Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   47 / 74

138K to 141K   out of 220.3K words

akula da lafiyarshi, bud'e mashi mota akayi yashiga motoci biyar ne a gaban wadda yake ciki sai biyar a bayanta duk na masu kula da shi, yana zaune a gidan baya ya kame nan wayarshi tafara ringing.
'Daukota yayi yai picking fuskarshi d'auke da murmushi yake wayar yana cewa nan da mintuna kad'an zan iso gida kujirani, wani irin burki da aka ja ne yakatseshi daga wayar da yakeyi cikin 'bacin rai yakalli driver d'in yace bakada hankali? Ko bakasan aikinka ba da zaka wani ja burki haka?
Ahankali yace kayi hak'uri megida nan yaja motar suka cigaba da tafiya.
Camera d'in wayarshi yabud'o dan yad'auki kanshi hoto dan yatura ma iyalanshi kamar yadda suka buk'ata nan yak'yalla juyo da wayar yayi dan yaga hoton da yayi abinda yagani ne acikin wayar yai mummunan d'aga mashi hankali nan take yafara zufa cikin d'aga murya yace ma driver tsayar da motar nan!!!

K'iiittttt driver yaja mota yatsaya, security na ganin haka su ma duk suka tsayar da motocinsu, Alhaji Tanimu yana jin mota ta tsaya baijira aka bud'e mashi ba yabud'e dakanshi cikin sauri yafita yatsaya tsakiyar security yana mazurai.
Tambayarshi sukayi ko lafiya.
Hoton da yad'auki kanshi yanuna masu yace kuduba kugani wallahi aljanah ta biyoni har ta shigar min a hoto

Amsar wayar sukayi cikin sauri suka duba sai kuma suka mik'a mashi sukace basuga komai ba.
Amsa yayi yasake kallo shima baiga komai ba nan yasaki ajiyar zuciya.

Driver d'inshi ne yace ranka yadad'e k'ila idanunka ne sukayi maka gizo kaga kamar aljanah ammah ni dai banga komai ba.
Katseshi yayi yace dallah malam rufe ma mutane baki, yanzu kowa yashiga mota mucigaba da tafiya


Kowa komawa yayi yashiga mota nan aka cigaba da tafiya.

Alhaji Tanimu zaune yayi yai shuru duk a tsorace yake dan shi macemacen nan sun d'aga mashi hankali sosai musamman ma ta k'anenshi ya zama dole da ya yi masu gaisa zuwa gobe zai tattara iyalansa sukoma chan Europe da zama dan chan yafiye mashi kwanciyar hankali.

Yana cikin tunanin wayarshi tafara ringing dubawar da zaiyi da mamaki sai ganin number d'in Malam Salahu driver d'inshi yayi mamaki duk yakamashi yace wannan kiran fa bayan gashinan yana tuk'i shine kuma yake kiranshi.
Sharewa yayi har ta tsinke a karo na biyu wani kiran yasake shigowa da wata sabuwar number, tsaki yaja sannan yai picking daga chan 'bangaren yaji muryar driver d'inshi ya ce 'Dallabai gani na iso Airport d'in banganka ba kuma antabbatar min cewa jirginku ya safka.

Cikin Alhaji Tanimu murd'awa yayi sai ji kayi wani abu k'ululululuuu lokaci guda tsoro yad'arsu a ranshi yace Salahu kana nufin ba kai bane kazo d'aukata?
Daga chan 'bangaren cikin rashin fahimtar maganar megidan nashi yace 'Dallabai ai cemin kayi sai goma da ishirin saisa ban zo ba sai yanzu, Alhaji tanimu sakin wayar yayi a tsorace yalek'a mazaunin driver dan ganin wanene zaune sai gani yayi wayam motar babu kowa ita kad'ai take tafiya.
K'ara yasaki da dukkan k'arfinshi baisan lokacin da fitsari yakubce mashi ba nan yakai hannu zai bud'e murfin motar yafad'a waje dan bai damu da ko yaji ciwoba indai zai fita yatseratar da rayuwarshi sai ji yayi k'ofar a rufe take, bubbuga glass yashiga yi yana k'walah ma security kira a tunaninshi ta hakan zasu jiyoshi ammah babu ma wanda yasan yana yi, k'ara kallon mazaunin driver yayi yaga ba kowa still dai motar ita kad'ai take tafiya sai shi da yake zaune a cikinta, nan take yasume a inda yake zaune.........












_Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_



*PAGE 6*

....Kamar an tadashi haka yafarfad'o daga suman da yayi nan yafara tunani Allah yasa mafarkine ba gaske ba abinda yagani, k'ara lek'awa yayi yaga motar dai ita kad'ai ce take tuk'a kanta nan gabanshi yacigaba da dukan ukku ukku, motsin da yajine a kusa da shi yasa yai zumbur yawaiga, wata mata ce yagani zaune gefenshi sanye cikin shiga ta alfarma ta dad'e fuskarta da bak'in glass ta juya baya tana kallon tagar mota.
Saurin ja da baya yayi tare da jinginewa a jikin murfin mota kan kace mi zufa ta wanke mashi fuska dak'yar yabud'e bakinshi yana rawa yace dan Allah kiyi hak'uri kitafi ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba.
Juyowa tayi tare da bushewa da wata irin mahaukaciyar dariya, ahankali glass d'in fuskarta yacire kanshi nan take kyakkyawar fuskarta takoma wata irin mumunan halitta wadda ta ida firgitashi, har saida yakusan sake wani sumar yaji an wanka mashi wani gigitaccen mari ba shiri yafarfad'o, wata irin k'ara yasaki a tsorace tare da kai hannu zai bud'e k'ofar motar sai ji yayi an rik'e mashi hannu gam har saida yasake sakin k'ara.
Wata irin mummunan murya marar dad'in saurarece tafara fitowa daga bakin matar muryar da tasa gabad'aya motar saida ta amsa....Alhaji Tanimu bazan ta'ba barinka ba yadda kayi silar mutuwar mijina kaima ya zama dole kamutu!!!
Cikin Alhaji Tanimu katsawa yayi baisan lokacin da yafara zawo ba, cikin rawar murya yace kiyi hak'uri wallahi bansan komai ba, babu wanda nakashe dan Allah kibarni da raina.
Bushewa tayi da wata mahaukaciyar dariya tace bai kamata ace ka mance zunubin da ka aikata ba na kashe Alhaji Muhammad.
A firgice yamaimaita sunan yace Alhaji muhanmad?
Maimakon tabashi amsa sai cewa tayi kaduba kaga motocin da suke zagaye da kai gaba da baya saidai duk da wannan tsaron ya zama dole kamutu domin na dad'e ina jiran wannan ranar bayan kun raba mijina da ranshi ni kaina baku barni ba saida kuka ga bayana sannan dukiyar d'iyata kun cinyeta saboda zalunci irin naku.
Had'e hannuwa yayi waje guda jikinshi yana rawa yace dan Allah kiyi min rai wallahi bansan komai ba akai indai dukiya ce nayi maki alk'awali zan mallaka maki dukan abinda namallaka kar kikashe ni.
Cikin k'araji tace mutuwarka ta zama dole Tanimu rayuwarka batada sauran amfani domin maha'inci irinka baidace yacigaba da rayuwa ba, duba agogo kaga daidai lokacin da yadace kamutu ya yi nasan bakada wata wasiyya da zaka bayar tunda babu ma wanda zaka ba a kusa.
Alhaji Tanimu yana yin yunk'urin yin magana sai ganin hannun matar nan yayi ya cafki wuyanshi, numfashinshi d'aukewa yafara yi nan yacigaba da yunk'urin magana ammah yakasa, dariyar mugunta tashiga k'yalk'yatawa, nan idanuwanshi duk sukayo waje saboda tsananin shak'a, jijiyoyin kanshi duk suka mimmik'e hannu yasa zai k'wace kanshi daga mak'arar da tayi mashi ammah baida k'arfin haka dan gabad'aya k'arfinshi ya tafi nan yafara shure shuren mutuwa, saida taga jikinshi ya saki alamun ya mutu sannan tak'yaleshi tabushe da wata irin mahaukaciyar dariya daidai lokacin motar tafara kauce layi tana tafiya tana karkacewa lokaci guda tatsaya a saman titi nan duk sauran motocin suka tsaya ana tunanin lafiya motar Alhaji tai irin wannan tsayawar cikin sauri duk suka fito suka nufi wajen motar suna zuwa suka k'wank'wasa glass ammah shuru, sun dad'e tsaye a wajen ganin suna neman had'a go slow yasa d'aya daga cikinsu yafasa glass d'in da mamaki sai ganin Alhaji sukayi a kwance shi kad'ai cikin motar babu driver cikin sauri suka bud'e motar ganin kokad'an baya numfashi yasa suka d'aukeshi cikin sauri suka nufi asibiti inda wasu suka tsaya suka kira jami'an tsaro nan da nan titi yacika da mutane ana ta kora jawabi saidai abinda yafi d'aure masu kai babu driver kuma tunda suke tafiyar basuga lokacin da mota tatsayaba har driver yafita suna cikin wannan halin ne wayar Alhaji Tanimu tafara ringing d'aya daga cikin jami'an tsaro ne yad'auko wayar ganin driver d'in Alhaji ne yake kira yasa yai picking batare da ya yi magana ba, daga chan 'bangaren akace Alhaji ga dai ninan airport d'in ina ta jira ko jirgin da yasafka ba naku bane?
Jami'in tsaro ne yace kana magana da jami'an tsaro muna buk'atar ganinka a yanzu.
Wani wahalallen yawu yahad'e yace 'yalla'bai lafiya? Me yake faruwa? Ina Alhaji?
Bai bashi amsaba saidai yafad'a mashi inda zaizo yasamesu.


Cikin dak'ik'a kad'an ya iso wajen cikin d'aya daga cikin motocin Alhaji nan fa kowa mamaki yakamashi DPO yakalli security's yace wannan shine kuke nufi?
Sukace eh Ogah shine mune dai zai raina ma hankali yafita bayan ya kashe Alhaji yaje yad'auko wata motar.

Cikin rashin fashimtar maganarsu driver yace d'alla'bai me yake faruwa ne? Ina Alhajin?
DPO yace koma menene muje station yanzu a chan sai kayi bayanin komai.
Bayani kuma? Wani abune yafaru d'alla'bai?
Maimakon yabashi amsa sai ma ankwa da yasaka mashi nan suka tafi da shi station.


Koda aka kai Alhaji Tanimu asibiti nan aka tabbatar da mutuwarshi dan haka aka d'auki gawarshi aka kai gida hankalin iyalenshi ya tashi sosai nan sukaita kuka.
DPO ne yafad'a masu wanda ake suspecting da yin kisan nan fa kowa yaita mamaki.





Barr Faruk ya shiga damuwa sosai lokacin da yaga wannan go slow da aka had'a na abubuwan hawa ba adadi ya yi tsaki ya fi ak'irga musamman da yaga babbar mota ce tahad'a wannan go slow d'in, lokacin da yasamu damar wucewa yana isa airport yatarar jirgi tuni ya safka dan haka yafara tunani ina ma zaiyi shin wajen jawahir zai koma ko kuma zai je gidan Alhaji Tanimu nepa? Daga k'arshe yayanke shawara da yaje gidan Alhaji Tanimu nepa kasancewarshi babba yasa gidanshi yakasance ba 'boyayye bane dan haka yaja mota cikin sauri yanufi hanyar gidan.




Lokacin da ya isa daidai lokacin aka kawo gawarshi daga asibiti a gaban idanunshi iyalenshi suka dinga kuka suna zubewa, hankalin Barr Faruk ba k'aramin tashi yayi ba cikin ranshi yace wannan aikin jawahir ne, buga motarshi yayi da k'arfi a fili yace jawahir bansan irinki ba kin cika taurin kai, ganin yadda dangin mamacin suka tashi hankalinsu duk sai abun yabashi tausayi dan haka yashiga motarshi yabar gidan.





Koda aka tafi da driver chargi office tambayarshi aka yi akan mutuwar Alhaji Tanimu yanace akan baisan komai ba akai nan fa aka dinga dukanshi ammah yanacd da cewa shi dai ba shi yazo d'aukar Alhaji Tanimu ba dan a lokacin ma bai fito daga gida ba kuma koda sukayi wayar farko da Alhaji yafad'a mashi lokacin da zaizo d'aukarshi sai kuma daga baya yakirashi yace yabari sai goma da rabi lokacin jirginsu zai safka saisa ma baizo ba a lokacin sai wajen k'arfe goma da rabi, cikin galabaita yace ammah wallahi ba nine nazo d'aukar Alhaji ba.
Tsayawa DPO yayi yana kallonshi yanayin yadda yai maganar babu alamun k'arya a cikinta, jinjina kai yayi yace taya zamu tabbatar da hakan bayan motar Alhaji ce wacchan ma toh wanene yad'aukota bayan kowa kai yagani.
Cikin kuka yace wallahi iyakar gaskiya ta ce nafad'a maku bani bane ni lokacin ina gidana.
DPO kallon police d'in da yake tsaye wajen yayi yai mashi nuni alamun yazo zasuyi magana dan haka yabiyoshi suka fita.

Bayan sun fitane DPO yakalleshi yace gaskiya wannan lamarin akwai d'aurin kai a ciki banga alamar mutumin nan shine yai kisan nan ba.
Yace Eh gaskiya nima na lura da haka dan jiya da mukaje gidan mukayi tambaya megadi ya ce mana yaga anfita da mota kasancewar glass d'in motar bak'ine yasa bai gane wanda yake cikiba ammah ko a lokacin ya san Driver yana cikin Quarters d'in gidan saisa baikawo komai a ranshi ba dan ya san shine kad'ai yake fita da motar toh bayan wasu mintuna kuma ya ga driver ya fito da wata motar har suka gaisa yace Alhaji zai je yad'auko airport ya san yanzu jirginsu yana gab da safka nan megadi yayi mashi adawo lafiya iya abinda yasani kenan bai kawo komai a ranshi ba game da fitar wacchan motar ta farko kuma akwai tazarar kusan rabin awa tsakanin fitar wacchan motar da wadda driver yafita da ita, babu alamun da yanuna na cewa ya ga dawowar driver bayan fitar motar farko.
Fuzgar da iska DPO yayi yace tabbas hakane dan daga airport zuwa inda aka kashe Alhaji Tanimu tafiya ce me d'an nisa ammah ya akayi haka bayan kowa ya ce shine yagani a cikin motar sannan a lokacin da aka kashe Alhaji Tanimu ba'a ga tsayawar motar ba bare ace anga fitar wani toh wai duk ya hakan tafaru?
Shuru officer yayi yana nazarin maganar DPO chan DPO yace saidai idan har wanda yai kisan layar zana yayi yafita daga motar toh ammah taya hakan?,,, ahankali yace jawahir fa? Juyowa yayi yakalli officer yace ina tunanin wani abu akan haka yanzu kuyi sauri kuje kubincika min motar da aka kashe Alhaji kuga ba wani hoto da aka ajiye a ciki.
Ohk Sir angama.



Barr Faruk koda yakoma gidan kaso samun Jawahir yayi zaune ta zuba ma gefe d'aya idanu yana isa cikin d'aga murya yace menene haka kika aikata? Tabbas nasan kece kika kashe Alhaji Tanimu miye amfanin shara'ar da ake da har bazaki iya hak'ura kotu tak'watar maki hak'k'inki ba.
Mik'ewa tayi tsaye tana kallonshi ido cikin ido cikin murya me kama da ta kuka tace bana son kotu tak'watar min hak'ina nafiso ink'wata dakaina shin ni a lokacin da suka kashe min nawa iyayen wanene yak'watar min nawa hak'in? Hawaye ne suka fara gangaro mata a idanunta tace babu wanda yai k'ok'arin taimakona haka aka banzatar da maganar mutuwar iyayena sai kace ankashe dabba, shin kuna tunanin hakan baimin ciwo ba? Ko kuna tunanin 'ya'yansu zasu shiga damuwa kamar yadda nashiga? Ko kad'an bazasu shiga damuwa kamar ni ba saboda su mahaifi kawai suka rasa ni kuma har da mahaifiyata narasa.
tsaye yayi yana binta da kallo matsawa tayi gaba kad'an tajuya mashi baya sannan tacigaba da cewa na rasa duk wani farin cikin rayuwata tun bayan rasuwar mahaifiyata a da ina ganin kamar bayan ran mahaifina ina da sauran gata tunda ga mahaifiyata ashe ba haka bane ita kanta saida suka rabani da ita, ban sake kwatanta shiga farin cikiba sai da yaya umar yashiga rayuwata ashe wannan ma nad'an lokaci ne, duk saboda dukiya suka rabani da kowa nawa sannan sukayi amfani da dukiyata duk wannan bai ishesu ba ina a cikin gidan nan sun je sun kwashe files d'in filayen da suke mallakina shin ni me na'aikata wanda ba daidai ba a nan? Juyowa tayi takalleshi tace dan kawai na rama abinda akayi min shikenan na aikata kuskure? Zalunta ta fa akayi ammah ba wanda yataimaka min sai yanzu da nasamu wacce take taimaka min sannan za'a ce banyi daidai ba?

Barr Faruk jikinshi sanyi yayi sosai cikin sanyin murya yace ba wai haka ba jawahir ni ina tare da ke zan taimaka maki nafiso sugurfana a gaban kotu dan su wankeki daga laifin da ake zarginki da shi.

Cikin muryar kuka tace ba wai zargi bane dagaske ne duk na kashesu kuma ban ta'ba nadamar hakan ba ina da burin in ida kashe sauran inyaso nima kotu tayanke min hukuncin kisa zanfi farin ciki da hakan.

Jawahir duk kibar wannan kiyi yadda nace maki na maki alk'awali zan taimaka maki na ganin an hukunta duk wani me laifi ko da ace d'an uwanane ko wani makusancina yake da hannu a ciki na maki alk'awalin sai na gurfanar da shi a gaban kotu, abu guda kawai zakayi shine kisanar da ni sauran suwanene? Sannan ina kawunki da umar?

Girgiza kai tashiga yi tace wannan ne ban saniba abinda dai nasani shine na kashesu, na kashe yaya umar da hannu wannan shine nadamar da nayi a rayuwata,,,, ta k'arashe fad'a tare da fashewa da kuka.

Mutuwar tsaye barr faruk yayi yace dagaske kin kashesu?

Ban san ya akayiba ta rabani da rabin raina dan kawai bata k'aunar aurenmu da shi bansan dalilin kasheshi ba kawai dai abinda nasani....tana zuwa nan sai kuma taja bakinta tayi shuru.

Ganin haka yasa Faruk yace jawahir kikwantar da hankalinki kiyi min bayanin komai nayi maki alk'awali zan taimaka maki.

Cikin sanyin jiki tace bansan me zan ce ba barrister ammah duk wani bayani yana cikin memory card d'in yaya umar.

Taya zan samu memory card d'in?

Girgiza kai tayi tace bana tunanin samunshi zai kasance acikin sauk'i.

Cikin rashin fahimtar maganarta yace meyasa bazai kasance acikin sauk'i ba, kar kidamu kifad'a min inda zan samoshi.

Shuru tayi na d'an lokaci sannan tace banaso wani abu yasameka saboda ni na tabbata bazata ta'ba barinka kaje kad'auko ba.

Kinga jawahir kicire komai a ranki kifad'a min insha Allahu ni zan je ind'akko shi.

Wucewa tayi wajen 'yar tagar nan tatsaya sannan tace yana a chan cikin gidanmu ina tunani a babban parlor saidai nemanshi ba abune me sauk'i ba a k'asa nayada shi nima kaina ban iya cewa ga inda yake ammah wani lokaci zan kwatanta tuna inda yake.

Jinjina kai Barr Faruk yayi yace shikenan ni zan je ind'auko shi kikwantar da hankalinki.
'Daga kai kawai tayi alamun toh sannan takoma tazauna tare da had'e kai da gwiwa tana jin wani irin ciwo a ranta dan ya ta'bo mata inda yake mata k'aik'ayi.
Ganin haka yasa Barr Faruk yajuya yafita.




Ko da police suka je suka bincika motar basu samu wani hoto ba dan haka suka koma suka sanar da DPO duk da haka saida yakira Alhaji Mahadi yatambayeshi jawahir yashaida mashi tana nan cikin gidan yarin ba'a fita da ita ko'ina ba.


Saida Drivern Alhaji Tanimu yayi kwana ukku a wajensu suka tabbatar da badai shi d'in bane yai kisa sannan suka sakeshi kisan ya d'aure ma kowa kai nan jama'a suka dinga tunanin aljannu ne inda DPO yafi tunanin da sa hannun jawahir a ciki saidai baida shaidar da zai iya zarginta ya dai bar abun a ranshi.










_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in

47 / 74