Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
niyar zuwa ba
Kai Inna bafa haka bane kinsan komai sai Allah ya yi, marairaicewa tayi tace dan Allah ba dan halina ba Aunty Nasiba kiyi hak'uri wallahi nima kaina na san ban kyauta ba.
Sai a lokacin Nasiba tajuyo tace shikenan tunda kema kin gane baki kyauta ba na hak'ura ammah inji yaushe za'a zo mana.
Murmushi tayi tace nagode sosai Auntyna insha Allahu ina nan tafe dan idan nazo sai na dad'e a wajenku.
Hmm toh Allah yasa.
Ameen Auntyna, nan suka gaisa tatambayeta gida da su hajitarta tace duk suna lafiya lau.
Hira suka zauna suka dinga yi kamar daman irin sun san juna sosai har su khausar suka shigo suka gaisa.
Bayan sunyi azuhur ne sunci abinci Inna Mairo tafito tsakar gida tana dafa madarar shanu, d'akin yarage daga Jawahir sai Nasiba dan su Khausar tunda suka shiga cikin gida basu dawo ba, kallonta Nasiba tayi tace dan Allah Jawahir ina k'ara baki hak'uri akan abinda mahaifinmu ya aikata maki wallahi bamusan komai ba akai.
Kai Aunty Nasiba dan Allah kibar tuna abinda yawuce.
K'walla ce tacika mata idanu tace dole intuna jawahir domin ko kema har kikoma ma mahaliccinki bazaki ta'ba mance hakan ba, kar kiyi k'arya a fili alhalin azuciyarki ba haka bane.
Hawaye ne suka gangaro ma Jawahir tace tabbas nasan *DA CIWO A RAYUWATA* ammah babu yadda na iya komai muk'addarine dama chan Allah ya k'addara ba zan k'are rayuwata tare da iyayenaba *K'ADDARA CE* ta rabamu dan Allah mubar maganar Aunty Nasiba banaso tunawa domin inajin wani iri a duk lokacin da natariyo rayuwar da nayi a baya saidai ina jin d'an sanyi idan natuna da d'aukar *FANSAR RAI* na iyayena da nayi.
Murmushi Nasiba tayi tace hakane Allah yajik'ansu yasa sun huta.
Jawahir Amsawa tayi da Ameen daga nan kuma duk suka yi shuru.
Inna Mairo ce tashigo da wani galan a hannunta tamik'a ma Jawahir tace jeki gidan Ladidi ki amso min Man Shanun da nabata ta dafa min d'azu.
Amsa jawahir tayi tace toh nan tatashi tafita.
Tana fita Baba Nura yashigo yace amarya kina nan anbarki ke kad'ai ko?
Murmushi tayi tace a'a basu dad'e da fita ba ma yauwa dan Allah Malam Nura ko zaka taimaka kayi min magana da su Baba dan akwai magana me muhimanci da nakeso zamuyi da su.
Baba Nura yace toh shikenan bari inje insanar da su.
Fita yayi yaje yafad'a ma su Baba Malam sak'on Nasiba dan har lokacin suna zaune a k'ark'ashin bishiyar da yake zama saman tabarma dan a nan ma suka ci abinci, Faruk yana jin sak'on Nasiba yagane maganar da takeso tayi masu duk sai yaji wani iri.
Haka suka tashi suka shiga cikin gida a tsakar gida aka shimfid'a tabarma Baba Malam, Baba Musa, Baba Jamilu, Baba Nura, Faruk sai Inna Mairo suka zauna daga chan gefe Nasiba tafito tazauna.
Baba Malam ne yayi gyaran murya yace ance kina son magana da mu Allah dai yasa lafiya.
Duk'ar da kai tayi cike da ladabi tace lafiya lau Baba daman wata alfarma ce nake nema a wajenku bansaniba ko zan sameta.
Wace irin alfarma ce wannan?,,, baba malam yatambayeta.
Kallon Faruk tayi sannan tace mijina nake son nema ma auren Jawahir.
Su duka da mamaki suke kallonta, Baba Musa yayi k'arfin halin cewa keko wace irin magana kike ni na d'auka wata magana ce me muhimmanci taya zakice mijinki ya auri Jawahir bayan ba'a dad'e da bikkinku ba.
Cikin sanyin jiki tace wannan maganar ma tana da muhimmanci dan Allah kutaimaka mana idan har hakan zai yuwu wallahi ni babu matsala na amince zan zauna da ita da zuciya d'aya ko bakomai rayuwar Jawahir yaci ace antausaya mata.
Faruk ne cikin kwantar da murya yace zan auri Jawahir idan har kuka ban dama na yi maku alk'awali zan kula da ita bazan ta'ba bari tazubar da hawayeba tayi da tasani akan aurena ba amincewarku mukeso idan har batada wanda zata aura inkuma tana da shi shikenan sai in hak'ura domin komai nufine na ubangiji.
Jinjina kai sukayi gabad'ayansu Baba Malam yace wannan gaskiya ne Faruk tunda dai har kaida matarka kun amince zaku zauna da ita tsakani ga Allah shikenan muma mun amince ka aureta domin ko bakomai ka cancanci hakan idan har muka ce zamu hanaka jawahir toh mun zama butulu dan ko halarcin da kayi mata ya ci ace mun amince, na yarda da kai 100% nasan zaka kula da ita da dukiyarta indai har ina da iko da Jawahir toh na mallaka maka ita.
Su Baba Musa ne sukace wannan gaskiya ne muma mun amince da hakan.
Inna Mairo ita kanta ta yi farin ciki sosai ko bakomai ta san Faruk zai kular mata da jikarta jinjina ma k'arfin halin Nasiba tayi ganin wai dakanta take nema ma mijinta aure.
Faruk da Nasiba godiya sukayi masu.
Su ko farin ciki baki har yak'i rufuwa dan daman sunaso Jawahir tasamu miji wanda zai kula da maraicinta, nan sukaita shi masu albarka, kowa farin ciki fal a ranshi dan sunsan indai ta auri Faruk ta more miji.
Nasiba ce tace kar afad'a ma Jawahir abari su zssu fad'a mata da kansu.
Su Baba Malam suka amince da hakan.
Wajen k'arfe ukku Jawahir tadawo takawo ma Inna Mairo sak'onta tace kiyi hak'uri inna sai yanzu tagama dafawa ashe bata soyaba sai da naje.
Murmushi Inna tayi tace bakomai ai daman na yi tunanin haka daman ina ta Allah Allah tasoya kafin sutashi tafiya.
Murmushin itama Jawahir tayi tace ai nan zasu kwana gaskiya bamu yarda sutafi yau ba.
Nasiba da take cikin d'aki tana jiyota saidai tayi murmushi kawai.
Shigowa Jawahir tayi tace gaskiya babu inda zakuje yau Aunty Nasiba bari ma inma Yaya Faruk magana.
Au keda baki ma lek'a inda mukeba kike da bakin cewa haka.
Dariya Jawahir tayi tace dole ma inyi zuciya inzo ko dan inhuta da gorin da ake min.
Ai da dai ya fi maki, yauwa Jawahir akwai magana me muhimmanci da nakeso muyi.
Wace magana kenan Aunty?.
Ina zuwa,,, wayarta tad'auko takira Faruk tace yashigo dan Allah suyi magana, ya amsa da toh.
Bayan ya shigo ne ya zauna takalli Jawahir da tayi shuru tana jira taji abinda zasuce sannan Nasiba tace dan Allah Jawhir wata 'yar alfarma ce muke nema a wajenki.
Alfarma kuma?,,, tatambaya cike da mamaki.
Janye kai Nasiba tayi gefe guda sannan tace dan Allah ina so ki auri Faruk.
Zumbur tamik'e tsaye tace ni kuma? Aunty Nasiba kinsan abinda kike fad'a kuwa?
'Daga kai tayi tace Eh na sani cewa nayi kitaimaka ki aureshi.
Jawahif juyawa tayi takalli Faruk da yajingine kanshi a jikin kujera idanuwanshi suna a lumshe yana saurarensu, d'auke kai tayi tace gaskiya ba zan iya auren mijinki ba ni kawai matsayin Yaya yake a wajena.
Saurin bud'e idanu Faruk yayi yakalleta.
K'walla ce ta cika ma Nasiba idanu tace kar kice haka Jawahir dan Allah kitaimaka ki aureshi na maki alk'awalin zamu zauna da ke lafiya, bazamu ta'ba cutar da rayuwarki ba, idan har baki auri Faruk ba hankalina bazai ta'ba kwanciya ba, dan Allah kitaimaka ki auri Faruk na tabbata zai kula da ke fiye da yadda Umar yakula da ke.
Zama Jawahir tayi tare da juyawa tana kallon gefe guda nan hawaye suka fara fita daga idanunta.
Faruk ganin yadda take hawaye yasa jikinshi yayi sanyi nan yayi ma Nasiba nuni alamun tabasu waje, mik'ewa Nasiba tayi tafita cikin sanyin jiki, Nan yamaida kallonshi ga Jawahir ahankali yakira sunanta tajuyo takalleshi cikin muryar kuka tace Yaya Faruk dan Allah kace min maganar da Aunty tayi da wasa take ba da gaske ba.
Murmushi yayi yace Jawahir dagaske take ina sonki kuma zan aureki idan har kin amince.
Saurin tarar numfashin shi tayi tace ban amince ba bazan ta'ba aurenka ba domin kai Yayana ne.
Wani irin haushi Faruk yaji ammah yadanne yace idan har kin d'aukeni a matsayin Umar zaki iya aurena Jawahir tunda shima kin aureshi ko kin mance lokacin da muke bankwana zaki dawo nan kikace infad'i duk abinda nake so kiyi min nace bana buk'atar komai sai abu guda, kikace menene nace zan sanar da ke ba yanzu ba, inzaki tuna cewa kikayi Allah yakaimu lokacin insha Allahu komenene zan nema zaki mallaka min shi, idan ko haka ne Jawahir aurenki nakeson yi dan Allah ki amince min.
Kallonshi tayi fuska sha'be sha'be da hawaye tace taya zan iya aurenka Yaya Faruk? Taya zan auri mijin Aunty Nasiba idan har nayi haka ban mata adalciba ga mahaifinta anrufe sanoda ni sai kuma in auri mijinta dan Allah kacanza wani abun ammah bazan iya aurenka ba.
'Dan guntun murmushi yayi yace wannan alfarmar ita kad'ai nake nema a wajenki idan kuma har baki amince ba shikenan zan hak'ura Jawahir saidai na san kisan girman alk'awali da hukincin rashin cikashi.
Cikin kuka tace ni ba wai alk'awalin bane bazan iya cikawa ba kawai dai aurenka ne bazan iyaba kai fa matsayin Yayana kake kuma Aunty Nasiba ban mata adalci ba idan na auri mijinta nidai kayi hak'uri bazan iyaba Barrister...tun kan tarufe baki sai jin muryar Inna Mairo sukayi ta ce Jawahir indai kika k'i amincewa da aurenshi tabbas kin zama butulu domin duk halarcin da mutanen nan sukayi maki baidace kice haka ba.
Cikin kuka tad'ago takalli Inna Mairo sai kuma tajuya cikin sauri tashige uwar d'aka tamaida k'ofa tarufe.
Inna Mairo kallon Faruk tayi tace kar kadamu Faruk zamu fahimtar da ita.
Nasiba ce tashigo ganin yadda sukayi cirko cirko yasa tagane Jawahir bata amince ba, dan haka tace Inna dan Allah kulallasheta ta amince da auren nan zamu zauna lafiya bazan ta'ba cutar da itaba insha Allahu zatayi alfahari da auren nan da zatayi.
Murmushi inna mairo tayi tace kubarta kawai Nasiba zata amince, muma ai abun farin cikine agaremu ko bakomai munsan zata rage yawan shiga damuwa da tunane tunanen da take.
Faruk dai baice komai ba dan ya san daman mawuyacine ta amince ta aureshi saidai shima a yanzu yana da burin aurenta dan yacanza mata rayuwa yamaido mata farin cikin da tarasa a rayuwarta.
Har sakayi sallar la'asar bata fitoba dan haka Baba Malam yaje yabuga mata k'ofa lokacin tana kwance har lokacin tana kuka dan jin abun take wani iri wai itace Nasiba take rok'o ta auri mijinta, jin muryar Baba Malam yasa tayi saurin tsaida kukan tare da tashi cikin sauri tabud'e k'ofar takoma tazauna tana sheshek'ar kuka.
Baba Malam ne da Inna Mairo suka shigo suka samu waje suka zauna nan Baba Malam yakalleta yace Jawahir idan har kikayi ma mutanen nan haka baki kyauta ba, kar kimance halarcin da Faruk yayi maki a rayuwa kar ki kasance me manta alkhairi, kar kisaka kanki cikin mutane marassa godiya, tunda su suka nemi ki aureshi ba ke ce kika nema ba Jawahir na tabbata idan har kika auri Faruk bazaki ta'ba yin da kin saniba dan shi d'in mutumin kirki ne.
Girgiza kai tayi cikin muryar kuka tace ni ba wai na k'i bane kawai dai hakan ba adalci bane in auri mijinta nidai sutaimaka subarni ink'are rayuwata a haka dan Allah na rok'eku.
Baba Malam ne yace shikenan Jawahir mu bazamuyi maki dole ba zamu hak'ura da abinda mukeso dan bamu muka haifekiba dole mubari kiyi abinda zai faranta maki rai.
Inna Mairo ce tace tabbas haka ne Alhaji domin mu mahaifiyarta muka haifa itace zata kasance me biyayya da duk abinda mukeso Allah sarki rayuwa mutuwa bata barin wani dan wani yaji dad'i, ina ma ace Khausar tana raye.
Jawahir tana jin haka k'ara sautin kukanta tayi tare da zamowa k'asa cikin kuka tace dan Allah Inna da Baba kuyi hak'uri wallahi nima mai biyayya ce zanyi maku biyayya ga duk abinda kukeso na amince zan auri Faruk dan Allah kusa ma rayuwata albarka.
Suna jin haka duk sai wani irin farin ciki yalullu'besu nan sukaita shimata albarka, gefe d'aya kuma tausayinta suke ji.
Jawahir kasa cewa komai tayi saidai cigaba da kukanta da tayi.
Fitowa sukayi suka samu su Baba Musa da su Faruk zaune sunyi shuru suna jira sufito suji yadda sukayi da ita dan Faruk tsintar kanshi yayi da jin wani iri akan nunawa da Jawahir tayi bata sonshi, yana ganin su Baba Malam sun fito saida gabanshi yafad'i wanda yarasa dalilin fad'uwar gaban, idanu yazuba masu yana kallonsu, Nasiba ce tayi k'arfin halin cewa Baba ya kukayi da ita ta amince?
Murmushi su Baba Malam sukayi sukace Eh ta amince.
Gabad'ayansu hamdala sukayi Faruk ko ajiyar zuciya yasafke yaji wani irin sanyi ya ziyarceshi.
Nan shi da Nasiba sukayi masu godiya.
Nasiba jikkarta tad'auko tafiddo dubu d'ari taje tatsugunna gaban Baba Malam tace Baba ga wannan kud'in neman aurene ni nad'auki nauyin biyansu, sannan insha Allahu su Dad zasu zo atsaida ranar aure mudai muna rok'on ataimaka mana kar asa rana dayawa dan munfiso ayi bikkin batare da anja lokaci ba.
Su dukansu mamaki yakamasu ganin yadda ko kad'an bata nuna damuwa ba saima murna da take.
Inna Mairo ce takasa daurewa tace tabbas wannan mata zuciyarki me kyau ce tunda nake a tarihin rayuwata da idanuna kece macen da nata'ba ganin ta yi hakan, Allah ubangiji yasaka da alkhairi, Allah yabiyaki da gidan aljanna.
Murmushi Nasiba tayi tace babu komai Inna ai Jawahir 'yar uwatace kuma duk musulmi na k'warai zaiso ma d'an uwanshi abinda yake so ma kanshi, ko bakomai Jawahir ta cancanci fiye da hakan a wajena dan itama ta taimaka mani a lokacin da nake buk'atar taimako taya zan kasance me manta alkhairi.
Maganar da tayi ta shigesu sosai nan sukaita mata godiya, Faruk ko saidai idanu yazuba mata cikin zuciyarshi yana gode ma ubangiji da yamallaka mashi Nasiba a matsayin mata dan tabbas ita d'in macece ta gari.
A chan 'bangaren Jawahir tana ganin su Baba Malam sun fita komawa tayi takwanta nan tafara rera sabon kuka, dan dole ta amince da za'bin su saboda a yanzu batada na sama da su suna k'ok'arin yi mata duk abinda take buk'ata, alk'awaline tayi ma kanta bazasu ta'ba kuka da itaba babu abinda zasu nema a wajenta surasa itace zata koma madadin mahaifiyarta a wajensu, wannan dalilin ne yasa tayi saurin amincewa da auren Faruk.
Har wajen k'arfe biyar Jawahir bata fitoba dan haka wajen biyar da rabi suka bar Kebbi sunso suyi bankwana da Jawahir ammah tak'i fitowa dan koda Inna Mairo tashiga dan tafad'a mata tafiyar da zasuyi samunta tayi tana bacci ko da ma ba baccin gaske takeba dan bataso tasake had'a idanu da mutanen ne saisa tatsiri baccin k'arya zuciyarta a tunkushe.
Nasiba Alk'awali tayi masu insha Allahu da sunje zasu sanar da su Dad azo ayi maganar auren, Faruk ko saidai yabita da idanu ta k'ara daraja sosai a cikin idanunshi.
K'aramin galan d'in kindirmo da man shanu aka basu da k'ananun tsarabobi suka tafi da su har airport su baba musa suka rakasu saida jirginsu yatashi sannan suka baro airport d'in.
Suna komawa gida Nasiba part d'inta tawuce Faruk kamar jira yake yabi bayanta fara cire kaya tayi sai gashi ya shigo kallonshi tayi tai murmushi tace ya dai ango bazaka d'an watsa ruwaba kafin magrib?.
Matsowa yayi kusa da ita yace yanzu saboda Allah Nasiba hakan da kikayi kin kyauta?.
Murmushi tayi tace me nayi, dan kawai na nema maka auren Jawahir sai yazama laifi, kaima fa kana sonta malam kafiddo farin cikinka a fili kawai ba sai ka 'boye min ba.
Rik'o ta yayi yana mata kallon mamaki yace Nasiba wa yafad'a maki ina son Jawahir?
Cikin idanunshi takalla tace soyayyarta nagani a cikin idanunka ko zaka iya rantsewa kace baka sonta.
Jan hancinta yayi yace ni bance ina sonta ba.
Janye hancinta tayi tace wash da zafi fa Lovely, ni dai nasan kana sonta kawai dai kana basarwa ne,,, tana fad'in haka tajuya tana k'ok'arin cire skirt d'inta, rik'o hannunta yayi yace ya akayi kikasan haka?.
Batare da ta juyo ba tayi murmushi tace tun daga yanayin yadda kake waya da ita da yadda kake yawan min labarinta kai tunma kafin nan zan iya cewa tun a kotu nafara ganin alamar hakan.
Faruk kasa cewa komai yayi nan yaja yai tsaye yana kallonta cike da mamaki.
Juyowa tayi takalleshi fuskarta d'auke da murmushi tace ko zakayi wanka muje muyi kar magrib yayi kaga na gaji sosai yau.
Batare da ya ce komai ba yafara cire kayanshi dan rasa abinda zaice mata yayi.
------*****-------
A daren Nasiba takira su Dad da Mom tafad'a masu yadda sukayi da su Baba Malam, washe gari Faruk yaje gida nan yasake fad'a masu komai har da irin k'ok'arin da Nasiba tayi wajen nema mashi auren Jawahir.
Daga Dad har Mom sun jinjina mata nan sukaji ta k'ara shiga ransu sukayi Allah yasa alkhairi.
Dad yasa mom takira Nasiba a waya tatambayeta wata nawa yadace asa bikkin nan Nasiba tace kar yawuce wata biyu kamar yadda akasa nata suka amince da haka.
A cikin satin ne su Dad da abokinshi sukaje Kebbi suka nema ma Faruk auren Jawahir wajen Baba Malam yace ai Nasiba ta nema mashi auren saidai ayi baiko, haka ko akayi akasa bikki wata biyu masu zuwa, dan a lokacin bikkinsu Khausar sati bakwai yarage nan aka ce za'a k'ara sati guda ayi tare da na su Jawahir jin haka yasa su Dad sukace a'a kar ak'ara kawai arage sati guda daga cikin wata biyun da akasa sai ayi bikkin tare nan da sati bakwai nan su Baba Malam suka amince su Dad dayake a mota sukazo suka fiddo kayan sa bikkin da suka ciko boot da su suka bada sannan suka juya saboda tafiyar mota ce basuso suyi dare dan ma driver yakawo su.
_________Jawahir ko tun ranar da su Faruk sukazo sukayi maganar aurenta tad'auki damuwa tasa a ranta saida Inna Mairo tadinga mata nasiha tare da bata shawara tabar ma ubangiji za'bi acikin rayuwarta sannan tarage sa damuwa tadinga tashi kullum cikin dare tana kaima ubangiji kukanta tare d neman za'binshi a cikin rayuwarta.
Su khausar ko murna suka dinga yi suna tsokanarta dan cewa suke daman chan sun ga alamar faruk yana sonta yanayin yadda yake kallonta, Rashida tace yoh itama d'in bakiga yadda take d'oki idan yazoba tana sonshi gulma ce kawai mudai munji dad'i.
Shuru jawahir tayi tak'yaleshi nan magana tazagaye gida akaita murna tare da yin Allah yasa alkhairi.
Lokacin da akasa bikki ko jawahir kasa fitowa tayi a d'aki ta'boye tadinga kuka.
Sauran mutanen gida aka dinga murna musamman da akaji tare da nasu Khausar za'a had'e ayi ......
_Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:22 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]
_Follow