Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   67 / 74

198K to 201K   out of 220.3K words

tayi tace na san d'iyata babu abinda tatuna kawai dai soyayyar Faruk ce take d'awainiya da ita saidai Faruk bana tunanin zai cigaba da sonta saboda abinda mahaifinta ya aikata ya kamata kubata shawara tahak'ura da shi.

Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata cikin sauri tajuya tashige d'akinta tamaida tarufe saman gado tafad'a nan tashiga rusa kuka da k'arfi.

Su Yaya Sadiya da Yaya Na'ima sunyi juyin duniya akan tabud'e k'ofar ammah tak'i kan dole suka rabu da ita.


Saida tayi kuka me isarta sannan tayi shuru idanunta duk sun kumbura kanta taji ya fara mata ciwo nan tamaida idanunta taruntse.


Faruk motarshi yashiga yakife kanshi a kan steering yana jin babu dad'i akan abinda yayi ma Nasiba, sun had'a mata tension biyu ga nashi ga na mahaifinta ya san dole ta shiga damuwa sosai ba abinda yafi tada mashi hankali sai fitar da tayi cikin 'bacin rai baisan yanayin da zata isa gida ba, saurin d'ago kai yayi yad'auko wayarshi yakirata ammah har tagama ringing ba'a d'agaba sake kiran yayi nan ma ba'a d'aga ba dan haka yatada motarshi yatafi cikin ranshi yana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya.

Nasiba ko tana kwance lokacin da yayi mata 2 missed tana ji ammah takasa bud'e idanunta taduba me kiran dan gabad'aya taji komai ma ya fita ranta batason jin muryar kowa a yanayin da take ciki.


Bayan kamar minti goma wani kiran yasake shigowa a wayarki tsaki taja tare da bud'e idanunta tajawo wayar zata kashe nan idanunta suka safka ga sunan me kiranta wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tamaida wayar ta aje har tatsinke wani kiran yasake shigowa ji tayi bazata iya k'in d'agawaba dan haka tayi picking tare da mannawa a kunnenta, muryar Faruk taji ya ce please Nasiba kifito gani a waje ina jiranki, ahankali ta amsa da toh sannan takashe wayar.


Su Yaya Sadiya suna zaune sukaga ta fito sanye da hijab, mummy ce tace ina kuma zakije?
Batare da ta juyoba tace ina nan waje sannan cikin sauri tawuce tatafi.

Yaya Na'ima tace oh ni lallai Nasiba soyayya ta rufe mata idanu lallai tana son guy d'innan sosai.

Hmmm kece daman baki saniba ammah Nasiba k'aunar da take ma Faruk ni har mamaki take bani daman zata taimaka tacireshi a ranta dan bana tunanin zai aureta.

Mummy da take saurarensu tace a'a kudaina cewa haka ku dai kutayata da addu'a Allah yaza'ba mata abinda zaifi zama alkhairi.
Su duka suka amsa da Ameen.



Kanta sunkuye a k'asa tafito a harabar gidansu taganshi tsaye a jikin motarshi ammah ko da sau d'aya bata d'ago takalleshi ba har ta iso wajen, shi ko idanu yakafeta da su yana kallon yadda take tafiya a nutse dan Nasiba ba bayaba wajen nutsuwa, har ta iso wajen idanunshi suna a kanta.

Tana zuwa ja tayi tatsaya sai a lokacin tad'ago idanunta da sukayi ja saboda kuka tace gani.
Cikin idanunta yakalle cike da nuna damuwa yace yanzu Hearty duk akaina aka zubar da wad'annan hawayen?.
Harara tawurga mashi tace kaga kafad'a min abinda yakawoka inma biyoni kayi kaimin wani wulak'ancin toh babu damuwa bismillah kayi zan iya jurewa saboda duk abinda yafaru laifina ne nice namallaka zuciyata ga wanda bai damu da ita ba, zan iya hak'ura Faruk ko da ace zan rasa rayuwata bazan sake matsa maka ba domin na san bakada laifi a ciki duk abinda yafaru na san mahaifinane yaja min.

Jikin Faruk sanyi yayi sosai yace Nasiba ko d'aya banzo dan inci mutuncinki ba saidai na zone dan inbaki hak'uri sannan inmaido martabar soyayyata.
Da mamaki take kallonshi tana so tayi magana ammah takasa.

Ganin haka yasa Faruk yayi murmushi yace inbanda abun Nasiba taya za'ayi tayi tunanin Faruk zai iya daina sonta bayan ya riga da ya mallaka mata zuciyarshi, Nasiba ina sonki da zuciya d'aya kamar yadda kike sona wallahi nayi maki hakane dan kema kid'and'ani bak'in cikin da kika d'and'ana min a lokacin da kika nisantar da kanki agareni, bana ji zan iya daina sonki Nasiba domin kece Rayuwata.


Wasu irin hawaye ne suka gangaro a fuskarta muryarta tana rawa tace dagaske kake Faruk? Dagaske kana sona zaka aureni?
'Daga kai yayi yace sosai ma indai ba kece kika daina sona ba, ammah a yanzu haka a shirye nake idan kikace inturo sai inturo ayi maganar aurenmu.
'Daga hannunta tayi sama tace Allah nagode maka da kamaido min masoyina, kallonta tamaida ga Faruk tace wallahi bazan iya daina sonka ba Faruk na riga na gama mallaka maka zuciyata idan nabarka taya zan iya son wani.

Ajiyar zuciya yasafke tare da furta Alhamdulillah na yi farin ciki da jin haka daga gareki Nasiba, nima bazan iya son wata ba dan kin riga kin mamaye gabad'aya zuciyata, yanzu dai ina fatan za'a yafe min sannan acigaba da bani kulawa kamar da, komai yawuce mucigaba da nuna ma juna soyayya har zuwa aurenmu.

Murmushi tayi cikin jin dad'in maganarshi tace insha Allahu Faruk na yi maka alk'awalin haka zan cigaba da baka kulawa har k'arshen rayuwata wallahi bakaji farin cikin da kasaka ni ba a yau ji nake kamar a mafarki kadawo gareni.

Su duka dariya sukayi Faruk yace duk farin cikin da zaki shiga na fiki Nasiba yanzu dai kiyi min iso wajen Mummy inshiga mugaisa yau dai zan cire kunya in nemi aurenki dakaina inyaso idan nakoma gida sai insanar da su Dad su kuma su ida nasu.

Wayyoo kar kuso kuga farin ciki wajen Nasiba rasa inda zata sa kanta tayi, haka tanufi hanyar cikin gida tana shiga da gudu ta isa parlor tana k'wala ma Mummy kira, su duka suka d'ago suna kallonta.
Kusa da mummy tazauna cike da farin ciki tace Mummy Faruk ne yazo ya ce zai shigo yanzu kugaisa.

Su duka farin ciki suka nuna nan Mummy tace taje tace yashigo.
Mik'ewa tayi tafita cikin sauri suka bita da idanu, mummy tace kungani ko ai nasan suna k'aunar junansu sosai shima bazai iya barinta ba sai ya biyota.

Su Aunty Sadiya sukace lallai kam ga alama nan mungani.


Tana fita tasanar da shi sak'on Mummy sannan tafad'a mashi batada lafiya, a tare suka jero suka shigo gidan bakinshi d'auke da sallama yashiga parlorn suka amsa mashi har zai zauna a k'asa Mummy tace a'a kar yasaki yazauna yahau kujera dan haka yazauna saman kujera d'an zamowa yayi yagaisheta ta amsa nan yayi mata ya jiki sannan suka gaisa da su Yaya Sadiya da suke zaune gefenta.

Nasiba ko baki k'in rufuwa yayi haka tafita tafara had'a mashi kayan motsa baki.

Mummy ce cikin k'arfin hali tace dan Allah Faruk kayi hak'uri da abinda yafaru wallahi ba da saninmu bane Alhaji yake aikata wad'annan mugayen halayyar daga ni har 'ya'yana babu wanda yasan haka sai daga baya ashe su ne suka saceka dan Allah kayi hak'uri kar kadubemu da laifin da bamu muka aikata ba.

'Dago kai yayi yakalleta cike da girmamawa yace kod'aya Mummy bana kalkonku da laifin da ba naku bane ai laifin wani baya ta'ba shafar wani nima kaina banyi hakan dan in tozartasu ba saidai nayi ne dan intseratar da yarinyar da aka zalunta sannan daga baya ake shirin ganin anrabata da rayuwarta.

Mummy tace hakane na san haka Faruk wannan dalilin ne yasa na k'ara son Nasiba takasance mata ga miji irinka domin ka cancanci asoka ko dan saboda gaskiyarka.

Su yaya Sadiya sukace hakane muma muna k'ara bada hak'uri Faruk.
Murmushin jin dad'i yayi yace bakomai nagode sosai, daidai lokacin Nasiba tashigo d'auke da k'aton tray ta ajiye gabanshi nan duk suka mik'e zasu bar wajen yace Mummy daman magana nakeso muyi da ke.
Toh Faruk kagama sannan sai muyi maganar.
Kanshi sadde k'asa yace wallahi mummy Alhamdulillah daga gida nake.
Komawa tayi tazauna tace nan ma gidan ne ban yarda ba sai ka ci.
Kallon Nasiba yayi da tatsiyaya mashi lemu a cup tamik'o mashi nan ya amsa tare da sakar mata lallausan murmushi itama tamaida mashi da martani.

Kur'ba yayi ya ajiye sannan yaduk'ar da kanshi k'asa yace daman Mummy akan maganar auren Nasiba ne idan anban dama sai insanar da su Dad inyaso cikin satin nan atsaida rana.

Mummy kallon Nasiba tayi nan Nasiba tamik'e cikin jin kunya tawuce sumi sumi tabar wajen tana ji kamar tanutse saboda kunya.

Murmushi Mummy tayi tace haba Faruk wannan ai abun farin ciki ne agaremu ba damuwa kasanar da su Alhaji kawai akowane lokaci mu ai ashirye muke.
Godiya yayi mata tace bakomai Faruk ai mune da godiya dan kai d'in mutum ne wallahi, dan Allah katayamu godiya a wajen Jawahir akan taimakon da tayi mana kaduba kaga yadda tamaido mana gidan da yake mallakinta da dukiya.
Murmushi yayi yace ai cancanta ce tasa haka mummy kuma ku ai bakuda laifi a ciki saisa itama ta ga dacewar maido maku kayanku.
Jinjina kai tayi tace Allah dai yasaka da alkgairi.
Amsawa yayi da Ameen sannan yamik'e yace Mummy bari inwuce.
Tun yanzu? Baka dai ci komai ba.
Allah mummy a k'oshe nake ne.
Toh shikenan Faruk mungode sosai Allah yasaka da alkhairi dan Allah kagaishe min da Hajiya Nuratu kafin ink'ara samun k'arfin jiki inshigo.
Toh Mummy insha Allahu zata ji.


Yana fita tak'wala ma Nasiba kira nan tafito tabishi a wajen mota tasameshi nan sukayi bankwana kasancewar magrib ta yi nan yaimata alk'awalin kiranta da dare.
Haka suka rabu kowa zuciyarshi fal da farin ciki........









_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 24*

A ranar farin ciki ne fal acikin ran Faruk da dare tunda suka zauna yin dinner Mom da Dad suna lura da shi da bakinshi yak'i rufuwa saboda farin ciki, su dukansu shuru sukayi suna jira suji ya fad'a masu dalilin farin cikin da yake yi.

Bayan sun gama dinner ne yakalli iyayen nashi yace Dad Mom daman akwai maganar da nakeso muyi da ku.
Su duka sukace toh muna saurarenka.
Sosa kai yayi cikin jin kunya sannan yace daman Mummynsu Nasiba ce tace inturo ayi maganar aurenmu.

Dad kallon Mom yayi takalleshi suka bushe da dariya yace Daman Nuratu ban fad'a makiba kurabu da shi dakanshi zai koma sushirya kansu.
Murmushi Mom tayi tace ai gashinan yanzun na gani daman ban tsaya 'bata lokacina ba wajen yi mashi fad'a.
Toh ai yanzu gashinan dai kin gani dan nasan wannan soyayyar tasu ta riga ta gama bin jinin jikinsu dan ma dai d'an nan naki ya cika taurin kai, ammah dai yanzu shikenan Faruk fad'i yaushe kakeso aje nema maka auren?

'Dago kai yayi cikin jin kunya yace ni Dad?
Uhm hum muna saurarenka.
Duk'ar da kanshi yayi ahankali yace cikin satin nan.
Su dukansu sunji dad'in hakan da yace sukace toh shikenan babu damuwa insha Allah nan da kwana biyu zasu tura a tsaida ranar aure kawai.
Cike da farin ciki yace nagode sosai Mom and Dad Allah yasaka da alkhairi, Allah yak'ara girma.
Sukace Ameen.
A karo na biyu suka tambayeshi ko wata nawa yakeso asa bikkin.
Mik'ewa yayi tsaye saida yafara tafiya sannan yace kar yawuce wata biyu please,,, yana fad'in haka yawuce cikin sauri yanufi part d'inshi, muryar Dad ce yajiyo yana cewa kar kasamu damuwa yadda kakeso haka za'ayi Son.

Yana shiga d'akinshi wanka yayi yai shirin kwanciya sannan yakira Nasiba a waya da itama tun bayan tafiyarshi bakinta yak'i rufuwa saboda farin ciki nan hankalin mahaifiyarta da 'yan uwanta yakwanta dan a yanzu sun gane duk Faruk ne dalilin damuwarta ba wai rashin mahaifinsu kawai ba.


Hira suka sha sosai a waya a nan ne yake sanar da ita yadda sukayi da su Dad nan itama tayi ta murna, soyayya suka sha sosai sai da dare yaraba tsaka sannan sukayi bankwana suka kwanta tare da yi ma juna alk'awalin had'uwa gobe.


Bayan kwana biyu Dad yasanar da su Malam da Su Aunty Kilima nan abokan Dad su ukku da d'an uwanshi sukaje suka nema ma Faruk auren Nasiba a wajen wani k'anen mahaifinta Malam sulaiman mutumin kirkine sosai nan ya amince aka tsaida rana nan da wata biyu masu zuwa.

Haka aka koma aka fara shirye shiryen aure inda Faruk yak'ara gyara gidanshi da zai tare da amaryarshi nan da wata biyu.



A chan 'bangaren Jawahir hankalinta ya kwanta sosai zamanta a wajen dangin mahaifiyarta dan tana samun kulawa yadda yadace gabad'ayansu kowa nan nan yake da ita dan haka tasaki ranta kud'ad'e tafiddo daga account d'inta dayawa taraba biyu taba kakanninta rabi sauran rabin kuma taraba ma yayyen mahaifiyartata sukaita mata godiya inda motar tabarta da sunan duk wanda zai fita yana iya d'auka yafita da ita ammah yayyen mahaifiyartata basu amimce da hakan ba su dakansu suka koya mata mota dan tadinga tuk'awa dakanta.
Khausar d'iyar Baba Musa itace tsararta dan haka suka k'ulla abota sosai Jawahir tana sonta saboda sunan mahaifiyarta gareta islamiyyarsu aka sata nan tafara karatu hankali kwance inda a cikin zuciyarta taci burin cigaba da karatunta na high institution.
A 'bangare guda kuma suna waya da Faruk da su Mom dan kusan kullum sai sun gaisa, a wajen Mom ne take jin labarin sa ranar auren Faruk nan tayi Allah yasa alkhairi, abun ya tsaya mata a rai sosai koda suka gama waya da Mom kiran Faruk tayi lokacin yana wajen aiki ya yi busy dayawa bai d'agaba saida yagama aikinshi sannan yakirata a waya, lokacin tana kwance suna kallo ganin me kiran yasa tatashi zaune tare da yin picking tayi sallama.
Amsa mata Faruk yayi yace k'anwata ina fata kina lafiya.
K'walla ce tacika mata idanu tace Yaya Faruk shine har akayi maka baiko tsawon sati biyu ammah baka fad'a min ba hakan da kayi ka kyauta ma k'anwarka?

Ayya k'anwata yi hak'uri wallahi ba haka bane ina ta so infad'a maki mancewa nakeyi.
"Ammah ai kusan kullum muna yin waya kawai dai bakaso kafad'a min ba sai gashi ita Mom ta fad'a min"
Kiyi hak'uri Jawahir ba haka bane ai zan zo.
"Uhm Allah yasa alkhairi kayi zamanka kawai,,, tana fad'in haka takashe wayarta.
Faruk sake kira yayi ammah batayi picking ba murmushi yayi yace lallai ana fushi da ni

Jawahir kasa samun sukuni tayi a ranar ba dan komai ba sai dan abinda Faruk yayi mata su Innah damunta sukayi da tambaya akan abinda yake damunta tace bakomai.
Tun daga ranar indai Faruk zai kirata a waya bata d'agawa koda itama bata jin dad'in hakan da takeyi mashi saidai tana fushi da shi akan abinda yayi mata.


++++++++++++

A 'bangaren Hajiya Maijidda kud'i tafitar sannan tasiyar da k'addarorinta tayo ma d'iyartata order d'in kayan d'aki na gani na fad'a set biyu sannan tasiya mata kayan kitchen dan itace uwa da uba har a lokacin babu wanda yalek'a Alhaji Sufyan daga cikinsu bare susan halin da yake ciki dan su kansu kunyar tunkarar gidan yari suke da sunan sune iyalanshi.



______Wasa wasa haka aka ci wata guda ana saura wata guda bikki Mom taje itada Aunty kilima k'anwar mahaifinsu Mom suka had'o lefe na gani na fad'a akwati goma sha biyu akayi mata anzuba duk wani abu da yadace sannan aka kai lefe.

Su Mummy da danginsu Nasiba sun yaba sosai da irin kayan da aka zubo mata nan suka bada tukaici me tsoka su ma.


* * *
Faruk ganin har lokacin Jawahir bata kulashi ba yasa yashirya ranar wata asabar yaje Kebbi batare da ya sanar da ita ba.
Yana isa yakira Baba Nura yaje yad'auko shi suka nufi gidan.

A waje suka gaisa da Baba Malam sannan suka shiga ciki suka gaisa da Innah a d'akinta yazauna nan takawo mashi fura me sanyi yasha, su Baba Musa duk zuwa sukayi suka gaisa nan aka cika mashi gabanshi da abinci da balango, furar yanark'a sosai dan ta yi mashi dad'i.
Hira sukayi sosai da su Baba Malam da su Baba Nura duk wannan bidirin jawahir tana cikin gida wajen su Khausar batasan abinda ake ba har saida su Faruk sukayo sallar la'asar sannan Baba Nura yashiga cikin gida yasamesu zaune suna hira kallon Jawahir yayi yace kizo kugaisa da bak'o gashichan ya zo tun d'azu.
Bak'o kuma?,,, jawahir tatambaya.
Eh kishiga yana chan 'bangaren su Innah.
Amsawa tayi da toh nan tamik'e tajawo hijab d'inta tasaka, Khausar tace wai wanene yazo?
Oho nima ina sani Baba Nura bai fad'a min ba saidai kitaso muje mugani.

Dariya Khausar tayi tace babu inda zanje dan wannan bak'on da alama na musamman ne lallai garinmu ya amsheki nan da nan anyi mana sabon kamu eyyen ba.
Harara Jawahir tadoka mata tace kinga Khausar kidaina wannan maganar ko kin mance ni matar aure ce.
Ta'be baki khausar tayi tace wallahi ba mecewa haka idan ba ke kika fad'a ba kuma ma auren da babu shi yanzu.

Tsaki Jawahir taja tawuce tatafi batare da ta bata amsaba tana jiyota tana cewa agaishe man da surukin namu ammah tayi shuru.

Tana shiga part d'in inna fuskarta kicin kicin tawuce tanufi inda inna take zaune tace wai inna wanene yazo?
Kishiga ciki man sai kigane ma idanunki.
Jawahir tsayawa tayi cikin ranta tace wallahi indai har wajena akazo zan wulak'anta mutum dan ni samari basu gabana, muryar Inna taji ta ce bazaki shigaba sannan tawuce tashiga.

Tana d'age labule bakinta d'auke da sallama nan sukayi ido biyu da Faruk batasan lokacin da murmushi yasu'buce mataba cikin sauri ta ida shiga d'akin tace lah yaya Faruk kaine kazo ashe shine baka fad'a min ba?
Murmushi yayi yace taya zan fad'a maki bayan k'anwartawa fushi take da yayan nata saisa nazo dan in goge laifina.

Waje tasamu tazauna nan tagaisheshi ya amsa tatambayeshi su Mom yace duk suna lafiya lau.
Amaryar fa ko ma ince Auntyna?
Murmushi yayi yace tana nan lafiya lau itama tana gaisheki, nidai yanzu ayi hak'uri adaina fushin nan da akeyi da ni na amsa laifina insha Allahu bazan sake ba.
Turo baki tayi batare da ta ce komai ba.
Ahankali yace please my k'anwa kiyi hak'uri wallahi na shafa'a ne.
Juyawa tayi gefe guda sannan tace shikenan na hak'ura.
Yauwa kokefa har na ji dad'i ina fata babu wata matsala?
Girgiza kai tayi tace babu.
Ajiyar zuciya yasafke yace toh yanzu yaushe zakizo katsina?

67 / 74