Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
min da hawayenki My Jawa kinga yau ranar murna ce agaremu kicire kowace damuwa acikin ranki kinga and'aura aure yanzu andamk'a min amanarki insha Allahu zan baki duk wata kulawa da tadace dan zan nuna maki ni d'in me k'aunarki ne zan mantar da ke duk wata damuwa da kike cikinta dan Allah Jawahir kisama min gurbi acikin zuciyarki ko yayane.
Runtse idanunta tayi nan hawaye suka fara gangaro mata tana jin maganganunshi har cikin kwanyar kanta.
Jin ta yi shuru yasa yace shikenan Jawahir bari inbarki kar incika ki da surutu ni zan nema ma kaina matsugunni a cikin zuciyarki da sannu zan koya maki sona, kihuta lafiya.
Tana ji ya kashe wayar janye wayarta tayi tad'aura saman k'irjinta batare da ta bud'e idanunta ba nan hawaye suka cigaba da fita.
Tana cikin haka Inna Mairo tashigo tasameta a gefenta tazauna tafara lallashinta har tasamu tayi shuru sannan tad'auko wani tsumi tabata tace ga wannan kisha
Wani irin haushi Jawahir taji dan har ta fara gajiya da abubuwan da Inna Mairo take d'irka mata babu yadda ta iya ta amshi tsumin tafara sha jinshi tayi da dad'i ba kamar sauran ba dan haka tad'age kai tashanye shi tas.
Nan inna tabata wata gumba ta amsa tafara ci wani irin gard'i taji ba kamar ta jiyaba wannan tafi dad'i dan kwakwa da zuma ne a jikinta haka tacita sosai.
Wajen k'arfe ukku aka had'a mata ruwan wanka tayi bayan ta gama aka shiryata cikin lace me tsada saida sukayi sallar la'asar sannan su Baba Malam suka shigo haka aka fito da amare aka kaisu d'akinshi yayi masu nasiha sosai.
Nan sukaita kuka.
Su Khausar aka d'auka a motoci aka tafi da su gidajen mazajensu inda Jawahir kuma sai k'arfe biyar sannan aka rakata filin jirgi ita da mijinta da abokanshi suka shiga jirgin.
Dakyar aka 'bam'bareta daga jikin Inna Mairo da zasu tafi.
Tunda suka shiga jirgin tahad'e kanta da gwiwa tadinga rusa kuka.
Duk yadda Faruk yaso yalallasheta kasawa yayi dan kuka tadinga yi sosai.
Suna isa Katsina suka tarar da motoci biyu su Aunty Kilima k'anwar Malam sunzo tararsu nan Aunty Kilima da wata k'awar Mom suka shiga mota d'aya da amarya inda gudar motar da driver yazo da ita su Faruk da Barr Nas suka shigeta.
Jawahir tana k'udundune cikin gyale har lokacin hawaye take ahaka suka isa gidan iyayen Faruk, d'akin Mom aka wuce da ita ganin har lokacin da sauran mutane a gidan.
Aunty kilima ce tazauna da ita a d'akin saboda kunya Jawahir takasa bud'e lullu'bin haka su Mom suka shigo suka gaisa suka sake mata nasiha bayan sallar isha'i aka tattarata aka kaita gidan mijinta Aunty Kilima da Hajiya Maimuna k'awar Mom ne kad'ai suka kaita direct part d'in Nasiba suka wuce da ita lokacin gidan ba kowa sai ita kad'ai tana ganinsu cikin sauri tazo tataresu tarungume Jawahir da ke lullu'be tana mata sannu da zuwa.
Su Hajiya Kilima sunji dad'in yadda Nasiba tanuna kulawa nan suka zaunar da su suka yi masu nasiha daga nan aka wuce da Jawahir part d'inta da yasha gyara sosai.
A saman gado suka zaunar da ita suka sake mata nasiha sannan sukai mata bankwana suka tafi.
Saida taji ba motsin kowa sannan tayaye mayafinta tana bin d'akin da kallo.
Wajen k'arfe tara Faruk yadawo gidan Nasiba ce tatareshi tarakashi part d'inshi yayi wanka yashirya ledojin da yashigo da su guda biyu tad'auki guda tace mashi suje.
Da mamaki yake kallonta yace ina zamuje?
Murmushi tayi tace wajen amarya man.
Cikin wasa yaharareta yace kamar irin kin gaji da ni kike nema kibada ni.
Dariya tayi tace eh d'in na ji bakomai nidai muje malam inrakaka dan bacci nakeji.
Haka suka fito tare sukaje part d'in Jawahir a parlor Nasiba tazauna yashiga ciki yasameta zaune dan tunda taji shigowarsu tamaida lullu'binta daga gefenta yazauna yana murmushi yace amarya ta ango kinsha k'amshi.
Shuru tayi nan yakai hannu zai yaye lullu'bin tayi saurin fad'awa jikinshi
Murmushi yayi a karo na biyu tare da rungumeta yace hanani ganin kyakkyawar fuskar za'ayi? Ko sai na siya?.
Shuru tayi nan yajanyeta tare da mik'ewa yace bakomai zan siya yanzu muje ga Nasiba chan a parlor tana jiranmu.
Mik'ewa tayi tabi bayanshi ta cikin gyalenta me shara shara take ganin hanya har suka fito parlor inda Nasiba take, a kujerar da take zaune yazauna inda Jawahir tazauna a 1 seater nan yayi masu nasiha.
Nasiba yafara tambaya ko tana da abinda zatace saidai tayi murmushi tace babu saidai abu guda shine yayi adalci atsakaninsu yarik'esu amana.
Murmushi Faruk yayi yace insha Allahu zanyi bakin k'ok'arina wajen ganin na yi adalci, kallon Jawahir yayi yace kefa akwai abinda zakice?
Girgiza kai tayi alamun a'a.
Nan yayi masu addu'ar zaman lafiya.
Mik'ewa Nasiba tayi tace toh Amarya da Ango sai ince mukwana lafiya.
Kallonta Faruk yayi yace Hearty tun yanzun?
Murmushi tayi tace wallahi na gaji sosai ga bacci ina ji.
Mik'ewa yayi yace toh bari inrakaki.
Saurin wucewa tayi gaba tana cewa a'a kabarshi nagode amaryarmu ga amanar miji nan na damk'a maki mukwana lafiya.
Tana fita taja masu k'ofa cikin sauri takoma part d'inta tana shiga tafashe da kuka tare da fad'awa saman gado wani irin kishine tadinga ji ganin yau mijinta ne zai kwana da wata ba itaba, kuka tadinga yi sosai kamar k'irjinta zai fito duk yadda taso tayi controlling d'in kukanta kasawa tayi saida tayi me isarta, har wajen k'arfe d'aya tana kwance zugum zuciyarta tadinga ayyana mata wasu abubuwa akan Faruk da Jawahir daga k'arshe takori shaid'an tamik'e taje tad'auro alwallah, sallah tayi raka'a biyu sannan tazauna karatun alk'ur'ani dan ji tayi kwatakwata bata ma jin baccin.
Sai wajen k'arfe ukku sannan tasamu taruntsa.
A chan 'bangaren su Faruk bayan fitar Nasiba komawa yayi gefen Jawahir yazauna tare da yaye mata malullu'binta saurin sadda kanta tayi k'asa.
Idanu yazuba mata yana k'are mata kallo duk sai taji ta tsargu nan gabanta yafara fad'uwa.
Saida yayi kusan minti biyar yana kallonta sannan yasa taje tad'auro alwallah sukayi sallah a nan parlor bayan sun gama ne yakama kanta yayi mata addu'a sannan yad'akko masu ledar da Nasiba ta ajiye masu dakanshi yatashi yaje kitchen yad'akko plate da cups.
Kaza yafara bata da fari ta k'i amsa saida yafara lalla'bata sannan tayarda taci cike da jin kunya take amsa, saida yatabbatar ta k'oshi sannan shima yafara cin nashi.
Mik'ewa jawahir tayi tashige bedroom d'inta toilet tafad'a tawanke hannu da bakinta sannan tazo tahaye gadonta ko kaya bata cireba gabanta yana dukan ukku ukku ita abun har mamaki yake bata ganin wannan ba shine aurenta na farko ba ammah duk tsoro ya kamata.
Tana nan kwance Faruk yashigo hawa yayi saman gadon tare da kallonta ganin yadda take wuk'i wuk'i da idanu yace Rabin ran ya kamata kicire kayan nan bazakiji dad'in bacci da su ba.
Cikin rawar murya tace a'a zan iya.
Murmushi yayi yace toh ai ni zasu takura man ammah bakomai tunda kince haka bari inrage maki su dakaina
Saurin tashi tayi zaune cike da tsoro tace bari inje incanza dakaina.
Rik'ota yayi yamatsa gab da ita nan yazuba mata manyan idanunshi saurin sadda kanta tayi k'asa tare da cewa bari inje incire....bata rufe bakiba taji hannunshi a bayanta yana neman yazage mata zip d'in riga saurin d'ago kai tayi takalleshi wanda hakan ya yi daidai da zage Zip d'in da yayi.
Tureshi tanemi tayi saima yarungumeta jikinshi tare da zame mata doguwar rigar nan hannunshi yafara yawo acikin jikinta.
Yadda gabanta yake fad'uwa Faruk yana ji dan har lokacin tana manne a jikinshi, cike da tsoro tace dan Allah Yaya Faruk kadaina.
Cikin kunnenta yarad'a mata Habibti yau fa ranar farin ciki ce agaremu dan Allah kibarni inyi.
Runtse idanunta tayi jin ya kirata da sunan da Umar yake kiranta da shi, jin ta yi shuru yasa yakwantar da ita ahankali nan yazuba mata idanu yana k'are mata kallo, ahankali tabud'e idanunta takalleshi ganin yadda yatsareta da mayun idanunshi sai a lokacin yakashe masu fitila.
Jawahir koda take ba sabuwar shiga ba ammah ta gurzu a hannun Faruk dan har kuka saida tayi saboda wahalar da tasha, Faruk ko za'a iya cewa fita yayi hayyacinshi, saida yasamu nutsuwa sannan yabarta.
'Daukarta yayi sukayi wanka tare sannan suka dawo suka kwanta yana manne da ita a jikinshi.
Washe gari bayan sunyi sallar asuba komawa sukayi bacci ba sune suka tashi ba sai wajen k'arfe tara da rabi, Faruk nema yayi suyi wanka tare da Jawahir tak'i dan kasa had'a idanu tayi da shi saboda kunya daga k'arshe yad'auketa yashiga da ita toilet tana ta nuk'u nuk'u da jiki yashareta yawanketa tas sannan shima yayi wanka.
Bayan sun fito ne suka shirya sannan yajata suka nufi babban parlor.
Suna zuwa suka samu Nasiba zaune ta sha gayu tana jira sufito.
Tana ganinsu murmushi tasaki tare da tashi cikin sauri tanufi inda suke tana zuwa tarik'e Jawahir da kanta yake sadde k'asa tace amarya sannunku da fitowa.
Maimakon ta amsa saima duk'awa da tayi tagaisheta amsawa tayi tare da rik'o hannunta tamik'e tace ina fata dai kina lafiya.
'Daga Kai tayi cike da jin kunya.
Kallon Faruk tayi da yake ta faman murmushi nan itama tayi murmushi sannan tagaisheshi, jawota yayi yarungume ahankali cikin kunnenta yarad'a mata kin mance irin gaisuwar da kikeyi min?.
Murmushi tayi itama ahankali tace yanzu ai bamu kad'ai bane Lovely dole mucanza,,, tana fad'in haka tazare jikinta tare da rik'o hannun Jawahir gudan hannun tarik'o nashi tace muje kuyi breakfast kar mubar amarya da yunwa.
Dining suka wuce tayi serving d'in kowa nan suka fara ci Jawahir ba wani ci take sosai ba Faruk yana lura da ita ji yake kamar yayi mata d'ure dan de kawai Nasiba da ke wajen.
Nasiba tana gama ci tatashi takoma d'akinta dan tabasu waje Faruk ko kamar jira yake nan yafara feeding d'in Jawahir saida yatabbatar ta k'oshi sannan yabarta.
Waya aka kirashi dan haka tatashi takoma part d'inta tagyara abunta sannan tazauna takira su Baba Malam a waya suka gaisa.
Tana cikin wayar Faruk yashigo daga gefenta yazauna har saida tagama sannan ya amshi wayar ya ajiye yace habibty shine kika gudo kika barni ko?
Murmushi tayi tace ba gudowa nayi ba.
Rungumeta yayi sannan yace toh me kikayi?.
Shuru tayi nan yasafke ajiyar zuciya sannan yace dan Allah Habibty ataimaka a ajiye kunyar nan dan ina buk'atar kulawarki sosai.
'Dagowa tayi takalleshi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa ganin haka yasa yakwantar da ita sannan shima yakwanta gefenta yadinga janta da hira tana d'an biye mashi.
Wajen azuhur sukayi wanka sannan yatafi masallaci ita kuma tayi sallarta a gida bayan ya dawo Nasiba tazo takirata sukayi lunch.
Da marece yafita dan haka suka samu damar zama ita da Nasiba suka sha hira sosai dayake Nasiba akwaita da son mutane nan da nan tasa Jawahir tasake da dare tare suka shiga kitchen sukayi girki duk yadda taso Jawahir tabarshi ammah tak'i saida takama mata sukayi.
Tun daga ranar tare suke girki breakfast ne kawai bata samun damar fitowa suhad'a tare saboda Faruk baya bari ahaka har suka cinye kwana ukkunsu a ranar da zai koma wajen Nasiba nan tace ta k'ara masu sucike sati guda dan a lokacin bata jin dad'in jikinta kawai dai bata nuna masu ba dan kar sutada hankalinsu, koda Faruk ya ji dad'in hakan ammah bai nuna mataba, a fili yanuna bai yarda ba saida tadinga lalla'bashi sannan ya amince yakoma suka ida sati gudansu yakoma hannun uwargidanshi inda yanuna ya yi missing d'inta sosai, ta ji dad'in ganin yadda yanuna mata ya yi missing d'inta.
*****
Zaman lafiya sukeyi sosai idan kaga Nasiba da Jawahir baka ta'ba cewa kishiyoyine dan suna k'aunar junansu suna mutunta juna, Faruk ko ya zage wajen kula da matanshi ko da sau d'aya baya yarda a fuska yanuna ga wadda yafi so saidai idan ya ke'be da matanshi ne yake nuna masu yadda yake k'aunarsu nan kowace hankalinta yakwanta ganin ta ciri tuta a wajen mijinta
*BAYAN WATA 'DAYA*
Kasancewar lokacin Hajji ne daman tuni ya biya masu batare da saninsu ba nan yad'auki matanshi sukaje aikin hajji.
Tunda sukaje Nasiba batada cikakkar lafiya ahaka tayi hajjinta saidai jawahir take kula da ita da mijinsu.
Sai da suka gama hajji sunje umrah sannan taga likita a chan ne yake sanar da su tana da shigar ciki na wata biyu nan su Faruk da Jawahir sukaita murna.
Bayan sun dawo ne suka cigaba da kula da ita dan Jawahir bata bari ko cokali tad'auke inda a 'bangaren goga Faruk ma haka duk motsin da zatayi sai sun tambayeta abinda yake damunta hatta abinci sai ta fad'i irin wanda za'a dafa.
Tana jin dad'in irin kulawar da suke bata da cikinta.
Watansu d'aya da dawowa suka shirya suka je kebbi lokacin cikin Nasiba yana wata ukku kwanansu biyu suka dawo gida.
Jawahir kanta ta samu nutsuwa sosai dan har k'iba ta yi koda su Baba Malam suka ga yadda take cikin kwanciyar hankali sai hankalinsu yakwanta, sunje gidan Khausar dan ita Rashida ta dawo gida saboda laulayin da takeyi.
Ranar wata litinin Jawahir tashigo parlor tasamu Nasiba zaune tana cin yalo gefenta Faruk ne zaune, zuwa tayi tazauna tana cewa Auntyna me kuma ake ci?
Murmushi Nasiba tayi tace kinganni nan wallahi yalo naji inaso shine oga yasiyo min.
'Daukar guda tayi tace bari inci wannan dan gaskiya ya biya raina.
Dariya Nasiba tayi tatura mata robar yalon tace kici iya cinki sister ni har ya fara isata tun d'azu nake ci.
Murmushi Jawahir tayi nan tace nagode Auntyna sannan tafara ci, kallon Faruk tayi tace Lovely (dayake itama sunan da take kiranshi da shi kenan) maimakon kasiyo har da d'ata ?
Murmushi shima yayi yace toh ai bakice asiyo makiba habibty Auntyn taki yalo kawai tace asiyo.
Ajiye yalon tayi tace ni d'ata nakeso Allah ban iya cin yalon.
Faruk kallon Nasiba yayi itama takalleshi sukai murmushi sannan tace 'yar k'anwata ko dai kin kamu ne kema?
Turo baki tayi tace ban kamu da komai ba Aunty kawai dai d'ata nakeso.
Murmushi Faruk yayi yace toh shikenan bari insa asamo maki ai duk zan iya da ku nan yad'akko wayarshi yakira megadi yafad'a mashi.
Mik'ewa tayi taje kitchen tad'aura masu girki daurewa kawai take dan kwana biyun nan itama ba isassar lafiya gareta ba......
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:22 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 27*
Cikin Nasiba yana da wata hud'u lokacin aka fiddo da su Alhaji Sufyan daga gidan yari za'a ratayesu dan a lokacin shekararsu guda cif a gidan kaso, duk sunyi bak'i sun rame, a mota aka kaisu gidajensu dan suyi bankwana da iyalansu, Mummyn Nasiba a waya takirata dan taje ammah tace babu inda zata batason sake sakashi a cikin idanunta, nan tazauna tadinga kuka, Jawahir ganin yadda Nasiba take kuka yasa duk sai jikinta yayi sanyi duk'awa tayi gabanta tana hawaye tace dan Allah Aunty Nasiba kiyi hak'uri nasan ni najamaki da badan haka ba da duk haka bata faruba dan Allah kiyafe min.
'Dago kai Nasiba tayi takalleta cikin kuka tace wallahi ba laifinki bane Jawahir bakida laifin komai a ciki *SON ZUCIYA* ne da kwad'ayi suka ja ma Daddy ina nadamar kasancewarshi mahaifi agareni yanzu gashinan abinda yaja ma kanshi, ba wai ina kuka akan abinda za'ayi mashi bane kawai dai ina kuka akan mutuncinmu da yazubar mana yanzu shikenan kowa zai dinga kallonmu da abinda mahaifinmu ya aikata na tabbata yau dai ta kasance *RANAR NADAMA* agareshi ranar da bai ta'ba tunanin zata zo mashi ba saidai nadamar bazata ta'ba kasancewa mai amfani agareshi ba.
Jawahir ma fashewa tayi da kuka nan aka rasa me rarrashin wani saida sukayi me isarsu sannan sukayi shuru dan lokacin Faruk baya gida.
Su Alhaji Sufyan da Alhaji Mansur bayan ankaisu sunyi bankwana da iyalansu nan aka wuce da su wajen da za'a ratayesu su dukansu kuka suke sha'be sha'be kamar k'ananun yara, d'aura su akayi saman wani dogon gini aka rufe masu fuska sannan aka sa igiya aka rataye masu kai sasu akayi sukayi kalmar shahada sannan aka saki igiyar sukayo k'aya, ji kake k'yat alamun karyewar wuya nan sukaita wuntsila wuntsila da k'afafu har saida ransu yarabu da jikinsu.
________
Jawahir tunda tatashi yau dakyar tayi sallar asuba nan saman darduma tayi kwance dan ranar Faruk ba a d'akinta yakeba, wajen k'arfe shidda yashigo yasameta kwance ta k'udundune tana ta kwasar bacci wajen da take yanufo yana cewa Habibiti ba dai har yanzu bacci kike ba, ta'bata yayi yaji jikinta da zafi.
Rud'ewa yayi yace subhanallahi ba dai bakida lafiya ba.
Maganarshi ce tatasheta daga baccin da take nan tabud'e idanu dak'yar k'amshin turarenshi ne yadoki hancinta tayi saurin tureshi tamik'e tashiga toilet tafara kwarara amai.
Hankalin Faruk ya tashi sosai ganin yadda take amai kamar zata amaye 'yan hanjin cikinta gabad'aya ta galabaita tana gama aman taimaka mata yayi tai wanka tashirya sannan yafito da ita yace ma Nasiba zasuje asibiti Jawahir bata da lafiya hankalin Nasiba ya tashi sosai tace saidai suje tare.
Haka ko akayi atare sukaje wajen family doctor d'insu da yace susameshi a asibiti nan yadubata yaimata tambayoyi tabashi amsa sannan yarubuta mata tests yace taje ayi mata a lab.
Bayan sunyo sun kawo sakamako nan yake tabbatar masu da tana d'auke da ciki tsawon wata ukku, murna wajen Faruk da Nasiba ba'a magana dan ita ko uwar gayyar kunya ce takamata.
Haka suka dawo gida suna ta murna Faruk ko baki har kunne yana ta godiya ga ubangiji ganin matanshi dukansu ciki garesu Nasiba nata wata hud'u Jawahir kuma wata ukku.
Zuwa yayi yasanar da su Mom su ma sukaita murna nan tasamo masu wata mata tazo gidan tazauna tana masu girki da gyaran gida.
'Dakunansu da na mijinsune kawai basu bari agyara masu su suke abunsu.
Faruk ko indai yana gida toh yana manne da matanshi yana basu kulawa sosai duk abinda sukeso sai ya samo masu shi, kusan tare suke rainon cikin da shi.
Dan ma Jawahir nata ba mai laulayi bane sosai saisa take samun damar yin wasu ayyukan indai bai gida tare da ita ake girkin abinci.
Faruk d'aukarsu yayi yakaisu gidan Ummah