Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
yadda duk kuka tsara daidai ne ko Hajiya?.
Mom da take kallon Nasiba cike da mamaki d'aga kai tayi tace hakane Alhaji suyi shawara a tsakaninsu kawai zai fi.
Fashewa da kuka Nasiba tayi tace dan Allah Dad kutaimaka kusa baki a ciki na tabbata kune kad'ai zakuyi mashi magana yasaurareku wallahi idan har bai auri Jawahir ba banyi ma rayuwata adalci ba ta rasa mijinta a lokacin da take buk'atar shi kuma duk ta silar su mahaifina dan Allah na rok'eku Mom kuce wani abu.
Ganin yadda take kuka yasa su dukansu suka ji tausayinta Dad yace kidaina kuka hakanan Nasiba, sannan yamaida kallonshi ga Faruk da yahad'e fuska idanunshi suna a kan waya yana dannawa kamar baisan abinda ake tattaunawaba Dad yace toh kai Faruk ka ji abinda matarka tace tana neman wannan alfarmar.
'Dagowa yayi yakalli mahaifin nashi yace Dad ni fa ban da burin auren mata biyu.
Duk da haka Faruk tunda matarka ce tanemi kayi auren sai kataimaka kayi bare ko bakomai Jawahir ta cancanci ka aureta.
Ammah Dad duka aurenmu fa wata ukku da yinshi.
Toh ai ba matsala bane.
Faruk juyawa yayi yakalli mahaifiyarshi da jikinta yayi sanyi sosai nan tad'aga mashi kai alamun Eh.
Duk'ar da kanshi yayi k'asa yama rasa abida zaice ganin iyayen nashi duk sun goya ma maganar Nasiba baya.
Nasiba idanu tazuba mashi tana jira taji abinda zai ce har lokacin hawaye basu daina fita daga idanunta ba.
Jin ya yi shuru yasa Dad yace kai muke saurare Faruk.
Sai da yayi kusan minti ukku sannan yace shikenan na amince.
Saurin rik'oshi Nasiba tayi tace dagaske ka amince zaka aureta?
Harararta yayi yace tunda kun nuna kuna son hakan.
Janye hannunta tayi daga rik'on da tayi mashi cikin sanyin jiki tace dan Allah kar kayi duba da abinda mukeso kataimaka kaima kaso auren a cikin ranka insha Allahu zakayi alfahari da mu.
Toh wai Nasiba ita d'in Jawahir tace maki batada wanda take so?
Jim tayi sannan tace na tabbata insha Allahu bata da shi.
Jinjina kai yayi yace shikenan ammah da sharad'i guda idan dai har tana da wanda takeso dole mubarta ta aureshi,,, Cewar Faruk.
Tace toh shikenan na yarda da wannan.
Dad da Mom dai idanu suka zuba masu suna kallonsu cikin ransu suna jinjina ma k'ok'arin Nasiba dakanta take neman mijinta yak'ara aure wanda itama d'in basu dad'e da yin auren ba.
Nasiba godiya tayi mashi sannan tajuya tayi ma su Mom su ma godiya.
Addu'a su Dad suka dinga yi mata dan tabbas sunsan d'an nasu ya yi dacen mata dan samun irinsu Nasiba a yanzu sai an tona, mik'ewa Faruk yayi yai ma su Dad sallama sannan yace kisameni waje ina jiranki.
Itama mik'ewar tayi tai masu sallama sannan tabi bayan Faruk da tuni ya yi gaba.
Suna fita Mom kallon Dad tayi tace oh Alhaji kaga ikon Allah wallahi Nasiba yarinyar kirki ce ta san abinda yakamata.
Jinjina kai Dad yayi yace ai kedai bari gaskiya Nasiba ta yi kuma nima kaina na ji dad'in hakan da tayi dan tuni nayi ma Faruk sha'awar auren Jawahir dan nasan zasu dace kuma ko bakomai shi zai kula da maraicinta.
Ammah Alhaji yanzu kana ganin shi Faruk d'in zai aureta kalli fa yadda yanuna baya sonta.
Murmushi Dad yayi yace Hajiya kibarni da shi kawai.
Mom tace toh shikenan Alhaji Allah dai yatabbatar mana da alkhairi.
Amsawa yayi da Ameen.
Tunda suka shiga mota suka kama hanyar gida Faruk shuru yayi Nasiba ko ganin yadda yad'auke kai yasa tayi shuru dan ta san fushi yake da ita.
Suna isa gida d'akinta tawuce, zama tayi bakin gado tadafe kanta nan wasu siraran hawaye suka gangaro mata saurin gogesu tayi tamik'e taje tayi wanka tai shirin kwanciya sannan tafito tanufi part d'in Faruk.
Tana shiga tasameshi kwance murmushi tayi tace Lovely har ka kwanta kenan?
Shuru yayi nan tataka ta isa wajen gadon takwanta daga bayanshi tana kwanciya yakai hannu yakashe hasken d'akin.
Matsowa tayi kusa da shi cikin sanyin murya tace Lovely dan Allah kayi hak'uri idan har abinda nayi ya 'bata maka rai wallahi banyi hakan da wata manufaba nayi ne saboda hakan shine dacewa.
Muryarshi taji ya ce Nasiba a wajenki ne hakan yake dacewa watau shine zaki d'auki maganar da kika tsara kije kifad'a ma iyayena koda ace ni bana da ra'ayin hakan ke tunda kinaso dole kenan inyi ke awajenki hakan kin min adalci.
Fashewa tayi da kukan da tun tuni yake cinta ammah tadanne shi sai a lokacin tasamu damar yin shi, cikin kuka tace dan Allah Faruk kayi hak'uri banyi hakan saboda son zuciya ba, nayi ne kawai saboda ina tsoron alhakin abinda mahaifina yayi mata yahau kanmu banda kwanciyar hankali a duk lokacin da natuna mahaifinmu ya bamu munci da hak'in wata ya suturtamu da hak'in wata ya salwantar da ran wasu, dan Allah Faruk kataimaka ka auri Jawahir ba dan halinaba na san kai mutumin kirki ne kuma me fahimta zaka fahimci abinda nake nufi dan Allah kayi min wannan taimakon ko da ace shine taimako na k'arshe da zakayi min a duniya, na maka alk'awali zamu zauna lafiya tamkar 'yan uwan juna please Faruk kataima min,,, nan tasake fashewa da wani sabon kukan.
Wani irin tausayinta ne yad'arsu a ran Faruk, juyowa yayi yafuskanci inda take tare da rungumota jikinshi cikin lallashi yace Nasiba kidaina kukan nan bana so kinsan dai banason jin kukanki, shikenan na amince zan aureta ammah da sharad'i d'aya.
Saurin d'agowa tayi takalleshi tace wane irin sharad'ine dan Allah kafad'a min insha Allahu zan kiyaye.
Idanu yazuba mata yana kallon cikin idanuwanta sannan yace sharad'in shine idan har Jawahir tana da wanda takeso dole kijanye daga k'udurin nan dan bazan ta'ba amince ma aurenta ba idan tana son wani na daban domin gudun kar incutar da ita.
'Daga kai tayi tace ba damuwa na amince da wannan sharad'in.
Gyara mata kwanciya yayi a jikinshi yace toh shikenan yanzu muyi bacci dan ni bacci nake ji.
Toh nagode sosai Lovely Allah yasaka da alkhairi Allah yabarmu tare.
Amsawa yayi da Ameen daga nan kuma babu wanda yak'ara cewa komai daga cikinsu kowa da abinda yake tunani a cikin ranshi.
***********
Ranar juma'a Faruk yakira Baba Nura yasanar sa shi zuwan da zasuyi da amaryarshi dan dama suna gaisawa sosai ko bayan bikki saida Baba Nura yazo yaga amarya yai masu wuni guda, a ranar Faruk yaje yayi masu booking d'in jirgi.
Washe gari jirgin k'arfe goma sha d'aya suka bi suka je Kebbi wajen sha biyu sun isa Baba Nura yaje yad'aukosu daga airport.
Suna isa gidan tarba me kyau akayi masu musamman Nasiba a 'bangaren su Inna Mairo tazauna matan 'yan uwan maman Jawahir suka zo aka dinga gaisawa cikin mutunci da sakin fuska ana mata Allah yasa alkhairi na aurensu.
Nasiba haka tadinga gaisawa da mutanen gidan cikin sakin fuska dan a lokacin da sukazo su jawahir basu gidan sai wajen k'arfe d'aya suka dawo daga islamiyya saboda suna tsayawa tahafiz, su ukku suka jero suka nufo gidan ita da su Khausar da Na'ima lokacin su Baba Musa da su Faruk suna zaune a waje, Khausar ce tahangoshi tace lahh Jawahir wanchan kamar Barrister ne yazo.
Batare da ta d'ago kanta da ke duk'e k'asa ba tace uhm kedai bakida aiki sai hango mutane ko ma ince sa ido toh bashi bane.
Tsaki Khausar tayi tace kokuma kece bakida aiki sai afad'a maki magana kik'i yarda bayan baki d'ago kika ga kowanene ba, toh nidai na ce wallahi shine kuma kid'ago kigani.
Jin ta rantse yasa Jawahir tad'ago dan tagane ma idanunta aiko d'agowar da tayi ya yi daidai da kallosu da Faruk yayi nan suka had'a ido.
Saurin safke idanunta tayi k'asa tare da yin murmushi cikin ranta tace ashe dai shine wani irin dad'i taji ya d'arsu a ranta suna zuwa shiga gidan duk suka gaishesu sannan suka wuce zasu shige Baba Malam ne yace Jawahir bakiga Faruk ba ne?
Tsayawa tayi nan su Khausar suka shige.
'Dago kai tayi takalleshi tana murmushi tace lah Yaya Faruk ashe kaine sannu da zuwa ina wuni?
Murmushi yayi cikin ranshi yace lallai yarinyar nan har tad'ago takalleni muhad'a idanu shine yanzu zata wayance bata ganeni ba, basarwa yayi yace yauwa jawahir andawo islamiyyar ko?
Eh Yaya Faruk ya su Mom da Dad?
Hmm suna chan fushi suke da ke.
Marairaicewa tayi tace Allah sarki ni wallahi inaso inje hutun ne ba'a bamu shi dayawaba lokacin ammah insha Allahu kwanan nan zan je inyo maku sati biyu, ina Auntyn tawa?
Murmushi yayi yace kedai kije da dad'in bakinki kullum maganar kenan zakije ammah har yau shuru bakije ba ai Auntyn taki tana nan ciki sai kije kikaranta mata dad'in bakin naki k'ila ta yarda da ke.
Cike da jin dad'i tace dagaske tare kukazo da ita?
Eh tare mukazo zatayi maku wuni.
Saurin juyawa tayi tace bari inje ingaisa da Auntyna wallahi na ji dad'i sosai.
Su dukansu murmushi sukayi Baba Malam yace ina ruwan Jawahir.
Cikin sauri tashiga 'bangaren Inna a parlor tajuyo muryarsu suna hira, d'age labule tayi tana cewa oyoyooo ga Auntyna.
Nasiba na ganin ta shigo d'auke kai tayi tare da juyawa tace ni ba ruwana da ke fushi nake.
Saurin matsawa gabanta jawahir tayi tatsugunna tace dan Allah Auntyna kiyi hak'uri wallahi ina so inzo Allah ne bai nufa ba.
Inna Mairo ce tace kokuma bakiyi niyar zuwa ba
Kai Inna bafa haka bane kinsan komai sai Allah ya yi, marairaicewa tayi tace dan Allah ba dan halina ba Aunty Nasiba kiyi hak'uri wallahi nima kaina na san ban kyauta ba.
Sai a lokacin Nasiba tajuyo tace shikenan tunda kema kin gane baki kyauta ba na hak'ura ammah inji yaushe za'a zo mana.
Murmushi tayi tace nagode sosai Auntyna insha Allahu ina nan tafe dan idan nazo sai na dad'e a wajenku.
Hmm toh Allah yasa.
Ameen Auntyna, nan suka gaisa tatambayeta gida da su hajitarta tace duk suna lafiya lau.
Hira suka zauna suka dinga yi kamar daman irin sun san juna sosai har su khausar suka shigo suka gaisa.
Bayan sunyi azuhur ne sunci abinci Inna Mairo tafito tsakar gida tana dafa madarar shanu, d'akin yarage daga Jawahir sai Nasiba dan su Khausar tunda suka shiga cikin gida basu dawo ba, kallonta Nasiba tayi tace dan Allah Jawahir ina k'ara baki hak'uri akan abinda mahaifinmu ya aikata maki wallahi bamusan komai ba akai.
Kai Aunty Nasiba dan Allah kibar tuna abinda yawuce.
K'walla ce tacika mata idanu tace dole intuna jawahir domin ko kema har kikoma ma mahaliccinki bazaki ta'ba mance hakan ba, kar kiyi k'arya a fili alhalin azuciyarki ba haka bane.
Hawaye ne suka gangaro ma Jawahir tace tabbas nasan *DA CIWO A RAYUWATA* ammah babu yadda na iya komai muk'addarine dama chan Allah ya k'addara ba zan k'are rayuwata tare da iyayenaba *K'ADDARA CE* ta rabamu dan Allah mubar maganar Aunty Nasiba banaso tunawa domin inajin wani iri a duk lokacin da natariyo rayuwar da nayi a baya saidai ina jin d'an sanyi idan natuna da d'aukar *FANSAR RAI* na iyayena da nayi.
Murmushi Nasiba tayi tace hakane Allah yajik'ansu yasa sun huta.
Jawahir Amsawa tayi da Ameen daga nan kuma duk suka yi shuru.
Inna Mairo ce tashigo da wani galan a hannunta tamik'a ma Jawahir tace jeki gidan Ladidi ki amso min Man Shanun da nabata ta dafa min d'azu.
Amsa jawahir tayi tace toh nan tatashi tafita.
Tana fita Baba Nura yashigo yace amarya kina nan anbarki ke kad'ai ko?
Murmushi tayi tace a'a basu dad'e da fita ba ma yauwa dan Allah Malam Nura ko zaka taimaka kayi min magana da su Baba dan akwai magana me muhimanci da nakeso zamuyi da su.
Baba Nura yace toh shikenan bari inje insanar da su.
Fita yayi yaje yafad'a ma su Baba Malam sak'on Nasiba dan har lokacin suna zaune a k'ark'ashin bishiyar da yake zama saman tabarma dan a nan ma suka ci abinci, Faruk yana jin sak'on Nasiba yagane maganar da takeso tayi masu duk sai yaji wani iri.
Haka suka tashi suka shiga cikin gida a tsakar gida aka shimfid'a tabarma Baba Malam, Baba Musa, Baba Jamilu, Baba Nura, Faruk sai Inna Mairo suka zauna daga chan gefe Nasiba tafito tazauna.
Baba Malam ne yayi gyaran murya yace ance kina son magana da mu Allah dai yasa lafiya.
Duk'ar da kai tayi cike da ladabi tace lafiya lau Baba daman wata alfarma ce nake nema a wajenku bansaniba ko zan sameta.
Wace irin alfarma ce wannan?,,, baba malam yatambayeta.
Kallon Faruk tayi sannan tace mijina nake son nema ma auren Jawahir.
Su duka da mamaki suke kallonta, Baba Musa yayi k'arfin halin cewa keko wace irin magana kike ni na d'auka wata magana ce me muhimmanci taya zakice mijinki ya auri Jawahir bayan ba'a dad'e da bikkinku ba.
Cikin sanyin jiki tace wannan maganar ma tana da muhimmanci dan Allah kutaimaka mana idan har hakan zai yuwu wallahi ni babu matsala na amince zan zauna da ita da zuciya d'aya ko bakomai rayuwar Jawahir yaci ace antausaya mata.
Faruk ne cikin kwantar da murya yace zan auri Jawahir idan har kuka ban dama na yi maku alk'awali zan kula da ita bazan ta'ba bari tazubar da hawayeba tayi da tasani akan aurena ba amincewarku mukeso idan har batada wanda zata aura inkuma tana da shi shikenan sai in hak'ura domin komai nufine na ubangiji.
Jinjina kai sukayi gabad'ayansu Baba Malam yace wannan gaskiya ne Faruk tunda dai har kaida matarka kun amince zaku zauna da ita tsakani ga Allah shikenan muma mun amince ka aureta domin ko bakomai ka cancanci hakan idan har muka ce zamu hanaka jawahir toh mun zama butulu dan ko halarcin da kayi mata ya ci ace mun amince, na yarda da kai 100% nasan zaka kula da ita da dukiyarta indai har ina da iko da Jawahir toh na mallaka maka ita.
Su Baba Musa ne sukace wannan gaskiya ne muma mun amince da hakan.
Inna Mairo ita kanta ta yi farin ciki sosai ko bakomai ta san Faruk zai kular mata da jikarta jinjina ma k'arfin halin Nasiba tayi ganin wai dakanta take nema ma mijinta aure.
Faruk da Nasiba godiya sukayi masu.
Su ko farin ciki baki har yak'i rufuwa dan daman sunaso Jawahir tasamu miji wanda zai kula da maraicinta, nan sukaita shi masu albarka, kowa farin ciki fal a ranshi dan sunsan indai ta auri Faruk ta more miji.
Nasiba ce tace kar afad'a ma Jawahir abari su zssu fad'a mata da kansu.
Su Baba Malam suka amince da hakan.
Wajen k'arfe ukku Jawahir tadawo takawo ma Inna Mairo sak'onta tace kiyi hak'uri inna sai yanzu tagama dafawa ashe bata soyaba sai da naje.
Murmushi Inna tayi tace bakomai ai daman na yi tunanin haka daman ina ta Allah Allah tasoya kafin sutashi tafiya.
Murmushin itama Jawahir tayi tace ai nan zasu kwana gaskiya bamu yarda sutafi yau ba.
Nasiba da take cikin d'aki tana jiyota saidai tayi murmushi kawai.
Shigowa Jawahir tayi tace gaskiya babu inda zakuje yau Aunty Nasiba bari ma inma Yaya Faruk magana.
Au keda baki ma lek'a inda mukeba kike da bakin cewa haka.
Dariya Jawahir tayi tace dole ma inyi zuciya inzo ko dan inhuta da gorin da ake min.
Ai da dai ya fi maki, yauwa Jawahir akwai magana me muhimmanci da nakeso muyi.
Wace magana kenan Aunty?.
Ina zuwa,,, wayarta tad'auko takira Faruk tace yashigo dan Allah suyi magana, ya amsa da toh.
Bayan ya shigo ne ya zauna takalli Jawahir da tayi shuru tana jira taji abinda zasuce sannan Nasiba tace dan Allah Jawhir wata 'yar alfarma ce muke nema a wajenki.
Alfarma kuma?,,, tatambaya cike da mamaki.
Janye kai Nasiba tayi gefe guda sannan tace dan Allah ina so ki auri Faruk.
Zumbur tamik'e tsaye tace ni kuma? Aunty Nasiba kinsan abinda kike fad'a kuwa?
'Daga kai tayi tace Eh na sani cewa nayi kitaimaka ki aureshi.
Jawahif juyawa tayi takalli Faruk da yajingine kanshi a jikin kujera idanuwanshi suna a lumshe yana saurarensu, d'auke kai tayi tace gaskiya ba zan iya auren mijinki ba ni kawai matsayin Yaya yake a wajena.
Saurin bud'e idanu Faruk yayi yakalleta.
K'walla ce ta cika ma Nasiba idanu tace kar kice haka Jawahir dan Allah kitaimaka ki aureshi na maki alk'awalin zamu zauna da ke lafiya, bazamu ta'ba cutar da rayuwarki ba, idan har baki auri Faruk ba hankalina bazai ta'ba kwanciya ba, dan Allah kitaimaka ki auri Faruk na tabbata zai kula da ke fiye da yadda Umar yakula da ke.
Zama Jawahir tayi tare da juyawa tana kallon gefe guda nan hawaye suka fara fita daga idanunta.
Faruk ganin yadda take hawaye yasa jikinshi yayi sanyi nan yayi ma Nasiba nuni alamun tabasu waje, mik'ewa Nasiba tayi tafita cikin sanyin jiki, Nan yamaida kallonshi ga Jawahir ahankali yakira sunanta tajuyo takalleshi cikin muryar kuka tace Yaya Faruk dan Allah kace min maganar da Aunty tayi da wasa take ba da gaske ba.
Murmushi yayi yace Jawahir dagaske take ina sonki kuma zan aureki idan har kin amince.
Saurin tarar numfashin shi tayi tace ban amince ba bazan ta'ba aurenka ba domin kai Yayana ne.
Wani irin haushi Faruk yaji ammah yadanne yace idan har kin d'aukeni a matsayin Umar zaki iya aurena Jawahir tunda shima kin aureshi ko kin mance lokacin da muke bankwana zaki dawo nan kikace infad'i duk abinda nake so kiyi min nace bana buk'atar komai sai abu guda, kikace menene nace zan sanar da ke ba yanzu ba, inzaki tuna cewa kikayi Allah yakaimu lokacin insha Allahu komenene zan nema zaki mallaka min shi, idan ko haka ne Jawahir aurenki nakeson yi dan Allah ki amince min.
Kallonshi tayi fuska sha'be sha'be da hawaye tace taya zan iya aurenka Yaya Faruk? Taya zan auri mijin Aunty Nasiba idan har nayi haka ban mata adalciba ga mahaifinta anrufe sanoda ni sai kuma in auri mijinta dan Allah kacanza wani abun ammah bazan iya aurenka ba.
'Dan guntun murmushi yayi yace wannan alfarmar ita kad'ai nake nema a wajenki idan kuma har baki amince ba shikenan zan hak'ura Jawahir saidai na san kisan girman alk'awali da hukincin rashin cikashi.
Cikin kuka tace ni ba wai alk'awalin bane bazan iya cikawa ba kawai dai aurenka ne bazan iyaba kai fa matsayin Yayana kake kuma Aunty Nasiba ban mata adalci ba idan na auri mijinta nidai kayi hak'uri bazan iyaba Barrister...tun kan tarufe baki sai jin muryar Inna Mairo sukayi ta ce Jawahir indai kika k'i amincewa da aurenshi tabbas kin zama butulu domin duk halarcin da mutanen nan sukayi maki baidace kice haka ba.
Cikin kuka tad'ago takalli Inna Mairo sai