Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   56 / 74

165K to 168K   out of 220.3K words

ne dalilin zuwana ba.
Toh menene dalilin zuwan naka?
Shuru Faruk yayi.
Nan Alhaji Sufyan ya ida harzuk'a yace ba tambayarka nake ba!.....








_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 14*

Ganin yadda yaharzuk'a yasa Faruk yayi murmushi yace kakwantar da hankalinka ba wai dalilin d'iyarka yasa nazoba na zone akan aikina.
Cikin nuna rashin fahimtar inda zancen yadosa yace ban fahimceka ba wane irin aikin kenan?

Juyawa yayi yakalli gefe d'aya sannan yace a matsayina na barrister ko ma ince akan case d'in jawahir na zone dan ind'an maka wasu tambayoyi wad'anda suka shige min duhu.

Wani irin kallo Alhaji Sufyan yayi mashi mai wuyar fassarawa koda Barr Faruk bai san ya yi ba saboda ba shi yake kallo ba, ida harzuk'a Alhaji Sufyan yayi yanuna kanshi yace ni ni zakazo kayi ma tambaboyin banza akan wacchan yarinyar? Miye had'ina da ita da har zakazo kace zaka tambayeni, inma kana yi ne saboda na hakana ka auren d'iyata toh bari kaji kayi duk abinda kaga dama ammah Nasiba ta fi k'arfinka dan haka kabar gidan nan yanzu tun kan insa'ba maka,,, yana fad'in haka yajuya a harzuk'e zai koma gida.
Sai a lokacin Faruk yajuyo yakalleshi yace shin me zaka iya cewa akan kisan da akayi ma Alhaji Muhammad Mai kud'i?
Chak Alhaji Sufyan yaja yatsaya batare da ya juyoba ganin haka yasa Faruk yacigaba da cewa sannan dukiyar yarinyar chan da take hannunku shin kun ajiye mata ne da sunan idan ta fito zaku mallaka mata ita? Sannan dukiyarta da kuka amsa hannun Alhaji Mu'azu da sunan zakuyi business shin ya maganar business d'in?

Jikin Alhaji Sufyan sanyi yayi yai saurin juyowa yakalleshi cikin 'bacin rai yace ban fahimceka ba kana nufin dukiyarta tana wajenmu ko kuma kana nufin muna da hannu a cikin mutuwar shi? Faruk kana da hankali kuwa?

Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace ba wai haka ba Alhaji kowa ya san kusancinku da Alhaji Muhammad sannan bayan mutuwarshi kuka koma abota da d'an uwanshi wanda yake da gurin ganin ya mallake dukiyarshi sannan sanin kanku ne Alhaji Muhammad ya bar duniya yana binku bashi kuma kun ci guri sosai akan wasu abubuwa nashi hatta.......katseshi yayi yace ya isa haka Faruk wannan tatsinniyoyin naka duk kasan wanda zakayi masu ba wai niba kowa ya san cewa Alhaji Muhammad abokin alk'alla ta ne ba wai abokina bane akan wane dalili zan so mallakar wani abu nashi bayan dukiya nima ina da ita tun daga tsarin gidana da matsayina ya kamata kafahimci hakan.

'Daga kai Faruk yayi yana kallon gidan sannan cikin nuna rashin damuwa yace ammah toh idan yakasance wannan gidan mallakinshi ne fa mezaka iya cewa?

Kai!!! Banason shashancin banza me kake nufi da maganarka gidan nawa ne mallakin wani? Inji wane mak'aryacin yafad'i haka? Fad'amin!

Girgiza kai Faruk yayi yace babu wani mak'aryaci da yafad'i hakan saidai ka sayi gidan a hannun Alhaji Mu'azu a kan farashi me sauk'i bayan kuma kun san gidan ba mallakinshi bane.

Tsawa yadaka mashi yace Faruk na gaji da jin wad'annan k'aryayyakin naka na banza wanda me hankali bazai ta'ba d'aukarsu ba tun muna mu biyu kafita kabar min gida!

Har Faruk ya bud'e baki zaiyi magana yayi saurin tarar numfashinshi cikin d'aga murya yace na ce kafita kabar min gida ko bakaji abinda nace ba!?

Ganin yadda yad'au zafi sosai yasa Faruk yace shikenan na ji zan tafi ammah.....
Kar kasaki kafad'i wani abu a wajen nan katafi nace!!!

Gyad'a kai yayi yajuya yabud'e motarshi yashiga yana jin Alhaji Sufyan yana ta fad'a haka yatada motar, yana fitar da motarshi daga gate d'in gidan Nasiba tana 'bullowa da tata motar wani irin dad'i taji a ranta dan ta d'auka wajenta yazo saidai abinda yabata mamaki ya ganta ammah yashare yayi tafiyarshi, duk sai taji babu dad'i cikin ranta tace ko lafiyarshi shi kuma? Girgiza kai tayi tashigar da motarta cikin gidan hango Daddynta tayi yana ta kaiwa da kawowa a wajen ranshi duk a 'bace, mamakine yacikata tayi saurin yin parking d'in motar tafito tanufi wajen mahaifin nata tana cewa Daddy lafiya? Me yafaru?

Juyowa yayi yai mata wani irin kallo cikin 'bacin rai sannan yajuya yashige gida.

Mutuwar tsaye Nasiba tayi tace ikon Allah me yafaru? Ko dai dan Faruk ya zo gidan ne yasa ranshi ya'baci kuma fa na ga shima Faruk ya tafi ranshi a 'bace toh me yafaru? Ajiyar zuciya tasafke sannan itama tabi bayan Daddynta tashiga cikin gidan a parlor tasameshi tsaye Hajiya Maijidda tana tambayarshi abinda yafaru.
Hucci kawai yake dan ranshi ba k'aramin 'baci yayi ba chan yajuyo yakalli Nasiba sannan yamaida kallonshi ga matarshi cikin d'aga murya yace wai ni ni Faruk zai zo yaci ma mutunci har cikin gidana.

Kusan a tare sukace cin mutun kuma?
Cize le'be yayi sannan yace eh man duka nawa yaron nan yake da har zai kalli tsabar idona yatuhumeni akan mutuwar Alhaji Muhammad har yana ik'irarin cewa wai muncinye ma d'iyar shi dukiya, gidan nan ma da nake ciki cewa yayi na yarinyar ne.
Nasiba a kid'ime tace Daddy, nan tasa hannu tatoshe bakinta tare da fashewa da kuka ahankali tace Faruk meyasa kayi haka.

Hajiya Maijidda cike da mamaki tace Faruk d'in yace haka Alhaji?
Toh in ba shiba wanene? murmushi yayi mai ciwo sannan yace duka yaron nan nawa yake wallahi da ace bani mutunci da mahaifinshi da yau yau d'innan sai na sa an d'aureshi a garin nan!

Baya baya Nasiba tafara ja sannan taruga dagudu tanufi d'akinta tare da fashewa da wani irin kuka me shiga rai tana shiga saman gadonta tafad'a tana me cigaba da kukan, wani irin haushin Faruk ne taji cikin ranta tace wai shine yaci mutuncin mahaifina daman ya san abinda zai aikata saisa yace insamo mashi number d'in Alhaji Mansur,, , kuka tacigaba da yi sosai.


Hajiya Maijidda kallon mijin nata tayi da ranshi yayi matuk'ar 'baci tace Alhaji baidace ka'bata ranka saboda wannan yaron ba ina tunanin ya yi hakane kawai dan ka hanashi auren d'iyarka ammah ko indai dan hakane baida mutunci.

K'wafa yayi yace kibarni Hajiya baisan wanene ni ba wallahi idan baibi a sannuba sai na sa and'aureshi a garin nan inga ubanda yatsaya mashi babu ruwana da mutuncin da muke da mahaifinshi tunda shi haka yake, ba barister ba ko alk'aline babu ruwana.
A'a Alhaji kayi hak'uri abi komai a sannu kawai dai kaje kayi ma mahaifinshi magana dan yagargad'i d'anshi yafita daga harkar ka idan har bai daina ba toh shine kake da damar yi mashi kowane irin hukunci.
Jinjina kai Alhaji Sufyan yayi yace kibarni da shi kawai Hajiya zai san da ni yake, je kid'auko min key d'in motata.
Amsawa tayi da toh, taje tad'auko mashi har tadawo yana nan tsaye inda yake mik'a mashi tayi ya amsa yawuce yafita cemashi tayi Allah yakiyaye ammah bai amsataba saboda yanayin da yake na 'bacin rai.

Rik'e baki tayi tace oh ni Maijidda wannan yaro ammah dai baida mutunci da ace mahaifinshi shima ba mai kud'i bane da nace bak'in ciki yake da dukiyarmu,,, tunowa tayi da Nasiba dan haka cikin sauri tanufi part d'inta tana isa tasameta a bedroom kwance sai faman rusar kuka take daga gefen gadon tazauna tare da kiran sunanta nan Nasiba tayi shuru.
Ganin haka yasa tace kindai ji abinda Faruk yayi ma mahaifinki yaron nan ashe baida mutunci bai gaji arzik'iba.
Tashi tayi zaune tare da tsaida kukanta tace wallahi Mummy da ace banga fitar Faruk daga gidan nan ba da bazan ta'ba yarda da cewa shine ya aikata ba yanzu dan rashin mutunci yakalli tsabar idanun mahaifina yafad'a mashi haka? Kenan soyayyar da yakeyi min duk ta k'aryace.
Ta'be baki tayi tace toh ai yanzu gashinan dai kin gani da idanunki.
Fashewa tayi da wani sabon kukan tace wallahi indai har Faruk ya yi min haka dan yatozarta mu toh yaje ya yi ma kanshi ni kuma zanyi k'ok'ari wajen ganin na cireshi a raina dan iyayena sun fiye min komai ba'ayi wanda zai zo yaci musu fuska har ransu ya'baci ba.

Jin kalaman da tayi yasa Mummynta tajawota jikinta kamar jira take tafad'a tare da rungume mahaifiyartata tana cigaba da rusa kuka.
Lallashinta Hajiya Maijidda tashiga yi dak'yar tasamu tashawo kanta har tahak'ura tadaina kukan.


________


A chan wani k'urmin daji dake wajen garin katsina tsakanin wasu k'auyuka biyu, dajin yana da duhu da yawan itatuwa sosai, iska kawai yake kad'awa a cikinshi baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye kawai babu mahalukin da yake shigarshi saboda ansan had'arin da ke cikinshi dan a tsakiyar dajin wasu 'yan fashi su biyar da suke rayuwa a cikinshi a duk lokacin da sukaso suna fita suyi fashi a gari ko kuma agayyacesu wani wajen suje suyi kisa saboda k'auran sunan da sukayi yasa mutane suke tsoron dajin.



'Yan fashin zaune suke suna zuk'ar shisha inda iskan da ke cikin dajin yake kad'asu, daga chan gaba da su kad'an ogansune zaune a bisa kujera hannunshi rik'e da k'walbar giya ya kame yana sha, su dukansu sun duk'ufa suna sharholiyarsu nan suka fara jiyo k'arar tafiya kamar ana tun karo wajen da suke, saurin ajiye shishir sukayi kowa yad'auko makaminshi yarik'e a hannu, inda ogansu yanuna ko inkula hankalinshi kwance yana ta shan giyarshi, suna nan a tsaye suna ta mazurai suna jira suga wane me k'arancin kwananne zai kawo kanshi, sun dad'e tsaye a haka sai ganin 'bullowar wata kyakkyawar budurwa sukayi basusan lokacin da suka saki baki suna kallonta ba, sanye take cikin wata gown wadda takama jikinta sosai inda gashin kanta yake baje a tsakiyar bayanta kyakkyawar fuskarnan tata ta sha makeup tafiya take ta jan hankali tatunkarosu tana masu murmushi me jan hankali su dukansu sun shagala suna kallonta har saida takusa isowa wajen da suke sannan sukayi saurin nunata da bindiga sukace kitsaya nan idan har kika matso zamu harbeki.
Cikin nuna rashin damuwa taja tatsaya tare da waigawa takallo ogansu da yake zaune har lokacin yana shan giya, fuskannan tata d'auke da murmushi tabud'e baki cikin siririyar murya me dad'in saurare tace idan ba damuwa inaso kubani dama inyi magana da oganku.
Juyawa sukayi suka kalli ogan suna shirin yin magana sai jin muryarshi sukayi ya ce kubarta ta iso muji da me tazo.
Saurin matsawa sukayi suka bata hanya tawuce tana karairaya duk suka bita da kallo suna lasar le'be, tana isa gabanshi taja tatsaya idanu yazuba mata yana kallonta daga sama har k'asa ganin haka yasa tajuya baya sannan tajuyo, ajiye kwalbar giyar yayi cikin muryar maye yace wacece ke? Me yake tafe da ke wajena?

Maimakon tabashi amsa sai fad'awa da tayi jikinshi tazauna tana cigaba da yi mashi murmushin nan nata me saurin rikita mutun.
Ganin haka yasa yabushe da dariya yace da alama wannan 'yar hannu ce tamuce.
Ganin haka yasa su ma suka bushe da dariya sannan suka koma suka zauna, hannu yakai yafara shafa gashin kanta yace gaskiya kina da kyau sosai,
Fari tayi mashi da idanu tace nagode.
Ajiyar zuciya yasafke yace lallai ke d'in ta dabance, hannunshi yad'aura bisa wuyanta tayi saurin janye wuyanta, gashinta yadamk'o dak'arfi yana shirin tura fuskarshi a wuyanta tureshi tayi da dukkan k'arfinta tamik'e tsaye tana jifanshi da wani mugun kallo.
Kyalkyacewa yayi da wata muguwar dariya yace tunda har kika kawo kanki ya zama dole kiyi abinda nakeso, hannu yakai zaya jawo ta tayi saurin yin baya tare da girgiza kai.
Gyatsa yayi sannan yajuya yakalli yaranshi da suke tsaye cirko cirko cikin muryar maye yace kukaimin ita cikin bukkata, su dukansu suka kwashe da dariya sukace angama oga ashe har muma yau zamu yagi rabonmu daman mun kwana biyu bamu samu namaba, juyawa tayi takallesu taga sun nufota gadan gadan nan tanuna su da hannunta sai ga wata irin iska ta tashi me kama da guguwa su dukansu saida suka tsorata sukayi saurin sa hannu suka rufe idanunsu dan kar ta shiga, bud'e baki tayi tasaki wata irin razanannar k'ara wadda tasa gabad'ayansu saida suka firgita suka juya zasu bar wajen sai ganin wani haske sukayi a gabansu dan haka suka had'e waje guda kowa yana raba idanu, ogansu kuma yunk'urin tashi yayi daga kujerar da yake zaune nan iska tajashi da k'arfi sai gashi a kusa da sauran 'yan uwanshi 'yan fashi,
Nuni tayi da hannunta a sama tafara karanto wasu irin d'alasimai sai ga wata k'atuwar macijiya ta bayyana a wajen su dukansu saida suka tsorata suka san yau sun gamu da gamonsu, bushewa tasakeyi da dariya nan tayi girgiza tazama wata k'atuwar dodanniya, murya suka fara jiyowa wadda tasa gabad'aya dajin yadinga amsawa ji sukayi ana cewa kuuuu azzalumai ban zo wajenku domin komai ba sai dan d'aukar *FANSAR RAI* zan kasheku kamar yadda kukaga bayana ku d'in azzalumai ne bazan ta'ba barinku ba.

Su dukansu tsaye suke sunaso suyi magana ammah tsoro ya hana babu wanda bai saki zawoba a wajen da suke tsaye, macijiyar ce sukaga tana tunkaro inda suke tsaye dukkansu yunk'urin guduwa sukayi ammah sai ji sukayi kasala ta safkar masu har macijiyar ta iso wajensu tana zuwa tasakar masu tsartuwa nan duk suka zube k'asa kowa yana jijjiga suna safke numfashi.

Ganin haka yasa tasake bushewa da wata razanannar dariya me kama da kukan hadari, sannan tanunasu da hannunta sai ga wasu k'ananun macizzai sun fito daga bakin wannan babbar macijiyar suna fitowa suka nufi wajen da mutanen nan suke kwance suna zuwa suka fara sarinsu, nan 'yanfashin suka fara ihu hayak'i yana fita daga jikinsu, sun dad'e a haka kafin daga bisani duk suka mace, saida tatabbatar da babu me motsi a cikinsu sannan lokaci guda ta'bace ita da macizzan.



***** *****
Barr Faruk tunda yabaro gidan Alhaji Sufyan cikin 'bacin rai ya isa gida saidai duk da haka baiyi nadamar hakan ba saboda akowane lokaci ashirye yake dan ganin ya tafiyar da aikinshi yadda yakamata, yana isa a k'ofar gate gidansu sai ganin motar Barr MB yayi anfaka ta, tsayar da motarshi yayi tare da fitowa yajingina a jikinta yana jira yaji da me yazo.
Ganin haka yasa Barr MB yafito yanufo wajen da Faruk yake tsaye yana murmushi yace ashe na zo a daidai yanzu nake shirin kiran wayarka sai gaka.
Shima murmushin yayi yace gaskiya ka taki sa'a.
Hannu Barr Mahamud Bello yamik'a mashi sukayi musabaha sannan yace ya aiki?
Murmushi yayi yace Alhamdulillah gashinan muna ta tayi.
Ajiyar zuciya yasafke yace hakane saidai nasan ka yi mamakin zuwana wajenka ko?
Ta'be baki Faruk yayi yace ko d'aya dan nasan zuwanka yana da nasaba da Alhaji Mansur a matsayinka na lauyanshi da wad'anda suke k'ara.

Jinjina kai yayi yace tabbas hakane ammah Barrister ka bani mamaki ace wai kaine da kanka kake zarginsu abun kunyanma har da surukinka dan kawai sun hanaka auren d'iyarsu, hakan bai dace da kai ba dan duk garin nan inzaka kewaye babu wanda bai san arzik'in nan nasu bane ko da Alhaji Muhammad yana da kud'i ammah bayada kud'in da zasu nemi suci dukiyarshi ya kamata kasan irin abinda yake fitowa daga bakinka a matsayinka na lauyan wadda ake k'ara.
Murmushi ne yabayyana a fuskar Barr Faruk yazuba mashi idanu yana kallo har saida yakai aya sannan yace dakyau Barrister aikinka yana kyau, saidai maganar da kayi akwai gyara a cikinta dan ko da ace kowa zai yarda da cewa dukiyarsu ce toh ni bazan ta'ba yarda da hakan ba dan nasan ba dukanta bace dukiyarsu, kaidai kawai katsaya a matsayinka baka san komai ba akai kabarni da su kawai dan duk abinda zaka fad'a ba zan ta'ba yarda ba dan ni nasan abinda baka saniba, am ina da abunyi idan babu sauran abinda yakawoka zaka iya tafiya saidai ince sai munhad'u a kotu.
Murmushi Barr Mahamud Bello yayi yace toh shikenan tunda ka ce haka ammah Barrister ya kamata kabi a sannu akan su Alhaji Mansur gudun kar wani abu yafaru.
Jinjina kai kawai yayi yabud'e motarshi yashiga sannan yayi horn megadi yazo yahangeme mashi gate d'in gidansu yacinna motarshi a ciki inda Barr Mb yashiga tashi motar yakama gabanshi......







_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 15*

Alhaji Mansur da yake manne da waya a kunnenshi duk ya saurari komai su Barr Faruk suka tattauna kasancewar sa Barr MB yayi yakirashi a waya yadda zai saurari hirar tasu, yana gama saurare wurgi yayi da wayar tare da komawa yazauna yace lallai yaron chan ya cika taurin kai idan har bai janye k'udurinshi ba ya zama dole inyi wani abu akanshi dan bai isa ya'bata min duk wani shirye shirye na ba.
Toh ammah ta ya yakamata in'bullo mashi? Shuru yayi yana tunani sai kuma chan yayi murmushi yace idan ka san wata bakasan wata ba nan yatashi yad'auko wayarshi.







Washe gari yana office d'inshi zaune ya d'age kanshi sama yana kallon ceiling a ka ga yanayinhi ka san tunani yake, yana nan a haka sai ji yayi anturo k'ofar d'akin anshigo.
'Dago kai yayi dan ganin wanene yashigo batare da annemi iziniba karaf suka had'a idanu da Nasiba yanayin yadda tashigo babu alamun fara'a a fuskarta yasa yagane akwai wata a k'asa, zaune yayi yana kallonta har ta iso wajen table d'in da yake gabanshi, kujera yanuna mata yace bismillah kizauna.
Zare glass d'in da yake fuskarta tayi tare da yatsina fuska tace ba wannan yakawoni wajenka ba Faruk.
Murmushi yayi cikin ranshi yace na san za'a rina,,, ajiye jakkarta tayi

56 / 74