuma? Da yaushe nace zan kasheku? Kallon umar tayi da yake ta huci tace yaya umar dan Allah kace susakeni kar sukasheni.
Tsanarta ce tagani k'arara a idanunshi ranshi a 'bace yace idan har su basu kasheki ba ni zan kasheki dan d'aukar ma d'an uwana fansa tabbas ke butulu ce jawahir duk halarcin da nayi maki a rayuwa baki ganiba.
Hawaye ne suka gangaro mata tace Yaya Umar bai dace kace hakaba wannan ba shine butulci ba, shin laifi ne dan na d'auki fansar ran iyayena?
Tsawa yakwatsa mata yace ya isheki haka! wanene yakashe iyayen naki kina nufin Aliyu?
Juyawa tayi takalli malam da yaruntse idanunshi yadage yana ta karanto wasu d'alasimai a cikin wani abu me kamar mai cikin roba, wata irin razanannar k'ara tasaki nan kamanninta suka fara sauyawa k'iba tafara k'arawa lokaci guda sukaga ta rikid'e ta koma wani k'aton biri malam saurin bud'e idanunshi yayi kafin yayi yunk'urin yin wani abu tuni ta fisge igiyar tsafin da yad'aureta da ita wani irin tartsatsin wuta yatashi tasa hannu takare fuskarta.
Ummah saman kujera tayi saurin fad'awa tare da fasa k'ara tace mun shiga ukku wayyo jama'a kutaimaka min, Abba ko saurin ja da baya yayi yatsaya bayan Umar da yake rik'e sa wuk'a yana nunata alamun idan har ta iso zai caka mata, bushewa tayi da wata irin mahaukaciyar dariya sannan tace bazan ta'ba fasa abinda nayi niya ba.
'Debo maganin malam yayi dasauri zai watsa matayi tayi saurin gocewa ya sake d'ebowa a karo na biyu nan ma tagoce, zai sake d'ebowa tasa dogon hannunta tak'wa'be robar nan yazube.
Girgiza tayi tadawo siffar Khausar Ammin jawahir gashin nan nata ya mimmik'e saman iska juyawa tayi takalli Abba nan tanuna shi da hannunta sai gashi ya yi saman iska, wuntsila wuntsila yafara yi da k'afafu saitin da fanka take wanawa tanufa da shi nan yafara ihu, cikin sauri malam yanufi wajen 'yar jakkarshi nan tayi saurin juyawa tanuna jakkar da yatsa sai ga hayak'i yana fita cikinta k'ara malam yasaki cikin sauri yad'auko jakkarshi da mamaki yake kallon khausar da tunda yake itace aljanar da tata'ba ja da shi ganin yadda hayak'i yake fita daga cikin jakkarshi yasa yayi layar zana ya'bace cikin sauri dan kar ta'ba mata tsafi.
Umar na ganin haka yayi sauri yanufi inda mahaifinshi yake kafin ya isa gashin khausar wani siriri guda ya shak'o wuyan Alhaji Mu'azu sai gashi a jikin fanka ta d'aureshi, ummah saurin mik'ewa tayi takoma bayan kujera ta'boye.
Umar saita khausar yayi da wuk'ar hannunshi cikin sauri yanufo inda take zai caka mata hannunta tanuna shi da shi sai ga wani irin haske ya fito yanufi wajenshi sakin wuk'ar hannunshi yayi yasa hannuwanshi duka biyun yashak'e wuyanshi karkata kanta tayi tana k'yalk'yala dariya nan shima yakarkata kanshi yana so yajanye hannunshi daga wuyanshi ammah ya kasa saboda tsananin mak'arar da tasa yayi, chan sai tayi wurgi da shi yafad'a k'asa yana nishi ummah da take tsaye bayan kujera tana kuka cikin sauri ta iso wajenshi tana zuwa tarik'eshi tana cigaba da kuka.
Khausar kallon Abba tayi da yake saman iska saitin fanka nan wani haske yafito daga idanunta sai ga gashinta ya sargafe akan fankar k'ara Abba yafara yi yana neman agaji, dariya tacigaba da k'yalk'yalawa tace mu'azu nice ajalinka kamar yadda karaba ni da mijina da rayuwarmu har kanaso kaga bayan 'yata a yau buri na zai cika zan kasheka kaima kamar yadda nakashe sauran mugayen abokanka dan haka dak'ik'un mutuwarka sun kusa cika, bud'e baki yayi a galabaice yana so yayi magana ammah ya kasa sai nishi da yakeyi sama sama duk jijiyoyin kanshi sun mik'e, idanuwanshi sunyo waje, ja tad'anyi da baya nan fanka tacigaba da juyawa da Abba yana ta wuntsila k'afafu saboda tsananin azaba har wuyanshi yakare ranshi yarabu da jikinshi.
Ummah ko tana zaune a gaban idanunta Abba yamutu kuka kawai takeyi tana kiran sunan Alhaji.
Faruk hankalinshi yana fara dawowa jikinshi ganin yadda tayi ma mahaifinshi yasa yasake yunk'urin mik'ewa dak'yar yajawo wuk'ar yanufi wajenta zai caka mata a karo na biyu, juyowa tayi tanuna shi da hannunta sai ga wani haske ya bayyana me kama da shocking yana shiga jikin umar nan yafara k'ara, murmushi tayi tace na so in k'yaleka ammah ka nema ma kanka mutuwa dan haka dole kaima kamutu, fad'uwa yayi k'asa yana tirje tirje
Ummah mik'ewa tayi dak'yar tana kuka tafara takowa muryarta tana shak'ewa tana kiran sunan umar chan sai tayanke jiki tafad'i k'asa.
Nuna Abba tayi da hannu sai gashi ya fad'o k'asa a mace, ja tayi da baya tare da tsagaitawa daga dariyar da take nan wani haske yafara fita daga jikinta sai ga suffar jawahir kamanninta ya dawo saurin bud'e idanunta tayi, akan Abba tasafkesu da yake kwance k'asa abinda yafaru ne yafara dawo mata a k'walwa har zata nufi inda Alhaji Mu'azu yake kamar ance tajuya tana waigawa sai ganin umar tayi kwance yana ta shure shure.
Cikin sauri ta isa wajenshi jikinta yana rawa ta tallabo kanshi tad'aura saman cinyarta tare da fashewa da kuka tace Yaya Umar dan Allah katashi muje asibiti, kallonta yake yana motsa baki yana so yayi magana ammah ya kasa, ganin haka yasa jawahir tak'ara sautin kukanta tana cigaba da kallon masoyin nata, chan taji muryarshi chan k'asa a hankali ya ce na tsaneki jawahir, tsagaitawa tayi daga kukan da take cike da mamaki take kallonshi tace Yaya umar meyasa zaka tsaneni ba laifina bane.
Juyar da kanshi yayi yana kallon ceiling ahankali yake motsa baki kamar me karanta wani abu chan kuma sai taga ya ja numfashi da k'arfi ya rufe idanunshi. girgiza shi tafara yi tana cewa dan Allah Yaya Umar katashi kar katafi kabarni, duk yadda take girgizashi ammah ko motsi bayayi ganin haka yasa tafasa wata irin k'ara wadda tasa gabad'aya gidan saida ya amsa, rungumeshi tayi jikinta tana cigaba da kuka tana cewa dan Allah katashi ina sonka ina son cigaba da rayuwa da kai, Yaya Umar kaine gatana idan kabarni ban san halin da zan shiga ba, kaga taso muje ga abinci chan na girka inzuba maka kaci yau ranar farin ciki ce agaremu ranar zagayowar shekarar aurenmu ina sonka sosai Yaya Umar, sumbatu tadinga yi kamar zararra, ganin har lokacin bai motsa ba yasa tasake fasa wata k'ara tace Ammi meyasa kikayi min haka kin rabani da rabin rai na wallahi na tsaneki bana k'aunarki ke azzaluma ce.
Bata rufe bakinta ba sai ga Ammi ta bayyana cikin wata irin mummunan halitta zaune saman iska ta kishingid'a kamar wadda take zaune saman kujera, cikin muryarta marar dad'in saurare tace shin laifi ne dan na taimaka maki na rabaki da wanda yayi yunk'urin kasheki?
Cikin kuka jawahir tace k'arya kike Umar bai chan chanci hakaba bazai ta'ba kasheni ba tabbas a yanzu na yadda da maganarki da kika ta'ba cewa sai kin rabani da shi toh a yau kin rabani da shi hankalinki ya kwanta saidai ina so kisani na tsaneki fiye da yadda natsani su Abba a rayuwata.
Bushewa tayi da wata irin mahaukaciyar dariya tace yau kece kike ik'irarin cewa kin tsani mahaifiyarki wadda tafi kowa k'aunarki saboda soyayyar wani? Matsowa tafara yi kusa da jawahir
Janye Umar tayi cikin sauri tare da d'auko wuk'ar da ke gefenta tamik'e tsaye tace eh na fad'a na tsaneki kika saki kika matso kusa da ni sai na kasheki.
Rage sautin dariyarta tayi tace daman ni ai matatta ce banda sauran rayuwa saidai ina so kijanye kalmar tsanar da kikayi min, kiduba kiga bayanki babban mak'iyinki ne kwance a mace, runtse idanu jawahir tayi hawaye suna zubo mata, ta'ba hannu aljanar tayi sai ga hotuna guda ukku sun bayyana a hannunta ajiyesu tayi a k'asa gaban jawaahir tace duba hotunan nan na san zakiyi farin ciki idan kika ga guda daga cikinsu, ahankali tabud'e idanuwanta da suka fara kumbura tasafkesu akan hotunan guda na Abba ne sai na Yaya Umar a kan na k'arshen tatsaida idanunta tare da fashewa da kuka hoton ta ne ita da iyayenta suna rungume da ita, saurin duk'awa tayi tad'auki hotonsu ita da iyayenta sannan tamaida kallonta ga Aljanar d'an guntun murmushi tayi sai kuma tahad'e fuska lokaci guda sannan tace na tsaneki ke ba Ammina bace.
Bushewa tayi da dariya a karo na ba adadi saida tayi me isarta sannan tace kidaina furta kalmar tsana agareni ya zama dole kidinga min biyayya.
Cikin d'aga murya jawahir tace baza'ayi maki biyayya ba daga yanzu ina so kifita daga rayuwata babu ke babu ni idan har kika sake shiga rayuwata zan kasheki!
Wata irin k'ara aljanar tasaki tace wannan kuskure ne kike aikatawa jawahir.
A fusace jawahir tanufi wajenta da gudu rik'e da wannan wuk'ar tun kan ta isa Aljanar tanuna ta da yatsanta me kama da sanda sai ga wata iska ta taso tana zuwa sai d'aukar jawahir tayi tai wurgi da ita sai gata chan gefe ta fad'a ta baya dak'arfi.
Kwance tayi k'asa tana jin wani irin zafi a bayanta, chan kuma tayi yunk'uri tatashi zaune.
Matsowa Aljanar tayi kusa da ita tamik'a mata hannu alamun tamik'o hannunta.
Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanun jawahir ba tare da ta mik'a hannunta ba tace na tsaneki Ammi kikasheni kawai kamar yadda kika kashe Yaya Umar inko baki kasheni ba ni zan ga bayanki bana k'aunarki.
Muryar Aljanar ce tafara fita bibiyu tace wannan kuskure ne kike aikatawa na gargad'eki akan kidaina cewa kin tsaneni ammah kin k'i to dasannu zani azabtar da ke yadda baki tunani kisaurareni.
Alhaji Tanimu koda ya iso gidan a k'ofar da zata sadaka da cikin gidan yatsaya yakira wayar Alhaji Mu'azu ammah har ta k'arashi ringing bai d'agaba kusan missed call biyar yayi mashi yana shirin yin na shidda ne yajiyo anfasa k'ara a cikin gidan dan haka cikin sauri yanifi cikin gidan yana shiga yai sallama yaji shuru a parlor yafara jiyo kuka ahankali yana tashi dan haka yanufi parlorn yana d'aga labule da gawar Alhaji Mu'azu yafara cin karo.....
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 9*
Cikin sauri yashiga parlorn yanufi wajen gawar tashi yatsaya cike da firgita yace Alhaji Mu'azu lafiya? Kwanciyar me kakeyi nan ko bakada lafiya ne? Jin sautin kukan jawahir yasa yajuya sai a lokacin yakula da ummah da ke shimfid'e k'asa itama babu alamun numfashi atare da ita gefe guda kuma jawahir ce wajen gawar Umar tana jijjigashi tana kuka, tsorata yayi sosai cikin sauri ya isa wajen jawahir yana zuwa akid'ime yace ke me yasamesu ya akayi suke a nan ba dai mutuwa sukayi ba dai ko?
Ko d'agowa batayi takalleshi ba bare yasa ran samun amsar tambayarshi ganin haka yasa yace tambayarki nake me yafaru da su?
Nan ma shuru wuk'ar da yagani gefenta ne yasa a fusace yace bazaki bani amsar tambayar da nake maki ba? Sai a lokacin tajuyo takalleshi da rinannun idanuwanta da suka fara firgicewa kallo d'aya tayi mashi tad'auke kai shi kanshi saida yasha jinin jikinshi ammah hakan baisa yayi shuru ba jinjina kai yayi yace wannan mutuwa sukayi kuma nasan kece kika kashesu, mi yasa zaki kashesu? Me suka aikata maki? Wallahi bazan ta'ba barinki ba ya zama dole hukuma tasani kema akasheki.
Mik'ewa tayi tsaye bai ankaraba kawai sai ganinta yayi gabanshi baisan lokacin da ta isoba har saida yad'an tsorata, kallonshi tatsaya yi bata ko k'yaftawa ganin haka yasa yad'an ja da baya dan yanayin kallon da takeyi mashi na tuhuma ne cikin dakewa yace ke lafiya ko nima kasheni zakiyi kamar yadda kika kashe sauran? Wallahi sai na sanar da hukuma.
Sai a lokacin tabud'e baki dak'yar cikin dashewar murya tace Alhaji Tanimu Nepa ka zo ne dan ka amshe sauran dukiyata a wajen Abba ko?
Gabanshi wani irin mummunan fad'uwa yayi dak'yar yahad'iye wani yawu dake mak'ale cikin bakin shi nan yafara inda inda yace ni ni kuma? A'a ni ni ziyara nakawo mashi.
'Dan guntun murmushi tayi tace na san komai,, matsowa tafara yi wajenshi yayi saurin ja dabaya yace k'aryane ni bansan komai ba akan dukiyarki wai ma wacece ke?
Binshi tafara yi yanda cigaba da yin baya baya tace tabbas nasan haka kuma nasan kana da hannu akan mutuwar mahaifina kaima.
Tsorata yayi sosai da jin maganar da tayi cikin ranshi yace wanene yasanar da ita mune muka kashe iyayenta bayan lokacin da mukayi maganar a d'aki muka yita mu takwas ne acikin gidan babu wani mahaluki a ciki toh ammah kuma....muryarta yaji ta ce wannan haka yake na san kana da hannu a ciki.
Hanyar k'ofa yanufa yana cewa a'a bansan komai ba akan mutuwarsu.
Tsaye jawahir tayi tana kallonshi chan sai tafad'a saman kujera tazauna tare da dafe kanta ganin haka yasa yayi saurin juyawa zai bar d'akin sai jin muryarta yayi ta ce idan har kasanar da wani abinda yafaru sai na kasheka!
Da gudu ya ida fita ko motarshi bai tsaya shiga ba dan kar ma ya'bata lokaci yabar gidan.
Wani irin kuka tadinga yi a nan inda take zaune k'arar wayar da taji kusa da itane yasa tajuya sai ganin wayar Umar tayi tana d'aukowa taga recording ne yayi saving cikin sauri takunna tana saurare taji duk abinda yafaru ne akayi recording a tsorace ta ajiye wayar tana tunanin wanene yayi recording d'in......
Faruk yana gama saurare ajiyar zuciya yasafke ahankali yace watau abinda yafaru kenan dukkansu ta kashe har da Umar? Toh ammah banji.....k'arar buga gida yafara jiyowa ana knocking nan yakalli agogo yaga duka k'arfe d'ayan dare cike da mamaki yace to wanene yake buga gida a wannan lokacin ko dai megadi ne
Mik'ewa yayi sai ji yayi andaina bugawa har zai je yabud'e sai kuma yafasa yakoma yazauna.
Dariya ce yafara jiyowa tana tashi daga wajen tagar d'akinshi dan haka yak'ara sautin karatun alk'ur'ani sannan yacigaba da aikinshi har wajen k'arfe biyun dare sannan yakwanta bacci.
Wajen k'arfe sha d'aya yaje gidan kaso yana isa yasamu jawahir tsaye a wajen da tasaba tsayuwa, tsayawa yayi daga bayanta har ya bud'e baki zaiyi magana sai jin muryarta yayi cikin sheshek'ar kuka ta ce ka yi k'ok'ari sosai da har ka iya ku'buta daga hannun Ammin saidai ina baka shawara kacigaba da addu'a dan itace zata cigaba da tseratar da kai daga sharrinta dan daga baya na gane ba taimako kawai Ammi ta ke ba har da zalunci take tunda har ta iya kashe wanda baida hak'k'i acikin mutuwar Abbu.............
A lokacin da nagama sauraren recording d'in na yi mamaki sosai kuma na tabbatar Yaya Umar ne yayi shi tabbas a ranar na san dole sai police sun zo tunda har nayi sakacin barin Alhaji Tanimu a raye yafita saidai ban yi nadamar abinda Ammi ta aikata ba saidai rad'ad'in mutuwar Mijina da nakeji, cikin sauri nad'auko wayar dan inaso tazama sheda akan abinda na aikata dan akasheni nima sai ji nayi an fizge wayar daga hannuna sai gani nayi ta fad'i k'asa safkowa nayi daga saman kujera zan d'auko wayar sai gani nayi anjata tayi hanyar k'ofa tsayawa nayi ina kallonta sai jin muryar Ammi nayi ta ce bazan ta'ba bari kid'auki wayar nan ba babu wanda ya isa yad'auketa har yasaurari abinda yafaru.
Juyawa jawahir tayi tana waige ammah bata gantaba dan haka tafara takawa saida tad'auki diary d'inta da Umar yashigo da shi parlorn, sannan tanufi wajen k'ofar sai wayar tacigaba da tafiya tafita daga cikin d'akin motsin da takeji a bayantane yasa tagane Ammi tana bayanta dan haka tacigaba da tafiya har saida takai wajen wani bokitin k'arfe da tafiddo d'azu zata d'ibi ruwan mopping tagoge kitchen dan a lokacin da akayi abin 'yar aikinsu ta je gidansu zata kwana biyu, rarimo bokitin tayi cikin sauri tajuya daidai lokacin da Ammi take bayyana cikin zafin nama tabuga mata shi a kai, sannan tayi wurgi da shi da sauri tad'auki wayar dagudu tanufi d'akin 'yar aikinsu da bakomai a cikinshi tana shiga tazauna k'asa jikinta yana rawa tabud'e wayar taciro Memory card d'in, dariya tafara ji gabad'aya d'akin yana amsawa da ita cikin wata irin kakkausar murya taji muryar Ammi tana cewa kin aikata kuskure jawahir bazaki ta'ba yin nasara ba akan abinda kike son samu.
Rik'e memory d'in tayi gam a hannunta cikin rawar murya tace k'arya kike Ammi baki isa kihana ni samun abinda nakeso ba, na fad'a maki kifita daga rayuwata bana sonki na tsaneki.
Wata irin k'ara taji anfasa sannan cikin muryar fushi taji Amminta tana cewa ina gargad'inki da furta kalmar tsana agareni jawahir domin hakan zai iya jawo maki shiga cikin wani irin mawuyacin hali a rayuwarki.
Cikin kuka tace taya zan daina tsanarki bayan kinyi amfani da jikina da hannuna wajen kashe mijina? na tsaneki Ammi, tana fad'in haka tahad'e kai da gwiwa tacigaba da rusa kuka.
Bayan fitar Alhaji Tanimu wayarshi yad'auko yakira DPO