Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   66 / 74

195K to 198K   out of 220.3K words

Ashe kina nan shine baki ko lek'o mu ko dan mahaifiyarki ai ya kamata kidinga zuwa wajenmu.

Jawahir kallonta tayi cikin muryar kuka tace ku ne dai baku nemana dan kunga iyayena basu raye.

Baba Malam ne yace a'a jawahir ba haka bane kiyi hak'uri wallahi bamuda laifi a ciki d'an uwan babanki ne bayaso muna zuwa gidanku ga su Musa nan kitambayesu kiji irin wulak'ancin da yake mana idan munje, ko bayan rasuwar mahaifiyarki saida mukaso yabamu ke mudawo da ke hannunmu ammah yak'i yaci mana mutunci yace kar yasake ganinmu gidanshi idan har ba zuciyar kare garemuba, Musa ko ba haka yace mana ba?

Wanda aka kira da Musa ne yace tabbas hakane Baba ni kaina raina ya 'baci da cin mutuncin da yayi mana ko bakomai khausar 'yar uwarmu ce baidace yahanamu zuwa ganin d'iyartaba

Dad ne yace gaskiya bai kyauta ba cin mutunci baida dad'i, ba adalci bane ace ya rabata da danginta ba.
Gyad'a kai Baba Malam yayi yace kaima dai ka fad'a bawan Allah raina ya 'baci sosai a duniyar nan yara hud'u namallaka ukku maza sai khausar ita kad'ai ce mace dole hankalina yatashi domin ita kad'ai ce talula wani gari tayi aure na san batada matsala da mijinta dan mutumin kirki ne saidai d'an uwanshi, wallahi tun bayan rasuwarta ban ta'ba kwana ba tare da na tuna jawahir a raina ba dan ina tausaya mata halin da zata shiga a hannun wannan mutumin.

Dad jinjina kai yayi yace gaskiya ne ai Alhaji Mu'azu baida kirki, kallon jawahir yayi da take ta kuka yace Jawahir kinji dai abinda sukace ya kamata kiyi masu uzuri, tunda basuda laifi a ciki.

Kallon Dad tayi tace hakane Dad na san duk Abba ne yaja min, babu komai na yafe.

Su duka sun nuna farin cikinsu nan Baba Malam yatambayeta ina su Abba ya akayi yabarta tazo,
Shuru tayi nan yayi murmushi cike da talaici yace wallahi Alhaji Mu'azu baida kirki wai har yayi maki aure batare da ya fad'a manaba saboda bai d'aukemu da darajaba saidai muji labari a wajen wasu, nuna Faruk yayi yace wannan ne mijin naki?

Girgiza kai tayi tace a'a ba shi bane.
Toh wanene? Baba Musa yajefo mata tambayar.
Shuru tayi tarasa abinda zata ce masu ganin haka yasa Faruk yace Jawahir ya kamata kisanar da su komai.
Fashewa tayi da kuka tace ban san abinda zan ce masu ba me zan fad'a masu? Infad'a masu duk na kashesu?

Su duka a zabure sukace kin kashesu kuma?
Faruk ne yace a'a Jawahir kidaina cewa haka.
Cikin kuka tace toh ai ko bance ba haka yake, Baba Malam bari insanar da ku komai, gyara zamanta tayi tare da k'ok'arin tsaida kukan da take sannan takwashe komai tafad'a masu tun daga mutuwar mahaifinta da mahaifiyarta har aurenta da Umar da kisan da suka dinga yi, hatta zamanta a gidan yari da taimakon da Faruk yayi mata babu abinda ta'boye masu.

Ba Baba Malam ba hatta 'yan uwan mahaifiyartata da kakarta saida suka yi kuka saboda tsananin tausayi, sukaita jimamin abun nan suka dinga yi ma su Faruk da iyayenshi godiya sukace bakomai.



Baba Musa yaje yasanar da iyalanshi bak'in da sukayi yace ashirya masu abinci inda shima Baba Bello ma haka sannan yakira k'anensu Baba Nura yasanar da shi zuwan d'iyar autarsu khausar nan da nan yabaro gona yazo gida.

Suna nan Driver ya iso garin ta waya akayi mashi kwatancen inda zaizo dan dama ya san garin sosai ahaka ya iso da motar.


Matan su Baba Musa da yaransu ne suka zo dan sugaisa da bak'i nan Baba Musa yagwada masu Jawahir inda suma yagabatar da su a wajenta, mata biyu yanuna mata da yara bakwai yace matanshi ne da yaranshi akwai wasu yaran nashi biyar suna gidan mazajensu, sannan yanun wasu matan biyu da yara goma yace na maibi mashi ne Baba Bello, sannan mata d'aya da yara biyar yace na Baba Nura ne, nan sukaita farin cikin ganin 'yar uwartasu inda itama tanuna mafarin cikin ganin dangin mahaifiyartata.


Hira aka dinga yi tsakanin su Baba Malam da su Dad inda Faruk yabi Baba Nura suka shiga gari yana nuna mashi garin nasu.


Saida sukayi sallar azuhur nan suka zauna a babban tsakar gida aka baje tabarma abinci aka dinga shigowa da shi daga cikin gida had'ad'd'en dambu ne wanda yasha zogale da Tuwon dawa miyar ku'bewa d'anya gefe d'aya kuma Fura ce wadda tasha zuma sai kaji soyayyu da madarar shanu da aka dafa masu haka suka zauna suka kwashi girki abincin sosai yayi ma su Dad dad'i dan sun ci shi sosai.


Bayan sun gama ne wajen k'arfe ukku Dad yace ma Faruk ya kamata yaje yayi masu booking d'in jirgin da zasu koma, Baba Malam yace ina bazai yuwuba sukoma yau saidai sukwana suka nuna a'a dan gobe akwai aiki kan dole yahak'ura yabarsu, Baba Nura ne yaraka Faruk yaje yayi booking d"in jirgin k'arfe shiddan marece sannan suka dawo.

Wajen k'arfe biyar Faruk yana waje shi da Baba Nura suna hira nan Baba Nura yamik'e yace bari yad'an shiga gida yafito Faruk yace toh ba damuwa yana shiga nan Faruk yakira Jawahir a waya dan a lokaci tana cikin danginta suna ta nan nan da ita kamar sumaidata ciki, ganin Faruk ne yake kiranta yasa tayi saurin yin picking.
Yana ji ta d'aga yace kifito waje Jawahir akwai maganar da nakeso muyi.
Amsawa tayi da toh nan tamik'e tafito tasameshi shi kad'ai,
Faruk murmushi yayi yace watau anga dangi har anmance da mu.
Itama murmushin tayi tace a'a Barrister ni na isa inmance da ku bana ma fatan haka.
Ajiyar zuciya yasafke yace toh Allah yasa, kiran sunanta yayi ta amsa sannan yace na so ace kin amince kizauna da mu dan Mom zatayi farin ciki da hakan ammah kin k'i, duk da banga laifin hakan ba dan kema zakifi jin dad'in zama da danginki.

Cikin sanyin jiki tace hakane Barrister na za'bi zama da dangina ba wai dan bazan iya zama da ku ba kod'aya kun cancanci hakan saidai kawai sune kad'ai dangina da suka rage min a duniya zan zauna da su inyi alfahari da hakan ko da nasan da banbanci irin zaman da zanyi a nan da kuma wanda nayi a gidanmu nan gidan jama'a ne ni kuma ba mace bace da tasaba zama cikin mutane saidai a haka na san zan koyi wani darasin a cikin rayuwa.

Tausayinta ne yakamata Faruk yace hakane Jawahir na san ma zaki ji dad'in zamanki da su dan su d'in dangine na gari mutanen kirki, saidai kina da dukiya a katsina bansan yadda za'ayi da gidaje da filayenki ba.
Murmushi tayi tace kabar wannan a hannunka kawai.
Toh shikenan zan ajiye maki ammah a duk lokacin da kika samo yadda zakiyi da su sai kisanar da ni yauwa kinga ga motar nan ya kawo maki sannan kiduba akwai akwatin kayan sawa a ciki.
Da mamaki take kallonshi tace kayan sakawa kuma? Wa yabani bayan na san banda su?

Ni na had'a maki dan naga bakida su kuma baki nema ba, Jawahir idan kinason wani abu kidinga fad'a min, na ce maki kid'aukeni a matsayin yaya kamar yadda kika d'auki Umar ina neman wannan alfarmar a wajenki jawahir.

K'walla ce tacika mata idanu tace na d'aukeka tamkar Yaya Umar shin ka amince indinga kiranka da sunan Yaya Umar?
Murmushi Faruk yayi cike da farin ciki yace na amince jawahir, nagode da wannan matsayin da nasamu a wajenki.
Itama murmushin tayi tace nice da godiya akan karamcin da kuka nuna min.
A'a kidaina godiya domin kin fi k'arfin hakan,,, Suna nan a haka Baba Nura yadawo nan suka zauna suna hira.


Wajen k'arfe biyar da rabi su Dad suka fito nan duk mutanen gidan suka rakosu a cikin motar Baba Musa suka shiga aka kaisu Airport, jawahir kasa fitowa tayi suyi bankwana a d'akin Inna Mairo tazauna taci kukanta dan duk sai taji ba dad'i tafiyar da zasuyi daga k'arshe ko da Baba Nura yashigo yace tafito suyi bankwana da su Faruk cewa tayi ace tana masu Allah yakiyaye bayi zata shiga yanzu.

Haka yaje yafad'a masu sak'onta, Dad yace Jawahir ko dai kuka take dan na ga koda zamu fito kamar zatayi kuka.
Baba Nura yace nima naga tana kukan ammah ta shiga toilet yanzu.
Su dukansu duk sai sukaji babu dad'i haka suka shiga mota suka tafi.

Tsaraba nik'i nik'i aka had'a masu cikin ledar Viva guda biyu saboda tafiyar jirgi ce, k'arfe shidda daidai jirginsu yad'aga suka kama hanyar katsina.




Tunda suka dawo gida duk sai suka ji ba dad'i da ba jawahir dan d'an kwana biyun da tayi sun saba sosai kamar ta yi wata,

Bayan sallar isha'i duk takirasu tayi masu barka da safka tare da masu godiya akan taimakon da sukayi mata.

Zamanta a cikin danginta ya yi mata dad'i sosai dan suna nuna mata so saisa nan da nan tasake sukaita hira, yayyen mahaifiyarta kowa ya so tazauna a 'bangarenshi ammah Baba Malam yace a'a a wajensu zata zauna dan haka suka hak'ura suka barta wajen iyayen nasu.


*BAYAN KWANA BIYU*

Su Nasiba sun koma a gidansu da Jawahir tamaido masu inda suka cigaba da zama ita da mahaifiyartata koda ba dad'in zaman suke ji ba saboda rashin Alhaji Sufyan ko ma ace tashin hankalin abinda yafaru, yayyen Nasiba kusan kullum sai sunzo gidan saboda mahaifiyarsu da tafi kowa sa damuwa a ranta dan har jininta saida yahau kwana biyu tad'an kwanta ciwo.


Nasiba ko abu goma da ishirin suka taru sukayi mata yawa bayan tashin hankalin da tashiga ta rashin mahaifi ga kuma soyayyar Faruk da take d'awainiya da ita saidai a yanzu tana tunanin kamar bazai sake saurarenta ba.

Yau ma dai tana zaune a d'akinta ita kad'ai ta buga tagumi tana tunanin masoyin nata, Aunty Sadiya ce tashigo tana mata magana ammah Nasiba bata ma san tana yi ba har saida tad'an ta'bata sannan tadawo hayyacinta saurin goge k'wallan da suka cika mata idanu tayi tace Yaya Sadiya yaushe kika shigo?

Zama tayi gefenta cike da jin tausayinta tace haba Nasiba wane irin abune kike haka kina ganin hankalin kowa ba'a kwance yakeba duk muna k'ok'arin danne damuwarmu saboda mahaifiyarmu yanzu da ace ta shigo ta ganki me kike tunani kinsan dai dole hankalinta yasake tashi, kinsan dai ciwonta.

Girgiza kai tayi tace Yaya Sadiya bazaku fahimceni ba, ba wai ina kuka akan Daddy bane a'a kawai ina kuka akan Faruk da nariga namallaka ma gabad'aya zuciyata wallahi yaya sadiya ina mashi son da ni kaina bazan iya misulta shi ba, ammah a yanzu Faruk ya tsaneni na san bazai ta'ba aurena ba saboda abinda mahaifina ya aikata wannan wace irin jaraba ce ya zanyi? Kifad'a min Yaya Sadiya ya zanyi Faruk yasoni?
Hannunta tajanyo tad'aura saman k'irjinta tace ji kiji yadda zuciyata take bugawa akan sonshi.

Tausayinta ne yakama Sadiya tajanye hannunta tare da zuba ma k'anwartata idanu da soyayya take nema tazautata.
Ganin haka yasa Nasiba tafashe da kuka tace kice wani abu Yaya Sadiya dan Allah kifahimceni na san Mummy ce kawai tasan irin halin da nake ciki gashi batada isassar lafiya bare yanzu intunkareta da maganar.

Dafata Sadiya tayi tace kikwantar da hankalinki Nasiba zan taimakeki nima na fahimceki kibani hankalinki gabad'aya zan fad'a maki yadda zakiyi kisamu Faruk.
Saurin goge hawayenta tayi tare da tattara hankalinta gaba'aya ga yayartata dan jin abinda zata fad'a mata.



_______

Mom ce zaune a Parlor tana kallo nan tafara jin sallama a wajen k'ofa.
Amsawa tayi tare da bada izinin shigowa.
Nasiba ce tashigo cikin ado kanta sadde a k'asa cike da jin kunya.
Mom na ganinta nan cikin fara'a tace a'ah wai Nasiba ce bismillah kishigo man.
Shigowa tayi a nutse taduk'a k'asa Mom tace miye haka zaki zauna k'asa kihau kujera man.
Girgiza kai tayi tace a'a Mom nan ma ya yi, ina wuni?
Amsawa Mom tayi sannan tatambayeta Mummynta tace tana nan lafiya lau.
Daga nan kuma duk sukayi shuru Nasiba duk tarasa me ma zatace ita kuma Mom duk sai taji ba dad'i da bata jajanta masu abinda yafaru ba koda ta san Alhaji Sufyan ya yi masu laifi.
Mom mik'ewa tayi tace bari inkawo maki ruwa kitashi kikoma saman kujera Nasiba.
Har ta bud'e baki zatayi magana sai muryar Faruk tajiyo yana waya saurin d'ago kai tayi takalli hanyar part d'inshi da tajuyo muryar daidai lokacin da yake safkowa saman step karaf suka had'a idanu tsaye Faruk yayi a wajen yana kallonta cike da mamakin ganinta, inda itama Nasiba tazuba mashi idanu lokaci guda k'wallah suka cika mata ido, Mom tsaye tayi tana kallonsu sai chan tace Faruk ka fito ne?
Jin muryar Mom yasa yayi saurin d'auke idanunshi daga kan Nasiba tare da ida safkowa yanufi wajen Mom yana cewa Eh Mom yanzu zan d'an fita ne.
Ganin yadda yabasar yasa tace ga Nasiba baku gaisaba ko baka ganta ba?
Batare da ya kalli inda take ba yace sannu Nasiba ya gida?
Wani irin k'ululun bak'in ciki ne yatsaya mata a mak'ogoro cikin ranta tace lallai ma Faruk watau dagaske yanzu ya daina sona.
Mom tace jirani Faruk inkawo ma Nasiba ruwa zan d'akko maka sak'o.
Bai musaba yatsaya batare da ya ce komai ba, maida kallonta tayi ga Nasiba tace ina zuwa sannan tawuce tafita.

Kamar jira suke tana fita nan duk suka zuba ma juna idanu, Nasiba saurin mik'ewa tayi tsaye tamatso inda yake cikin muryar kuka tace dan Allah Faruk kar ka azabtar da zuciyata bazan iya jure rashinka ba abubuwa biyu sun taru sun min yawa dan Allah kasafsafta min kayi hak'uri kar ka kamani da laifin da ba nawa ba.

Har lokacin idanunshi suna a kanta duk ta d'an fad'a da kaga yanayinta ka san tana cikin damuwa, kauda idanunshi yayi gefe yace Nasiba ni me nayi maki? Ina ce kece da kanki kikace baki sona toh minene nawa a ciki ko ance maki ni marar zuciya ne da zanta bibiyarki.

Tun kan yarufe baki tafashe da kuka tace Faruk wallahi rashin fahimta ne yasa nafad'i haka dan duk tunanina kana so katozarta mahaifina ashe ba haka bane daga baya na fahimci haka, tabbas su Dad sun kasance azzalumai da har suka aikata haka ga abokinsu saboda dukiyarshi, ni kaina ina da na sani akan kasancewata d'iya ga Alhaji Sufyan domin bai cancanci kasancewa uba agareni ba, dan Allah Faruk kayi hak'uri da abinda su Daddy suka aikata maka sannan kuma na gane kuskurena dan Allah kayi hak'uri kayafe min Faruk.

Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace koma me kikayi daidai ne Nasiba ni ban rik'eki ba akan abinda yafaru kije kawai.

Tun kan yarufe baki tace ammah kana nufin ka daina sona?
Ta'be baki yayi yace tun lokacin da kika nemi indaina sonki ni kuma nadaina dan haka a yanzu babu sonki a raina.

Saurin ja da baya tafara yi tare da k'ara sautin kukanta tace shikenan Faruk nagode ashe har zaka iya daina sona a lokaci guda? Meyasa haka Faruk? Miyasa bazaka fahimceni ba?
Shuru yayi yak'yaleta jin motsin Mom yasa tayi saurin tsaida kukanta tare da sa hannu tagoge fuskarta kallon Faruk tayi da yake kallon gefe sannan tajuya cikin sauri tafita daidai lokacin da Mom zata shigo da tray a hannunta tsayawa tayi tana kallon Nasiba tace ah-ah Nasiba ina kuma zakije?

Duk'ar da kanta tayi k'asa tace Mom zanje gidane.
Ammah ai da kin bari kinsha ko ruwane nan fa ba bak'on waje bane Nasiba gida ne.
Ahankali tace kiyi hak'uri Mom wani lokacin zan sha yanzu sauri nake su Yaya Sadiya suna jirana nagode sosai Mom,,, tana fad'in haka tawuce cikin sauri tafita.

Mom mamakine yacikata tayi saurin shiga parlorn tasamu Faruk a tsaye yana dannar waya cikin 'bacin rai tace Faruk me kayi ma Nasiba?
'Dagowa yayi yakalli Mahaifiyartashi yace ni kuma Mom? Banyi mata komai ba.
Ajiye tray d'in hannunta tayi tace na tabbata akwai abinda kayi mata tunda har tafita tana kuka, haba Faruk bai dace kakasance butulu ba ko bakomai Nasiba ba ita tayi maka laifi ba mahaifinta ne dan su basusan ma ya yi ba, duk wannan zaman jajen da mukayi duk da ita mukayi shi ta shiga tashin hankali sosai dan ko abinci bata iya ci sannan bata barin gidan nan sai dare shima sai su Dad d'inka sun sa ta tatafi gida, shin wannan ba k'auna bace? wallahi Faruk ba baki zan maka ba ammah na tabbata mawuyacine kasamu me sonka kamar Nasiba domin ita da zuciyata d'aya take k'aunarka.


Shuru yayi duk sai yaji jikinshi ya yi sanyi dan tabbas ya san Nasiba tana k'aunarshi shima kanshi yana sonta ya yi mata haka ne kawai saboda abinda tayi mashi.

Mom cigaba tayi da cewa Faruk baka isa kacanza ma zuciyarka abinda take k'auna ba a lokaci guda ammah shikenan kayi abinda kake gani daidai ne a wajenka,
tana fad'in haka tawuce tabarshi wajen tsaye, runtse idanunshi yayi ahankali yace inko hakane banyi ma Nasiba adalci ba, saurin zama yayi tare da dafe kanshi yana tunanin yanayin da Nasiba tafita lokaci guda yayi saurin mik'ewa yad'auki wayarshi yafita cikin zuciyarshi yana addu'a Allah yasa Nasiba ta isa gida lafiya.



Mom direct d'akin Dad ta isa tasameshi zaune yana karanta Newspaper ganin yadda tashigo yasa yace lafiya Hajiya naga duk ranki a 'bace?
Zama tayi gefenshi tace dole raina ya'baci Alhaji wallahi Faruk baya kyautawa wai menene laifin Nasiba a ciki da har zai rabu da ita?
Nuratu wani abun yafaru?
Kwashe komai tayi game da zuwan Nasiba tasanar da shi, girgiza kai Dad yayi yace Faruk kenan kirabu da shi Hajiya ni nasan yana son Nasiba kawai dai yana dannewane, kinsan halin d'an naki ammah ina nan da ke dakanshi zai koma wajenta.
Cikin sanyin jiki tace Allah yasa haka Alhaji.
Ameen Nuratu kar ma kisa damuwa a ranki, yauwa daman ke naje jira ad'an kawo min coffee d'innan me dad'i wanda kika saba had'a min.
Mik'ewa tayi tana murmushi tace toh Alhaji yanzu ko.



Nasiba da taimakon Allah ta samu ta isa gida lafiya tana shiga a parlor tasamu mahaifiyarta da 'yan uwanta zaune k'ok'arin 'boye damuwarta tayi tamatsa kusa da Mummynta tace sannu Mummy ya jikin naki?

Hajiya Maijidda ajiye ruwan da tasha magani da shi tayi idanunta suna akan d'iyartata tace Nasiba lafiya naganki haka me yafaru dan idanunki sun nuna kinyi kuka?
Saurin duk'ar da kanta tayi tace bakomai Mummy ba kuka nayi ba.

Haj Maijidda kallon Yaya Sadiya tayi tace wannan k'anwartaku bansan irinta ba ita akowane lokaci tana son 'boye damuwarta.
Yaya Sadiya tace hakane Mummy saidai k'ila kuma ko wani abun tatuna yasata kuka.
Murmushi Haj Maijidda

66 / 74