Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
saman table d'in sannan tace na zo ne inyi maka godiya akan abinda kayi ma mahaifina Faruk tabbas kai butulu ne ban ta'ba sanin haka ba sai a yanzu, na yi da nasani da har na amince namallaka maka zuciyata, ina maka kallon mutumin kirki wanda nakeso yakasance abokin rayuwata ashe har akwai ranar da zakaje kakalli tsabar idanun mahaifina kaci mashi mutunci har kazargeshi akan kisan wani.
Dafe kanshi yayi da hannuwanshi duka biyu jin tana neman tak'ara mashi wani zafin da yake saman kanshi, muryarta yaji ta fashe da kuka dan haka yad'ago kanshi cikin sanyin murya yace haba Nasiba meyasa zakice haka bayan ke bakisan abinda yake faruwaba.
Cikin d'aga murya tace taya zan san abinda yake faruwa bayan ka ci mana mutunci tabbas kai butulu ne Faruk kuma insha Allahu kamar yadda kaso katozarta mahaifina ubangiji bazai ta'ba baka daman haka ba, na yi nadamar saninka a rayuwata Faruk.
Saurin mik'ewa yayi tsaye yace wai wace irin maganace kikeyi haka Nasiba baidace kice hakaba ni fa akan aikina nake ba wai tozarta mahaifinki nakeson yi ba.
Koma me zakace kafad'a Faruk nima kaina ban wuce matsayin da zaka tozartani ba, ashe wannan dalilin ne yasa kace insamo maka number d'in Alhaji Mansur dan kawai sun hanaka aurena shine zaka 'bullo masu ta wannan hanyar har kana ik'irarin cewa gidan mahaifina ba nashi bane, wai me yake damunka ne haka faruk!?
Ajiyar zuciya yasafke yace Nasiba yakamata kifamceni duk yadda kike tunani ba haka bane.
'Daga mashi hannu tayi fuskarta sha'be sha'be da hawaye tace babu abinda zanji daga gareka bayan wanda kayi ahakan ma nagode Faruk a yanzu na ida tabbatarwa kai d'in ba masoyina bane mutum ne meson tozarta ni, ashe nikad'ai nake haukana na d'auki soyayyata na baka da zuciya d'aya kaikuma a wajenka ba hakaba nagode sosai Faruk na tayaka murna da kayi silar zubar da hawayena sannan kayi yadda kakeso rayuwace ubangiji yana sane da duk abinda kake aikatawa, na barka lafiya, jakkarta tad'auka cikin sauri tajuya tafita tabar d'akin.
Dunk'ule hannuwanshi yayi yabuga a jikin table d'in da yake gabanshi yace meyasa haka Nasiba? Meyasa bazaki saurareni ba? Hannu yasa yashafa kanshi tare da wucewa cike da tashin hankali yakoma bayan kujerarshi yatsaya nan yafuzgar da wata irin iska me zafi daga bakinshi kan kace mi ya fara zufa, wayarshi ce tafara ringing ammah ko kallon wajen da take ajiye baiyi ba, komawa yayi yazauna tare da dafe kanshi da dukkan hannuwanshi biyu cikin d'aga murya yace daman nasan ba kowane zai fahimceni ba tabbas wannan shine matsalar da jawahir take ji min tsoron inshiga, na rasa masoyiyata adalilin case d'inta ammah ya zama dole inyi abinda yadace dasannu zan maido da martabar soyayyata, nasiba bazan ta'ba bari inrasaki ba zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin kowa ya fahimceni, ya fi awa d'aya a nan zaune yana ta 'yan tunane tunane kafin daga baya yadanna k'ararrawa masinja yashigo wasu files ne yad'auko yamik'a mashi yace wad'annan kakaisu office d'in Director sannan yamik'e yahad'a duk abinda yake buk'ata yafita, tunda yafito daga office d'in yanufi harabar da motocinsu suke wata bak'ar mota ce Jeep yaga a kusa da tashi motar saboda glass d'in bak'ine yasa bai lura da mutanen da suke cikiba saidai bai ta'ba ganin wani ma'aikacinsu a cikin motar ba, ganin ta d'an tare mashi hanya yasa yanufi wajen zaiyi knocking d'in glass dan amatsa yafitar da tashi motar, tun kan ya isa sai gani yayi anja motar antafi dan haka shima yashiga tashi yakama gabanshi.
Yana cikin tuk'i Daddynshi yakirashi a waya yace kazo gida kasameni yanzu murmushi yayi yace toh Daddy ganinan zuwa ina hanya.
Bayan sun gama wayar cikin ranshi yace Allah yasa dai lafiya.
Yana isa yasameshi a parlornshi zaune ganinshi yasa yanuna mashi waje alamun yazo yazauna.
Fuskarshi d'auke da murmushi yace toh Dad, kallon drink d'in da yake saman table yayi ganin haka yasa Dad yad'auko cup yatsiyaya yamik'a mashi, amsa yayi tare da yin godiya sannan yafara sha.
Gyaran murya Alhaji Sani yayi sannan yace Faruk me yahad'aka da Alhaji Sufyan.
Saurin janye kofin yayi daga bakinshi yace na'am Dad.
'Daga kai yayi yace na san ka ji abinda nace.
Shuru yayi cikin ranshi yace watau har ya sanar da Dad,, muryar Dad yaji ya ce kai nake saurare.
'Dagowa yayi yakalli mahaifin nashi yace babu komai Dad.
A'a bazakace babu komai ba kaga Faruk banson rigima kafita harkar Alhaji Sufyan dan shi ba abokin yinka bane nayi mamaki sosai da naji wai kaine kaje har gida kaci mashi mutunci har kana fad'a mashi cewa wai gidanshi ba mallakinshi bane, wa ya aikeka ko ma ince ina kaji hakan?
Jikin shi sanyi yayi sosai yace kayi hak'uri Dad ina akan aikina ne.
"Dakata banason irin haka kar insake ji ka shiga harkarshi dan shi d'an siyasa ne ka san yana da kud'in da zai mallaki fiye da wannan gidan, sannan katsaya iya aikinka babu ruwanka da duk abinda bai shafeka ba.
Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa dan ya san ba lallai ne Dad yafahimci abinda zai fad'a ba, Dad yace ka yi shuru.
Toh Dad insha Allahu.
Yauwa haka nakeson ji Son.
Murmushi yayi yace toh Dad.
Kallon agogo Dad yayi yace bari intashi daman fita zanyi natsaya jiranka.
Shikenan Dad sai ka dawo.
Zaune yayi wajen har mahaifin nashi yatashi yatafi sai kuma chan shima yamik'e yakoma part d'inshi, yana jin babu dad'i a cikin ranshi.
______Da dare yana kwance yana ta tunanin yadda zai 'bullo ma lamarin dan hankalinshi ya tashi sosai da aka saka mahaifinshi a ciki saboda indai dan shine kar mahaifansa susan komai a game da wannan case d'in, yana nan kwance bai saniba har k'arfe d'aya tagota, dariya ce yafara jiyowa a falon d'akinshi tana tashi, saurin tashi yayi zaune cikin ranshi yace wannan dariyar fa?
Ji yayi ancigaba da yi babu k'ak'k'autawa dan haka yakunna fitila tare da mik'ewa tsaye yanufi hanyar fita, yana bud'e k'ofar bedroom d'in sai yaji kamar takun mutum ana tafiya a chan babban parlor sautin dariyar yana cigaba da tashi kasancewar da k'arfi akeyinta, ji yayi kamar yajuya yakoma bedroom d'inshi sai kuma yafasa dan yanaso yaga me yin dariyar dan haka yabud'e k'ofa yafita daga saman matattakalar bene yatsaya yaji ana cigaba da taku na tafiya ammah baiga kowaba dan haka yagane Ammin jawahir ce har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa saboda kar su Dad sujiyo dan haka yajuya yakoma part d'inshi, yana shiga bedroom yamaida yarufe juyowar da zaiyi sai ganinta yayi a tsaye bayanshi cikin siffar da tasaba bayyana saidai wannan karon gashin nan nata farine kal har yana ta'ba k'asa saboda tsawonshi tana tsaye da 'yar sandarta tana kallonshi da k'wala k'walan idanunta wanda girmansu sun kai na goruba saurin jingine jikinshi yayi a jikin k'ofa cikin dakiya yace mi yakawo ki wajena?
Bushewa tayi da dariya wadda tasa gabad'aya d'akin saida ya amsa, saida tayi me isarta sannan tabud'e baki cikin kakkausar murya tace aduk lokacin da naso ganin mutum ina bayyana a gareshi kuma kaima ka san haka, bana neman umurni bare har abani izini,,, dogara sandarta tayi tana tafiya a dudduk'e har saida taje tsakiyar d'akin sannan tatsaya tare da juyowa takalleshi yana nan tsaye a inda yake, sake bushewa tayi da wata dariyar tayi wadda ta wannan karon ta sha bambam da ta farko da wannan jinta yayi kamar kukan jaki saboda rashin dad'inta saida tayi me isarta sannan tace babu abinda zaka iya yi akan case d'in su Alhaji Mansur domin wuk'a da nama duk suna a hannu na sai na kashesu kamar yadda sukayi silar barina duniya ni da mijina sannan zan tseratar da d'iyata daga gidan kaso da kaina.
Cikin nuna rashin tsoro yace wannan ne bazaki iyaba domin tun farko yakamata kitseratar da ita ammah kika kasa, sannan maganar su Alhaji Mansur na riga na maido case d'in a hannuna ni yadace inwanke jawahir a idanun duniya sannan inyi silar da zaisa arufesu a gidan yari ayi masu d'aurin rai da rai.
Sake bushewa tayi da dariya sannan tace bakada iko a wannan hurumin domin nice me power, ina sake gargad'inka akan kajanye hannunka a cikin case d'in nan domin tseratar da kanta daga bala'o'in da suke tunkarar rayuwarka, su Alhaji Mansur bazasu ta'ba barinka ba zasuyi k'ok'arin ganin sunga bayanka ammah idan har ka za'bi mutuwarka akan komai toh shikenan saidai duk wannan abun da kake bai ta'ba burgeni ba dan nasan wuk'a da nama suna a hannuna.
Nunata yayi da yatsaya yace ke d'in azzalluma ce bawai kina taimakon jawahir bane kawai dai kina cutar da rayuwarta ne gashinan ta dalilinki kowa guje mata yake.
Wata irin razanannar k'ara tasaki wadda tasa har saida akayi k'aramar girgizar k'asa a cikin d'akin.
Saurin toshe kunnuwanshi yayi har saida k'arar talafa sannan yasakesu.
Nunashi tayi da yatsanta cikin 'bacin rai tace idan har kacigaba da jifata da munanan kalamai zan d'and'ana maka azabata.
Bud'e baki yayi zaiyi magana sai ji yayi kamar anrik'e bakin nashi, juyawa tayi baya tace bana buk'atar jin komai daga gareka, nan tafara takawa tink'is tink'is tanufi wajen da ya ajiye briefcase d'inshi ganin haka yasa Faruk cikin sauri yanufi wajen da take, juyowa tayi ahankali tare da nunashi da hannunta nan wata irin iska tataso sai ji yayi and'aukeshi anyi wurgi da shi gefe d'aya ya fad'i kanshi ya bugu da k'asa.
Jawahir da take k'wance a cikin d'an kurkukun d'akinta tana bacci cikin daren nan, lokaci guda tafarka tare da fasa k'ara da dukkan k'arfinta wadda tasa saida duk mutanen da suke kusa da d'akin da take suka farka, hatta shi kanshi megadin saida yafarka rik'e kanta tayi tare da jan gashinta da dukkan k'arfinta ahankali tace a'a Ammi kar ki aikata haka ya kamata kibar Barr Faruk kar kiyi mashi komai bai chanchanci hakan daga garekiba, bazan ta'ba bari kiyi mashi wani abu ba,
'Daga murya tayi tace a'a Ammi na ce kar kiyiiiii!! waige waige tafara yi chan kuma tamik'e cikin sauri tanufi wajen bango tana zuwa tabuga kanta da k'arfi, wani irin zafi ne taji ammah ahaka tasake bugawa nan take jini yawanke mata fuska tasulale k'asa a hankali tare da furta sunan Amminta.
Daidai lokacin maigadi ya iso d'akin yadallota da fitila ganinta a kwance shame shame yasa yayi saurin bud'e k'ofar yashiga.
Ammi ko da komai yafaru a cikin kunnenta ta jiyo sautin d'iyartata tsayawa tayi chak a inda take tsaye tare da fasa k'arar da tasa saida Faruk yafarfad'o daga suman da yayi, cikin d'aga murya tace a'a jawahir bazan ta'ba bari wani abu yasameki ba, nan take tayi girgiza ta'bace.
Yunk'urin tashi yayi daga inda yake kwance ammah yakasa jin jikinshi yayi duk yana yi mashi ciwo saboda buguwar da yayi, dafe kanshi yayi da hannunshi sai a lokacin yasamu damar fara karanto addu'o'i sannan yasamu yamik'e dak'yar yanufi toilet, ruwan zafi yahad'a yagasa jikinshi bayan ya fito ne yanufi wajen briefcase d'inshi yabud'e ajiyar zuciya yasafke ganin bata ta'ba mashi komai ba saidai me ya jiyo lokacin da tafurta sunan jawahir to me yafaru da ita?
Jin k'arar bugawar agogo alamun k'arfe ukku yasa yakwanta yana jin jikinshi duk yana mashi ciwo ahaka yasamu yayi bacci.
____
Megadi yana shiga d'akin tsaye yayi a wajen kan jawahir cike da mamaki ganin ko kad'an bata motsi ga jini yana fita daga goshinta hakan yasa yayi saurin fita yad'auko wayarshi yakira shugaban su yasanar da shi halin da ake ciki, nan da nan aka kira First Aid Member na prison d'in sukazo suka fara mata dressing ammah jinin bai tsayaba, ruwa aka d'ebo aka watsa mata bata farfad'o ba daga suman da tayi sunyi kusan minti talatin akanta ganin har lokacin bata farfad'oba yasa suka kira shugaban suka sanar da shi yace to suyi k'ok'ari sutsayar da jinin da yake zuban kafin zuwa safe idan har bata farfad'oba sai akaita asibiti.
Haka ko akayi har asuba bata farfad'oba dan haka ana yin sallah aka d'auketa aka saka cikin mota aka nufi asibiti da ita inda motocin 'yansanda biyu suka rakasu har babban asibiti da ke cikin garin, a emergency unit aka wuce da ita a lokacin cike yake babu gado dan haka aka kama mata d'aki a aminity aka kwantar da ita nan likitoci suka yo kanta ganin daga gidan yari akazo da ita, dubata sukayi sannan suka nad'e mata kai da bandage bayan sunyi mata dressing sannan suka sa mata drip, daga k'ofar d'akinta 'yansanda biyar ne tsaye suna kaiwa da kawowa.
Sai wajen k'arfe goma sha biyu sannan tafarfad'o daga suman da tayi.
Tana bud'e idanunta taganta kwance a wani wajen na daban mamakine yakamata tace ina ne nake nan?
Yunk'urin tashi tayi sai kuma takasa, hannu tasa tafizge drip d'in da aka sa mata tatashi zaune tare da dafe kanta da taji kamar zai cire saboda tsananin ciwon da yakeyi mata, daidai lokacin doctor yashigo yana ganinta yayi saurin nufo inda take yace lafiya me yafaru?
Runtse idanunta tayi tana ji kamar zai fad'o nan yazo yarik'eta takoma takwanta yamaida mata drip d'in sannan yafita yarubuta wata allura yace aje asamo yanzu zaiyi mata ita.
Ba a dad'eba aka kawo allurar yayi mata sannan yafita yace kar wanda yashiga abarta tana buk'atar samun hutu tsawon awanni bakwai, nan suka amsa da toh sannan yawuce, d'aya daga cikin police d'inne yabud'e d'akin yalek'a ganinta a kwance yasa yamaida k'ofar yarufe.....
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 16*
...Yana gama shirin shi ko wajen aiki bai biyaba yau yawuce gidan kaso dan yana so yaga halin da jawahir take ciki yana isa yasamu labarin abinda yafaru dan haka daga nan yawuce asibitin, yana isa likita yana fitowa daga d'akin yatabbatar masu da har lokacin bacci take.
Awanta biyar tana baccin lokaci guda tabud'e idanunta tafara waresu a cikin d'akin ganin babu kowa yasa tatashi zaune hannunta takalla wanda aka sa ma kanula tasa gudan hannun tafizgeta sannan tayi saurin safkowa daga saman gadon, fara takawa tayi ahankali tanufi wajen taga, d'an d'age labule tayi talek'a ganinsu tayi tsaye wasu zazzauna a k'ofar d'akin, ganin wani yana shirin kallon tagar yasa tayi saurin sakin labulen tare da komawa takwanta tana ji suka bud'e d'akin suka lek'ota sannan suka maida suka rufe, tana jin sun rufe tatashi zaune tana bin d'akin da kallo kamar me neman wani abu sai kuma chan tamik'e wasu kaya tahango ajiye saman 'yar k'aramar drowar da take cikin d'akin cikin sauri taje tad'auka tashiga toilet nan tatsaya tana bin toilet d'in da kallo, 'yar tagar da tagani ne yasa tayi murmushi ajiye kayan tayi sannan tataka drum talek'a tagar, ganin wajene bayan d'akin yasa tasafko tad'auki kayan tasaka nan tafara tunanin ta yadda zata iya fita, juyowa tayi taje tarufe k'ofar toilet d'in ahankali sannan tataka drum d'in taja ragar (net) d'in tagar da k'arfi ammah tak'i 'balluwa dan haka tasa bakinta tafara ciccirewa da hak'oranta abinda zai baka mamaki kamar ba hak'oran mutum ba yanayin yadda take cire ragar da su saida tafara cire na 'bari guda sannan tasa hannunta taja dak'arfi sai gashi ta 'ba'b'bakota gabad'aya, koda tagar ba wani girma gareta ba ammah ahaka tatura kanta tafitar da shi saida taga babu motsin kowa a wajen sannan ta ida fidda jikinta dakyar tadira bayan ginin, gyalen kayanta tasa tarufe fuskarta da shi sannan cikin sauri tawuce zata zagaya tana 'bullowa sai ganin 'yansandar tayi tsaye a gaban d'akin suna kaiwa da kawowa dan haka sai tak'ara jan mayafinta a fuskarta sannan tacanza hanya cikin sauri tafita tabar asibitin tana fita tasamu me napep tatsaida tafad'a mata anguwar da zai kaita cikin sauri tashiga tace suje dan haka yajata suka tafi, tana yi tana kallon agogon da ke manne a gaban napep d'in har suka isa inda tace yakaita, suna isa tafita daga napep d'in tajuya zata tafi me keke napep d'in yace Hajiya kud'ina.
Tsayawa tayi cak tare da juyowa dan ita ta ma mance da zata biya wasu kud'i gashi batada su, k'ara maimaita mata yayi.
Ahankali tace kud'i? A'a kayi hak'uri banda su.
Harara yawurga mata yace da kinsan bakida kud'in shine zaki shigo min napep.
Ganin wani mutum ya nufo wajen yasa tad'aga murya tace dan Allah kayi hak'uri wallahi a rud'e nake saisa ban tsaya d'auko kud'i ba, fitowa yayi daga cikin napep d'in yace wallahi babu inda zakije sai kin biyani kud'ina.
Ganin haka yasa mutumin yanufo wajen yana cewa lafiya me yafaru?
Cikin fushi me napep d'in yace wannan yarinyar ce dan rainin wayo zata shigo min napep bayan na kawota inda takeso sai tace min batada kud'i.
Kallonta mutumin yayi yace haka akayi?
'Daga kai tayi alamun Eh.
Toh shikenan ni zan biya nawa ne kud'in naka?
Jawahir tana jin haka sai tayi murmushi tace nagode sosai sannan tajuya tatafi cikin sauri, tana zuwa k'ofar gate d'in gidan taja tatsaya kamar tayi knocking sai kuma tafasa, tura k'ofar gidan tayi ahankali sai jin motsi tayi a toilet na wajen k'ofar alamun megadin yana ciki dan haka tatura tashiga tamaida tarufe sannan tafara takawa sad'af sad'af ahaka tanufi hanyar cikin gidan tana shiga nan ma shuru batare da wani tsoro ba tafara taka matattakalar benen ahaka tahau sannan tamurd'a k'ofar wani d'aki jinta a bud'e yasa tad'an bud'e ahankali sai gani tayi babu kowa a ciki, k'arar shower tajiyo a toilet dan haka tabud'e d'akin ahankali tashiga tana lalla'bawa dan kar ajiyo k'arar takun ta, daga tsakiyar d'akin tatsaya tana binshi da kallo sai kuma chan tanufi wajen bedside tana zuwa tajawo drower k'asa tajita a datse dan haka tabud'e ta saman taji ita kuma a bud'e, lalubawa tafara yi sai ga key ta gani tafiddo cikin sauri tabud'e ta k'asar tana jawowa sai ga wasu files a ciki fiddosu tayi gabad'aya tafara