Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
buga masu k'ofa da k'arfi a firgice duk suka farka Abbu yatambaya wanene? Muryar wani k'ato sukaji ya ce kazo Kabud'e mana ko mubud'e dakanka.
Abbu salati kawai yake inda Ammi take kuka tana salati.
Cikin tsawa mutanen sukace bazakazo Kabud'e ba sai mun bud'e dakanmu? Mik'ewa Abbu yayi zaije yabud'e Ammi tayi saurin rik'eshi tace dan Allah Alhaji kar kaje.
Yana shirin yin magana suka harbe k'ofar da bindiga suka shigo su duka fuskokinsu da face Max d'aya yake rik'e da bindiga d'aya kuma shar'be'biyar wuk'a d'ayanko bai rik'e da komai.
A ranar su Ammi sunga tashin hankali dan sasu sukayi sukai kneeldown karon farko takardun gidan Ammi da na company suka tambaya Abbu yace shi baida wani company kuma wannan shi kad'ai ne gidanshi.
Kan bindiga suka buga mashi Ammi tasaki wata irin k'ara, har saida wajen yafashe sukace kabamu mukace yace ni na fad'a maku banda su.
Sukace zaka rasa rayuwarka idan har kayi mana gardama dan munsan akwai.
Abbu nacewa yayi akan babu nan d'aya daga ciki yad'aga wuk'a biyun suka rirrike Abbu itako Ammi zuwa tayi tarikesu tana kuka tace dan Allah kar sukashe mata miji zata basu duk abinda sukeso.
Wurgi sukayi da ita gefe kafin tataso anyi ma Abbu yankar rago sai jini da yafara tsartuwa,,,,jawahir fashewa tayi da wani irin kuka tace sun kashe min Abbu nah a lokacin ni ina chan d'akina ina bacci koda lokacin ban wuce shekaru sha biyar ba a duniya, goge hawayen tayi tace
Ammi wata irin razanannar k'ara tasaki daidai lokacin mutane biyu suka cire Max d'insu suna goge hannuwansu da suka 'baci da jini nan ita kuma tasulale k'asa a sume.
Ashe d'aure megadin gidanmu sukayi yana ta yunk'urin yakwance ammah yakasa sai bayan tafiyarsu yasamu yakwance dakyar sannan yashigo yagane ma idanunshi abinda yafaru su ma masu aikin gidanmu tsoro ne yahanasu fitowa sai bayan tafiyarsu nan akaje aka sanar da Abba Mu'azu yazo yadinga kuka kowa wajen kuka yake, me gadi ne yakira police inda aka yayyafa ma Ammi ruwa tafarfad'o hatta ni da nake k'arama nayi kuka sosai da naga cin mutuncin da akayi ma Abbu nah.
Kafin safe gidanmu ya cika da mutane inda yan sanda suke ta binciken gidan suna so sudauki report aka dinga ma Ammi tambayoyi tana fad'in abinda yafaru har wajen k'arfe tara sannan akayi ma Abbu wanka da za'aje kaishi Abba Mu'azu yashiga d'akin da aka sitirta gawar yana kuka yana ma d'an uwan nashi addu'a nan aka barshi dan yayi mashi addu'a akaba Ammi dama itama taje tayi ammah takasa.
Ahaka aka tafi da Abbu gidanshi na gaskiya nan aka fara zaman makoki ammah abinda zai baka mamaki ba wani bincike da aka cigaba da yi dan gane wad'anda sukayi aika aikar Ammi saidai tagaji tasamu Abba Mu'azu tayi mashi maganar yace ai yan sanda suna chan suna bakin k'ok'arinsu suna ta bincike.
A rana ta biyu da rasuwar yaya Umar yazo k'asar nan shima yayi kuka sosai har saida akayi arba'in sannan yakoma school, Ammi damuwa tad'auka ta aza ma kanta nima haka kusan kullum sai na ce akaini wajen Abbu nah daga ni har Ammi idan kaganmu sai ka tausaya mana dan duk mun fita hayyacinmu.
Anayin arba'in su Abba Mu'azu suka dawo cikin gidanmu ya amshi key d'in part d'in Abbi yace nan zai zauna shi da matarshi inda d'akina yakoma na yaya Aliyu saidai nakoma d'akin Ammi nazauna aiko nan su Abba Mu'azu suka dinga zuba mulki a gidan Ammina takoma abun tausayi dan Ummah Fatima matsa mata tadinga yi a cikin gidan ma ba ko'ina take da ikon zuwaba ita da gidan mijinta ammah aka sa mata dokoki, hatta shi kanshi Yaya Aliyu taka Ammina yake son ranshi wani lokacin saidai muyi zamanmu a d'aki Ammi tayita kuka ina tayata, Abinci ma kanshi sai angama dama abamu saidai 'yan aikin gidan suke fakar Idanun su Ummah Fatima sukawo mana a d'aki idan Ammi tayi masu magana akan sudaina sai suce a'a koda ace zasu rasa aikinsu sai sun taimaka mata dan su kansu sunsan sun mori matar nan sosai abun hannunta baya tsone mata idanu tana da kyauta.
Haka rayuwarmu tacigaba da tafiya a gidan namu da yazama kamar dodonmu duk motocin Abbina suka koma su Abba yake shiga motar da Abbu yasiya ma Ammi ita Abba ya amshe yaba ummah,
Wata rana muna zaune a d'aki Ammi tana min k'arin karatun islamiyya nan Ummah Fatima tashigo direct wajen wardrobe d'in Ammi tawuce batare da ta tanka ma Ammi ba tana zuwa tafara fitar da kayan Ammi daga cikin wardrobe d'in.
Ammi ce tace lafiya Hajiya kika zazzago min kaya?
Juyowa tayi tagalla mata Harara tace lafiyar kenan zan d'auki kayan da naga basu dace da kisaba dan a yanzu ba a matsayin komai kikeba.
Ammi tana kallo tazazzage mata kaya takwashe rabi da kwata hatta k'addarorin Ammi saida takwashe, babu yadda Ammi ta iya dole tahak'ura, yan aikin gidan gabad'aya korasu tayi lokacin da tagane suna kaima Ammi abinci saida tayi bala'i sosai sannan takoresu tace bazata iya zama da munafukai ba.
Tun daga ranar duk wani aikin gidan yakoma wajen Ammi, munga rayuwa sosai dan hatta karatuna saida yanemi yatsaya dan kud'in da za'a biyamin babu saboda makarantar tana da tsada sosai saida Ammi tasiyar da wasu gwalagwalenta wad'anda taboye sannan tabiya min nacigaba da makaranta ta har nayi JSCE.
Dawowa gidan da nayi yasa nacigaba da taimaka ma Ammi da ayyukan gida, dan rashin imanin su Abba abincin da suke bamu baifi mutum d'aya yaciba wani lokacin ma rabin plate.
Bayan shekara d'aya da Ammi taji shurun ya yi yawa ba'a ce komai ba akan maganar mutuwar mijinta da maganar gadonsu yasa tashirya taje gidan wani Aminin dadynshi tafad'a mashi tanaso araba masu gadon su.
Ya amince da toh zaizo suyi magana da Abba Mu'azu.
Koda yazo sukayi magana baice ma Ammi komai ba yatafi saima Alhaji Mu'azu da yazo yadinga fad'a dan mi zataje takai k'ararshi tace wai araba masu gado, a ranar wulak'anci yayi ma Ammi sosai har yakirata da matsiyaciya d'iyar talakawa.
Kwana d'aya biyu bataji Alhaji Lurwan ya zo ya yi maganaba dan haka tasake d'aukar k'afa taje gidanshi yace tayi hak'uri ana ta k'ok'ari anaso ahad'a dukiyar Alhaji Muhammad sannan araba masu gado.
Duk atunaninta dagaske ne dan haka takoma gida ammah har sati biyu bataji wata maganaba dan haka tabarshi tasake zuwa wajen wani abokin Abbu me suna Alhaji Surajo shima dai ba bayani, saida taje wajen aminnan Abbu hud'u ammah da sun shiga maganar ana kwana biyu zata watse.
Nan hankalin Ammi yatashi sosai taje tasamu lauya d'in Abbu watau Barr Muhsin tafad'a mashi.
Abinda yabata mamaki shima baiyi wani yunk'urin taimakonta ba dan ganin gadonta ya fito, dan haka tafitar da kayan d'akinta tasiyar taje tashigar da k'ara kotu, duk wannan abun fa Ammi tana yine dan kawai nawa hak'k'in ba ma nataba saidai abinda ita bata saniba shine wannan k'arar da tashigar zata zame mata matsala a rayuwa.
_*Remain 1 page mugama free Page's😍*_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/14, 21:42] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAN RAI.......*
_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_
*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]
*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*
_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_
_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_
_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_
_Last Free Page_
*PAGE TWELVE*
Wasu siraran hawaye ne suka gangaro ma Jawahir masu d'umi saurin runtse idanunta tayi tacigaba da cewa Ammi tana shigar da k'ara a Shara'a Court suka aiko ma Abba da takardar shammaci na ana gaiyatarshi a court akan k'arar da Ammi tashigar nashi dan wani tsohon alkali Makobcinmu yasama mata lauyan da zai tsaya mata, Abbu na jin haka hankalinshi yatashi yaje yasamu Barr Muhsin yafad'a mashi nan sukazo suna lallab'ata akan taje tajanye k'arar ammah tak'i dan haka Barr Muhsin yace zai tsaya yakare wanda ake k'ara, ana saura sati d'aya azauna kotu Abba Mu'azu yazo yasamu Ammi a d'akinta yace shi ya yarda zai bada duk wata dukiyar Abbu araba idan ta amince takawo duk wasu takardu nashi da suke hannunta shima zaisa atattaro sauran, Ammi tace bata yadda ba bazata bayarba abin ya 'bata ma Abba Mu'azu rai sosai da yaje yana fad'a ma matarshi ne Yaya Aliyu yaji nan ranshi ya'baci yace yanzu Abba wacchan matar har ta isa takaika k'ara akan kud'in dan uwanka? Wallahi bata isaba sai na nuna mata batada wayau, wacece ita,,,cike da jin dad'in kalamanshi Abba yace kabarta kawai Aliyu nasan ta inda zan biyo mata dan bata isa tatozarta ni a Idanun jama'a ba.
Wallahi Abba batada amfani acikin gidan nan kawai akorata takoma garinsu tunda wanda ya aurota ya mutu ya bar duniyar.
Murmushin mugunta Abba yayi yace Son kai ma kake fad'a ana ji, katayani tunanin hanyar da zamubi mukoreta tatafi tabar mana garin.
Uhm shikenan Abba zan samo mana mafita.
Bayan kwana ukku da yin abun Ammi tana kwance tana bacci da rana nikuma ina gefenta inayin homework d'ina dan a lokacin na cigaba da zuwa school ina SS 2 kamar an mintsireta sai ganin Ammi nayi ta tashi a firgice da mamaki nake kallonta nace Ammi Lafiya?
Bin d'akin tashiga yi da kallo sai chan tace Jawahir kebbi nakeson zuwa hankalina ya yi gida.
Zaro ido jawahir tayi tace Ammi kebbi kuma?
Murmushi tayi tace Eh jawahir inason zuwa dan ina ji a raina bazan kai wani lokaci ba,,hawaye ne suka gangaro mata tace ganinsu shine kwanciyar hankalina zanje kawai.
Fashewa jawahir tayi da kuka tace nima zan biki Ammi.
A'a Jawahir bazanje dakeba kizauna kawai insha Allahu zuwa jibi zan dawo,,,Ammi na fad'in haka tafara had'a kayanta cikin wata yar k'aramar jakka tazuba kaya kala ukku da takardun gidanta da Abbu yabata take ta faman boyesu tana gama had'awa tasaka hijab tajuyo takalli jawahir da ke tafaman kuka tace kiyi hak'uri jawahir idan da rabo zan dawo gareki.
Rik'ota jawahir tayi tace dan Allah Ammina kar kitafi kibarni.
Cikin sanyin jiki Ammi tak'wace jikinta tace jawahir kikula da kanki,,,tana fad'in haka tajuya cikin sauri tafita daidai zata fita Aliyu yashigo gidan tsayawa yayi yana kallonta a wulak'ance saida taganshi tatuna batayi sallama da su Ummah ba dan gabad'aya jin jikinta take wani iri,,tsayawa tayi tace Aliyu kafad'a ma ummanku na tafi kebbi.
Yatsina fuska yayi yace toh menene namu a ciki kiyi ta tafiya mana.
Ammi batace komai ba tajuya tafita dan indasabo ta saba da rashin kunyar Aliyu, malam Idi driver tagani wajen megadi suna hira nan ta isa wajensu suka gaisa sannan tace mashi kebbi takeso yakaita.
Da mamaki suke kallonta sukace Hajiya Lafiya zakije kebbi a wannan lokacin?
Murmushi tayi tace buk'atar hakan ne yataso min.
Malam idi yace toh Hajiya muje,,,megadi ne yataso yabud'e mata mota tare da yi mata Allah yakiyaye tana shiga motar idi na shirin tadawa sai ga Alhaji Mu'azu ya shigo gidan kallon malam idi yayi yace ina zakaje da ita?
Jikin malam idi yana b'ari yace daman kebbi tace inkaita.
Abba Mu'azu kallon Ammi yayi sannan yawuce yashige gida, Ammi runtse idanunta tayi wasu hawaye masu zafi suka gangaro mata ahaka suka kama hanya.
Tunda suka Kama hanya Ammi sharar hawaye kawai take ahaka sukayi tafiyar kusan awa biyu suna shiga wani d'an kauye dake mararrabar katsina nan suka fara ganin wasu motoci biyu suna bin bayansu ammah basu kawo komai a ransuba sai malam idi da yaga sunk'i wucewa sai yarage speed dan suzo suwuce su ammah da mamakinshi sai yaga su ma sunrage yace Hajiya wad'an chan motocin sai bin bayanmu sukeyi, Ammi ta cikin mirror takallesu tace k'ila su ma hanyarmu sukayi ko gari d'aya zamuje.
Malam idi yace hakane dan haka yacigaba da tafiyarshi normal ta wata boyayyar hanya suka ratsa sukabi dan suyi saurin isa kebbi da mamaki sai ganin motocin sukayi sun biyo bayansu lokaci guda d'aya daga cikin motar tak'ara gudu tazo ta wucesu tana wucewa tasha gabansu cikin sauri malam idi yaja wani irin burki dan kar yafad'a ma motar nan motar bayansu itama tatsaya, motar da take gabansu ce aka bud'e wasu karti biyar suka fito k'osassu rikicewa Malam idi yayi yafara salati tare da k'ok'arin so yatada motar ammah kafin yayi wani yunk'uri har mutanen sun iso ta window suka Fisge key d'in motar tare da bud'e k'ofar suka fiddoshi yafad'o k'asa, Ammi fasa k'ara tayi tare da furta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un nashiga ukku.
Zagayawa sukayi suka bud'e mata sukace tafito, jikinta yana rawa tafito tace dan Allah kuyi hak'uri kufad'a min abinda kukeso.
Dariya suka kwashe da ita gabad'ayansu sun dad'e suna yi kafin daga bisani sukayi shuru d'aya daga cikinsu ne yace bamu buk'atar komai a wajenki face ranki kawai da mukeso.
Ammi na jin haka ta ida rikicewa malam idi yace dan Allah kuyi hak'uri kar kukashemu.
Tsawa suka kwatsa mashi sukace yayi masu shuru nan wani k'ato bak'i k'irin yayo wajen Ammi da shar'be'biyar wuk'a baya tafara ja a tsorace tana cewa dan Allah kar kakasheni mi nayi maku da kukeson rabani da raina? Waige waige tadinga yi tahango wata yar hanya aiko nan tabaza aguje nan suka bita dukansu, gudu take iya k'arfinta duk k'ayoyin da suke cikin dajin ta taka ammah bata ma san tana takawaba saboda bala'in da take gani, ka san ba'a had'a gudun mace da namiji ganin sun kusa taddota yasa tak'ara gudu tana ambaton sunan Allah bata ankaraba sai ji tayi wani ya tad'e mata k'afa ta fad'i daidai wajen wani suri, ja tadinga yi da baya tana kuka tana cewa dan Allah kuyi min hak'uri, wani ne yazo yazare mata hijab tare da damk'ar gashin kanta yajuya yakalli sauran yace gaskiya tana da kyau da son samune ace yanzu na d'an huta da ita kafin akasheta.
Nan sukasa dariya sukace ai kana hutawa da ita muma sai mun huta da ita.
Ammi Khausar tana jin haka tabud'e baki dakyar tace babu wanda ya isa yata'ba min jiki saidai kukashe ni.
Daidai lokacin Malam idi ya iso wajen cikin sauri yaduk'a gaban wanda yake rik'e da Ammi yana rok'onshi kar yakasheta.
Shuru yayi yana kallonshi nan wani yatafo daga bayanshi batare da sanin malam idi ba saidai yaji anda'ba mashi wuk'a dakyar ya iya yin salati nan yafad'i k'asa yana shure shure jini yana ta malala har yamace.
Wata irin k'ara Ammi Khausar tasaki cike da tashin hankali nan wanda yake rik'e da ita yabuga mata kanta ajikin icce,dinga buga mata kan yayi a iccen da dukkan k'arfinshi jini yadinga fita ta kan, kumbura yayi sosai tun tana motsi har tamace saida yatabbatar da mutuwarta sannan yasaketa tafad'i k'asa ya amshi wuk'a yaluma mata sannan suka wuce cikin sauri suka bar wajen.
'Daid'aikun mutanen da suke wucewane a saman abin hawa suka ga motar a gefen titin a bud'e suka kira police sukazo sukayi bincike har aka gano gawarwakin aka bincika motar aka d'auko jakkar Ammi Khausar aciki aka samu duk wani address d'inta.
Aka d'auki gawarwakinsu aka kai gida.
Jawahir wani irin kuka tadinga yi mai shiga rai tana jin kamar yanzu ne abun yafaru kasa cigaba da labarin tayi saboda kukan da takeyi Barr Faruk jikinshi sanyi yayi sosai d'ago kai yayi yakalleta yace jawahir kiyi hak'uri Allah ubangiji yajik'an su Abbu da Ammi.
Goge hawayenta tayi tace Ameen sannan tacigaba da cewa....
A ranar naga tashin hankali sosai a lokacin da nacikaro da gawar Ammina a tsakar gidanmu an kawo kanta ya yi suntum kamar zai fashe bansan lokacin da nasulale nasuma ba saidai gani na nayi a gadon asibiti wata mata tana jiyyata ashe har nayi sati bansan lokacin da aka kai Ammi gidanta nagaskiya ba saida na'kara kwana d'aya nan namatsa saida aka sallameni nakoma gida lokacin har anyi sadakar sati d'aya, kuka nadinga yi sosai saida wani malamin mu da yazo min gaisuwa yayi min wa'azi sannan nadaina, damuwa nad'auka nasa ma raina duk na fita hayyacina saida nayi wata d'aya nadawo daidai, na d'auka mutuwar Ammi zaisa su Abba Mu'azu sucanza ashe abun ba haka bane Ammi tana wata d'aya da rasuwa nan aka tasoni a gaba duk wani aikin gida yadawo kaina, nakoma kamar wata baiwa tun ba'aje ko'ina ba na ida fita hayyacina abinci sai anso ake bani inci, dakyar nasamu nagama SS2 rashin kud'in da zasusa incigaba da karatuna yasa karatun yatsaya dan Abba Mu'azu cewa yayi bazai biya min ba.......
Tana kawowa nan Barr Faruk yaji ta yi shuru d'ago kai yayi yakalleta da mamakinshi sai yaga tana bacci.
Saurin mik'ewa yayi ya isa bakin gadon yaga dagaske ko baccinta takeyi cikin ranshi yace ikon Allah tunda nake ban ta'ba ganin mutum irin wannan ba, d'aukar laptop d'inshi da wayoyinshi yayi yakoma parlor yazauna yana cigaba da aikinshi.
Tayi awa d'aya tana bacci ahankali tafara juya kanta tana girgizawa tanaso tabud'e idanunta ammah ta kasa wata irin k'ara tasaki tare da bud'e idanunta a firgice ta tashi zaune lokacin da taga jini duk a hannuwanta bin hannuwan tayi da kallo tare da girgiza kai tace a'a meyasa hakan tafaru? Hoton da yake kusa da ita tayi saurin d'aukowa taduba hoton Alhaji Sa'idu tagani tabbas shine wanda tayi mafarki dashi d'aukar hoton tayi tayaga gutsin gutsin tasaka cikin dosbin dakyar take tafiya tana jan k'afa har tashiga toilet wanke hannuwanta tayi cikin sauri tacire jallabiyar tasaka kayanta da tazo da su dasauri tafito daga bedroom d'in, barr Faruk d'agowa yayi yakalleta yace lafiya jawahir me yake faruwa? Muryarta tana rawa tace Barrister tashi muje kamaidani zama na a nan akwai had'ari, daman ba na