Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   69 / 74

204K to 207K   out of 220.3K words

kuka ja min da ace kun barni na cigaba da karatuna da duk hakan bai faru ba, goge hawayen tayi tare da cewa na mik'a ma ubangiji lamurrana domin shi ya fi kowa sanin halin da nake ciki Allah kaza'ba min abinda zaifi zama alkhairi a rayuwata.




******* ********

Faruk da Nasiba soyayyarsu kawai suke sha suna kula da junansu sosai ko da ace Faruk yana wajen aiki tana k'ok'arin kiranshi ko shi yakirata dan kawai suji lafiyar juna.


Faruk yana k'ok'arin zuwa dubo Ummah a asibitin da ake jinyarta har tafara samun sauk'i saidai duk k'ok'arin da suke akanta 'barin jikinta guda ya shanye bata iya komai daga k'arshe ma suka nemi susallameta takoma gida zasu d'aurata akan magani dan bazata ta'ba komawa daidai ba.
Faruk amincewa yayi da hakan nan yasa aka kwashe duk kujeru da kayan d'akin da suje gidansu Jawahir aka kaisu a gidan da taba ummah, gidane madaidaici me d'auke da d'akuna ukku kowane ciki da parlor.

A ranar da aka sallameta gidan yawuce da su itada masu jiyyarta su biyu inda d'aya daga cikinsu yayartace tana aure a chan funtua dan haka suka dawo gidan itada mijinta dan cigaba da kula da 'yar uwartata da a yanzu sai anyi mata komai kamar yadda Faruk yabata shawara.

Ummah kuka tayi sosai lokacin da Faruk yasanar da ita kyautar da Jawahir tayi mata na gidan da mota sai kuma kud'ad'en da tabada abata.
Kuka tadingayi tana cewa kaicona ina ma ace ban zalunci wannan yarinyar ba ko da sau d'aya ban ta'ba kyautata mataba daga ita har mahaifiyarta, yanzu ga shinan yadda rayuwata takoma dan Allah ina zanganta in nemi gafararta.
Faruk yace kar kidamu duk abinda Jawahir tayi maki cancantane yasa hakan sannan zuciyar jawahir mekyau ce akowane lokaci tana da burin kyautata ma mutane kidaina sa damuwa a ranki kinji dai abinda likita yace kafin kubaro asibiti.
Motsa 'barin jikinta me lafiya tayi tace dole inyi kuka Faruk dan na cutar da yarinyar nan fiye da tunanin wani me tunani sai gashi rayuwa ta juya min na rasa komai nawa a yanzu itace take taimakona dan tarufa min asiri.

Lallashinta suka dinga yi tayi shuru nan Faruk yadamk'a masu komai sannan yasa aka kawo masu kayan abinci sosai wanda yafitar da kud'inshi yasiyesu dan kawai saboda su.
Haka suka dinga yi mashi godiya suna shi mashi albarka har yatafi.


*BAYAN WATA UKKU*

Nasiba ce tafito daga kitchen d'auke da Cup a hannunta jikinta sanye cikin kayan bacci tanufi d'akin Faruk, tana shiga zaune yake ya d'aura laptop a saman cinyarshi yana wani aiki, daga gefenshi tazauna tace wash sannu lovely.
Batare da ya kalletaba yace kema sannunki hearty.
Hmm kaine da sannu kaida tun d'azu kake faman aiki yauwa lovely dan Allah akwai maganar da nakeso muyi da kai.
Janye laptop d'in yayi tare da janyota yad'aura bisa cinyarshi sannan yace ina saurarenki hearty wace magana kikeson muyi?
Murmushi tayi tamik'a mashi cup d'in da tashigo da shi tace toh kasha wannan kajik'a mak'oshinka sannan muyi maganar.
Amsa yayi bai musaba yasha saida yashanye kunun ayar da takawo mashi tas sannan yace toh ina saurarenki.
Kwantar da kanta tayi a k'irjinshi sannan cikin sanyin murya tace dan Allah Lovely kataimaka muje Kebbi wajen Jawahir muganota ko da wuni guda ne tunda ita har yau bata lek'o mu ba.
Jan hancinta yayi yace kedai baki gajiya, toh ai ita yakamata tazo taganki.
'Bata fuska tayi kamar zatayi kuka tace dan Allah Lovely kataimaka muje mu ai sai mukwashe ladar zumuncin.
Hmm tunda kince haka shikenan kibari sai weekend sannan muje wuni guda mudawo.
Rungumeshi tayi tace nagode sosai Lovely Allah yasaka da alkhairi, ai kam saidai kawai mubata mamaki dan bama zata san zamuje ba.
Hamma yafara yace kinga tashi muje mukwanta dan ni nan na gaji aikin ma bazan ida shi ba sai zuwa gobe.
Shagwa'be fuska tayi tace toh saidai kad'aukeni muje.
Cicci'barta yayi yace toh ya zanyi ai dole inyi yadda kikeso amaryata.
Dariya tayi tace a'a ni yanzu ba amarya bace ai na kwana biyu.
Baice mata komai ba saida yadireta saman gado sannan yace toh ke micece?
Maimakon tabashi amsa sai ma juyawa da tayi tana murmushi dan haka shima yakwanta daga bayanta tare da kashe masu haske.....






_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 25*

Ana saura kwana ukku suje Kebbi Nasiba tamatsa mashi suka je gidan su Dad, sunyi farin ciki da zuwansu nan Mom tadinga nan nan da ita dan tana son Nasiba sosai, a chan suka wuni sai dare sannan Faruk yaje zai d'akkota.

Suna a parlor zaune suna hira ita da Mom nan Faruk yakalleta yace sutafi dare ya yi.

Amsawa tayi da toh sannan tace Ammah kafin mutafi ina son zamuyi wata magana da su Mom daman tun d'azu naso yinta sai kuma naga Dad ya fita.
Muryarshi sukaji ya ce toh gani na dawo me za'a fad'a min
Su duka juyawa sukayi suka kalleshi sukai murmushi Mom tace ashe kana kusa.
Shima murmushin yayi yace Eh wallahi wani meeting ne yatsaida ni saisa kuka ji ni shuru har wannan lokacin ban dawo ba.
Sannu da zuwa sukayi mashi nan yashigo yazauna yana cewa wace magana ce d'iyartawa takeson yi da mu?

Faruk kallonta yayi yai murmushi sannan yamaida kallonshi ga iyayenshi yace wai maganar zuwan da zamuyi Kebbi zata fad'a maku batasan munyi maganar ba.
Eh toh kusan itace ammah ba ita bace.

Mom tace toh shikenan d'iyata fad'a mana fatana dai ba matsala bace kuka fara samu da mijin naki?
Duk'ar da kanta tayi cikin nutsuwa tace Mom Dad dan Allah alfarma nake nema wadda na san wajenku ne kawai zan iya nemanta.
Da mamaki suke kallonta sukace wace irin alfarma ce Nasiba kifad'i kowace irice insha Allahu zaki sameta.
Shuru tayi na d'an lokaci sai kuma chan tace dan Allah so nike kurok'ar man Faruk ya auri Jawahir.

Su duka idanu suka zuba mata mamaki k'arara a fuskarsu, Faruk ne yayi k'arfin halin cewa Nasiba wannan wace irin magana ce kikeyi kinsan abinda kike fad'a kuwa?
'Dagowa tayi takalleshi idanu cike da k'walla tace tabbas na san abinda nake fad'a Faruk ina son kataimaka ka auri Jawahir domin ko bakomai ta cancanci hakan ya kamata muyi duba da rayuwarta ita d'in yarinya ce me k'arancin shekaru tana buk'atar auren miji wanda zai bata kulawa sosai wanda zatayi farin cikin kasancewa da shi a matsayinta na marainiya na tabbata kaine kad'ai zata iya aura tasamu wannan gatan domin kai ka san halin da take ciki zaka tausaya ma rayuwarta.
Mom ce tayi k'arfin halin cewa keko Nasiba miyasa kikayi wannan maganar har kikeso mijinki yak'ara aure?
Hawaye ne suka gangaro daga idanunta tace Mom banaso inkasance mace me son kanta dayawa na san ina son Faruk kuma ina da kishi saidai ina ji a raina kamar idan Jawahir bata auri Faruk ba banyi ma kaina adalci ba domin shine kad'ai namijin da yadace ya aureta.
Wani irin kallo yawurga mata yace kar kisake wannan maganar kitashi mutafi gida tunda bani nace maki ina buk'atar k'ara aureba kuma duka wata nawa da yin bikkinmu har zaki wani ce ink'ara aure sannan Jawahir da kike gani matsayin k'anwa take a wajena ba wai sonta nake ba.

Had'e hannuwanta tayi waje guda alamun rok'o tace dan Allah Faruk kar kak'i amincewa da auren Jawahir wallahi na amince zan zauna da ita da zuciya d'aya domin ita d'in zuciyarta mekyau ce, shin ni idan nice zan so ace wani nawa ya fad'a irin halin da Jawahir take ciki? Ya kamata kayi tunani rayuwarta tana buk'atar tallafi duk yadda zataji dad'in zama a wajen kakanninta bazai ta'ba kai zaman da zakayi da ita ba domin na tabbata zaka bata duk kulawar da tadace, na maka alk'awali zamuyi zaman lafiya da ita zamu kasance abun koyi ga duk sauran mata har ayi alfahari da mu,,
Kasa cemata komai yayi saidai kallon mamaki da yakeyi mata.

Juyawa tayi takalli Mom da Dad tace dan Allah ina rok'onku kusa baki a ciki Dad na san ku zaku fahimci abinda nake nufi wannan dalilin ne yasa ban ta'ba mashi maganar ba sai yau da muke zaune a gabanku wallahi tun kan muyi aure da Faruk nasa ma raina ba zan ta'ba zama ni kad'ai da shi ba zai kasance mijinmu ni da Jawahir domin wannan shine adalcin rayuwa ko bakomai mahaifina yana cikin mutanen da suka ruguza mata duk wani farin ciki nata, dan Allah Dad kutaimaka kufahimci abinda nake nufi.

Jinjina kai Dad yayi yace tabbas Nasiba ke mace ce me adalci kinsan abinda yakamata, banyi niyar shiga cikin maganar nan ba na fiso kuje kuyi shawara a tsakaninku idan shi ya amince zai aureta to mu bamuda matsala yadda duk kuka tsara daidai ne ko Hajiya?.
Mom da take kallon Nasiba cike da mamaki d'aga kai tayi tace hakane Alhaji suyi shawara a tsakaninsu kawai zai fi.
Fashewa da kuka Nasiba tayi tace dan Allah Dad kutaimaka kusa baki a ciki na tabbata kune kad'ai zakuyi mashi magana yasaurareku wallahi idan har bai auri Jawahir ba banyi ma rayuwata adalci ba ta rasa mijinta a lokacin da take buk'atar shi kuma duk ta silar su mahaifina dan Allah na rok'eku Mom kuce wani abu.
Ganin yadda take kuka yasa su dukansu suka ji tausayinta Dad yace kidaina kuka hakanan Nasiba, sannan yamaida kallonshi ga Faruk da yahad'e fuska idanunshi suna a kan waya yana dannawa kamar baisan abinda ake tattaunawaba Dad yace toh kai Faruk ka ji abinda matarka tace tana neman wannan alfarmar.
'Dagowa yayi yakalli mahaifin nashi yace Dad ni fa ban da burin auren mata biyu.
Duk da haka Faruk tunda matarka ce tanemi kayi auren sai kataimaka kayi bare ko bakomai Jawahir ta cancanci ka aureta.

Ammah Dad duka aurenmu fa wata ukku da yinshi.
Toh ai ba matsala bane.

Faruk juyawa yayi yakalli mahaifiyarshi da jikinta yayi sanyi sosai nan tad'aga mashi kai alamun Eh.
Duk'ar da kanshi yayi k'asa yama rasa abida zaice ganin iyayen nashi duk sun goya ma maganar Nasiba baya.

Nasiba idanu tazuba mashi tana jira taji abinda zai ce har lokacin hawaye basu daina fita daga idanunta ba.

Jin ya yi shuru yasa Dad yace kai muke saurare Faruk.
Sai da yayi kusan minti ukku sannan yace shikenan na amince.

Saurin rik'oshi Nasiba tayi tace dagaske ka amince zaka aureta?
Harararta yayi yace tunda kun nuna kuna son hakan.
Janye hannunta tayi daga rik'on da tayi mashi cikin sanyin jiki tace dan Allah kar kayi duba da abinda mukeso kataimaka kaima kaso auren a cikin ranka insha Allahu zakayi alfahari da mu.
Toh wai Nasiba ita d'in Jawahir tace maki batada wanda take so?
Jim tayi sannan tace na tabbata insha Allahu bata da shi.
Jinjina kai yayi yace shikenan ammah da sharad'i guda idan dai har tana da wanda takeso dole mubarta ta aureshi,,, Cewar Faruk.

Tace toh shikenan na yarda da wannan.
Dad da Mom dai idanu suka zuba masu suna kallonsu cikin ransu suna jinjina ma k'ok'arin Nasiba dakanta take neman mijinta yak'ara aure wanda itama d'in basu dad'e da yin auren ba.

Nasiba godiya tayi mashi sannan tajuya tayi ma su Mom su ma godiya.
Addu'a su Dad suka dinga yi mata dan tabbas sunsan d'an nasu ya yi dacen mata dan samun irinsu Nasiba a yanzu sai an tona, mik'ewa Faruk yayi yai ma su Dad sallama sannan yace kisameni waje ina jiranki.
Itama mik'ewar tayi tai masu sallama sannan tabi bayan Faruk da tuni ya yi gaba.


Suna fita Mom kallon Dad tayi tace oh Alhaji kaga ikon Allah wallahi Nasiba yarinyar kirki ce ta san abinda yakamata.
Jinjina kai Dad yayi yace ai kedai bari gaskiya Nasiba ta yi kuma nima kaina na ji dad'in hakan da tayi dan tuni nayi ma Faruk sha'awar auren Jawahir dan nasan zasu dace kuma ko bakomai shi zai kula da maraicinta.
Ammah Alhaji yanzu kana ganin shi Faruk d'in zai aureta kalli fa yadda yanuna baya sonta.
Murmushi Dad yayi yace Hajiya kibarni da shi kawai.
Mom tace toh shikenan Alhaji Allah dai yatabbatar mana da alkhairi.
Amsawa yayi da Ameen.



Tunda suka shiga mota suka kama hanyar gida Faruk shuru yayi Nasiba ko ganin yadda yad'auke kai yasa tayi shuru dan ta san fushi yake da ita.

Suna isa gida d'akinta tawuce, zama tayi bakin gado tadafe kanta nan wasu siraran hawaye suka gangaro mata saurin gogesu tayi tamik'e taje tayi wanka tai shirin kwanciya sannan tafito tanufi part d'in Faruk.
Tana shiga tasameshi kwance murmushi tayi tace Lovely har ka kwanta kenan?
Shuru yayi nan tataka ta isa wajen gadon takwanta daga bayanshi tana kwanciya yakai hannu yakashe hasken d'akin.
Matsowa tayi kusa da shi cikin sanyin murya tace Lovely dan Allah kayi hak'uri idan har abinda nayi ya 'bata maka rai wallahi banyi hakan da wata manufaba nayi ne saboda hakan shine dacewa.
Muryarshi taji ya ce Nasiba a wajenki ne hakan yake dacewa watau shine zaki d'auki maganar da kika tsara kije kifad'a ma iyayena koda ace ni bana da ra'ayin hakan ke tunda kinaso dole kenan inyi ke awajenki hakan kin min adalci.

Fashewa tayi da kukan da tun tuni yake cinta ammah tadanne shi sai a lokacin tasamu damar yin shi, cikin kuka tace dan Allah Faruk kayi hak'uri banyi hakan saboda son zuciya ba, nayi ne kawai saboda ina tsoron alhakin abinda mahaifina yayi mata yahau kanmu banda kwanciyar hankali a duk lokacin da natuna mahaifinmu ya bamu munci da hak'in wata ya suturtamu da hak'in wata ya salwantar da ran wasu, dan Allah Faruk kataimaka ka auri Jawahir ba dan halinaba na san kai mutumin kirki ne kuma me fahimta zaka fahimci abinda nake nufi dan Allah kayi min wannan taimakon ko da ace shine taimako na k'arshe da zakayi min a duniya, na maka alk'awali zamu zauna lafiya tamkar 'yan uwan juna please Faruk kataima min,,, nan tasake fashewa da wani sabon kukan.

Wani irin tausayinta ne yad'arsu a ran Faruk, juyowa yayi yafuskanci inda take tare da rungumota jikinshi cikin lallashi yace Nasiba kidaina kukan nan bana so kinsan dai banason jin kukanki, shikenan na amince zan aureta ammah da sharad'i d'aya.
Saurin d'agowa tayi takalleshi tace wane irin sharad'ine dan Allah kafad'a min insha Allahu zan kiyaye.
Idanu yazuba mata yana kallon cikin idanuwanta sannan yace sharad'in shine idan har Jawahir tana da wanda takeso dole kijanye daga k'udurin nan dan bazan ta'ba amince ma aurenta ba idan tana son wani na daban domin gudun kar incutar da ita.
'Daga kai tayi tace ba damuwa na amince da wannan sharad'in.
Gyara mata kwanciya yayi a jikinshi yace toh shikenan yanzu muyi bacci dan ni bacci nake ji.
Toh nagode sosai Lovely Allah yasaka da alkhairi Allah yabarmu tare.
Amsawa yayi da Ameen daga nan kuma babu wanda yak'ara cewa komai daga cikinsu kowa da abinda yake tunani a cikin ranshi.


***********
Ranar juma'a Faruk yakira Baba Nura yasanar sa shi zuwan da zasuyi da amaryarshi dan dama suna gaisawa sosai ko bayan bikki saida Baba Nura yazo yaga amarya yai masu wuni guda, a ranar Faruk yaje yayi masu booking d'in jirgi.


Washe gari jirgin k'arfe goma sha d'aya suka bi suka je Kebbi wajen sha biyu sun isa Baba Nura yaje yad'aukosu daga airport.

Suna isa gidan tarba me kyau akayi masu musamman Nasiba a 'bangaren su Inna Mairo tazauna matan 'yan uwan maman Jawahir suka zo aka dinga gaisawa cikin mutunci da sakin fuska ana mata Allah yasa alkhairi na aurensu.
Nasiba haka tadinga gaisawa da mutanen gidan cikin sakin fuska dan a lokacin da sukazo su jawahir basu gidan sai wajen k'arfe d'aya suka dawo daga islamiyya saboda suna tsayawa tahafiz, su ukku suka jero suka nufo gidan ita da su Khausar da Na'ima lokacin su Baba Musa da su Faruk suna zaune a waje, Khausar ce tahangoshi tace lahh Jawahir wanchan kamar Barrister ne yazo.

Batare da ta d'ago kanta da ke duk'e k'asa ba tace uhm kedai bakida aiki sai hango mutane ko ma ince sa ido toh bashi bane.
Tsaki Khausar tayi tace kokuma kece bakida aiki sai afad'a maki magana kik'i yarda bayan baki d'ago kika ga kowanene ba, toh nidai na ce wallahi shine kuma kid'ago kigani.
Jin ta rantse yasa Jawahir tad'ago dan tagane ma idanunta aiko d'agowar da tayi ya yi daidai da kallosu da Faruk yayi nan suka had'a ido.
Saurin safke idanunta tayi k'asa tare da yin murmushi cikin ranta tace ashe dai shine wani irin dad'i taji ya d'arsu a ranta suna zuwa shiga gidan duk suka gaishesu sannan suka wuce zasu shige Baba Malam ne yace Jawahir bakiga Faruk ba ne?
Tsayawa tayi nan su Khausar suka shige.
'Dago kai tayi takalleshi tana murmushi tace lah Yaya Faruk ashe kaine sannu da zuwa ina wuni?
Murmushi yayi cikin ranshi yace lallai yarinyar nan har tad'ago takalleni muhad'a idanu shine yanzu zata wayance bata ganeni ba, basarwa yayi yace yauwa jawahir andawo islamiyyar ko?
Eh Yaya Faruk ya su Mom da Dad?
Hmm suna chan fushi suke da ke.
Marairaicewa tayi tace Allah sarki ni wallahi inaso inje hutun ne ba'a bamu shi dayawaba lokacin ammah insha Allahu kwanan nan zan je inyo maku sati biyu, ina Auntyn tawa?
Murmushi yayi yace kedai kije da dad'in bakinki kullum maganar kenan zakije ammah har yau shuru bakije ba ai Auntyn taki tana nan ciki sai kije kikaranta mata dad'in bakin naki k'ila ta yarda da ke.
Cike da jin dad'i tace dagaske tare kukazo da ita?
Eh tare mukazo zatayi maku wuni.
Saurin juyawa tayi tace bari inje ingaisa da Auntyna wallahi na ji dad'i sosai.

Su dukansu murmushi sukayi Baba Malam yace ina ruwan Jawahir.

Cikin sauri tashiga 'bangaren Inna a parlor tajuyo muryarsu suna hira, d'age labule tayi tana cewa oyoyooo ga Auntyna.
Nasiba na ganin ta shigo d'auke kai tayi tare da juyawa tace ni ba ruwana da ke fushi nake.
Saurin matsawa gabanta jawahir tayi tatsugunna tace dan Allah Auntyna kiyi hak'uri wallahi ina so inzo Allah ne bai nufa ba.
Inna Mairo ce tace kokuma bakiyi

69 / 74