Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
kai Mummy ni yaushe rabon da inyada waya anfi shekara biyu.
Daddy ne yamik'a mata wayarshi yace amsa rabu da ita shalele anfad'a mata da da yanzu d'aya ne bataga da bambanci ba.
Amsa Nasiba tayi tana dariya tace Allah Daddy ita Mummy da abu ya wuce sai tadinga tuno ma mutum
Kibarta Shalele na ma kusan canza maki sabuwar waya.
Mummy murmushi tayi tace oho dai na baku zuwa gobe ai sai anji ku indai Nasiba ce.
Fakar idanun iyayenta tayi tashiga cikin contact d'in Daddy tad'auki number d'in Alhaji Mansur sannan tamik'a ma mahaifin nata wayarshi.
Zama tayi na kusan mintuna biyar sanna tayi masu sallama tatashi takoma part d'inta cike da farin ciki, saida tahau saman gado sannan talalubo number d'in Faruk.
A chan 'bangaren Faruk bayan ya gama shirin shi na bacci yana kwance saman gadonshi yana tunanin abar k'aunarshi yana jin wani irin dad'i a ranshi akan had'uwarshi da ita, shi kanshi ya san yana son Nasiba sosai ya yi k'ok'ari sosai da har ya iya danne son nata a yau bai nuna mata ya yi missing d'inta ba, murmushi ne yasu'buce mashi lokacin da yatuno yadda suke nuna ma juna soyayya kafin wannan abun yafaru, lumshe idanunshi yayi ahankali sannan yace Nasiba kina raina a kowane lokaci, yadda kike missing d'ina nima haka nake naki, ina fata akwai lokacin da komai zai zo k'arshe muyi aure.....yana cikin haka wayarshi tafara ringing tashi yayi zaune tare da d'aukota saman bedside ganin Nasiba ce yasa yai murmushi tare da yin picking, daga chan 'bangaren tayi mashi sallama ya amsa nan kuma duk sukayi shuru sai chan kuma takauda shurun ta hanyar cewa ina fata ka koma gida lafiya?
Lafiya lau Nasiba.
Wani irin haushi taji ganin a yanzu wai Faruk ne yake kiranta da sunanta ko dai ya daina sonta ne? Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata cikin sanyin murya tace am daman na kira ne infad'a maka na samo number d'in.
Kai masha Allah na ji dad'i sosai Baby ina fata dai baki bari Daddy yagane ba?
'Dan guntun murmushi tayi cikin ranta tace wai kuma Baby dan na samo mashi abinda yake so, sai kuma chan tace uhm uhm bai gane ba.
Toh shikenan kituro min kinji?
Shuru tayi batace mashi komai ba, sake maimaita mata yayi nan ma shuru.
Ajiyar zuciya yasafke yace Nasiba kiyi hak'uri duk yadda kikeji nima kaina ina ji ba wai na daina sonki bane wallahi ina k'aunarki sosai saidai banda wani za'bi da zan iya hak'ura da case d'innan bayan alk'awali nayi akanshi kuma kema kinsan girman alk'awali.
Fashewa tayi da kuka tace ammah Faruk ka san ina sonka shine karabu da ni..
Katseta yayi yace kidaina cewa haka Nasiba wallahi ko d'aya ban rabu da ke akan son raina ba kuma har yanzu ina nan akan bakana zan dawo gareki a duk lokacin da muka gama shara'ar nan kikwantar da hankalinki kin ji ko?
Rage sautin kukanta tayi tace shikenan Faruk ina nan ina jiranka dan Allah kar kabarni.
Murmushi yayi yace kar kidamu da sannu zan baki mamaki dan banaso aja lokacin bikkin mu, nidai fatana kidaure kicire duk wata damuwa a ranki kikwantar da hankalinki sannan kidaina kirana a waya kar parents d'inki sugane har yanzu muna tare ransu ya'bace kibari mubi komai a sannu Nasiba.
Cikin jin dad'in kalamanshi tace toh shikenan Hearty duk yadda kakeso haka za'ayi.
Lumshe idanunshi yayi tare da sakin murmushi sannan chan k'asan mak'oshinshi yace kece rayuwata zan kasance da ke akowane lokaci acikin zuciyata, kikwanta kiyi bacci.
Ita kanta lumshe idanunta tayi tana fitar da murmushi me sauti "Nagode sosai Hearty hak'ik'a nayi farin ciki da jin kalmar nan a yau zanyi baccin da rabon da inyi irinshi tun muna tare shikenan sai dasafe.
Sallama sukayi suka kashe wayar kusan a tare suka manna wayoyinsu a bisa k'irjinsu suna murmushin farin ciki, kowa na jin soyayyar d'an uwanshi tana fizgarshi.
Chan Faruk yaji shigowar text yad'aga wayar yana dubawa sai ganin number d'in Alhaji Mansur yayi ta turo mashi.
Murmushin jin dad'i yayi cikin ranshi yace kin gama min komai My Life, nan yatura mata " Thanks my wife to be insha Allah, Good Nyt, kiyi bacci me dad'i.
A karo na biyu tasake lumshe idanunta cikin jin dad'i tace Night too My Everlasting,,, tana manne da wayar a k'irjinta a haka tayi bacci.
Achan 'bangaren Faruk tashi yayi yagama duk abinda zaiyi sannan yakoma yakwanta.
Washe gari yana zaune a parlorn d'akinshi yana kallon kwallo inda a saman d'an teburin da yake gaban kujerar da yake zaune fruit salad ne yana sha, sai wajen k'arfe sha d'aya yagama kallon yamik'e yad'auko wayarshi da yajona charge yakoma inda yake zaune kasancewar ranar bazaije wajen aiki ba, Number d'in Alhaji Mansur yalalubo yakira, har saida takusan tsinkewa sannan akayi picking, sallama yayi daga chan 'bangaren Alhaji mansur ya amsa a dak'ile tare da tambayar wanene.
Faruk bai damu da yanayin da ya amsa shi ba yace am Barr Faruk ne daman na kira ne intambayeka dan Allah in ba damuwa ina zan sameka dan akwai magana me muhimmanci da zamuyi.
Tun kan yarufe baki yaji muryar Alhaji Mansur cikin fad'a yana cewa babu wata magana me muhimmanci indai ba janyewa kayiba kabari aka kashe yarinyar chan kamar yadda takashe wasu.
Murmushi Faruk yayi dan yanayin yadda yayi maganar ta so tabashi dariya ammah yadanne sannan yace koma menene kaban dama muhad'u sai mutattauna.
Toh shikenan zan turo maka adress d'in Guest House d'ina sai kazo kasameni.
Cikin jin dad'i Barr Faruk yace toh shikenan sai na jika,,, bai jira jin abinda zai ce ba yakashe wayar tare da saving d'in recording d'in da yayi,
gudar wayarshi yad'auko yakunna muryar da yake tunani ta Alhaji Mansur ce yasake saurare tabbas ya ida gasgatarwa da tashin ce, yana nan zaune sai ga message ya shigo wayarshi yana dubawa yaga Alhaji Mansur ne, murmushi yayi yace dakyau haka nakeso nan yamik'e yashige bedroom d'inshi bai dad'eba yafito hannunshi rik'e da key d'in motarshi fuskarnan ya dad'eta da bak'in glass d'aukar wayoyinshi yayi yafita yabar gidan.
Yana isa k'ofar gate d'in gidan duk security's suka taso suka nufo wajen motarshi ganin haka yasa yagane bazasu barshi yashiga ba nan suka fara tambayarshi me yazo yi? batare da ya basu amsaba yad'auko wayarshi yakira Alhaji Mansur yana yin picking yace gani a k'ofar gidanka wad'annan k'attin da katara sun hanani shigowa.
Ba su da akace ma k'atti ba hatta shi kanshi Alhaji Mansur ya ji ciwon abun dan de kawai yana so yasan abinda yakawoshi saisa yadanne fushinshi yace basu waya muyi magana.
Mik'ama d'aya daga cikinsu wayar yayi yace oganku yana son magana da ku.
Amsa yayi yakanga a kunne nan sukaji yana cewa ohk sir angama, mik'a ma Barr Faruk wayar yayi sannan yabada umurni aka hangame mashi tank'amemen gate d'in yashigar da motarshi parking yayi yafito nan d'aya daga cikinsu yayi mashi jagora zuwa cikin gidan, Faruk ko kanshi d'aurewa yayi ganin makeken Guest House d'in Alhaji Mansur ahaka har suka isa wani tank'amemen parlor inda Alhaji Mansur d'in yake zaune ya kame sai hura hanci yake.
Sucurity d'in komawa yayi inda Barr Faruk yayi sallama yashiga, amsawar ma cikin tak'ama aka yi mashi, murmushi kawai Faruk yayi yaje yazauna saman kujerar da take opp d'in wadda Alhaji Mansur yake zaune cikin tak'ama yazauna tare da d'aura k'afa d'aya saman d'aya, koda Alhaji Mansur yakalleshi saida yaga ya yi mashi k'warjini, zare glass d'in da yake fuskarshi yayi sannan yace sannu Alhaji.
Cikin isa ya amsa da yauwa ka ce kana son ganina ko?
Murmushi yayi yace Eh saboda inaso ka amsa min wasu tarin tambayoyi da ke gareni.
Da mamaki yake kallonshi yace wane irin tambayoyine haka?
Ta'be baki yayi yace ba wasu tambaboyi bane masu wuya kawai dai akan case d'in mutuwar su Alhaji Muhammad Mai kud'i ne.
Gaban Alhaji Mansur wani irin mummunan fad'uwa yayi yai saurin gyara zaman shi tare da kallon Faruk yace ban fahimceka ba me kake nufi?
Murmushi yayi yace daman bazaka fahimceni ba saidai yanayin yadda kafirgita ya sa na gane ka d'an fahimci wani abu, ammah dai kar kadamu da wannan na san dai Alhaji Muhammad abokinka ne kai da su Alhaji Tanimu toh abin mamakin bayan mutuwarshi kuka koma kuka k'ulla abota da yayanshi Alhaji Mu'azu, saidai hakan baisa kuyi tunanin ko za'a iya zarginku da wani abu ba? Ko ma ace akwai wani abu da kuka shirya ku d'in?
Zumbur Alhaji Mansur yamik'e tsaye cikin fushi yace ban ganeba me kake nufi, wannan ai zancen banza ne ka zo ne daman dan karaina min hankali?
Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace kaga Alhaji da ka zauna munyi magana cikin kwanciyar hankali ba sai an jiyo abinda muke tattaunawa ba.
'Daga murya yayi yace kowa yajiyo man ina ruwana, watau ni kake zargi ko kenan?
Shima mik'ewar yayi yace ni ba zarginka nakeba tambayoyi suka kawoni wajenka kuma ya kamata ka amsa min su, shin ya labarin kud'ad'e, gidaje, filayen marigayi Alhaji Muhammad da suke hannunku ko kun ajiyesu ne sai d'iyarshi ta fito daga gidan kaso sannan kumallaka su a wajenta tunda kawunta wanda kuke tayawa ajiyewa ya rasu?
Alhaji Mansur mutuwar tsaye yayi yana kallon Faruk da tsantsan mamaki jin kalaman da suka fito bakinshi bayan babu wanda yasan wannan sirrin sai su kad'ai toh ina yaji hakan?
Yana cikin tunanin yaji muryar Faruk ya cigaba da cewa sannan takardun kamfanin yarinyar chan ya kamata ace kun damk'a mata abunta, filayen da gomnati tasiya ma a wajenku ko tana da alak'a da su?
A fusace cikin d'aga murya yace ya isheka haka Barrister! ya isa!!! Watau ni zakazo kaci ma mutunci dan kawai mahaifin Nasiba ya hanaka auren d'iyarshi ni zaka ja ma sharri? Toh wallahi ya zama dole indamk'a ka a hannun hukuma dan bazan lamunci hakan ba da girmana a gari kanemi kazubar min da shi, duka dukiyar muhammad nawa take da har zamu so mucita kaduba girman Guest house d'ina wanda ko rabin girman gidana bai kai ba shin wannan bai isa yazama shaidaba akan cewa na fishi dukiya? Bazan barkaba dole kotu tashiga ciki,,, wayarshi yad'auko yana shirin lalubo number.
Murmushi Barr Faruk yayi yace kiran wayar da zakayi daidai yake da tona ma kanka asiri, shin zaka iya tuna wata mota sabuwa fil da Alhaji Muhammad yasiya wadda kaci burin kamallaketa Wadda cikin motocinka babu kamar ta? Ko zaka iya tuna wayar da kukayi da Alhaji Mu'azu akan son mallakar dukiyar jawahir da take cikin account d'in mahaifinta?..
Wayar da take hannunshi ce tasu'buce tafad'i nan yafara zufa 'yan cikinshi saida suka kad'a, wuta tad'auke mashi d'if saida yayi kusan minti biyar suna kallon kallo da Barr Faruk sannan yayi k'ok'arin saita kanshi sannan cikin inda-inda yace ina kaji wannan? wanene yafad'a maka hakan?
Tsayawa Barr Faruk yayi yana kallonshi ganin haka yasa Alhaji Mansur yanufoshi a harzuk'e yana cewa tambayarka nake kabani amsa!
Ja yayi da baya yace ka ga kar kamatso min nan ni tambayarka nayi kuma amsa nakeso.
Idanuwan Alhaji Mansur jajir sukayi saboda 'bacin rai cikin fushi yanuna mashi hanya yace fitar min daga gida tun kan insa afitar da kai ta k'arfi, wannan cin fuska ya yi yawa ace katako har cikin gidana kaci min fuska, kai wanene a garin nan da har zakayi min haka?
Ta'be baki yayi cikin nuna rashin damuwa yace na ji zan fita kuma ni ba kowa bane saidai inaso kasani na san abubuwa da dama agame da duk abinda kuka aikata, sannan kashirya zan k'ara dawowa gareka dan neman amsar wad'annan tambayoyin kai har ma da wasu na daban, murmushin gefen baki yayi sannan yace na barka lafiya,,, yana fad'in haka yajuya yafita.
Alhaji Mansur tsaye yayi yakasa ta'buka komai mamaki duk ya gama cikashi nan kuma yafara zagaye d'akin yaje yadawo haka yaitayi cikin ranshi yana tunanin wanene yasanar da Barrister duk wannan to kodai yarinyar chan ce? Toh ammah ita kanta batasan abinda duk muka shiryaba, saidai ya kamata inyi wani abu a nan, komawa yayi yazauna yad'auko wayarshi yalalubo wata number bata dad'e tana ringing ba akayi picking ko sallama bai tsaya yi ba yace Alhaji da matsala.
Daga chan 'bangaren akace matsala kuma? Wace iri kenan?
"Lauyan wannan yarinyar ya zo ya sameni ya tisani a gaba yana min wasu tambayoyin da suka nemi surikita min k'walwa wanda bansan amsoshinsu ba ammah ba ma wannan ba tambayar a nan itace duk ina yasan wad'annan abubuwan?
Daga chan 'bangaren dariya aka fara kyalkyatawa har saida Alhaji Mansur yafusata ganin dariyar batada niyar k'arewa yasa yace watau kai dariya ma kakeyi ko?
Dole inyi dariya Alhaji Mansur wannan abun bai kamata yad'aga maka hankaliba.
Ajiyar zuciya yasafke yace hakane ammah ya zama dole inyi wani abu akan yaron nan kafin yanemi tozartani koda na san hakan ba zai ta'ba yuwuwa ba ammah dole inga bayanshi, ya kamata muhad'u da kai zuwa anjima domin musan ta inda zamu 'bullo mashi.
Toh shikenan babu damuwa zan shigo.
Kashe wayar yayi tare da mik'ewa yana cigaba da zagaye d'akin still dai wayarshi tana a hannunshi, ya dad'e a tsaye yana kaiwa da kawowa daga k'arshe yatsaya waje guda tare da duba wayarshi yakira wata number ana yin picking batare da ya yi sallama ba yace Barrister ina son muhad'u da kai yanzun nan kazo gidana kasameni.
Ohk ba damuwa sai ka zo ina nan ina jiranka.
Yana gama wayar komawa yayi yazauna tare da cije le'be yana jinjina kai yace tabbas ya zama dole inyi maganinka Barrister ba ma kai ba duk wanda yace zai shiga rayuwata sai naga bayanshi dan haka muje zuwa.
Bayan ya bar gidan Alhaji Mansur direct gidan kaso yawuce yana isa yasamu jawahir zaune jingine da bango ta d'age kanta sama tana kallon rufin d'akin inda hawaye suka fara wanke mata fuska, daga gefenta yatsaya yana mata kallon mamaki.
Ahankali tajuyo takalleshi tare da goge hawayen fuskarta sannan tasadda kanta k'asa tace Barrister ina jin tsoro dan Allah kazare hannunka daga cikin wannan case d'in kar wani abu yasamu rayuwarka.
Jikinshi sanyi yayi nan yatsugunna gabanta yace jawahir meyasa kikace haka? Kikwantar da hankalinki babu abinda zai faru zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin na fitar da ke a cikin gidan kason nan ke yakamata kibani k'warin gwiwa domin wannan shine zama na k'arshe da za'ayi ya kamata mucigaba da addu'a insha Allahu mune da nasara.
Girgiza kai tayi tace baka fahimceni ba Barrister.
Na fahimceki man indai akan su Alhaji Mansur ne kicire duk wata damuwa a ranki daidai nake da su sannan basu isa suyi abinda ubangiji baiyi ba.
Cikin sanyin jiki tace hakane.
Toh kikwantar da hankalinki kinga daga nan ma wajen DPO nakeson wucewa dan yasanar da ni asibitin da aka kwantar da matar Alhaji Mu'azu dan haka koma mekenan zan sanar da ke kikwantar da hankalinki komai zai zo cikin sauk'i.
'Daga kai kawai tayi alamun toh.
Nan yayi mata sallama yatashi yatafi.
Yana isa station number d'in DPO yakira yasanar da shi zuwanshi nan yabada izini da ashigo da shi office d'inshi.
Faruk yana shiga yasameshi yana waya dan haka yaja kujera yazauna har saida yagama sannan yamik'a mashi hannu suka gaisa.
Bayan sun gaisa ne DPO yace ina saurarenka me ke tafe da kai?
Murmushi yayi sannan yace ba komai bane yake tafe da ni sai akan dai case d'in jawahir kamar yadda a binciken da nakeyi nagano cewa matar Alhaji Mu'azu tana nan a raye ana jinyarta a wani asibiti shine nakeso asanar da ni asibitin dan inason ganawa da it.
Da mamaki DPO yake kallonshi dan ya san in ba shi da su Alhaji Mansur ba babu wanda yasan tana asibiti, Faruk kamar ya san abinda yake tunani yace baidace ace kun 'boye ma kotu tana raye ba domin duk a cikin k'undin case d'in jawahir da naduba banga inda aka fad'i matarshi tana raye ko ta mutu ba.
Jikin DPO sanyi yayi yace tabbas tana raye kuma wannan ba laifina bane polices d'in da suka bada sheda ne basu rubuta ba ammah shikenan zan sanar da kai asibitin saidai ko ka je babu abinda zaka samu daga wajenta dan har yanzu batasan inda kanta yake ba.
Jinjina kai Barr Faruk yayi yace babu damuwa.
Nan DPO yasanar da shi.
Sallama yayi mashi yatafi shi kanshi cikin ranshi ya yi mamakin yadda yau DPO bai mashi rainin wayo ba haka yashiga motarshi yawuce private hospital d'in, yana isa baisha wahalar gane room d'in da takeba dan haka yawuce, yana shiga yasameta a kwance tsaye yayi yana kallonta tana kwance bata ko motsi, wata dattijuwa ce tajuyo takalleshi tace sannu da zuwa.
Murmushi yayi sannan yayi sallama tare da ida shiga d'akin.
Bayan ta amsa gaisawa sukayi yatambayeta ya me jiki?
Cikin sanyin jiki tace toh Alhamdulillah za'a ce.
Kallonshi yamaida ga Ummah da akasa ma drip idanuwanta a rufe kamar me bacci yace bacci ma takeyi ko?
Uhm wane bacci yaro ko ma idanonta biyu ba'a ganewa dan har yanzu kusan shekara d'aya kenan babu uhm bare uhm uhm saidai kallon mutane kawai da take.
Mamaki ne yakama Barr Faruk yace Allah yasauk'e Allah yabata lafiya ko zan iya sanin Doctor d'in da yake dubata.
Goge hawayen da suka zubo mata tayi tace Eh Dr Aminu ne.
Ohk Allah yabada lafiya.
___________
Washe gari da marece yanufi gidan su Nasiba yana isa megadi yasanar da shi bata nan murmushi yayi sannan yace toh babu damuwa Alhaji fa?
Eh toh Alhaji yana ciki.
Toh ko zan iya ganinshi?
Wani yaron gidan ne megadi yatura yace yaje yace ana sallama da Alhaji, sannan yabud'e ma Barr Faruk gate yashiga da motarshi yana yin parking yafito yajingina a jikin motar sai ga yaron ya fito ya ce ance wai wa ke nemanshi?
Kace mashi Faruk ne.
Toh yace nan yakoma yashaida mashi.
Barr Faruk ya yi kusan mintuna goma a wajen tsaye kafin Alhaji Sufyan yafito.
Fuska a murtuk'e yanufo wajen da Faruk yake tun kan ya ida isowa yace lafiya me yakawo ka gidana? Ko ka zone kashaida min ka janye daga case d'in.
'Dan rissinawa Faruk yayi yagaisheshi a maimakon ya amsa sai ma k'ara jefo mashi tambaya yayi yace ina fata ba'a kan aurenku da d'iyata kazoba ko, dan bazan ta'ba amincewa ba har sai ka janye k'udurinka.
'Dagowa Faruk yayi yakalleshi sannan yace ko d'aya Alhaji ba wannan