Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 74

99K to 102K   out of 220.3K words

banason kud'inki ni zanyi maki komai da aljihuna domin ko bakomai akwai amana tsakanina da mahaifinki.
Duk da haka Dad na fi so ayi da dukiyar nan domin hankalina zaifi kwanciya,.
Katseta Dad yayi yace dangin mahaifiyarki suna buk'atar wani abu daga gareki.
Dad zan basu zan raba dukiyar ukku inbasu kashi guda sauran sai ayi amfani da ita.

A'a jawahir tunda dai kin nace zan amshi kashi d'aya kibasu d'aya, sauran kuma kiyi amfani da ita.
Ganin bataso tacigaba da yi mashi gardama amatsinyishi na babba yasa ta amince da hakan.

Kallonta tamaida ga Faruk da yake jiran jin abinda zatace akan files d'in da tabashi, murmushi tayi tace wannan kuma kaza'bi gida d'aya da fili guda duk na mallaka maka sannan Dad yad'auki mota guda Mom kuma abata fili d'aya, na san kunfi k'arfin hakan ammah nima na baku ne saboda Allah dan ni kaina na san banda abinda zan iya biyanku da shi saidai addu'a

Su duka sukace a'a bazasu d'auki komai ba tayi amfani da abunta duk yadda taso sud'auka ammah suka k'i dan haka tafitar da gida da mota tace zata mallaka su ga Ummah dan ko bakomai uwace gareta.
Nan suka amince da hakan indai har ita zata ba babu matsala saboda ta cancanta saboda matsayinta.

Bayan sun gama tattaunawane take sanar da su gobe takeso tawuce Kebbi nan suka nuna basu yarda ba, nacewa tayi da hakan saboda garin ji take duk ya gundureta komai ji take babu dad'i tunda tafito daga gidan yarin ba dan komai ba sai dan rashin wani makusancinta a cikin garin, wannan dalilin ne yasa tanace.
daga k'arshe dai suka amince ba dan sun so ba sukace Allah yakaimu, sai kowa yakasance cikin shiri gobe sai muje Kebbi ammah ta flight zamu bi, inyaso sai insa driver yatafi da motar da kikeso atafin maki da ita chan, kai kuma Faruk a yau kaje kayi mana booking d'in jirgi.
Toh Dad insha Allahu.
Jawahir godiya tayi masu sosai har da k'wallarta nan Mom talallasheta sukace tadaina kuka.



Da marece tare da Mom suka shiga kitchen tatayata girkin dare, Mom jin son yarinyar take a cikin ranta ji take ina ma ace d'iyarta ce dan a rayuwarta tana son 'ya'ya mata saidai ubangiji bai bataba sai d'a d'aya tilo.


Wajen k'arfe tara Jawahir tana kwance a chan part d'in mummy kallon agogo tayi nan tamik'e tad'auko hijab d'inta tasaka tafito a main parlor, tana safkowa tasamu Faruk zaune yana dannar waya, Murmushi tayi tataka ta isa wajen da yake tayi sallama.

Sai a lokacin yalura da ita nan ya amsa yace daman bakiyi bacci ba?
Zama tayi tace Eh na kasa baccin ne.
Idanu yazuba mata yace meyasa kika kasa?
ina tunani sai zuwa anjima,,, tabashi amsa.

Ajiyar zuciya yasafke yace ammah Jawahir bazaki hak'ura da tafiyar nan ba sai zuwa jibi, kinga gobe na so kije kiga filayenki da gidajen sannan gidanku ya kamata afitar da duk kayan da suke ciki.

Duk'ar da kanta tayi k'asa tace ba damuwa Yaya Umar kai zaka iya.....saurin d'ago kai tayi tace am yi hak'uri wlh na saba cewa yaya umar ne.
Murmushi yayi yace ba damuwa nima ai Umar d'inne ko kin mance?
Murmushin itama tayi tace kaima yayanane ammah saidai ince Yaya Faruk.
A karo na biyu yayi murmushi yace nagode sosai jawahir da wannan matsayin da kika bani daman kinga ban da kowa ni kad'ai ne wajen iyayena sai 'ya'yan k'anwar iyayena.
Jawahir tace Allah sarki, ashe bakasan dad'in k'anneba.
Tarar numfashinta yayi yace au ke kin sani ashe?
Dariya tayi har saida hak'oranta suka bayyana tace ina fa nasani, ni dai gobe zan tafi Kebbi.
Hmmm kedai kin k'agara kitafi kamar wani abu muke maki to wai ma kin san inda suke zaune?

Eh Man a cikin garin Fanah a lantarki, ko da ba lallaine ingane gidan ba ammah gidan ba wani me wuyar ganewa bane da ance gidan Malam me salati duk an sanshi acikin lantarki.
Toh shikenan goben sai muje ammah naso kije kigano gidajen, ko zaki shirya tun da wuri mufara zuwa.
Girgiza kai tayi tace a'a Yaya Faruk bazan iyaba ni fa duk sun fita raina banason ganin gidajen da filayen,
K'wallar da yaga sun cika mata idanu ne yasa yace shikenan Jawahir ya kikeso ayi maki da su a aje maki har sai ranar da kikazo katsina?.
Shuru tayi sai chan tace cikin gidajen aba Ummah guda sannan duk kayan da suke cikin gidanmu na mallaka mata su tasa akwashe sannan abata mota guda sai kuma kud'i zan turo a account wanda za'a basu na maganinta.

Faruk jinjina ma jawahir yayi sosai irin tausayinta da son taimako tabbas ba kowa ne zai iya irin haka ba, yace toh shikenan jawahir zanyi duk yadda kikeso.

Nan yafiddo wayarshi yace bari kiga wani abu, gidaje ne guda hud'u da filaye ukku sai motoci ukku duk yagwada mata taduba tace wad'annan fa?.
Kallonta yayi yace d'azu naje nagano su shine nad'auko maki su hoto dan na san wannam zumud'in na son zuwa kebbi bazai barki kije ganosuba kuma sai gashi hakan.

Dariya tayi tace kai dai ko Barrister.
Idanu yazuba mata yace nidai me?
Girgiza kai tayi tace bakomai sannan takalli agogo tace bari inje inkwanta dare ya yi fa.
Faruk yace toh shikenan sai Allah ya kaimu nima yanzu zanje inkwanta.
Har ta juya zata tafi yace am baki ji ba.
Juyowa tayi tace na'am.
Murmushi yayi yace kije kawai ba komai.
Itama murmushin tayi tajuya takoma part d'in Mom cike da farin cikin gobe zata je Kebbi.....







_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 23*

Washe gari tun da safe suka tashi suka fara shirin tafiya dan jirgin k'arfe goma zasu bi, tun wajen k'arfe tara driver yakama hanyar kebbi da mota inda aka zuba duk wata tsaraba da akwatin kayan jawahir da aka saka wanda bata san da shi ba, dan mamaki ma taba Faruk sam bata yi tunanin tatanadi kayan sawa ba.


Wajen k'arfe goma saura Barr Nas yakaisu airport, goma daidai tana yi jirginsu yad'aga zuwa KEBBI STATE tunda suka baro gida jawahir shuru tayi duk kuma sai taji wani iri sai a lokacin tayi tunanin shin ko har yanzu dangin mahaifiyartata suna a nan cikin garin Kebbi, gabanta saida yafad'i tace Allah yasa dai suna nan.
Suna safka suka samu mota suka yi shata suka kama hanyar FANAH jawahir dai titi kawai take kallo yanayin garin yana burgeta dan zata iya tunawa tun tana k'arama rabonta da garin a lokacin da Amminta taci burin k'ara zuwa da ita a lokacin tarasu, saurin goge jawayen da suka gangaro mata tayi Faruk ne kawai yalura da su ammah bai ce komai.


Sun d'an d'auki lokaci suna tafiya har suka isa garin a lantarki wani dattijo suka tambaya gidan Malam me salati dan ita bazata iya ganewaba saboda da jimawa rabonta da garin nan yayi masu kwatance me mota ya ida isa da su har k'ofar gidan suka biyashi kud'inshi suka fita.


Wani gida ne babba wanda da kagani ka san family house ne, daga gaban gidan akwai icce a k'ark'ashin iccen wani tsoho ne da wasu manya biyu zaune hannun tsohon rik'e da carbi yana masu magana, ganinshi yasa Jawahir taganeshi tace tabbas wanchan ne kakana na ganeshi, cikin sauri tanufi wajen da yake tace Baba Malam, daga shi har mutanen d'ago kai sukayi suka kalleta lokaci guda sukace Jawahir yau kece a garin namu?
Jikin tsohon tafad'a tare da fashewa da kuka tace Baba Malam meyasa kukayi min haka kuka daina sona.
Su dukansu jikinsu yayi sanyi dan basuda bakin magana, tsohon ne yayi k'arfin halin cewa bamu daina sonki ba jawahir muna k'aunarki wallahi ba laifinmu ba.
'Dagowa tayi cikin muryar kuka tace koma menene Baba malam baidace laifin wasu yashafeni ba ku duka dangin mahaifiyata kun yadani babu me k'aunata sai wad'anchan, tanuna su Faruk da suke tsaye.


Juyawa su duka sukayi suka kalli su Faruk sukace bismillah sannunku da zuwa.
Amsawa sukayi da yauwa nan suka zo zasu zauna d'aya daga cikin mutanen ne yace a'a kuzo mushiga gida ya za'ayi mubarku waje bismillah mushiga ciki.


Gabad'aya suka mik'e suka nufi cikin gidan inda suka nufi 'bangaren Baba Malam dan gidan irin family house d'innan ne suna shiga da sallama wata 'yar dattijuya tafito daga cikin wani d'aki tana gyara zane, Baba Malam ne yace Mairo kawo mana tabarma muna da manyan bak'i yau.
Cikin fara'a tace masha Allah marhabanbikum bak'inmu muna maku barka da zuwa, amsawa sukayi da yauwa.

Babbar tabarma tad'auko tashimfid'a nan duk suka zauna suka fara gaisawa tsohuwar ce tazuba ma Jawahir idanu tace oh ni Mairo wannan d'iya kamar 'yar wajen khausar.

Baba Malam yace itace man baki ganeta ba.

Saurin rik'o jawahir tayi tace oh ni 'yar nan kece? Ashe kina nan shine baki ko lek'o mu ko dan mahaifiyarki ai ya kamata kidinga zuwa wajenmu.

Jawahir kallonta tayi cikin muryar kuka tace ku ne dai baku nemana dan kunga iyayena basu raye.

Baba Malam ne yace a'a jawahir ba haka bane kiyi hak'uri wallahi bamuda laifi a ciki d'an uwan babanki ne bayaso muna zuwa gidanku ga su Musa nan kitambayesu kiji irin wulak'ancin da yake mana idan munje, ko bayan rasuwar mahaifiyarki saida mukaso yabamu ke mudawo da ke hannunmu ammah yak'i yaci mana mutunci yace kar yasake ganinmu gidanshi idan har ba zuciyar kare garemuba, Musa ko ba haka yace mana ba?

Wanda aka kira da Musa ne yace tabbas hakane Baba ni kaina raina ya 'baci da cin mutuncin da yayi mana ko bakomai khausar 'yar uwarmu ce baidace yahanamu zuwa ganin d'iyartaba

Dad ne yace gaskiya bai kyauta ba cin mutunci baida dad'i, ba adalci bane ace ya rabata da danginta ba.
Gyad'a kai Baba Malam yayi yace kaima dai ka fad'a bawan Allah raina ya 'baci sosai a duniyar nan yara hud'u namallaka ukku maza sai khausar ita kad'ai ce mace dole hankalina yatashi domin ita kad'ai ce talula wani gari tayi aure na san batada matsala da mijinta dan mutumin kirki ne saidai d'an uwanshi, wallahi tun bayan rasuwarta ban ta'ba kwana ba tare da na tuna jawahir a raina ba dan ina tausaya mata halin da zata shiga a hannun wannan mutumin.

Dad jinjina kai yayi yace gaskiya ne ai Alhaji Mu'azu baida kirki, kallon jawahir yayi da take ta kuka yace Jawahir kinji dai abinda sukace ya kamata kiyi masu uzuri, tunda basuda laifi a ciki.

Kallon Dad tayi tace hakane Dad na san duk Abba ne yaja min, babu komai na yafe.

Su duka sun nuna farin cikinsu nan Baba Malam yatambayeta ina su Abba ya akayi yabarta tazo,
Shuru tayi nan yayi murmushi cike da talaici yace wallahi Alhaji Mu'azu baida kirki wai har yayi maki aure batare da ya fad'a manaba saboda bai d'aukemu da darajaba saidai muji labari a wajen wasu, nuna Faruk yayi yace wannan ne mijin naki?

Girgiza kai tayi tace a'a ba shi bane.
Toh wanene? Baba Musa yajefo mata tambayar.
Shuru tayi tarasa abinda zata ce masu ganin haka yasa Faruk yace Jawahir ya kamata kisanar da su komai.
Fashewa tayi da kuka tace ban san abinda zan ce masu ba me zan fad'a masu? Infad'a masu duk na kashesu?

Su duka a zabure sukace kin kashesu kuma?
Faruk ne yace a'a Jawahir kidaina cewa haka.
Cikin kuka tace toh ai ko bance ba haka yake, Baba Malam bari insanar da ku komai, gyara zamanta tayi tare da k'ok'arin tsaida kukan da take sannan takwashe komai tafad'a masu tun daga mutuwar mahaifinta da mahaifiyarta har aurenta da Umar da kisan da suka dinga yi, hatta zamanta a gidan yari da taimakon da Faruk yayi mata babu abinda ta'boye masu.

Ba Baba Malam ba hatta 'yan uwan mahaifiyartata da kakarta saida suka yi kuka saboda tsananin tausayi, sukaita jimamin abun nan suka dinga yi ma su Faruk da iyayenshi godiya sukace bakomai.



Baba Musa yaje yasanar da iyalanshi bak'in da sukayi yace ashirya masu abinci inda shima Baba Bello ma haka sannan yakira k'anensu Baba Nura yasanar da shi zuwan d'iyar autarsu khausar nan da nan yabaro gona yazo gida.

Suna nan Driver ya iso garin ta waya akayi mashi kwatancen inda zaizo dan dama ya san garin sosai ahaka ya iso da motar.


Matan su Baba Musa da yaransu ne suka zo dan sugaisa da bak'i nan Baba Musa yagwada masu Jawahir inda suma yagabatar da su a wajenta, mata biyu yanuna mata da yara bakwai yace matanshi ne da yaranshi akwai wasu yaran nashi biyar suna gidan mazajensu, sannan yanun wasu matan biyu da yara goma yace na maibi mashi ne Baba Bello, sannan mata d'aya da yara biyar yace na Baba Nura ne, nan sukaita farin cikin ganin 'yar uwartasu inda itama tanuna mafarin cikin ganin dangin mahaifiyartata.


Hira aka dinga yi tsakanin su Baba Malam da su Dad inda Faruk yabi Baba Nura suka shiga gari yana nuna mashi garin nasu.


Saida sukayi sallar azuhur nan suka zauna a babban tsakar gida aka baje tabarma abinci aka dinga shigowa da shi daga cikin gida had'ad'd'en dambu ne wanda yasha zogale da Tuwon dawa miyar ku'bewa d'anya gefe d'aya kuma Fura ce wadda tasha zuma sai kaji soyayyu da madarar shanu da aka dafa masu haka suka zauna suka kwashi girki abincin sosai yayi ma su Dad dad'i dan sun ci shi sosai.


Bayan sun gama ne wajen k'arfe ukku Dad yace ma Faruk ya kamata yaje yayi masu booking d'in jirgin da zasu koma, Baba Malam yace ina bazai yuwuba sukoma yau saidai sukwana suka nuna a'a dan gobe akwai aiki kan dole yahak'ura yabarsu, Baba Nura ne yaraka Faruk yaje yayi booking d"in jirgin k'arfe shiddan marece sannan suka dawo.

Wajen k'arfe biyar Faruk yana waje shi da Baba Nura suna hira nan Baba Nura yamik'e yace bari yad'an shiga gida yafito Faruk yace toh ba damuwa yana shiga nan Faruk yakira Jawahir a waya dan a lokaci tana cikin danginta suna ta nan nan da ita kamar sumaidata ciki, ganin Faruk ne yake kiranta yasa tayi saurin yin picking.
Yana ji ta d'aga yace kifito waje Jawahir akwai maganar da nakeso muyi.
Amsawa tayi da toh nan tamik'e tafito tasameshi shi kad'ai,
Faruk murmushi yayi yace watau anga dangi har anmance da mu.
Itama murmushin tayi tace a'a Barrister ni na isa inmance da ku bana ma fatan haka.
Ajiyar zuciya yasafke yace toh Allah yasa, kiran sunanta yayi ta amsa sannan yace na so ace kin amince kizauna da mu dan Mom zatayi farin ciki da hakan ammah kin k'i, duk da banga laifin hakan ba dan kema zakifi jin dad'in zama da danginki.

Cikin sanyin jiki tace hakane Barrister na za'bi zama da dangina ba wai dan bazan iya zama da ku ba kod'aya kun cancanci hakan saidai kawai sune kad'ai dangina da suka rage min a duniya zan zauna da su inyi alfahari da hakan ko da nasan da banbanci irin zaman da zanyi a nan da kuma wanda nayi a gidanmu nan gidan jama'a ne ni kuma ba mace bace da tasaba zama cikin mutane saidai a haka na san zan koyi wani darasin a cikin rayuwa.

Tausayinta ne yakamata Faruk yace hakane Jawahir na san ma zaki ji dad'in zamanki da su dan su d'in dangine na gari mutanen kirki, saidai kina da dukiya a katsina bansan yadda za'ayi da gidaje da filayenki ba.
Murmushi tayi tace kabar wannan a hannunka kawai.
Toh shikenan zan ajiye maki ammah a duk lokacin da kika samo yadda zakiyi da su sai kisanar da ni yauwa kinga ga motar nan ya kawo maki sannan kiduba akwai akwatin kayan sawa a ciki.
Da mamaki take kallonshi tace kayan sakawa kuma? Wa yabani bayan na san banda su?

Ni na had'a maki dan naga bakida su kuma baki nema ba, Jawahir idan kinason wani abu kidinga fad'a min, na ce maki kid'aukeni a matsayin yaya kamar yadda kika d'auki Umar ina neman wannan alfarmar a wajenki jawahir.

K'walla ce tacika mata idanu tace na d'aukeka tamkar Yaya Umar shin ka amince indinga kiranka da sunan Yaya Umar?
Murmushi Faruk yayi cike da farin ciki yace na amince jawahir, nagode da wannan matsayin da nasamu a wajenki.
Itama murmushin tayi tace nice da godiya akan karamcin da kuka nuna min.
A'a kidaina godiya domin kin fi k'arfin hakan,,, Suna nan a haka Baba Nura yadawo nan suka zauna suna hira.


Wajen k'arfe biyar da rabi su Dad suka fito nan duk mutanen gidan suka rakosu a cikin motar Baba Musa suka shiga aka kaisu Airport, jawahir kasa fitowa tayi suyi bankwana a d'akin Inna Mairo tazauna taci kukanta dan duk sai taji ba dad'i tafiyar da zasuyi daga k'arshe ko da Baba Nura yashigo yace tafito suyi bankwana da su Faruk cewa tayi ace tana masu Allah yakiyaye bayi zata shiga yanzu.

Haka yaje yafad'a masu sak'onta, Dad yace Jawahir ko dai kuka take dan na ga koda zamu fito kamar zatayi kuka.
Baba Nura yace nima naga tana kukan ammah ta shiga toilet yanzu.
Su dukansu duk sai sukaji babu dad'i haka suka shiga mota suka tafi.

Tsaraba nik'i nik'i aka had'a masu cikin ledar Viva guda biyu saboda tafiyar jirgi ce, k'arfe shidda daidai jirginsu yad'aga suka kama hanyar katsina.




Tunda suka dawo gida duk sai suka ji ba dad'i da ba jawahir dan d'an kwana biyun da tayi sun saba sosai kamar ta yi wata,

Bayan sallar isha'i duk takirasu tayi masu barka da safka tare da masu godiya akan taimakon da sukayi mata.

Zamanta a cikin danginta ya yi mata dad'i sosai dan suna nuna mata so saisa nan da nan tasake sukaita hira, yayyen mahaifiyarta kowa ya so tazauna a 'bangarenshi ammah Baba Malam yace a'a a wajensu zata zauna dan haka suka hak'ura suka barta wajen iyayen nasu.


*BAYAN KWANA BIYU*

Su Nasiba sun koma a gidansu da Jawahir tamaido masu inda suka cigaba da zama ita da mahaifiyartata koda ba dad'in zaman suke ji ba saboda rashin Alhaji Sufyan ko ma ace tashin hankalin abinda

34 / 74