Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
k'aunarki saboda mu mune iyayenki saidai mahaifinki nakeji kinsan idan har yafad'i magana to baya canzata.
Ruk'o hannuwan mahaifiyartata tayi tana kallonta da idanuwanta da suka kumbura saboda tsananin kuka tace Mommy dan Allah ke kikasance da ni domin ke uwace na tabbata ke kad'ai zaki iya fahimtata.
Rungumeta tayi tare da shafa bayanta tace ina tare da ke d'iyata tabbas nice kad'ai yafi dacewa infara fahimtarki, kidaina kukan mucigaba da addu'a insha Allahu Faruk zai bayyana.
Ajiyar zuciya tasafke tace nagode sosai Mummyna.
Bakomai d'iyata yanzu dai kidaina kukan nan bari inje inkawo maki abinci kici kiwatsa ruwa kikwanta ko?
Goge hawayenta tayi tare da yin murmushi tace nagode mummyna.
***** *****
A chan 'bangaren Faruk yana chan da mutanen nan a cikin d'akin a d'aure dan a yanzu ma ya samu ansafkeshi daga saman kujerar a saman gado aka d'aureshi indai har zaiyi wata buk'atar kusan mutum ukku suke rakashi wajen toilet yashiga yagama abinda zaiyi sannan sumaidoshi sud'aure Alhaji Mansur kusan kullum sau ukku yake zuwa yadubasu yakawo masu abinci koda shi a wulak'ance ake bashi abinci kuma ba ci yakeyi ba sai yaga yunwa ta cishi sosai sannan yaci, wulak'anci da cin mutunci kala-kala yake sha a wajensu Alhaji Mansur da mutanenshi saidai shi duk wannan bai dameshiba abu d'aya ne yake d'aga mashi hankali halin da iyayenshi suka shiga sai kuma case d'in jawahir baisan yadda zai kasanceba ita kanta ya san sai ta zargi wani abu kar ma tad'auka yaudararta yayi.
A yau ma yana zaune a inda aka d'aureshi hankalinshi a tashe yana tunanin kotun da za'a zauna gobe sai gani yayi anwurgo mashi takeaway a saman jikinshi, kallo d'aya yayi mashi yad'auke kai, d'aya daga cikinsu ne yataso yana cewa watau sai ma kad'auke kai idan bazaka ci abincin ba sai kayi magana ba sai na kwanceka ba.
Shuru yayi kamar baiji abinda yace ba.
Cikin 'bacin rai yace kai wai wane irin banzan mutum ne ayita maka magana kayi shuru kak'yale mutane ka san kabi a sannu inba hakaba zan nakasaka a wajen nan nace zaka ci abincin ko ka k'oshi.
Nan ma shuru yayi yaba bango ajiyarshi.
A fusace yad'aga bindigar da take hannunshi yabuga mashi a kai, Faruk saida yasaki k'ara saboda zafin bugun.
'Dago mashi kai yayi dak'arfi yace idan har kacigaba da mana taurin kai sai mun azabtar da kai a gidan nan, kalleka dan Allah a yanzu gakanan a wulak'ance a wajenmu duk wannan jin kan nan da tak'ama babu su.
Wani daga cikin sauran da suke zaune ne yace cinnaka ni ko naga ba jin kai kaga fa yadda yake taka k'asa kamar irin baya so d'innan shi a dole ga me kud'i barrister sai ga rayuwar barrister ta k'are a hannunmu ya koma wani k'ask'antacce.
Su dukansu dariya sukasa suna cewa dan Allah jibarshi, duk ina dukiyar yanzu.
Bud'e baki Faruk yayi ahankali yace koma me zakuce bazan ta'ba damuwa ba saidai inaso kusani a duk ranar da nayi nasarar barin gidan nan gabad'ayanku sai na sa and'aureku.
Kan bindiga wanda aka kira da cinnaka yasake buga mashi a fuska har saida jini yafito daga hancinshi, runtse idanu yayi dak'arfi yana jin rad'ad'in bugun.
'Daya daga cikin wad'anda suke zaune ne yace a'a Cinnaka kadaina dukanshi ka ga Alhaji bai ce mubugeshi ba kabari abani izini sannan mucasashi tunda shi har yana ma tunanin zaya fita daga nan har yasa ad'auremu, wayyoo Allah har ma na d'an tsorata dan Allah kutaimaka min zasu kamani wallahi tsoron zaman gidan kaso nakeji......su dukansu kwashewa sukayi da dariya, wani kuma yace ahaka wai shashashan yake gani zamu barshi yafita lallai da sauranka.
Haka sukaita tsokanarshi shi dai yayi shuru bai sake cewa komai ba saboda rad'ad'in da yakeji a fuskarshi.
Yana ji Cinnaka yakoma yazauna batare da ya kwance mashi hannuwa ba koda daman shima ba yunwar yake ji ba inma yana ji sai ta cishi sannan yake cin abincin da suke bashi.
Jawahir da take zaune a d'an kurkukun d'akinta tun bata damu da rashin zuwan Barrister ba har abun yazo yafara damunta dan bai ta'ba d'aukar wannan lokacin bai zoba gashi ma abun tashin hankalin gobe ne zama na k'arshe da zasuyi a kotu,,, mik'ewa tayi tsaye tare da jingine jikinta a jikin bango ahankali tace ko dai Barrister ya janye ne shima bazai iya taimakona ba? Girgiza kai tayi tace ah'ah ko kuma wani abu yafaru da shi?
Hannu tasa tatoshe bakinta nan k'wallah ta cika mata idanu tace na shiga ukku ba dai akaina wani abu yafaru da shi ba, idan ko hakane ya zanyi, nice sila,,,
Tana nan tsaye a haka akazo aka bud'e d'akin juyowa tayi dan ganin wanda zai shigo sai taga ma'aikaciyar gidan ce, ajiyar zuciya tasafke
Kallonta matar tayi a wulak'ance tace ke zo muje ana son ganinki.
Nuna kanta tayi tace ni?
Harararta tayi tace akwai wani ne cikin d'akin?
Batare da ta bata amsaba tad'auko kallabinta tad'aure kanta sannan tabi bayanta suka fita, da mamaki take kallon inda suka nufa tabbas wajen da ake kaisune idan wani ya zo ganawa da su.
Suna zuwa sai jin matar tayi ta ce kawo hannunki, mik'awa tayi nan taga ansa mata ankwa sannan matar tace kishiga ciki d'allabai yana ciki.
Tambayar kanta tayi tace Faruk kenan yazo ganawa da ni ammah kuma yau bai shigo wajenaba sai nan....Daka mata tsawa matar tayi tace me kika tsaya jira?
Shiga tayi d'akin da mamaki take kallon wanda yake tsaye.
Murmushi yasakar mata yace sannu d'iyata ina fata kina lafiya? Wannan dai mahaifin bai kyautaba da baya zuwa ganin d'iyarnan tashi.
'Daure fuska tayu tace menene dalilinka na zuwa wajena?
Matsowa yayi kusa da ita yana murmushi yace kikwantar da hankalinki na zo ne kawai duba lafiyarki sannan injajanta maki 'bacewar da akace Barrister Farukya yi tsawon kwana ukku.
Zaro idanu tayi waje da mamaki take kallonshi tace kana nufin Barrister ya 'bace?
Alhaji Mansur dariya yasake yi yace ya naga kin tsorata, nima dai haka naji ban saniba ko akan wani case aka saceshi gashi mu kuma gobe ce ranar shara'a ta k'arshe.
Idanu tazuba mashi tana kallonshi cikin ranta tace ko dai akan case d'ina ne?
Ya kikayi shuru ko kina tsoron makomarki ta gobe?
Sai a lokacin tayi murmushi tace ban damu da makomata ba saidai na san duk abinda yafaru da Faruk ku ne sila, shin ko shima kun kasheshi kamar yadda kuka kashe iyayena?
Tarar numfashinta yayi yace ko kuma kin kasheshi kamar yadda kika kashe sauran lauyoyinki, shin taya ma gobe za'a barki bayan kin kashe lauyoyi ukku.
'Daga murya tayi tace idan har kuka bari wani abu yafaru da Barrister bazan ta'ba barinku ba da duk wanda yake da hannu a ciki sai naga bayanshi, kukyaleshi yayi rayuwarshi domin shi baida laifi a ciki nice me laifin kuma idan har saboda ni kuka kamashi kusakeshi ni na amince akasheni ammah kar ku kashe wanda baisan komai ba a kai.
"Jawahir mu bamu kamashi ba dan baya hannunmu kece ma nayi tunanin kin kasheshi ammah dai shikenan ke kad'ai kikasan wannan sirrin dan nasan daman ba fad'a min gaskiya zakiyiba nima daman jaje nazo maki, ni zan tafi ko ma mekenan sai munhad'e a kotu gobe ina fata zaki kasance cikin bak'in ciki kasancewar yau itace ranarki ta k'arshe gobe kamar yanzu kina cikin k'abarinki, na barki lafiya.
Hawaye ne suka gangaro mata a kuncinta ganin ya juya zai tafi yasa cikin d'aga murya tace na fad'a maka kar kabari wani abu yafaru da rayuwar Barrister wallahi idan har kakasheshi nima sai naga bayanka kafin nima akasheni.
Bai tsaya bata amsaba yawuce yatafi.
Dafe kanta tayi da hannuwanta da suke da ankwa, matar ce tazo tatisata gaba tamaidata chan d'akinta tamaida tarufe.
Tana shiga sulalewa tayi k'asa tazauna tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka, cikin kuka tadinga cewa Ammi kizo gareni ina buk'atar taimakonki ko da ace wannan shine taimako na k'arshe da zakiyi min a duniya dan Allah kizo gareni......bata rufe baki ba sai ga wani farin haske ya bayyana a gabanta, saurin mik'ewa tayi tana kallon haskenan nan yafara komawa siffar mutum kafin k'iftawar idanu sai ga tsohuwarnan ta bayyana.
Bud'e baki tayi zatayi magana tatari numfashinta tace tabbas Barrister yana cikin mawuyacin hali dan yana hannunsu sun kamashi saidai bazan ta'ba taimaka mashi ba.
Saurin zamewa tayi k'asa tatsugunna tare da had'e hannuwanta biyu waje guda cikin muryar kuka tace dan Allah Ammi kitaimaka min kitseratar da shi domin rayuwarshi tana da muhimmanci sosai bai dace ace wani abu ya sameshi ba a dalilina ni k'wara akasheni dan tawa rayuwar batada sauran amfani.
Dariya matar tayi sannan tace Jawahir yau gaki a gabana tsugunne kina rok'ona bayan da baki ta'ba hakan ba, saidai tsanar da kikayi min ammah yau kece a haka dubeki.
Fashewa tayi da kuka tace tabbas ni k'ask'antatta ce kar kiyi duba da abinda yafaru dan Allah kiceci wannan bawan Allahn banaso sukasheshi.
Zureren hannunta tad'ago tace kiyi duba zuwa nan jawahir.
Saurin d'ago kanta tayi tadubi hannun Barrister Faruk ne tagani zaune an d'aureshi idanunshi a rufe.
Wasu sabbin hawayen ne suka gangaro mata nan tsohuwar tajanye hannunta sannan tace wannan itace k'addararshi bazan ta'ba iya zuwa inceceshi ba, ke kuma ya kamata kafin gobe kiyi nadamar maganar da kika fad'a min idan har kinason cigaban rayuwarki inko ba haka ba kema kanki zaki mutu.
Matsowa tayi kusa da matar tana me cigaba da kuka tace bazan ta'ba nadama ba indai a kan kainane saidai zan iya Nadama indai har zaki ceci Faruk kije kiku'butar da shi.
Bushewa tsohuwar tayi da dariya sannan tace dakyau jawahir hakan ya yi miki kyau, saidai ni bazan ta'ba taimaka ma wanda kikeso intaimaka ba saboda ni bana taimako abu guda kawai nake kuma shi na iya shine *'DAUKAR FANSA*
Jawahir kasa cemata komai tayi nan taduk'ar da kanta tana me cigaba da kuka cike da tashin hankali.....
______
Gidan su Faruk mutane zuwa suke suna yi ma iyayenshi jaje dan gidan komawa yayi kamar gidan gaisuwa mutane sai shiga da ficce sukeyi inda suke addu'a Allah yabayyanar da shi.
Hatta limamin unguwar kullum sai ya zo anyi safka sannan ayi abincin sadaka a raba.
Iyayenshi duk sun fita hayyacinshi saboda tashin hankalin da suka shiga.
A ranar yau da takasance kwanan Faruk ukku baya gida, Dad d'inshi yana zaune a setting room shi kad'ai ya buga tagumi Barr Nas yazo gidan duk sallamar da yayi Dad baijiba saida yad'an buga k'ofa sannan yad'ago yakalleshi yace bismillah Nasir kashigo man.
Shiga yayi yazauna a k'asa suka gaisa bayan sun gaisa ne Dad yace Nasir kuna ta k'ok'ari gaskiya mungode sosai, a yanzu mudaina wahalar da kanmu wajen yawon nemanshi mucigaba da addu'a indai har yana raye Allah zai bayyana mana shi, saidai abinda nake zargi mutanen da suka ta'ba kirana waya sukace ingargad'eshi yacire hannunshi daga wani case ina tunanin sune suka sace min shi dan a ranar da akayi maganar a ranar ya'bata.
Cikin sanyin jiki Barr Nas yace Dad wane mutane ne? Me sukace maka?
Kwashe komai yayi yafad'a ma Barr Nas.
Mamaki yacikashi yace tabbas wad'annan mutanen akan case d'in Jawahir ne.
Eh tabbas hakan sukace wai yajanye akan case d'inta ammah wacece ita? Meyasa zasuyi min haka da sunbi ta lalama ai da na sashi ya janye.
Shuru Nasir yayi sai chan yace tabbas case d'in akwai rikitarwa a cikinshi saidai ita yarinyar tana a kan gaskiyarta wannan dalilin ne yasa Faruk yakeso yawanketa a idanun duniya daga zargin da akeyi mata, saidai a yanzu lokaci ya k'ure na tabbata a gobe idan har babu lauyan da zai tsaya mata kasheta za'ayi gashi Barr Faruk shine kad'ai zai iya tsaya mata.
Jinjina kai Dad yayi yace Allah yakyauta, Allah dai yabayyanar da shi a duk inda yake.
Barr Nas ya amsa da Ameen sannan yayi mashi sallama yatafi.
Nasiba saboda tashin hankalin da tashiga ko baccin kirki bata iyawa abinci ko ba'a magana sai Mummynta ta yi dagaske sannan take samu tana d'anci kullum cikin kuka take, Daddynta ko shareta yayi yafita batunta.
Yau ma kamar kullum Hajiya Maijidda ce tashigo da azuhur tasameta zaune saman darduma da alama sallah tagama saidai ta jingine jikinta a jikin gado tana hawaye, tsayawa Hajiya Maijidda tayi tana kallonta sai kuma chan tataka ta isa wajenta a saman gadon tazauna cikin lallashi tace haba Nasiba wai meyasa kikesa ma ranki damuwa addu'a fa yakamata kiyi mashi duk inda yake Allah zai bayyana mana shi.
Goge hawayen fuskarta tayi tare da gyara zamanta ta fuskanci mahaifiyartata sannan tace Mummy dan Allah taimako d'aya nakeso kiyi min.
Toh ina jinki wane irin taimako ne?
Saida takalli k'ofa sannan tace dan Allah kitaimaka min kibarni inje gidansu Faruk ingano Mom d'inshi na tabbata tana chan hankalinta a tashe, nima zuwana zai sa ind'anji sauk'in rad'ad'in da nakeji a raina.
Jimm tayi sannan tace Nasiba kinsan mahaifinki baya so ranshi 'baci zaiyi.
Kamar jira take tafashe da kuka tace Mummy kitaimaka min wajenki ne kawai nake jin dad'i kin san yadda nakeson Faruk hankalina bazai ta'ba kwanciya ba idan banje naji halin da ake cikiba yanzu.
Cikin sanyin jiki tace shikenan Nasiba tashi kije ammah kar kidad'e saboda kar Daddynki yadawo bakinan kinsan ba ke ba hatta ni kaina sai raina ya 'baci.
Murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai mummyna.
Shafa kanta tayi tace bakomai dota idan kinje kigaishe min da Hajiya Nuratu.
Toh insha Allahu zataji Mummy, nan tamik'e tashirya tafita tana Allah Allah kar suhad'u da Daddynta a lokacin da zata fitar da motarta sai gashi cikin ikon Allah har tatafi bai dawo ba.....
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 19*
Washe gari ya kama ranar litinin tun da safe a gidan kaso akasa duk wani wanda za'aje kotu da shi yayi wanka yashirya, jawahir tunda tashirya zaune tayi tana tunanin halin da Faruk yashiga akanta ko kad'an fuskarta babu alamun fara'a dan jiya ko rintsawa bata samu tayiba, abinda zai ba mutum mamaki ita hankalinta bai tashi akan zaman kotun da za'ayi ba, bah wai kuma dan tana da tabbacin zata tsira ba dan tasa ma ranta dole cikin biyu ayi d'aya ko rayuwa ko mutuwa ko da ta ma fi bama ranta mutuwar dan tasan itace kawai makomarta.
Kamar yadda aka saba a duk ranar da za'a shiga kotu akan case d'in jawahir ana yin sanarwa a gidajen yad'a labarai saboda za'a iya cewa mafi yawa daga cikin mutanen da suke garin katsina sun san da case d'inta dan abinda ba'a ta'ba jin an aikata bane sai akanta, musamman ma da akasan manyan mutane ne masu hannu da shuni ake zarginta da kisansu, wannan dalilin ne yasa duk ranar da za'a shiga kotu akan case d'inta mutane dadama suke zuwa acika kotun mak'il, wasu ko ba komai yake kawosu ba sai dan suzo sugane ma idanunsu yarinyar da akace tana da k'arancin shekaru takeyin kisan.
Dad d'in Faruk da a yanzu ko baccin kirki baya samu yayi saboda 'bacewar d'anshi, yau ma tunda yadawo sallar asuba bai koma bacci ba Redionshi yajawo yakunna yana daga kwance saman doguwar kujera dan a yanzu ya fi sauraren Redio ko dan saboda yana tunanin a nan zai iya samun bayyanar d'anshi indai ma ansameshi a wani wajen, yana cikin sauraren labaran safiyar yau akan abubuwan da suka farune yaji ana sanarwa
"Gwamnatin jihar katsina zata bada tallafi ga wad'anda 'yan ta'adda suka shiga garuruwansu suka kashe masu 'yan uwa sannan suka kora masu dabbobi suka tafi da su, inda me girma gwamna yayi sanarwa zai taimaka masu da tallafi.
Sannan a cikin labaran na mu zakuji cewa a yau ne za'a yi zama na k'arshe a kotu akan case d'in Jawahir Muhammad Maikud'i wadda ake zargi da kashe kawunta da 'ya'yanshi wanda daga baya hukuma tagano hadda mijinta aciki sannan tasambad'a abokan mahaifinta suka ziyarci lahira inda dangin mamatan suke k'ararta akan suna so abi masu hak'k'in rayuwar 'yan uwansu, ko me ya jawo ma yarinyar yin kinsan? Wannan ne bamu saniba dan har yanzu ba'a samu wata k'wak'kwarar hujjaba guda d'aya da me laifin tabayar saidai jitajitan da mutane sukeyi, koma me kenan kukasance da mu da anjima acikin labaran mu dan jin yadda shari'ar ta kasance..
Haka kuma a cikin labaran namu zakuji cewa...
Dad tsaki yaja tare da kashe redion yakunna TV dan yakalli News tunda yakunna TV d'in kallo kawai yake ammah hankalinshi ba a wajen yakeba abinda yatsaya mashi a rai case d'in yarinyar da yaji ansanar musamman ma sunan da aka ambata Jawahir Muhammad Maikud'i tabbas zai iya cewa 'ya ce ga Marigayi Alhaji Muhammad Maikud'i inko ba haka ba toh sunan ya zo iri d'aya da nashi toh ammah shima ya san yana da d'iya guda d'aya bazai iya cewa ga sunanta ba, anya kuwa itace ba wata bace ta daban ba?
Toh ko dai itace Jawahir d'in da Faruk yatsaya mawa wadda saboda case d'in ake barazana a rayuwarshi, tabbas ko zaya iya zama itace dan zai iya tuna labarin da Faruk yabasu akan case d'in ya ce ana zarginta akan kisa.
Jinjina kai yayi yace tabbas itace wannan saboda ita aka d'auke min d'ana....haka yayi ta tunane tunane inda daga k'arshe yakasa kallon News d'in yakashe TV d'in yayi kwance yana tunanin halin da d'anshi yake ciki a yanzu ko da rai ko kuma babu rai.
_______
A chan 'bangaren Faruk yana kwance a saman gado ko runtsawa bai samu yayiba saboda tashin hankalin da yake ciki musamman akan shara'ar da za'a gabatar a yau ta jawahir, ko da daman ba samun wani baccin kirki yakeba saboda halin da yake ciki ga d'aurin da akayi mashi wai dan kar yagudu ahaka yake kwanciya.
Hatta sallah sai ya yi dagaske sannan suke barinshi yayi