Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
yadda kuke 'yar tsama akan case d'in yarinyar nan.
Ta'be baki Barr Faruk yayi yace koma menene dasannu zan wanke Jawahir daga zargin da ake mata.
Toh Allah dai yataimaka.
Ameen.
_________
Abban Nasiba ne yashigo yasameta Zaune ta tisa waya a gaba tana kallo ta shagala da kallon wayar bata ji shigowar mahaifinta ba, Alhaji Sufyan matsowa yayi idanuwanshi akan wayarta suka safka, girgiza kai yayi yace Nasiba har yanzu dai kina nan akan bakanki bazaki iya daina tunanin Faruk ba, inbakayi wasa ba sai na k'wace wayar nan tunda hotunanshi kike kallo a cikinta.
Saurin janye wayar tayi takifata a jikinta sannan tatashi zaune tare da sadda kanta k'asa.
Cigaba yayi da cewa kikwantar da hankalinki indai Faruk rabonki ne zaki sameshi kidaina sa damuwa a ranki kar kija ma kanki wani ciwon shi yana chan baima san kina yi ba.
'Dagowa tayi takalleshi tace toh Daddy insha Allahu zan kiyaye.
Amsawa yayi da yauwa 'yar lele haka nake son ji, tashi kije kikira min Hajiyarki sannan kije dining ga icecream chan na sawo maki dan nasan kina sonshi sosai.
Murmushi tayi tace toh Daddy nan tamik'e tatafi.
Bin ta yayi da kallo tare da girgiza kai yazauna saman kujera sannan yace Allah yakyauta.
_Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:13 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 11*
Tsawon kwana biyu Barr Faruk yad'auka yana tunanin hanyar da zaibi yashiga gidan Alhaji Tanimu har yasamu damar zuwa d'akinshi yad'auko wayar saidai babu hanyar da yaga zata 'bule mashi dan ranar sadakar ukku ma saida yaje gidan da sunan gaisuwa yaje masu hatta parlorn Alhaji Tanimi ya shiga yai ma 'yan uwanshi gaisuwa dan a cikin parlorn wasunsu suka zauna saidai hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba nan yasare yasan hakan saidai a mafarki zai iya faruwa.
A gefe d'aya ga Ammin Jawahir da tatakura mashi dan kusan kullum sai ya yi mafarki da ita ko kuma cikin dare tatasheshi daga bacci ayi ta tsorata shi.
Yau ma bayan ya gama had'a bayanenshi wajen k'arfe sha biyun dare ya gama shirin kwanciyarshi har ya kwanta nan ya
fara jiyo motsi kamar ana hawan step, ana kiran sunanshi tashi yayi zaune cikin ranshi yace tabbas nasan itace , jiyayi ana cigaba da hawa babu k'ak'k'autawa yanayin yadda ake taka benen kamar irin ansa takalmi masu tsini, sai ji yayi anfara k'wank'wasa mashi k'ofa, magana yafara jiyowa kamar ta mahaifinshi yana tambaya wanene nan?
Cikin sauri Faruk yamik'e yaje yabud'e ammah baiga kowaba dan haka yafita sai ganin Dad d'inshi yayi tsaye a chan wajen part d'insu gaban Faruk saida yafad'i ahankali yace ba dai tado su Dad tayi ba, muryar Dad yaji yana cewa Faruk wanene yake k'wank'wasa k'ofa na fito zan d'auki ruwa marassa sanyi dan na cikin freezer d'in part d'ina duk sunyi sanyi shine naji kamar ana knocking d'in k'ofa.
"Dad babu kowa nima ruwan nafito ind'auka ammah banji k'arar k'omai ba",, Cewar Faruk.
Tsayawa Dad yayi yana kallonshi yace yanzu kai baka ji ba? Ni na jiyo ana kwank'wasawa kamar ma ta part d'inka.
Murmushi Yayi yace Dad ka fara tsufa ne saisa kaji haka nidai da nake sabon jini ban jiyowa.
Girgiza kai Dad yayi yana murmushi yace kai ko faruk shikenan dai yanzu koma kakwanta k'arfe d'aya ta yi.
" Toh Dad kaje kakwanta bari inje ind'auko ruwan ammah dan Allah kadaina fitowa a wannan lokacin kaga darene".
Shikenan Faruk zan daina nima dai saboda k'ishin da nakeji yasa nafito ammah zan daina, je kad'auko ruwan bari intafi sai dasafe.
Yauwa Dad Allah yakaimu.
Saida yaga shigewar Dad sannan yafara safka daga saman step d'in ahankali yana lek'awa yaga ko zaiganta ammah baiga kowaba har yaje wajen fridge sai kuma yafara jiyo motsi achan tsakar gida har zai je yabud'e k'ofa yafita sai kuma yafasa dan ya san da ya bud'e sai su Dad sun jiyo kuma sai sun fito dan haka kawai yajuya zai koma part d'inshi sai jin k'ara yayi wajen kunnenshi wani irin shuuuuu kamar wucewar iska anbi ta bayanshi.
Juyawa yayi saurin yi tare da cewa wanene? Koma waye yabayya kanshi!!
Shurun da yaji anyi yasa yajuya yacigaba da tafiyarshi.
Yana zuwa part d'inshi shiga yayi batare da ya murza key ba yawuce yanufi bedroom tun kan yashiga sai ji yayi k'ofar parlor d'in da yarufe ta bud'e kanta da k'arfi, juyawa yayi cikin 'bacin rai yace koma wanene yabayyana kanshi mana, shuru yaji dan haka yaje yayi bismillah yarufe k'ofar sannan yaje yashiga bedroom d'inshi, yana shiga hasken d'akin yad'auke daidai da ya rufe k'ofa, jingine jikinshi yayi da k'ofar ahankali yafara karanto addu'o'i, muryace yafara jiyowa daga wajen gadon shi tana tashi da k'arfi ana cewa barka da wannan lokacin Barr Faruk.
Cikin dakiya da nuna rashin tsoro yace koma wacece na ce ya kamata tabayyana kanta.
Dariya yaji an bushe da ita kamar irin haniniyar dokin nan saboda k'arfin dariyar har saida yayi saurin toshe kunnuwanshi saida yatabbatar da dariyar ta lafa sannan yasaki kunnuwan tare da cewa wannan alama ce ta matsoraci duk jarumi bayyana kanshi yakeyi, na san kece Ammin Jawahir shin menene yakawoki wajena ko nima d'in kinzo ne dan kiga bayana?
Tun kan yarufe baki yaji wata irin murya me tsoratarwa cikin k'araji tana cewa da ace kana da hannu a ciki da sai na ga bayanka a yanzun nan, sannan ni ce kad'ai yakamata intaimaka ma jawahir tabar gidan nan aduk lokacin da naso, ikona ne wannan ba naka ba saidai jawahir tana da taurin kai sosai ta kasa yin nadama akan kalmar tsanar da tajefeni da ita, kai d'in kuma baka burgeni koda kana k'ok'ari wajen ganin ka taimaki d'iyata dan haka ina gargad'inka da kayi baya daga case d'in nan, wannan shine kad'ai abinda yakawoni wajenka,,, tana fad'in haka sai ji yayi shuru nan hasken d'akin yadawo.
Murmushi yayi ahankali yace wannan ne kuma bazai yuwu ba dan ni nasa kaina kuma babu wanda ya isa yasani injanye ban damu da koma wacece ke ba dan baki gabana da mutane irina nake da lokacin jayayya,,, wucewa yayi yadudduba ko'ina bai gantaba dan haka yaje yahau gado tare da yin addu'o'i yakwanta ko kad'an tsoro bai d'arsu cikin ranshi ba dan ya san addu'a itace takobin mumini, saidai tunda yakwanta bai samu yarintsa ba kamar kullum yana ta tunanin mafita har wajen k'arfe hud'u sannan yad'an samu bacci kafin daga bisani yatashi lokacin sallar asuba.
Hankalinshi k'in kwanciya yayi ganin kwanaki goma ne kawai suka rage mashi wata dabara ce tafad'o mashi dan haka bayan ya yi breakfast yakira wani abokinshi Barr Nas a waya tare suka yi karatu har wajen aikinsu d'aya lokacin da yake aiki a SHARI'A COURT abokai ne sosai dan koda a yanzu ba wajen aikinsu d'aya ba suna tare, bayan sun gaisa ne yatambayeshi inda zai sameshi yafad'a mashi kasancewar weekend ne babu aiki, shiryawa yayi yad'auki system d'inshi da komai wanda zai buk'ata yashiga motar shi yanufi gidan Barr Nas yana isa daidai lokacin shima yashawo kwana Barr Faruk tsayawa yayi har saida ya iso da motarshi nan yafito yanufo wajen Faruk yana murmushi yace Barrister kace dai dagaske kake zaka zo.
Hmm dole kace haka tunda ka san baka gidan kaja nazo ashe da saidai inkoma.
"A'a Wallahi ban dad'e da fitaba na kai Madam gidane ina safketa najuyo dan kar kazo ban nan, yanzu dai mushiga da mota ciki.
Barr Faruk ba tare da ya ce komai ba yatada motar shi, saida Barr Nas yashiga tashi motar yayi horn megadi yabud'e masu gate sannan suka shiga da motocin, bayan sunyi parking ne suka nufi parlorn gidan Barr Nas yana cewa yau dai kamar a mafarki sai gaka a gidana ina ji rabon da kazo tun bikkina.
"Toh ka dai san yanayin aikin mu bamuda lokacin zama bare har inzo gidanka, yanzu ma haka akan aikine yasa kaganni"
Hmm nasan haka kai kullum da aiki kake fakewa, malam muma fa duk aikin nan muke irin naka ammah a haka muna samun lokacin ziyara kai ko kullum saidai kabada wani uzuri, ko dai Nasiba ce take 'boye mana kai tun ba'ayi bikkin ba?
Murmushi yayi jin an ambaci sunan abun son shi saidai a ranshi yana tunowa da wani abu yasafke ajiyar zuciya yace Nasir muyi maganar da takawoni wajen ka.
Toh shikenan Barr ina saurarenka.
Barr Faruk yace daman wani taimako ne nakeso kayi min dan nasan kaine kad'ai zaka iya yimin yadda nakeso,
Gyara zamanshi yayi yace wani irin taimako ne wannan koma wane iri ne kafad'a zanyi maka indai baifi k'arfina ba koda ma ya fi zansan yadda zanyi intaimakeka.
Murmushi yayi sannan yace ranar sadakar ukku watau jiya na ga motarka ka fita daga gidan marigayi Alhaji Tanimu Nepa ni kuma lokacin nashiga gidan zanyi masu gaisuwa, shine nakeso inji ya kake da shi daman ka sanshi?
Allah Sarki ai Alhaji Tanimu Mahaifin abokina ne Nazir tare mukayi secondary school da shi muna mutunci sosai da shi, shi naje ma gaisuwa dan kusan tun ranar da akayi rasuwar kullum sai na je.
Wani irin sanyi Faruk yaji a ranshi har saida farin ciki yabayyana a fuskarshi Alhankili yafurta Alhamdulillah.
Da mamaki Barr Nas yake kallonshi yace lafiya Barrister me yafaru naga kana fara'a?
Lafiya lau Nasir na ji dad'i sosai da jin bayananka a yanzu ina da k'warin gwiwar samun abinda nakeso watau wani case ne me zafi mukeyi shine nake son kataimaka min a ciki kayi min jagorar zuwa gidanshi.
Cike da mamaki yace case kuma? Wane irin case ne haka? Ko akan kisan da ake zargin anyi mashi dan naji anata jitajitar kasheshi akayi saidai anrasa wanda yayi kisan dan ajiya ma aka sako driver d'inshi an wankeshi daga zargin da ake mashi, saidai har yau anrasa wanda yayi kisan ana tadai bincike ankasa samun k'wak'k'warar shaida za'a iya kama wanda yayi laifin.
Tsayawa yayi yana saurarenshi har yakai aya nan yarasa me zaice tunani yafara yi yasanar da shi komai akan case d'in jawahir ko kuma yayi shuru abunshi,,
Muryarshi yace yaji ya ce ya dai Barrister ka yi shuru lafiya dai ko?
Girgiza kai yayi yace babu komai saidai kawai.....shuru yayi batare da ya k'arasa fad'in kalmar da take bakinshi ba.
Ganin haka ya Barr Nas yatashi yakoma kusa da Barr Faruk bisa 2 seater d'in da yake zaune sannan yace Faruk kayi min bayanin koma menene zan fahimceka kuma zan taimaka maka saboda ka cancanci haka.
Har cikin ranshi ya ji dad'in bayanin abokin nashi sosai kuma ya san tunda har yafurta toh zai taimaka mashi dan tun a makaranta baya da aboki kamarshi da Barr Junaid dan duk tare sukayi karatu har gama makarantar su sannan wajen aiki d'aya saidai Barr Junaid ne kawai a lokacin baiyi zurfin karatu kamar nasuba dan shi daga HND yatsaya su kuma har masters sunyi saisa sukafi shak'uwa da Barr Nasir sai daga baya ne dayakoma a kotun da Barr Junaid yake aikine abotarsu tak'ara k'arfi,,, jijjigashi Barr Nas yayi yace wai lafiyarka Faruk sai wasu tunane tunane kakeyi ya kamata kanutsu kafad'a min koma menene.
Shikenan Nasir zan sanar da kai komai yanzu nasan zaka taimaka min, bayan na baro court d'inku anmaidoni a nan HIGH COURT shine natarar ana wani case wanda bayan rasuwar lauyan da yake jagorantar case d'in yake kare wadda ake k'ara shine ni kuma na amshi case d'in yadawo hannu na dan kare wadda ake k'arar a lokacin da na lura tana buk'atar taimako ana nema atauye mata hak'k'i mutane da dama sun nemi su fahimtar da ni had'arin da yake cikin case d'in ammah ni duk wannan bai dameniba burina d'aya shine inwanke wadda ake k'arar a idanun duniya........
Kwashe komai yayi akan case d'in Jawahir yafad'a mashi saidai ya 'boye mashi gaskiya a game da Fatalwar da ke tare da jawahir har tsorata shi da ake babu abinda yafad'a mashi.
Hankalin Barr Nas ya tashi sosai da yaji labarin saidai bai katseshi ba har saida yagama fad'a mashi komai sannan yace tabbas naji labarin case d'innan ko ba ita bace Jawahir Muhammad? wadda tayi kisa har takashe lauyoyinta saidai na ji labarin ya d'an sha banban da wanda kabani ammah tabbas ina tunanin itace.
Eh itace saidai abinda aka fad'a ba gaskiya bane Nasir ni kaina ina neman hujjojin da zan tabbatar ma mutane da haka saisa a yanzu haka nakeso kayi min jagora zuwa gidan Alhaji Tanimu dan akwai abinda nakeso ind'auko.
Tun kan yarufe baki cikin sauri Barr Nasir yamik'e tsaye yace ka san abinda kake fad'a kuwa Barrister?
Taya kake tunanin zamu iya shiga gidan Alhaji Tanimu har wai kad'auko wani abu a d'akinshi batare da sanin kowa ba, ka san dai za'a iya kamamu idan har kuma hakan yafaru har kotu za'a banka mu sannan kisan da ake cewa anyi mashi mu za'a ce mun kasheshi gaskiya hakan bazai yuwuba kama daina wannan tunanin.
Shima mik'ewa yayi cikin sanyin jiki yace Nasir kar kadamu insha Allahu babu abinda zai faru zanyi k'ok'ari wajen ganin na yi komai batare da angane mu ba.
Cikin karaya Barr Nasir yace Faruk anya hakan zai yuwu da dai ka hak'ura kawai.
"Nasir kadaina cewa haka na yi maka alk'awari babu abinda zai sameka koma menene yafaru bazan ta'ba bari asakaka cikiba laifin gabad'aya nawa ne wannan alk'awarine nayi maka.
Ganin yadda yanace yasa Nasir ya amince sutafi, nan suka zauna yana cigaba da tayashi aikin da yake a nan sukayi azuhur yaba megadin shi kud'i yayo masu takeaway suka ci dan matarshi sai marece zata dawo.
Bayan sunyi sallar la'asar ne suka kama hanyar gidan Alhaji Tanimu inda gabad'ayansu zuciyoyinsu babu dad'i jikinsu ya yi sanyi sosai saboda basusan abinda zasu tarar ba idan sukaje, Barr Nas yake driving inda Barr Faruk yake zaune gefenshi yana ta sak'e-sak'e cikin ranshi har suka isa gidan suna zuwa aka hangame masu tankamemen gate d'in gidan suka cinna kan motar su a ciki,
Motocine sosai a parking space dan haka suka samu waje su ma suka ajiye tasu motar.
Barr Nas juyowa yayi yakalli Faruk yace Barrister wallahi ina jin tsoro sosai taya kake ganin shiga d'akin Alhaji tanimu zai yi mana sauk'i bayan akwai mutane sosai a cikin gidan.
Ajiyar zuciya yasafke yace nima ina tunanin haka Nasir saidai banda yadda zanyi tunda tun farko ni nayi ma yarinyar alk'awari zan taimaka mata kuma dole sai na samo wayar itace zata taimaka min nan da kwana goma inku'butar da jawahir dan da kwanaki goman nan sun shud'e na tabba za'a yanke mata hukuncin kisa dan wannan zaman shine zama na k'arshe da za'ayi, mushiga kawai in gwada sa'a ta.
Ammah ta ya kake tunanin zamu iya shiga cikin gidanshi har d'akin shi?
"Kar kadamu da wannan ni zan shiga ba kai ba bazan sakaka cikiba Nasir koma menene zai faru saidai yafaru da ni kad'ai yanzu fito mushiga ciki muyi masu gaisuwa dan inga yanayin mutanen da suke ciki.
Ajere suka tafi suna tsayawa suna gaisawa da jama'ar da suke zaune saman tabarma har suka shiga setting room d'in gidan inda dangin mamacin suke zaune suna amsar gaisuwa bayan sun gaisa sunyi masu gaisuwa Nasir yaduk'o da kanshi saitin fuskar Faruk ahankali yace banga Nazir ba ina tunani baya nan ammah bari intambaya, matsawa yayi kusa da k'anen Nazir da yake zaune chan k'arshen bango yatambayeshi inda Nazir yake yace mashi yana cikin gida dan haka suka tashi suka shiga koda matane a ciki ammah ahaka sukayi ta ratsawa suna gaishesu har suka shiga babban parlor inda suka samu matan mamacin zaune da mutanensu, gaishesu sukayi sannan Nasir yatambayi mahaifiyar Nazir inda Nazir yake tace yana chan part d'in Abbansu ya yi wasu bak'i kuje chan kusameshi kuce na ce ina jiranshi yakawo min keys d'in part d'in.
Barr Faruk kallon Nasir Yayi yai murmushi irin na da alama zamuyi nasara, girgiza kai Nasir yayi alamun a'a sannan suka mik'e suka nufi part d'in da yake mallakin megidan.
Tun da suka tunkari hanyar part d'in suka fara jiyo hayani alamun ana labari haka suka isa suna shiga suka tarar da su tsaisaye alamun tafiya zasuyi Nazir yana ganinsu yace A'a Barrister sannunku da zuwa.
Hannu suka mik'a masu duk aka gaisa sannan suka k'ara yi mashi gaisuwa.
Mutane ukkun nan da suke tsaye ne sukace mu zamu wuce Allah yajik'anshi yace toh nagode muje inrakaku, kallon su Barr Faruk yayi yace dan Allah kuzauna ina zuwa bari indawo.
abu daman ga wad'anda suke nema dan haka suka zauna haka yafita da abokanshi dan yarakasu.
Barr Faruk kallon Nas yayi cikin sanyin jiki yace ban san ta inda zan faraba barrister ammah bari infara ta'ba bedroom d'in inji idan bud'e yake, Barr Nas da yanuna alamun tsorata yace a'a Barrister kar fa ashigo aganka.
Batare da ya ce komai ba yamik'e cikin sauri yanufi hanyar da zata sadaka da bedroom d'in yana zuwa yamurd'a k'ofar yaji datse take gam nan fa duk yaji ba dad'i yadawo yazauna tare da dafe kai yace hakan bazai ta'ba yuwuwa ba nasan bazan yi nasara ba Nasir.
Ajiyar zuciya Nas yasafke yace kakwantar da hankalinka Faruk ko ma ba ta wannan hanyar ba insha Allahu zaka samu k'wak'warar shedar da zaka bayar.
Yana bud'e baki zaiyi magana suka jiyo taku alamun an nufo d'akin dan haka sukayi shuru sai ga Nazir ya shigo fuskarshi d'auke da murmushi yace kuyi hak'uri na barku ku kad'ai, wallahi abokaina ne da mukayi karatu da su a London
Sukace Allah sarki a'a babu komai, zama yayi yana kallon Barr Faruk yace kaima Barrister d'inne irin Nas ko?.
Murmushi yayi yace a'a shi dai ne lauya.
"Ayyah Allah sarki aini tun farko mancewa nayi da abokina babban lauya ne da shi zan saka acikin case d'in kisan da akayi ma mahaifina