Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 74

54K to 57K   out of 220.3K words

yashaida mashi abinda yafaru nan DPO yace yajirasu gasunan zuwa.

Jawahir tana cikin kukan tajiyo jiniyar motoci ammah hakan bai sa tad'ago ba dan tasan daman tabbas sai hakan ya faru, tana jiyosu suna shigowa cikin gidan inda wasu duk suka zagaye gidan parlor suka fara shiga inda suka ga su Alhaji Mu'azu kwance, tsaye sukayi a wajen gawarwakin suna dubawa DPO hana kowa yayi yata'ba gawarwakin yace aje azo mashi da duk wani mahaluki da yake cikin gidan sannan yakira likita a waya.

Tana jiyo police suna bud'e sauran d'akuna ammah bata motsaba har suka shigo cikin d'akin da take zaune tsawa suka daka mata sukace me take a nan bata ko d'ago kai ba bare har tatanka masu dan haka biyu daga cikinsu suka shugo suka kamata memory d'in ne yakubce daga hannunta yafad'i tana so tayi magana ammah takasa babu wanda yalura da shi daga cikinsu saidai suka d'auko wayar Umar suka fita da ita a parlor suka kaita suka zaunar da ita k'asa inda tatadda megadinsu shima a zaune yayi zugum yana kallon gawarwakin iyayen gidanshi.

DPO kallonta yayi sannan yamaida kallonshi ga Alhaji Tanimu dake tsaye wajen gawar Abba yace wannan ce Alhaji?.
Kallonta Alhaji Tanimu yayi sannan yace Eh itace tabbas ita takashesu.
Daidai lokacin likita ya iso yana duba Abba da Yaya Umar yace ai sun mutu ammah ummah suma tayi dan haka aka tafi da ita asibiti.

Matsowa DPO yayi yatsugunna gabanta yana k'are mata kallo har lokacin kanta sunkuye k'asa tana hawaye jinjina kai yayi yace me zakice a game da mutuwar mutanen nan?
Shuru tayi bata amsa mashi ba, damk'o gashinta yayi tayi saurin runtse idanunta yace tambayarki nake shin kece kika kashesu?
A nan ma ban bashi amsar tambayar da yayi min ba muna a haka aka kawo mashi hoton Yaya Umar da na Abba wanda Ammi ta ajiye min ansa maker an yi masu tick koda yaduba yaga exactly irin wanda duk yatsinta ne lokacin da aka kashe su Alhaji Jamilu dan haka yasa aka kamani aka tafi da ni policestation aka rufe ni tsawon kwana biyu yana bincike inda yatabbatar da nice nayi kisan daga nan yamakani a kotu, kwana biyun nan da nayi kusan kullum sai Alhaji Tanimu ya zo ya dubani abinda yake bashi mamaki bana tare da wata damuwa atare da ni kuma har lokacin ban bud'e baki nayi magana ba, duk zuwan da Alhaji Tanimu yakeyi so kawai yake imbud'e baki in amsa ma police nice nayi kisan ammah nak'i a ranar da aka mik'a case d'ina kotu koda yazo yake tambayata shin ko akwai hanyar da zanbi inkare kaina a kotu?
'Dan guntun murmushi nayi ganin shi kad'ai ne a wajen yasa nace kar kadamu da wannan saidai ina so kaje kafara shiri dan kaine mutum na gaba da zaka bak'unci lahira.
Dariyar mugunta yayi yace taya kike tunanin zaki kasheni bayan ke hukuncin kisa ne za'a yanke maki bazan ta'ba bari kibar gidan ba koda kin bari a gidan kaso rayuwarki zata k'are, , sannan duk wasu takardu da suke mallakinki na samu nasarar d'auko su a cikin gidan ku zan mallake dukkan dukiyarki hatta ta cikin account d'inki zanyi k'ok'arin ganin na mallaketa.
Murmushi tayi a karo na biyu tace wannan ba matsala bane saidai inaso kasani daga kai har wad'anda kake tare d su babu wanda zai iya tsere wa daga hannuna dole sai kun mutu kamar yadda sauran suka mutu.

Dariya Alhaji Tanimu yadinga yi har saida aka zo aka koma da jawahir d'akin da take a rufeta.

Ranar litinin aka zo aka d'auketa cikin motar 'yansanda aka tafi da ita kotu koda aka je batace uffan ba tana ganin lauyoyi biyu suna ta fafatawa da wani lauya da taso taganeshi ammah takasa wanda yake a matsayin shi yake kareta har aka gama shara'ar bata fahimci komai ba tana ji ana ta mata tambayoyi saidai tabisu da idanu.
Ganin bata amsa cewa itace tayi kisan ba yasa Alk'ali yayanke mata hukuncin zama gidan yari na tsawon sati biyu kafin adawo zama na biyu, daga nan kotu aka wuce da ita gidan mata inda aka had'eta d'aki guda da wasu mata biyu masu irin laifinta na kisa,, saidai su kallo d'aya zakayi masu kaga babu alamun imani atare da su mugaye ne nan fa suka fara mata gani gani tare da nema surainata.
Saidai duk wannan baisa jawahir takula su ba saidai tayi zaune waje d'aya tayi shuru tana jinsu suna ta hira ammah bata kulasu ko kad'an bataga alamar damuwa a tare da su akan zaman da suke a cikin gidan kason nan ba, inda ita kuma saboda rashin sabo yasa takasa sakewa tana ji gabad'aya rayuwar ta canza mata saidai ko kad'an batayi nadamar abinda ta aikata ba, kusan kullum sai anzo anfita da su an kaisu sunyi aiki me wahala, a duk lokacin da suka fita dan yin aikin jawahir bata k'ara sanin inda hankalinta yake har sai anmaidasu d'an kurkukun d'akinsu.



Bayan sati d'aya lauya me kareta yazo aka fiddota aka kaita wajen da aka tanada dan ganawa da me laifi idan aka zo ziyartar shi musamman ma lauyoyi idan har lauyan ya buk'aci haka, koda tazo taga shine wanda taga yana kareta a kotu tsayawa tayi tana kallonshi murmushi yayi yace sannu jawahir na san dai kin sanni a matsayina na abokin mahaifinki yakamata kikwantar da hankalinki kinutsu ki amsa min duk tambayoyin da zanyi maki ni zan taimaka maki kifita daga gidan nan.
Tunda yafara magana idanu tazuba mashi tana kallonshi har yakai aya sai a lokacin tayi murmushi tace Barr Mubarak ko?
Shima murmushin yayi yace Eh haka ashe kin gane ni ai na d'auka bazaki iya tunani ba tunda tun bakida wayau sosai narabu da zuwa gidanku, nayi mamaki sosai da yakasance d'iyar abokina ce take rayuwa a nan gidan kaso har ake yayata labarinta a gari akan cewa ta yi kisa wannan dalilin ne yasa nazo inwanke ki akan zargin da akeyi maki.
Tarar numfashinshi tayi tace ba wai zargi ba Barrister bana buk'atar taimako irin naka domin baka dace kataimaka min ba katafi kawai.
Murmushi yayi yace baidace kice haka ba ga wanda yakeson taimaka maki.
Itama murmushin tayi cikin alamun nuna rashin damuwa tace fiye ma da hakan zan ce gareka barrister katafi kawai kanuna tausayawarka ga wani na daban ba wai wacce takasance abokiyar gabanku ba.
Da mamaki yake kallonta yace abokiyar gabanmu fa kikace? Wacece abokiyar gabanmu kuma ni da wa?
Ta'be baki tayi tace na san ka san komai, koma me kenan da sannu zan fahimtar da kai.


Haka suka rabu Barr Mubarak bai samu had'in kan jawahir ba a rana ta biyu koda yadawo nan ma bai samu yadda yakeso ba har suka zauna zama na biyu a kotu nan ma bata amsa laifinta ba akan zargin da akeyi mata dan haka akace ak'ara mata wata d'aya a gidan kaso sannan adinga sata aiki me tsanani.


Saida tayi sati biyu tana faman wahala duk wani aiki me wuya ana sata saidai abinda zai baka mamaki jikinta bai ta'ba nunawa ba, a lokacin da take sati na ukku ne Barr Mubarak yazo dan yagana da ita koda aka fiddota wajen da zasu gana kallonta yayi yai murmushi yace sannu malama jawahir
Idanu tazuba mashi batare da ta ce komai ba ganin haka yasa yacigaba da cewa jawahir taurin kanki ya yi yawa kin sanni kuma kinsan taimaka maki zanyi kisamu kifita da gidan nan dan baidace da ke ba a matsayinki na d'iyar babban mutum irin Alhaji Muhammad kibani had'in kai intaimaka maki.


Idanu tazuba mashi batare da ta ce komai ba ganin bata da niyar yin magana yasa yad'auko wasu takardu yamik'a mata yace amshi wannan signing kawai nakeso kiyi min idan har kikayi ni kuma na yi maki alk'awalin zan taimaka maki wajen ganin kin bar gidan nan.
Kallon takardun tayi sai taga na filaye ne guda biyu ga sunan Mahaifinta nan a jikin takardun, d'an guntun murmushi tayi sannan tace ba wai ka zo da niyar taimako na ba kawai dai kace ka zo da niyar cin dukiyata kaima, a matsayinka na abokin Abbuna baka kasance mutumin kirki irinshi ba.

Kinga ba wannan natambayeki ba indai har kinason barin gidan nan ya zama dole kiyi abinda nakeso inko ba haka ba kina ji kina gani za'a kasheki.
Matsowa tayi kusa da shi tace toh menene dan na je inda iyayena sukaje!
Ko ance maka bansan lokacin da kaje katsaya ma Abba ba wajen ganin kun k'wace ma Ammina hak'inta ta k'arfi da yaji ba? Kasan komai akan dukiyar mahaifina ammah son zuciya yahana kafad'i gaskiya, kuma tabbas nasan su Alhaji Tanimu ne suka turoka wajena, tir da hali irin naka.

Dariya Barr Mubarak yayi yace dakyau na ji dad'i da kika gane hakan a yanzu tunda kinsan halina ya kamata ki cika wad'annan takardun dan samun ku'butar ki daga gidan nan inko ba haka ba a banza zaki mutu sannan dukiyar da take mallakinki zata dawo k'ark'ashinmu hatta companyn mahaifinki kinga shikenan zuri'ar Muhammad me shadda ta zama tarih.....bai gama rufe baki ba tayi kukan kura tayo kanshi kafin yayi wani yunk'uri ta shak'e mashi wuya da dukkan k'arfinta, k'ok'arin k'wacewa yafara ammah yakasa dan k'arfin ba na mutum d'aya bane, buga table yafara yi dak'arfi sai ga masu kula da ita sun shigo dan dama suna bakin k'ofa nan fa aka fara k'ok'arin k'waceshi, kuka jawahir tadinga yi cikin d'aga murya tana cewa bazan ta'ba bari hakan yafaru ba bazan barka ba barrister, saida kusan maza biyar suka taru sannan suka samu suka 'ban'bare hannunta daga wuyan barrister mubarak tari yafara yi, bugunta suka fara yi a wajen saida suka bugeta sosai har tasuma sannan aka jata aka maidata d'akinta.


Barr Mubarak ya dad'e a wajen tsaye rik'e da wuyanshi yana tari idanuwanshi sunyi jajir kafin daga baya yad'auki takardunshi yafita.


Yana barin nan wani makeken gida yaje a parlorn gidan yasamu su Alhaji Tanimu su ukku zaune suna ganinshi suka fara murmushi wani da yake zaune kusa da Alhaji Tanimu ne yace ya dai barrister muna fata dai angama komai.
Zama yayi tare da tsiyaya wani swan water da yake saman center table yasha saida yashanye kofi guda sannan ya ajiye kofin yace hmm ina fa hakan yasamu yarinyar chan saura kad'an takasheni..
Su duka idanu suka zuba mashi sukace garin ya?
Ajiyar zuciya yasafke yace yarinyar chan ina tunani aljannu gareta.
Dariya Alhaji Tanimu yayi yace muma ai Aljannun kanmu ne akan kud'i haba Barrister ya kamata kayi wani abu man kar fa kamance da mak'udan kud'ad'en da mukayi maka alk'awalin su kaga idan har kataimaka mana tayi signing shikenan zaka iya zare hannunka akan case d'in inyaso ma akasheta babu ruwan wani.

Shuru Barrister Mubarak yayi kamar me nazarin wani abu ya d'auki mintuna sosai yana nazari sai chan yace kubarni da ita na san yadda zanyi tasa hannu yau d'innan zanje wajen likitana yataimaka min da wata allura ce da na caka mata ita zata fita daga hayyacinta na san a lokacin zata amince tayi signing d'in batare da ta saniba.

Su dukansu dariya sukasa sukace lallai barister ashe k'walwarka tana ja sosai.

Dariya shima yayi yace yoh ba dole tajaba ai bazan ta'ba mancewa da rashin mutuncin da Alhaji Muhammad yayi min ba lokacin da nanemi yataimaka min da wasu kud'i zan biya bashi yace min baidasu bayan gabana aka kawo mashi wata leda cike da kud'i sai cewa yayi wai ba na shi bane na ajiya ne aka kawo mashi, saidai dubu d'ari yabani ni da nake neman million guda, koma menene kukasance cikin shiri gobe dan zan kawo maku takardun nan da signing d'in yarinyar chan.

Shewa suka dinga yi a wajen suna cigaba da tattaunawa sun d'au lokaci sosai suna tattaunawa kafin su rabu akan gobe zasu sake had'uwa.




Barr Mubarak bayan ya bar nan kamar yadda yayi alk'awali saida yabiya wajen wani likita amininshi yasamo allurar sannan yawuce gidanshi lokacin da yakoma iyalanshi duk basu nan yana shiga d'akinshi wanka yayi yafito parlor yana magana shi kad'ai yana cewa wato har wannan lokacin su madam basu dawoba su da nace kar suyi marece tsaki yaja tare da zama bisa 3 seater yad'auko remote yana canza channel sallama aka yi aka shigo ciki ciki ya amsa nan wata babbar mata tashigo da tray d'auke da abinci da lemu ta ajiye a gaban Barr Mubarak tace 'Dalla'bai ga abincinka Hajiya tace akawo maka idan ka dawo, tana fad'in haka tatashi cikin sauri tafita tabar d'akin, saida tafita sannan yajuyo yakalli tray d'in, a karo na biyu aka sake sallama matar ce yaga ta dawo kallo d'aya yayi mata yad'auke kai dan shi ya tsani 'yan aiki suna shigo mashi d'aki, zuwa tayi ta ajiye wani jug da tashigo da shi tatsiyaya mashi kunun aya tamik'a mashi tace Alhaji ga shi.
Juyowa yayi a wulak'ance yakalleta yace ni nasaki kizuba min?
Girgiza kai tayi tace a'a.
Toh bar nan wajen

A saman table d'in da yake gabanshi ta ajiye sannan tamik'e tafita.
Tsaki yaja tare da kallon cup d'in ganin had'ed'en lemun kankana ne yasa yad'auka yafara sha dan yana son shi sosai, saida yasha kusan kofi biyu sannan yabarshi.


Bayan magrib yana zaune yafara jin cikinshi ya fara ciwo tun yana d'aukar abun wasa sai gashi ya kwanta har akayi sallar isha'i yana murd'e murd'e matarshi koda tadawo taganshi a wannan halin hankalinta ya tashi sosai dan haka taje tad'auko wayarta dan takira family doctor d'insu tana fita yana kwance yana ta murd'e murd'e sai ganin wata irin mata me mummunan halitta yayi ta bayyana a gabanshi tana tsaye tana kallonshi koda yana cikin halin ciwo saida yatsorata yunk'urawa yayi zai tashi ammah yakasa, murmushi tayi wanda yasa hak'oranta suka bayyana waje,
Cikin zafin ciwo yace wacece ke? Me kikazo yi a nan.
Rikid'a tayi takoma siffar kamannin Jawahir, yunk'urin mik'ewa yayi nan tanuna shi da hannunta sai gashi ya koma ya kwanta a nan take duk kasala tarufeshi.
Zagaye gadon da yake kwance tayi tana dariya saida tayi me isarta sannan tace bazan baka damar magana ba saboda bana buk'atar jin komai daga bakinka tambayar da kayi min itace maganarka ta k'arshe a duniya, kamar yadda nayi alk'awali bazan ta'ba barinka ba bare har kasamu damar cutar da ni dan haka kafin ka kasheni ni zan fara shafe babin rayuwarka, idanu Barr Mubarak yazuba mata yana kallonta ko hannunshi yakasa motsawa, cigaba tayi da cewa kun zalunceni kun cuci abokantaka da kuka yaudari mahaifina kuka kasance me fuska biyu a wajenshi saboda dukiyarshi har saida kukayi silar barinshi duniya sannan wannan bai ishekuba kunaso kushafe duk wani tarihi na rayuwarshi toh inaso kasan cewa nasan lokacin da kaje wajen likita ka amso allurar nan nikuma nayi amfani da damata nakawo maka lemu me guba kasha na tabbata ko minti goma bazaka k'araba yanzu zaka mutu, zaka rigani zuwa inda kakeso kakaini dan haka na barka lafiya.....k'arar k'ofar da tajine alamun za'a bud'e yasa tayi saurin 'bacewa.
Barr Mubarak hawaye ne suka fara fita daga idanunshi yana kallon matarshi tana ta faman yi mashi sannu tana shaida mashi likita yana nan tafe zai dubashi, a lokacin ne yafara yunk'urin amai ammah yakasa tashi nan inda yake kwance yafara aman jini yana jin ciwon cikin yana k'ara tsananta a nan take yamutu kafin isowar likita dan lokacin da ya iso tuni ya bar duniya.


Hankalin mutane ya tashi sosai akan mutuwar Barr Mubarak musamman ma da likita yatabbatar da guba aka bashi yaci saidai anduba ba'a ga alamun ya ci wani abu me guba ba acikin abincin da aka kawo mashi ba nan aka rasa inda yasamo guba yaci.


Mutuwarshi tasa su Alhaji Tanimu suka shiga damuwa sosai inda suka fara tunanin jawahir tana da hannu akan mutuwarshi sune suka fara yad'a abun nan aka d'auka ana cewa itace tayi layar zana daga gidan yari taje takasheshi saidai hakan bai zama k'wak'warar sheda ba saidai duk da haka ana zarginta ammah babu wanda zai iya bada shedar cewa itace tayi kisan.


Mutuwarshi ta tada hankalin Alhaji Tanimu sosai saboda haka ne asatin da yamutu yatattara yagudu Europe dan ya tsorata sosai akan kisan da aka yi ma nakusa da shi......


Jawahir na kawowa nan juyowa tayi takalli Barr Faruk tace wannan dalilin ne yasa ake cewa na kashe lauyana me son kareni saidai mutane basu san cewa shi d'in me fuska biyu ne ni a wajena fuskar azzalumi gareshi,,, hawaye ne tafara yi nan takoma wajen zamanta tazauna.

Barr Faruk kasa cewa komai yayi ganin yadda take hawaye yasa yaje yalek'a waje yace ma ma'aikacin gidan yana buk'atar ruwan sha nan yatafi dan ya samo mashi.

Dawowa yayi yakalleta yace Tabbas Alhaji Tanimu ya kasance shed'ani ne idan har abinda kika fad'a akanshi gaskiya ne, ammah shi Barr Muhsin fa, ya akayi yatsaya maki kuma kina nufin shima yana da hannu a ciki saisa kika kasheshi?

Shuru tayi tazuba ma gefe d'aya idanu tana kallo, daidai lokacin ma'aikacin gidan yakawo mashi purewater me sanyi saman tray yad'auro cup a sama, amsa Barr Faruk yayi yai mashi godiya bayan ya fita ya basu waje ne yatsiyaya a cup d'in yamik'a ma jawahir.
Tsayawa tayi tana
Kallon cup d'in sai kuma chan ta amsa tare da yin murmushi tace nagode, nan takafa cup d'in a bakinta saida tashanye sannan tatsaya tana kallon cup d'in tana murmushi.
Shima kallonta yake ahankali yace ya burgeki ne cup d'in?
Girgiza kai tayi tare da mik'a mashi bayan ya amsa ne tace wannan cup d'in ankawo shi ne saboda kai ne zaka sha ruwan kuma kai mutum ne me daraja a wajensu mu ko k'ask'antattu ne a ko'ina.
Tarar numfashinta yayi yace a'a jawahir kidaina cewa haka kema mutum ce me daraja kuma insha Allahu zaki bar gidan nan rayuwarki zata koma irin wadda kikayi a da zaki cigaba da kasancewa a cikin farin ciki komai zai zama tarihi.
Murmushi tayi har saida hak'oranta suka bayyana sannan tagirgiza kai tace kaine kake tunanin haka barrister.

Shima murmushin yayi sannan yace ina saurarenki ya kamata ki ida sanar da ni abinda yafaru bayan mutuwar Barr Mubarak.
Ajiyar zuciya tasafke sannan tacigaba da cewa...........










_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da

19 / 74