Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
muzo, yanzu kuzo muje gidan.
Gabad'ayansu suka d'unguma suka nufi gida dan da fari har Jawahir ta k'i binsu ta ce ita dai subarta a nan zata tafi gidansu saidai Dad yace shin mu ba iyayenki bane Jawahir? Ko bakomai nima matsayin uba nake a wajenki saboda matsayin mahaifinki a wajena.
Da mamaki suke kallonshi tace daman ka san Abbu?
Murmushi yayi yace sosai ma muje gida zan sanar da ke inda nasanshi, bata musaba sannan tabisu suka nufi gidansu Faruk gabad'ayansu har da su Barr Nas da Barr Junaid.
Suna zuwa Mom d'akinta taja Jawahir tahad'a mata ruwan wanka tayi bayan ta fito tad'akko mata wata jallabiya tabata tasaka saida sukayi sallah sannan suka fito parlor Jawahir dai ta kasa sakin jiki dan ita rayuwarta ba mai saurin yadda da mutane bace tunda tataso haka take, suna nan zaune su Dad da su Faruk suka fito kusan lokaci guda bayan sun dawo daga masallaci, koda suka zauna Dad cewa yayi afara kawo abinci aci kafin afara wata magana dan haka Mom taje tasanar da masu aiki, nan da nan aka fara shigo masu da abinci iri iri kowa yafara serving d'in kanshi ammah banda jawahir ganin ta k'i sakin jiki yasa mom ta d'ibi abincin tajata sukaje d'akinta tace Jawahir kisaki jikinki nan ma gidane kiyi abinda kikeso mu bamuda matsala kinji.
Murmushi tayi tace nagode Mom.
Duk yadda Mom taso taci abincin k'i tayi dak'yar tad'anci kad'an tabarshi dan haka tak'yaleta.
Bayan kowa ya kimtsa cikinshi suka had'u a parlor.
Dad ne yafara cewa toh Alhamdllh a yanzu sai kasanar da mu yadda akayi kaku'buta.
Faruk murmushi yayi sannan yakwashe yadda akayi aka saceshi yafad'a masu da yadda yadinga shan wahala a wajensu har zuwa shigowar d'an uwan nasu da takeaway yakawo ma sauran.
Su duka idanu suka zuba mashi suna kallonshi cike da mamaki dan Mom ko hawaye tafara ganin haka yasa Faruk yacigaba da cewa "duk a tunanina wannan me dariyar ya tafi jin shurun da yayi sai chan naga bayyanar wata tsohuwa a gabana dudduk'e tafiyarta dakyar dakyar " kallon jawahir yayi yace ke dai na san kin gane ko wacece, d'aga kai tayi alamun Eh, cigaba yayi da cewa tana bayyana kallona tatsaya yi sai chan tace Barrister daman ban fad'a maka ba nice kad'ai nake da ikon taimaka ma Jawahir?
Wani irin kallo nayi mata cikin nuna rashin tsoro nace taimako na ubangiji ne shikad'ai yake iya taimaka ma bawansa.
Bushewa tayi da dariya tace bazanyi maka jayayya ba saidai ina farin ciki guda a yau Jawahir ta yi nadamar da dadad'ewa nake jira tayita ammah saboda taurin kanta batayiba a yanzun ma abun bak'in cikin ta yi ne ba dan komai ba sai dan tana neman intaimaka maka.
Kallonta faruk yadinga yi cikin nuna rashin fahimtar maganarta.
'Dan dogaro sandarta tayi tamatso kusa da shi sannan tacigaba da cewa a lokacin da za'a fito da su akaisu kotu hankalinta a tashe yake ganin haka yasa nabayyana a gareta natambayeta ko tana buk'atar taimakona?
Girgiza kai tayi tace bana buk'atar taimakonki.
Bushewa da dariya tsohuwar tayi tace cikin ke da Faruk dole sai wani ya riga wani shek'awa lahira.
A rikice jawahir tace ban fahimta ba me zai faru da faruk d'in?
Sake bushewa tayi da dariya saida tayi me isarta sannan tace zasu kasheshi a bayan an yanke maki hukunci a kotu saboda kar susakeshi yatona masu asiri.
Fashewa Jawahir tayi da kuka cikin sauri taduk'a k'asa tace Ammi na rok'eki dan Allah kitaimakeshi kar kibari sukasheshi bai cancanci hakan ba.
Girgiza kai tayi tace bakida ikon neman taimakona batare da yin nadama ba.
'Dago kai tayi fuska sha'be sha'be da hawaye tace indai har akan Faruk ne na amince saida taruntse idanunta cike da takaici sannan tace na yi nadamar kalmar da nafad'a maki kiyi hak'uri insha Allahu bazan sakeba, ina sonki Ammina....dariyar da taji ana kyalkyalawane yasa tayi saurin bud'e idanunta dan gabad'aya d'akin yake amsaba dubawa tayi taga babu Ammin tata saidai muryar dariyar taji tana fita, tana nan duk'e a haka akazo aka fita da su aka tafi da su kotu.
Tana kawowa nan a bayanin nata tanuna inda Faruk yake zaune da sandarta sai gani yayi d'aurin da akayi mashi ya kwance, cikin muryarta me ban tsoro tace zaka iya fita ga k'ofa chan a bud'e nan da minti takwas zata iya rufe kanta, jin haka yasa Faruk yayi saurin mik'ewa duk sai yajishi wani iri dakyar yafara takawa dan a lokacin matar har ta 'bace, bin gidan yadinga yi da kallo bai san inda yakeba da karambani yagano k'ofa yana fita k'ofar tana maida kanta tadatse tsayawa yayi yak'are ma gidan kallo saida yagane anguwar sannan yasamu abun hawa yahau yanufi gidan Barr Nas, ya yi sa'a ya sameshi a gida nan yayi ta murnar dawowarshi wanka yayi yashirya cikin sauri, sannan yace ma Nasir yad'auko mashi ajiyar da yakawo mashi ranar da za'a kamashi dan dama jikinshi ne yadinga bashi kamar akwai abinda zai iya faruwa da shi wannan dalilin ne yasa yad'auki dukkan shedun da yatara yakai ma Barr Nas ya ajiye mashi wajenshi hatta wayarshi da yafi amfani da ita saida yakashe yabashi dan ya san a cikinta ya ajiye abubuwa dadama masu muhimmanci,daga nan suka fito cikin sauri suka nufi kotu dan a lokacin sun makara dan sunsan dole cikin biyu ayi d'aya ko angama shari'ar Jawahir ko kuma ana cikin yi....yana kawowa nan a labarin yace wannan shine abinda yafaru da ni.
Hankalinsu gabad'aya saida yatashi sosai Dad yace tabbas Alhaji Sufyan ya kasance maha'inci ban ta'ba tunanin haka daga gareshiba ace da sa hannunshi aka sace min d'a duk kusancin da ke tsakaninmu ina mashi kallon abokina na k'warai ashe ba haka ba.
Jawahir sai a lokacin tad'ago takalleshi tace ya akayi kasamo Ummah katafo da ita?
Murmushi yayi yace lokacin da naje asibitin naga halin da take ciki nan nanemi taimakon likitocin suka taimaka suka ban ita nacanza mata asibiti inda zata fi samun kulawa dan asibitin da su Alhaji Mansur suka kaita wata k'aramar asibiti ce wadda basuda wadatattun kayan aiki kuma sunyi hakane dan kawai suna so tamutu itama, toh cikin ikon Allah ina maidata chan suka dinga bata kulawa sosai har tafara samun sauk'i, dan tana iya motsa 'bare d'aya na jikinta saisa ma nace atafo da ita tunda tana magana.
Shi kuma megadinku buzu wannan aikinki ne dan kece kika samar mana taimako Amminki tasanar da mu inda yake.
Jinjina kai su Dad suka dinga yi mamaki duk ya cikasu.
Barr Junaid yace lallai sharrin su Alhaji Mansur ya fi tunanin duk wani me tunani ashe duk wannan k'ulla k'ullan su sukayi shi sukaja aka kama baiwar Allahr nan.
Dad girgiza kai yayi yace wasu mutanen macen zuciya garesu babu abinda sukasa gaba sai son kansu, kallon jawahir yayi yace tabbas na san mahaifinki dan abokin kasuwancina ne a lokacin da yake raye kamfanina da nashi kusan tare suke tafiya dan ma baza'a had'a ba nashi kamfanin ya fi nawa d'aukaka saboda wasu kayan ya fini saidai shi ba mutum bane me bak'in ciki yana son cigaban mutane nan yasa muka had'a hannu tsakanin kamfanina da nashi muna shigo da kaya tare wani lokacin idan kamfaninshi yana buk'atar rancen kud'i a nawa kamfanin yake zuwa yana ranta nima haka akan wannan ne yasa muka k'ulla abota sosai akan kasuwancinmu dan kowa yana son cigaban d'an uwanshi bamufi wata takwas a haka ba nanemi rancen wasu kud'i saboda wasu kayan aikin injin da nakeso inje Dubai insiyo yad'auki kud'in yabani, koda naje Dubai saida nayi kusan wata ukku sannan nasamu yadda nakeso naturo da kayan ni ban dawoba a wata na biyar ne naturo mashi da kud'inshi daga chan saidai 1 million da tarage ban bashiba, ak'alla saida nayi wata goma sannan nadawo k'asar nan bayan na dawo ne nasamu labarin rasuwarshi nan hankalina yatashi sosai haka nad'auko million d'aya d'in nan naje gidanshi nayi sallama nasa aka kira man matarshi koda tafito nayi mata gaisuwa sannan nabata cheque d'in kud'in, tun bayan rasuwarshi na so mucigaba da kasuwanci tsakanin kamfanina da nashi ammah d'an uwanshi yak'i dan haka nabarshi lokaci guda kamfanin yadaina kawo kud'i yadda yakamata nawa yazo yafi shahara, a haka nak'ara nema muhad'a hannu da Alhaji Mu'azu mumaido ma kamfanin tattalin arzik'inshi ammah yak'i dan gani yake kamar wani cutarshi nakeson yi wannan dalilin ne yasa nafita harkar kamfanin.
Jawahir fashewa tayi da kuka tace tabbas kaine Alhaji Sanin da yazo gida yakawo ma Ammina cheque akan kud'in ne aka nemi a salwantar da rayuwarta
Su duka kallonta suke cike da mamaki Barr Nas yace kamar ya?
Kwashe komai tayi tasanar da su akan mutuwar Amminta nan duk jikinsu yayi sanyi sukayi ma iyayen nata addu'a.
Mom ce tarungumota jikinta tana lallashinta dakyar aka samu tayi shuru sannan Dad yace Jawahir kikwantar da hankalinki mu zamu zauna da ke zamu kula da ke duk abinda kikeso zamuyi maki kid'aukemu a matsayin iyayenki.
'Dago kai tayi takalleshi tayi murmushi tace nagode sosai Dad da wannan karamcin da kukayi min saidai ina so inkoma wajen dangin mahaifiyata zan je incigaba da rayuwata da su tunda suna raye, bazan iya cigaba da zama cikin garin nan ba.
Haba Jawahir mu ma fa zamu zauna da ke tsakani ga Allah bazamu ta'ba cutar da ke ba,,, cewar Faruk
Girgiza kai tayi tace a'a Faruk su ma suna buk'atata na sani kawai dai halin Abba ne yasa suka daina zuwa garin nan, na san ku d'in mutanen kirki ne saidai zamana a nan bazai yuwu ba.
Dad yace shikenan Jawahir mun fahimceki ammah kibari kikwana biyu a nan sannan kitafi.
Kallon agogo tayi tace a yau nakeson tafiya.
Faruk ne yayi saurin cewa a'a ba yau ba please kid'an mana kwana biyu kamar yadda Dad yace.
Shuru tayi batace komai ba.
Sallamar mutane da suka jiyo ne yasa gabad'aya suka tashi suka fita suka bar Mom da Jawahir a nan Mom tana k'ara lallashinta.
Mutane ne dayawa sukayo gungu guda sukazo tayasu murnar dawowar Faruk, a setting room d'in Dad suka zauna.
Nan da nan gida yafara cika har mata suka dinga zuwa, Jawahir tashi tayi takoma part d'in Mom tana zuwa takwanta nan da nan tafara baccin gajiya.
A ranar gidan Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan akaje aka tattara duk dukiyoyinsu da duk abinda suka mallaka hatta gidajensu.
Su Nasiba ba k'aramin tashin hankali suka shiga ba sunyi kuka sosai dan gidan da suke ciki ma amsheshi akayi akace za'a maida ma jawahir abunta dan haka suka koma wani madaidaicin gida na mahaifiyarta, yayyenta biyu masu aure saida sukazo suka ci kukansu har suka gode ma Allah, a gidajen sada labarai aka dinga yayata abinda yafaru hatta gidajen talabijin saida aka dinga nuna su Alhaji Sufyan ana fad'in abinda sukayi wannan abun ya yi ma iyalansu ciwo sosai.
A ranar aka had'a duk abinda suka mallaka aka fidda ma jawahir hak'ik'k'inta sauran dukiyar kuma aka damk'ata ga iyalansu.
Da dare aka kira Faruk aka sanar da shi dan washe gari yaje da jawahir adamk'a mata dukiyarta ya amsa da toh.
Mom nan nan take ta yi da Jawahir ammah ita ko ta k'i sakewa da ita magana ma sai tadaina yi masu dan tunda tatashi daga bacci tacanza koda Faruk yaga yanayinta yace subarta kawai wannan ba ita bace dan haka aka k'yaleta ita kad'ai tak'unshe kanta a d'akin Mom, abinci ma akayi akayi da ita taci ammah tak'i yadda aka ajiye mata haka akazo aka d'auka.
Ganin haka yasa Faruk yafara tunanin yadda zaiyi yarabata da Aljanar nan.
Washe gari koda suka tashi nemanta akayi aka rasa a cikin gidan nan hankalinsu yatashi sosai dan ba'a san lokacin da tabar gidan ba, wajen k'arfe goma Malam Nasir (Kakan Faruk) ya iso garin nan yasamesu suna shirin fita nemanta yace sudawo suzauna, bayan sun zauna an gaisa ne yakalli Alhaji Sani yace Faruk ya shaida min komai ta waya wannan dalilin ne yasa nazo dan intaimaka ma yarinyar na san saboda haka ne yasa tabar gidan dan tabbas aljanarta zata san komai akai, jiya ban samu naruntsa ba ina ta aiki akan yadda zan tunkareta kuma Alhamdulillah ina tunanin zamuyi nasara.
Su dukansu amsawa sukayi da masha Allah, Allah Ubangiji dai yasa adace, Dad yace ammah Malam ba a nan gizo yake sak'a ba ai ba'a san inda yarinyar take ba yanzu.
Jim Malam yayi sai chan yace tana da sauran dangi a garin nan?
Faruk yace a'a.
Tunani yafara yi sai chan yace toh gidansu fa akwai wani a ciki?
Nan ma Faruk yace a'a.
Jin haka yasa Malam yace tabbas babu inda zataje sai gidansu a chan ne kad'ai aljanar zata kaita tunda babu kowa a gidan, kallon Faruk yayi yace yi sauri katashi muje chan gidan nasu, kad'auko min wacchan ledar da nazo da ita.
Cikin sauri suka tashi suka fita a cikin motar Faruk suka shiga har da Dad suka tafi aka bar Mom a gida.
Gudu Faruk yadinga yi da motar har suka isa gidan suna zuwa suka tarar da gate d'in a bud'e dan haka a gaban gidan sukayi parking d'in motarsu suka fito Faruk yace nan ne gidan mushiga, har ya wuce zai shiga malam yayi saurin rik'oshi yace a'a kar kushiga kujira, nan suka ja suka tsaya, addu'a yayi sannan yace sushiga suna shiga filin gidan itacene suke ta kad'awa ga ganyaye a k'asa duk sun bushe, su dukansu bakinsu d'auke da addu'a suka nufi hanyar da zata sadaka da cikin gidan suna shiga tsakar gidan wata irin k'ara sukaji me had'e da iska, nan suka ja suka tsaya kallon d'akunan sukayi sukaga kowane rufe yake, dariya ce sukaji ta fara tashi a d'aya daga cikin d'akunan dan haka cikin sauri suka nufi d'akin kafin su isa k'ofar d'akin ta bud'e kanta sai duhu sukaga ya bayyana a ciki, malam ne yace masu kowa yacigaba da addu'a kar yadaina dan haka suka nufi d'akin, Faruk wayarshi yad'auko yakunna touch sannan suka shiga, a k'arshen bango suka ganta tsaye bisa iska k'afafuwanta sun nannad'e gashin kan nan ya mik'e tsaye ga bakin nan na jirkice, idanuwanta k'ara fitowa sukayi waje k'wayar kamar ba zaune take a cikin idanun ba, gabad'aya halittarta ta canza, kallonta suka tsaya suna yi cike da mamaki, Faruk ne yayi k'arfin halin cewa Jawahir ya akayi kikazo nan?
Wata irin murya sukaji me kama da gurnanin zaki ana cewa taya zan zauna bayan kunaso kurabani da rayuwata bazan ta'ba barin duk wanda yaso yarabani da duniyarnan ba.
Malam nuni yayi ma Faruk alamun yayi shuru sannan shi yace ya zama dole kirabu da yarinyar nan kidaina wahalar da ita hakanan.
Bushewa tayi da dariya tare da matsowa bisa iska har lokacin bata safka k'asa ba tace hakan ba zai ta'ba yuwuwa ba babu wanda zai rabani da d'iyata ko wanene yaso haka sai na ga bayanshi.
Malam na jin haka ya amshi ledar da take hannun Faruk yabud'e yad'auko wata roba k'arama wadda take d'auke da wani ruwa a ciki, sannan yad'auko wata leda me d'auke da wani farin abu kamar gari, bud'e ledar yayi yad'ebo farin abun yayi bismillah yawatsa mata, wata irin k'ara tasaki sai gata ta fad'o tim k'asa, hasken d'akin ya dawo.
cikin sauri yabud'e robar yawatsa mata ruwan, nan tasake sakin wata k'ara me k'arfi wadda tasa saida suka toshe kunnuwansu saboda kar k'arar ta lahanta masu dodon kunne, cikin k'araji tace kar kakuskura kasake watsa min ruwan nan banaso kadaina, wanene kai????
Malam kallonsu Faruk da Dad yayi yace kuje kurik'e man ita, su duka suka nufi wajen da take kafin su isa hannu tad'aga tanunasu sai gasu kamar anyi wurgi da su su biyun sun fad'a chan gefe.
Ganin haka yasa malam yafara karanta ayoyin Allah dak'arfi sannan yafara zagaye d'akin yana d'ibar ruwan yana watsawa nan tadinga ihu tare da yunk'urin ja da baya, Faruk ne yafara mik'ewa dakyar yanufi inda take malam wurgo mashi garin maganin yayi yace yawatsa mata a saman kanta nan ya amsa ya watsa mata tasake sakin wata k'arar sannan tasulale k'asa asume, ganin haka yasa malam yai saurin isa wajenta yace ma Faruk yabud'e mashi bakinta, nan yafara k'ok'arin bud'ewa dak'yar yasamu yabud'e mata nan Malam yazuba mata ruwan maganin a ciki, yagoga mata na garin a fuska, bud'e idanunta tayi tare da k'wala k'ara tature Faruk da ke rik'e da ita nan tabank'are jikinta tare da bud'e bakinta gabad'aya nan wani irin farin hayak'i ne yadinga fita daga bakin, idanuwanta duk sukayo waje, hayak'in yana gama fita kallonsu tayi d'aya bayan d'aya sai kuma tamaida idanunta tarufe tadaina ko da motsi.
Faruk yace Malam me yafaru da ita bata motsi ko ta suma?
Malam da yake kallonta girgiza kai yayi sannan yakalli su Faruk yace ba suma tayi ba tana raye bazata ta'ba tashiba har sai anyi abu d'aya.
Cikin rashin fahimtar maganarshi sukace bamu ganeba Malam
Jinjina kai yayi yace tabbas layar da aka sa ma gawar ne a kusa da iccen suri aljannun da suke cikin iccen ne suka tado fatalwarta kuma tana rayuwa ne a cikin hak'ark'arin jawahir wannan dalilin ne yasa take amfani da jikinta da ruhinta, sannan wannan fitar da tayi zata iya dawowa nan da 'yan awanni kad'an idan har ba'ayi saurin zuwa k'abarinta aka tono wannan layar ba dan a yanzu haka layar tana nan cikin k'abarin da antone aka k'one shikenan fatalwar zata koma bazata sake bayyanaba.
Saurin mik'ewa Faruk yayi yace ni zan je intone k'abarin kujirani bari inje ind'auko megadinsu yarakani mak'abartar.
Malam yace toh kutafi da ashana da kun tono ku k'oneta kar kubaro wajen baku k'onetaba Faruk ya amsa da toh nan yawuce cikin sauri yatafi.....
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in