Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
ne suka gangaro ma Jawahir.
Mik'ewa Nasiba tayi takomo kusa da ita tana cewa lafiya Jawahir kifad'a min abinda yafaru kinga hankalina ya tashi.
Tun kan tayi magana su Ameer suka nufo wajen dagudu suka fad'a jikin Jawahir cikin maganarsu da bata fita sosai suka ce Ammi kin siyo mana chocolate d'in?
Nasiba ce tarik'osu ganin suna neman haye Jawahir tace kunga Ammi batada lafiya kubarta.
Affan ne yaturo baki yace uhm uhm Ummi.
Murmushi Nasiba tayi tace ni bari inbaku chocolate d'in, nan tajasu taje tad'akko masu a part d'inta sannan suka zauna suna sha suna wasa.
Kusa da Jawahir takoma tana cewa kiyi min bayanin abinda yafaru Sister.
Shigowar Faruk ne yasa duk suka juya suka kalleshi Nasiba tace yauwa gaka wai me yake faruwa ne dan Allah me likita yace yana damunta.
Murmushi Faruk yayi tare da mik'a mata takardar hannunshi yace k'aruwa muka samu.
Saurin amsa tayi tana dubawa tayi saurin rungume jawahir tana cewa Alhamdulilah Sis ashe mun samu baby har na tsawon wata biyu wayyo dad'i.
Fashewa da kuka Jawahir tayi cikin kuka tace wallahi ba'a kyauta min ba duka yaushe na haifi Affan ko yayeshi banyi ba sai ace ina da wani cikin.
Nasiba kallon Faruk tayi sukai murmushi sannan tace toh menene Sister ai ba wani abu bane.
Wallahi wani abune Aunty Nasiba duka nawa nake da za'a ce ina da ciki na biyu kuma kema ai da sai yayi maki inda ta tsakani ga Allah yabi.
Faruk da Nasiba dariya ce take cinsu, yadanne tashi yace toh ai itama yi mata zanyi kikwantar da hankalinki.
Mik'ewa tayi tana turo baki tace ai da yi mata zakayi kamar yadda muka haihu tare wannan karon ma sai kayi mata,,, tana fad'in haka tawuce fuuu tanufi part d'inta.
Nasiba da Faruk ko me zasuyi inba dariya ba Nasiba tace ina ruwan Jawahir da wauta.
Tsagaitawa yayi da dariyar da yake yace toh kin dai ji abinda tace kema inyi maki kusake haihuwa tare.
Zaro idanu Nasiba tayi waje tace karufa man asiri Lovely idan nima nayi cikin wa zai kular mana da su Affan? Juyawa tayi takallesu taga har sunyi bacci a saman carpet d'in tace kaga tashi muje katayani d'aukarsu inkaisu d'aki inyaso sai kaje chan kayi ta lallashi dan ka yi laifi.
Mik'ewa yayi yace kedai bari hearty akwai aiki agabana.
Dariya tayi tad'auki Affan shi kuma yad'auki Ameer suka nufi part d'inta, saida tawanke masu hannu sannan takwantar da su a saman gado dan dama tuni ta yi masu shirin bacci tazauna jiran dawowarsu Faruk, itama tahau takwanta, daga gefenta Faruk yazauna yace hearty ba dai bacci zakiyi tun yanzu ba duka fa yanzu tara tayi.
Hamma tayi tace wallahi Lovely yau d'in ne jina nake duk wata iri kamar banda lafiya.
Kwantar da kanshi yayi a saman k'irjinta yace Hearty ko dai kema kin kamu?
Zaro idanu tayi waje tace karufa min asiri ni banda komai.
Murmushi yayi yace toh inma akwai ya kuka iya tunda kuna tare da lafiyayyen miji ni ai abun farin ciki ne agareni kuyi ta haifa min 'yan tagwaye.
Turo baki tayi tace nidai a'a.
Bakinshi yasa yaciji le'benta ahankali yace kedai Eh Hearty,
Kallon agogo tayi tace dan Allah katashi kaje kaji da 'yar uwata ka barota ita kad'ai.
Tallabo fuskarta yayi yace wai da ingama ji da ke kafin inje,,yafad'a yana kashe mata ido guda.
Tureshi tayi daga jikinta tatashi zaune tace dan Allah lovely katafi ka ga ka barta ita kad'ai gashi batada lafiya.
Shafa cikinta yayi yace kema d'in ai bakida lafiya.
Uhm uhm ni lafiya ta lau,, tafad'a tana ture mashi hannu.
Tallabo fuskarta yayi yamanna mata kiss a baki, nan takoma takwanta, shafa kanta yayi yace zan tafi Hearty sai dasafe.
Murmushi tayi tace Allah yakaimu masoyina abun alfaharin mu,, tana fad'in haka tayi saurin juya mashi baya dan tasan idan ba haka tayiba bazai barta ba, tana jinshi yabata peck a kumatu tare da cewa ina sonki sosai matata kikular min da kanki.
Murmushi kawai tayi batare da ta ce komai ba nan yakalli yaran nashi da suke ta bacci sannan yakashe masu fitala yafita yabar d'akin.
Part d'inshi yawuce yafara yin wanka saida yashirya cikin shirin bacci sannan yafito yanufi part d'in Jawahir yana zuwa yasameta kwance saman gado ta lumshe idanunta ammah daga ganin yanayinta ba bacci take ba, zama yayi a gefen gadon yakai hannu yashafa fuskarta sannan yace taya masoyiya zatayi fushi da masoyinta dan kawai Allah ya basu kyautar da ba wanda zai iya basu ita idan ba shi ba,
Ahankali tabud'e idanunta takalleshi sai kuma tajanye fuskarta gefe.
Ajiyar zuciya yasafke yace Habibty kinsan dai banason ganinki a wannan yanayin dan Allah kifad'a min menene laifina a ciki.
Turo baki tayi cikin shagwa'ba tace toh ba kaine kayi min ciki ni kad'ai ba bayan wanchan karon tare da Aunty Nasiba muka haihu.
Dariya ce take cinshi ammah yadanne dan kar yayi wani laifin sannan yace toh ai kece kin fita zalama saisa kika rigata samun ciki.
Kallon rashin fahimtar inda maganarshi tadosa tayi mashi tace me kake nufi da hakan? Wane irin zalama nafita?.
Ganin bata ganeba yasa yace babu komai itama ai tana da nata cikin ba wai ke kad'ai nayi mawa ba.
Saurin tashi zaune tayi cike da jin dad'i tace dan Allah dagaske kake lovely.
'Daga mata gira yayi nan tafad'a jikinshi tare da rungumeshi tace na ji dad'i sosai Lovely.
Shima rungumeta yayi yace dan Allah Habibty kuyi hak'uri da yanayina ina son 'ya'ya sosai in son samune kuyi ta haifa min su dayawa.
Ajiyar zuciya tasafke tace kayi hak'uri lovely nasan ban kyauta maka ba da fushin da nayi akan kyautar da ubangiji yabamu dan Allah kayafe min
'Dago kanta yayi yakalli cikin idanunta sannan yace babu komai Habibty ai ku d'in baku laifi ina k'aunarku fiye da tunaninku nidai fatana kucigaba da nuna min k'auna da tarairaya.
Zaka samu fiye da hakan ma Lovely, ina sonka so na gaskiya wanda ni kaina bazan iya misulta shi ba bana ji zan iya son wani kamar yadda nake sonka.
Tun kan tarufe baki yace kina nufin har Umar?
Murmushi tayi tare da komawa takwanta tace tabbas nasan na so Yaya Umar saidai son da nakeyi maka ya lunka wanda nayi mashi saboda kai da gabad'aya rayuwata nake k'aunarka shi kuma da zuciyata, na mallaka maka gabad'aya soyayyata.
Wani irin farin cikine yalullu'be Faruk yai saurin rungumeta yace nagode sosai Jawahir da irin wannan matsayin da nasamu awajenki, nagode ma Allah da yamallaka min ke amatsayin mata na soki tun lokacin da banyi tunanin zan sameki ba ashe ke d'in rabona ce.
Lumshe idanunta tayi tare da tura hannuwanta cikin sumar kanshi tana shafawa tana jin sonshi yana k'ara mamaye mata duk ga'b'ban jiki.
Lamo yayi a jikinta sai kuma chan yad'ago yakalleta itama bud'e idanunta tayi suka sakar ma juna lallausan murmushi tace ya dai Lovely?
Mik'a yayi sannan yace ya kamata aji da ni yanzun nan gaskiya.
Hararshi tayi cikin wasa sannan tace bayan cikin da kayi min sai kuma kace wani inji da kai.
Toh ya kika iya tunda kina auren lafiyayyen miji ko ana nufin baza'a baniba.
Saurin jawoshi tayi yafad'o jikinta tace ni wacece da zan hana mijina shi da kayanshi akoda yaushe ashirye nake domin kar'barka.
Murmushi Faruk yayi yakai hannu yakashe masu fitila tare da jawo bargo yalullu'besu.
_Ina ganin haka nayi saurin tattaro takarduna da alk'alamina nafito daga d'akin tare da jawo masu k'ofa nace asuba tagari Mr nd Mrs *FANAJ*_
*BISSALAM*
_Alhamdulillah anan muka kawo k'arshen wannan littafin me suna *FANSAR RAI* kurakuren da suke ciki Allah yayafe mana_
_*Nagode sosai da irin k'aunar da kuka nunamin da lokacinku da kuka bani Allah ubangiji yabar zumunci Allah yak'ara dank'on zumunci*_
_Ina maku albishir da sabon novel d'ina me suna *KUWWA DA KUWWA* (bata korar buzu)_
_Labari ne wanda yak'unshi abubuwa da dama wanda sai mutum ya karanta sannan zai fahimci hakan ga kad'an daga cikin labarin_
~~~~~~
_*KUWWA DA KUWWA.....*_
_(Bata korar buzu)_
Kwance take saman makeken gadonta tana bacci inda dogon gashinta yabaje mata a fuska, yanayin yadda take baccin kawai zaka kalla kagane cewa a nutse takeyin shi, lokaci guda tatashi zaune zumbur tare da saurin sa hannunta takare fuskarta, wani irin farin haskene yadaki tafin hannunta ji kake wata irin k'ara k'attt.
Janye hannunta tayi tare da sa gudan hannun tagyara gashinta da yake baje a fuskarta nan kyakkyawar fuskarta tabayyana, ajiyar zuciya tasafke tare da mik'ewa tsaye tanufi wajen makeken mirror da yake manne a bangon d'akin tatsaya tana duba fuskarta, komawa tayi tazauna tare da dafe kanta da hannu biyu cikin siririyar muryarta me dad'in saurare tace *Najma* meyasa kike kai ma fuskata hari meyasa kikeso ki'bata min fuska? sauri janye hannunta tayi takalli zobenta da yake manne a dogon yatsan hannunta na tsaka sai kuma tamik'e tanufo k'ofa tun kan ta iso k'ofar dakanta ta bud'e, tana fita parlor nan wasu mata kusan su goma da suke sanye da kaya iri d'aya suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, batare da ta amsa masuba taje bisa lumtsumemiyar kujerarta tazauna sannan da hannu tayi masu nuni da subar wajen.
Cikin sauri duk suka tashi suka fita tare da jawo mata k'ofa.
Duk wannan abun da yake faruwa tana gani a cikin wani d'an k'aramin madubi dake hannunta, wurgi tayi da madubin ganin batayi nasara ba tamik'e cikin fushi tana cewa ko da ba yau ba *Najla* sai na cika burina, sai na 'bata maki wannan kyakkyawar fuskar da kike tak'ama da ita bazan ta'ba barinki ba....
** ** ** **
Tunda suka shigo cikin garin kallon mutane kawai suke abun yana burgesu ganin yadda suke ta rayuwarsu, itako shugabar tasu yatsina fuska kawai take dan abun sam bai burgeta ba, suna tafiya a wajen titi wata mata tagifta ta gabansu nan d'aya daga cikinsu tafara lasar baki saurin shak'o wuyanta gimbiya najma tayi tace kar kikuskura kilashi wani a cikin garin nan domin garin nan yana da had'ari sosai duk mayen da suka kama basu barinshi a raye,,, tana fad'in haka tatureta gefe nan tayi saurin duk'awa cike da girmamawa tace kigafarceni ya shugabata.
Batare da ta amsa mataba tawuce gaba suna biye da ita a baya suna cikin tafiya a wajen kasuwa tana kallon wani shago da yad'auke mata hankali saboda cikowar mutanen da suke cikinsh nan wani tsoho yatafo da 'yar sandarshi yana dogarawa bai kulaba yad'an bugeta.
A fusace tajuyo takalleshi tare da shak'oshi cikin fushi tace kai wane irin dabba ne da zaka bugeni, bakasan wacece ni ba?.
Jikin tsohon yana karkarwa yace kiyi hak'uri bana gani sosai ne.
Batare da ta sakeshi ba tace bana yafiya a duk lokacin da akayi man laifi sai na d'auki fansa dan haka bazan ta'ba barinka ba, dogon harshenta tafara fiddowa daga cikin bakinta tana shirin lashe fuskar tsohon, daga bayanta taji andaka mata tsawa saurin maida harshen tayi tasaki tsohon tajuyo dan ganin wanda yayi tsawar
Wasu mutane ne tagani tsaye a bayan wani kyakkyawan saurayi yana sanye da kaya na sarauta duk sun fito daga cikin motocinsu, saurayin ne cikin 'bacin rai yace ke wace irin macece bakida hankali zaki shak'e tsoho ko iyayenki basuyi maki tarbiya ba?.
Tsayawa tayi tana kallonshi cike da mamaki jin kalaman da yake fad'a mata wanda tunda take a rayuwarta ba'a ta'ba fad'a mata irinsu ba sai yau da tashigo k'asar nan yawon bud'e ido.
Kallon tsohon saurayin yayi yaga yana ta kyarma sannan yakalli nakusa da shi yace aje arakashi gida.
'Dan russunawa yayi yace angama ranka yadad'e nan biyu daga cikin mutanen suka yi saurin nufar inda tsohon yake suka ruk'oshi suka sa cikin mota suka tafi da shi.
Kallon kallo suka dinga yi shi da Gimbiya Najma yana mata kallon tsana, inda ita kuma take jifanshi da mugun kallo, sai kuma chan yajuya aka bud'e mashi mota cikin k'asaita yashiga aka rufe nan sauran mutanen nashi kowa yashiga mota suka bad'a ma su Najma k'ura suka tafi.
Cikin 'bacin rai tace wanene wannan? Wanene shi da har zai d'aga min murya? Ya zama dole kubishi kugano min inda yake da kuma matsayinshi a garin nan dan bazan ta'ba barinshi ba!!!
Mata ukku ne suka 'bace lokaci guda.
Nan Najma takalli sauran tana hucci sai kuma tarufe idanunta tana motsa baki ahankali nan ita da sauran matan suka 'bace 'bat.
___kuyanginta ne zaune kusa da ita suna ta mata hidima inda ita kuma take ta murza zoben da yake hannunta, k'wank'wasa k'ofa akayi nan masu tsaron k'ofar sukayi saurin bud'ewa.
Wata farar macece tashigo fuskarnan fara fat.
'Dago kai Najla tayi takalleta tace Hasisa ina kika shiga yau tun d'azu ina ta nemanki.
Saurin duk'awa tayi tace kigafarceni ya shugabata hak'ik'a na zo maki da wani labari da zai sakaki cikin farin ciki.
Idanu Gimbiya Najla tazuba mata hakan yaba Kuyangar damar cigaba da maganarta dan tasan shugabar tasu ba me yawan hayaniya bace...
Yau 'yar uwarki tafita da bak'ak'en kuyanginta yawon bud'e ido inda ni kuma nayi amfani da tsafina nabisu batare da na bari ta ganni ba, wata k'asa ce me suna Miraj mukaje inda mutane ne suke rayuwa a k'asar suna rayuwa ta 'yanci sannan suna da arzik'i sosai k'asar tana cikin k'asashe da ake ji da su wajen dukiya sannan sarkinsu ya kasance me adalci saidai abinda zai baki mamaki su d'in suna bin wani addini sannan su mutane ne ba irin muba, kowane maye yana tsoron zuwa k'asar miraj saboda basu yarda da maita ba duk lokacin da suka kama maye basu barinshi suna had'a wuta me zafi suk'oneshi wannan dalilin ne yasa muke tsoron tunkarar k'asar tun shekaru d'ari biyu a chan baya, saidai wasu daga cikinmu sunsha suyi k'ok'arin zuwa k'asar sukama mutanen ciki wasu suna samun nasarar dawowa da ransu wasu kuma ana kamasu akashe.
Gimbiya Najla idanu tazuba mata tana saurarenta, cigaba tayi da cewa saidai abun mamaki da ban tsoro a yau d'innan wani mutum me shiga ta alfarma yanayinshi kawai zaki kalla kigane shi d'in jinin sarauta ne ya harzuk'a Gimbiya Najma da kalamanshi da yayi mata wanda taci alwashin d'aukar fansa bazata ta'ba barinshi ba dan a yanzu haka ta tura bak'ak'en kuyanginta dan sugano mata asalin mutumin......
____*****_____
....A yanzu nice shugabarku nice shugaba a k'asar Nairan ya zama dole kowane mahaluk'i yayi min mubaya'a fararen mayu da bak'ak'en mayu duk wanda yak'i haka zan kasheshi a yanzun nan,,, tana fad'in haka tazauna saman kujerar mulki...
Tsugunne take a gaban gawar tana ta rusa kuka nan wata kuyanga tashigo cikin sauri tamaida k'ofar tarufe cike da girmamawa tace ya shugabata ya kamata kitashi kibar masarautar nan dan a yanzu 'yar uwarki ta aiko azo akawo mata ke, jama'arta suna nan dayawa sun nufo d'akinki.
'Dago fuskarta tayi da tayi jajir saboda tsananin kuka takalli kuyangartata har ta bud'e baki zatayi magana sukaji anfara buga k'ofa dak'arfi, kuyangarce cikin sauri tanufo inda take tataimaka mata tamik'e tsaye..........
+++++++++++
...Ranka yadad'e ya kamata kaduba maganata baidace ace kamar kai ba a matsayinka na babban sarki ace d'anka yarima yana zaune babu aure bayan duk wata dukiya yana da ita shin idan baiyi aure yanzu ba sai yaushe zaiyi ko sai bayan mutuwarmu kaduba kaga 'yar uwarshi yadda take k'aunarshi tana binshi ammah ko kad'an baya kulata shin hakan da yakeyi ya dace kenan.....bud'e k'ofar da akayi aka shigone yasa taja bakinta tayi shuru saboda yanayin takun tafiyar da tajiyo yasa tagane Yarima ne, sai a lokacin sarki yad'ago kai yakalleta sannan yamaida kallonshi ga yarima d'an da yad'auki son duniya yad'aura mashi.....
_____
..Ya kamata ace Gimbiya ta fito a wannan ranar anyi girkin masarautar nan da ita kar kumance hakan shine al'adar masaraurar nan duk amaryar da aka auro acikinta dole ne bayan sati biyu tafito tashiga kitchen dakanta tagirka abincin da Yarima, sarki da sarauniya zasu ci a ranar nan wannan sak'one aje afad'a ma gimbiya!!!
Wata kuyanga ce cikin sauri tamik'e tafita dan ta isar da sak'on uwargijiyarta.
Wadda tagama bayanin juyawa tayi takalli Sarauniya mahaifiyar yarima da itama take kallonta nan tasakar mata murmushi mai cike da ma'anoni sannan tawuce gaba inda sauran kuyanginta suka take mata baya.
A lokacin da sak'on ya iso agareta tsaye tayi tarasa ta inda zata fara, k'arar k'araurawa tajiyo daga waje nan tafara jiyo muryar jakadiya tana cewa a yau ranar murnar ce agaremu auren yarima da gimbiyarshi ya cika sati biyu a yanzu haka muna jiran fitowar gimbiya zatazo tagirka ma yarima da iyayenshi abinci me dad'i wanda zasuci dan nuna farin cikin wannan ranar.
Kallon agogo tayi da daidai lokacin k'arfe sha d'aya daidai tabuga saurin matsawa tayi tad'age labule nan taga yanayin gidan ko akwai rana sosai.
Ja tafara yi da baya cike da tashin hankali tana tunanin ta yadda zata iya fita a wannan lokacin dan ta san ba irin wannan lokacin bane lokacin fitarta.....
*_KUWWA DA KUWWA....._*
(Bata korar buzu)
Labarin ya sha banban da wanda kuka saba karantawa.
shima ga duk me buk'ata zai sameshi akan farashi naira d'ari biyu (200), saidai bazan fara sakinshi ba har sai na gama typing d'in part 1.
Kar kubari abaku labari
Kukasance da ni acikin sabon free novel d'ina wanda yake tafe gajeren labari me suna *NADAMAR RAI*
_Taku har kullum sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-Nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
PART TWO
_~GORON SALLAH~_
*PAGE 1*
Kwance yake saman makeken gadonshi yad'age kanshi sama yana kallon Ceiling tare da lumshe idanunshi kamar me bacci ammah azahiri tunani yake rayuwar jawahir kawai yake tunani akan irin gwagwarmayar da tasha, tambayar kanshi yafara yi daman ashe tana da aure? Toh ina mijin nata? Meyasa bai ta'ba ganinshi ya je wajenta ba??tambayoyin da suka dinga mashi yawo kenan a k'walwa saidai me a gefe d'aya Allah Allah yake yi gari ya ida wayewa yayi wanka yatafi gidan kaso na mata dan yagana da ita dan ya fi so ya ida samun full details kafin yafara aikinshi,,,, yana cikin wannan