Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 74

90K to 93K   out of 220.3K words

yakeso yamallaka na Alhaji Muhammad a k'ark'ashin jagorancin d'an uwanshi, ko zaku iya tuna haka?

Su dukansu shuru sukayi suna kallon kallo sai chan Alhaji Mansur yagirgiza kai yace bansan anyi haka ba.

Shuru faruk yayi sai kuma yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a tabbas su Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan suna cikin mutanen da suke da hannu akan mutuwar Alhaji Muhammad dan a nan cikin wayar da namik'o duk akwai muryoyinsu da maganganun sirrin da sukayi a tsakaninsu sannan ga k'arin shedar da ke gareni ta k'arshe, juyawa yayi yakallesu sannan yabud'e file d'in da yake hannunshi yad'ago masu yace shin cikinku akwai wanda yagane takardun da suke cikin file d'innan?

Zaro idanu sukayi gabad'aya nan take cikin Alhaji Sufyan yakad'a yace ina kasamo wad'annan?.

Murmushi yayi sannan yace takardar farko original ce ta companyn Alhaji Muhammad inda ta biyu takasance jabu ce kun bugotane dan ku samu ku mallake companyn ga signing d'inku nan da komai.

Mai gabatar da k'ara ne yazo ya amsa yakai ma alk'ali, wasu takardun yafiddo yanuna masu yace wannan fa me zakuce akanta?
Shuru sukayi suna kallonshi sai Alhaji Mansur yayi k'arfin halin cewa wannan ai kai za'a tambaya dan kai kasan sharrin da kake shirin k'ullawa.
Girgiza kai yayi yace wannan ba sharri bane sannan yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a wannan takardun motocin Alhaji Muhammad ne da suka samo a cikin gidanshi bayan mutuwarshi sunyi amfani da wani ya yi masu yarjejeniya akan kowane d'aya daga cikinsu Alhaji Muhammad ya siyar mashi da motocinshi biyu ga signing nan irin nashi anje anyi, zuwa yayi yamik'a ma Alk'ali nan yaduba, sannan yace ya megirma me shara'a na tabbata da za'a tuhumesu da zasu fad'i gaskiyar cewa suna da hannu a cikin mutuwarshi da kuma irin k'ulle k'ullen da suka dinga shiryawa akan dukiyarshi wadda sunci fiye da rabin dukiyar dan Alhaji Sufyan shi yashirya masu yadda zasuyi susamo dukiyar da take cikin account d'in jawahir inda su Alhaji Mansur da Alhaji Tanimu sukaje suka shirya ma kawunta k'arya a matsayinshi na bagidaje sukace yasamo masu kud'in zasu yi kasuwanci wanda zai dinga kawo masu kud'i sosai shine yayi amfani da damarshi yatafi da jawahir a banki yasa tayi mashi signing d'in rabin dukiyarta aka fiddo daga acount d'in koda yakawo masu ba wai business sukayi ba sunje sun raba kud'in a tsakaninsu ne.

Alhaji Sufyan ne yayi saurin katseshi yace ya megirma me shara'a wannan k'arya ne sharri kawai yake son ja mana dan ya'bata mana suna bamusan komai ba akan abinda ake zarginmu da shi ba dan bamu aikata ba kawai dai yana da wani nufi akanmu ne dan kawai na hanashi auren d'iyata saisa yakeso ya'bata mana suna.


Faruk kallon Alk'ali yayi yace ko d'aya ba sharri bane Allah yagafarta malam duk sun aikata dan ga shedu nan na tara ga muryoyinsu nan a cikin wayata.

sake kunno recording d'aya daga cikin su yayi nan murya tafara tashi ana cewa "Hello kana jina ya kamata kayi k'ok'ari wajen ganin ka samo mana file d'in filin nan dan da alama zaiyi kud'i sosai ni na san yadda za'ayi asiyar da shi batare da kowa ya ganeba dan nima kaga wannan filin da kabarmin gwamnati nasiyar mawa kuma ta siya da kud'ad'e masu tsoka.
Toh shikenan Alhaji koma me kenan nasan hanyar da zanbi insamo dan dama maganar da muka gama yi da Alhaji tanimu kenan dan shine jagoran komai, da ace akwai hanyar da zanbi da a yau d'innan sai naga bayan yarinyar nan kowa yahuta dan na san idan har tamutu dole abarmin gadonta gabad'aya tunda ni kad'ai ne d'an uwan mahaifinta,,, Cewar Alhaji Mu'azu.

Daga chan 'bangaren dariya akayi akace kaidai kabi komai a hankali ko da baka kasheta ba zaka iya yin amfani da damarka wajen ganin mun samo dukiyar Alhaji Muhammad, inyaso idan har mun gama samun yadda mukeso zaka iya kasheta saidai kuma idan har zaka rufe ma mutane baki dan kar ayi zargin wani abu kamar yadda mukayi bayan munsa ankashe Alhaji Muhammad da matarshi.

Dariya Alhaji Mu'azu yayi yace ai fiye da hakan ma zan iya sa wa ayi mata dan ni ban had'a komai da kud'iba abokina, yanzu dai zuwa anjima zan kiraka idan har nagama tattara bayanan filin inyaso sai muje musiyar da shi.

Yauwa mutumina kayi k'ok'arin haka sai na ji daga gareka".



Yana k'arewa wani kuma yasake kunnowa me irin muryar sukaji yana cewa, Hello Alhaji Mu'azu ina jinka d'azu ka kirani bana kusa.
Eh Wallahi abokina cewa nayi ta samu fa a yanzu ga wani gida nan na Alhaji Muhammad da nagano yana da shi batare da sanin kowaba sai yanzu naga takardun gidan na je na ganshi kuma antabbatar min da nashine.
Daga chan 'bangaren dariya akayi akace lallai Alhaji Muhammadu wayonshi ya yi yawa watau yana da gida batare da sanin ka ba, toh bari zan zo inje muga gidan idan har yana da girma sosai ni zan sayeshi dan dama inaso mutashi da iyalina daga nan, kace abu ya zo gidan sauk'i ai wallahi mutuwar nan tashi dad'i tayi min dan ko bakomai munsan muma mun mori dukiyarshi.
Alhaji Mu'azu ma dariya yayi yace kaidai bari a yanzu gashinan ina ta facaka da kud'i yadda nakeso ba kamar lokacin da yake raye ba, ka san mutuwarshi ko kad'an bata d'aga min hankali ba sai waje d'aya lokacin da kabani layarnan insaka mashi a baki toh a nan ne nad'an tsorata dan ko da su Alhaji Mannir suka shigo gidan zasu kasheshi ban wani d'aga hankaliba dan na san zamuyi nasara.

Katseshi yayi yace a'a Alhaji Mu'azu kayi shuru kar ajiyo ka asirinmu yatonu agane mune muka kasheshi abar maganar kawai zan zo yanzun nan muje inga gidan dan ka san bana wasa da kud'i,,, su dukansu dariya sukayi....



Suna gama saurare yace shin wannan ba muryarka bace Alhaji Sufyan ko itama sharri akayi maka?
Fara raba idanu yayi yakalli Alk'ali cikin alamar rashin gaskiya yace ni bansan komai ba akai sharri yake son ja min wallahi.

Alk'ali baice komai ba yana dai cigaba da kallonshi sai kuma yad'auko takardun gidan yasake dubawa.

Barr Faruk cigaba yayi da cewa sannan akwai lokacin da Alhaji Mansur yakirani muka had'u yagargad'eni akan injaye daga shari'ar Jawahir har yad'auko mak'udan kud'i yabani ammah ban amsaba dan haka ne yasa aka kamani aka rufe a wani gida dan kar inzo inbada sheda a kotu wannan ne dalilin da yasa ban halarci kotu da wuri ba yau dan sai a yau nasamu natsero daga gidan


Cikin d'aga murya Alhaji Mansur yace k'arya yake wallahi sharri kawai yake ja min ba ni bane.

Kallonshi Faruk yayi yace ina da sheda da zata bayyanar da haka dan lokacin da muka had'u na yi recording d'in duk maganar da mukayi batare da ka saniba, nan yakunno recording d'in yakunna ma Alk'ali sannan yace bayan wannan akwai wata shedar, kallon Barr Nas yayi yace kace sushigo, nan yamik'e yafita duka mutanen cikin kotun juyawa sukayi dan ganin wanda zai shigo, police ne suka shigo da wasu mutane biyar a d'aure , Alhaji Mansur yana ganinsu zabura yayi nan yafara kalle kalle yana neman hanyar gudu yarasa, Barr Faruk kallon Alk'ali yayi yace wad'annan sune mutanen da yasa suka satoni suka tsareni

Alk'ali kallonsu yayi yace kufad'a ma kotu tsakaninku ga Allah abinda kuka sani inkukayi k'arya kotu zata hukuntaku.


Babban sune yayi k'arfin halin cewa wallahi wad'annan mutanen sune suka kiramu suka bamu kud'i sukace musato Barrister mutsareshi shine suka bamu gidan da muka zauna da shi, wallahi sune suka sa mu.

Alk'ali kallonsu Alhaji Mansur yayi da gabad'ayansu idanu sun raina fata yace toh kunji duk shaidar da aka samu akanku ya kamata kufad'a ma kotu gaskiya inko ba hakaba kotu zatasa atambayeku.

Shuru sukayi suna mazurai chan alk'ali yad'akko waya yakira ba'a yi minti biyar ba sai ga wasu k'atti su hud'u sun fito kowane d'aya hannunshi rik'e da shar'be'biyar bulala, Alhaji Sufyan yana ganinsu yayi saurin cewa wallahi zan fad'i gaskiya duk abinda yafaru mun aikata tabbas mu takwas ne muka shirya komai shidda daga ciki duk sun mutu, munci dukiyar Alhaji Muhammad sannan duk takardun nan mu mukasa aka had'a mana jabu muka siyar ma da gwamnati filayenshi guda biyu ko Alhaji Mansur?
Fashewa da kuka Alhaji Mansur yayi yace tabbas hakane mun aikata kuma sharrin shaid'anne dan Allah munaso kotu ta yafe mana insha Allahu bazamu sake aikata irin haka ba.

Alk'ali ajiyar zuciya yasafke yace Alhamdulillah kun amsa laifinku da kanku dan haka kotu zata yanke maku hukunci daidai da yadda shari'a tace, dan haka za'a yi maku hukunci guda biyu na farko dai bayan kun biya wannan baiwar Allahr dukiyarta da kukaci ku da kuke raye zakuyi zaman shekara guda a gidan kaso, na biyu kuma wannafsi binafsi dan haka ya zama dole za'a kasheku kamar yadda kuka kashe wasu.

Sannan kotu ta wanke Jawahir muhammad mekud'i daga zargin da akeyi mata dan haka kotu ta saketa zata koma tacigaba da rayuwarta sannan za'a damk'a mata dukkan dukiyarta da wad'annan 'barayin sukaci.

Su Alhaji Mansur duk'awa sukayi k'asa suna kuka suna cewa dan Allah Alk'ali ataimaka mana wallahi hukuncin nan ya yi mana tsauri ataimaka a safsafta mana tunda mun amsa laifinmu sannan kud'in da suka rage hannunmu basu kai wanda muka ci mata ba.

Girgiza kai Alk'ali yayi yace wannan ne kuma bazai yuwu ba dole ayi maku hukunci daidai da na kowa, kubar ma ta wannan sai kun biyata kud'in da kukaja aka rufeta tsawon shekara guda batare da hak'k'inta ba.


Mutanen da ke zaune cikin kotun salati suka farayi suna Allah wadai da halin su Alhaji Mansur.



Jawahir da take tsaye tun d'azu inba hawaye ba babu abinda take, hannu tad'aga tafara yi ma Allah godiya sai kuma chan cikin kuka tace tunda dai har gaskiya ta bayyana na ji dad'i bana buk'atar komai daga wajensu subar kud'in na yafe kawai dai akashesu su ma shine zan fi jin dad'i.

Alk'ali yace ba maganar yafewa a cikin hukuncin da kotu tazartas ya zama dole subiya wad'annan kud'in, kallon police yayi yace atafi da su subiya kud'in ga list nan na kud'inta da sukaci idan kud'ad'ensu basu isaba kusiyar da duk wata k'addara da suka mallaka.
Su kuma wad'annan (yanuna wad'anda suka sace Faruf yace) atafi da su gidan yari zasuyi bauta tsawon shekara guda sannan asakesu, yana fad'in haka yabuga table d'in gabanshi.


Nan take aka saka ma su Alhaji Sufyan da Alhaji Mansur ankwa aka fita da su.

Nasiba da take tsaye wajen motarta ita da mahaifiyarta suna kuka nan suka nufi wajen da mahaifin nata yake kafin su isa 'yan jarida har sun rufeshi sun fara mashi tambayoyi a matsayinshi na d'an siyasa, kutsawa sukayi suka isa wajen, yana ganinsu yayi saurin sadda kanshi k'asa......






_Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 21*

Nasiba cikin sheshek'ar kuka tace Daddy kalli abun kunyar da kajawo mana yanzu hakan da kayi daidai ne? Kaduba kaga halin da kajefa kanka da mu a ciki a idanun duniya, meyasa kabi son zuciya ka aikata hakan? Ba ka tunanin yadda rayuwarmu zata kasance, taya kake tunanin laifin nan da ka aikata zai goge a idanun mutane? Ya kakeso muyi da rashin ka? Meyasa haka Daddy, meyasa?,,, kukan da yaci k'arfinta ne yasa tayi saurin juyawa, har lokacin kan Alhaji Sufyan yana sadde a k'asa ji yake kamar a mafarki abin yafaru hawaye ne suka fara fita daga idanunshi, muryar matarshi yaji cikin muryar kuka tana cewa Alhaji ban ta'ba tunanin haka daga garekaba wallahi ka ban kunya ka zubar mana mutunci da k'ima daga ni har 'ya'yanka tirr da wannan halin naka, daman Nasiba ta fad'a min akwai abinda yake faruwa a kotu muzo mugane ma idanunmu ashe daman abinda zamuzo mugani kenan? Meyasa haka Alhaji!,, Nasiba ce tajuyo cikin sauri tarungume mahaifiyartata sai a lokacin yad'ago kai yakalleta.

Police tisashi sukayi a gaba aka wuce da shi dan dama tuni antafi da Alhaji Mansur mota, 'yan jaridar da suke ta mashi tambayoyi bai samu ya amsa ma kowaba saboda halin nadama da yashiga.
Suna jin tashin motar nan su Nasiba suka k'ara sautin kukan da suke dan sunsan tabbas a yanzu ya yi masu nisa daga rayuwarsu.



Ana gama shari'ar Barr MB ne farkon wanda yafara mik'ewa yaba Barr Faruk hannu suka gaisa sannan yatayashi murna, Barr Junaid ko dasauri yazo yarungume abokin nashi yana cewa Faruk ka dawo, nagode ma Allah da mutanen nan basu samu damar cutar da kai ba, muna ta wahalar nemanka ashe kana hannun azzaluman chan.
Murmushi Faruk yayi yace Junaid kaidai ko,
Sai a lokacin yajuya yakalli inda jawahir take tsaye tana kuka har ya taka zai tafi sai ji yayi anrungumoshi tare da fashewa da kuka, dubawar da zaiyi sai ganin mahaifiyarshi yayi cikin sauri yarungumeta yace Mom d'ina.
Cikin kuka tace nagode ma Allah da yamaido man kai Faruk wallahi na shiga damuwa sosai akan rashinka ashe zan sake sakaka a cikin idanuna, mutanen chan sun zalunceni ban yafe masuba da suka rabani da kai, ina sonka sosai d'a na.
K'ara rungumeta yayi jikinshi cike da jin tausayin mahaifiyartashi yace nima haka mummyna ina k'aunarki sosai, a yanzu babu wanda zai sake rabamu muna tare.
Dad da ya iso a lokacin dafashi yayi yace d'ana Faruk, k'wallah ce tacika mashi idanu yace ashe zamu sake ganinka nagode ma Allah da basu rabani da kai ba.
'Dan guntun murmushi yayi yace Daddyna nima ina farin cikin sake ganinku.
Farin ciki suka dinga yi sosai a wajen duk wani me k'aunar Barr Faruk saida yazo yatashi murna duk da haka hankalinshi yana wajen jawahir samu yayi yajanye Mom daga jikinshi yace yana zuwa nan yanufi inda take, yana zuwa yabud'e baki zaiyi magana sai tarigashi tace nagode sosai Faruk da namijin k'ok'arin da kayi akaina tabbas ka cika mutumin kirki ka taimakeni a daidai lokacin da nake buk'atar taimako ka wankeni daga zargi a idanun jama'a, koda akaina ka fuskanci matsalar rayuwa ammah hakan bai sa kabarni ba nagode, nagode, nagode sosai Faruk.
Cike da jin tausayinta yace jawahir kidaina cewa haka domin wannan ba komai bane kin cancanci hakan ko ma ba keba hak'k'inane intaimaka ma duk wani wanda yake buk'atar taimako irin wannan hatta rayuwata zan iya bayarwa akan aikina.
Da mamaki take kallonshi cikin ranta tana jinjina ma k'wazo irin na Faruk da son taimakonshi, wasu sabbin hawayen ne suka gangaro mata tace ina ma ace Ammina tana raye taga irin wannan ranar, ina ma ace zanga irin farin cikin da zata shiga, ina ma ace Yaya Umar yana raye,,,, kukan da yaci k'arfinta ne yasa tayi saurin juya mashi baya.
Faruk har ya bud'e baki zaiyi magana sai ganin Nasiba yayi gabanshi tsaye tana kuka, idanu yazuba mata ganin yadda take kuka bilhak'k'i, cikin sheshek'ar kuka tace Faruk dan Allah kayi hak'uri da abinda yafaru tabbas na yi kuskure da nakasa fahimtarka, mahaifina baiyi mana adalciba dan duk shine yajefamu a cikin wannan halin nayi nadamar kasancewarshi a matsayin uba agareni dan bai cancanci hakan ba, Allah wadai da mahaifi me hali irin nashi.
Tarar numfashinta yayi yace a'a Nasiba kidaina cewa haka ko ba komai shi ubane.
K'ok'arin rage sautin kukanta tayi sannan tace tabbas shi ubane ammah ba irin uban da yadace ayi alfahari da shi ba domin ya 'bata mana suna a idanun duniya wallahi na yi nadamar rayuwata ina ma ace inmutu inhuta da wannan rayuwar Faruk ban ta'ba tunanin haka daga mahaifina ba ashe daman shine yasaceka, hannuwanta tahad'e waje guda tace dan Allah Faruk kar kakamani da laifin da bani na aikata ba, tabbas nayi maka mummunan fahimta a lokacin da kaso kafahimtar da ni komai saidai duk hakan daman ubangiji ya k'addara hakan zai faru dan Allah kayafe min ba dan halina ba.
Wani irin tausayinta ne yaji ya d'arsu a cikin ranshi yace Nasiba wallahi bakiyi min komai ba inma kinyi na yafe maki dan baki cancanci inrik'eki acikin raina akan wani laifi da ba nakiba.

Fashewa tayi da kuka tace nagode sosai Faruk nagode, sai a lokacin tajuya inda jawahir take tsaye ta juya baya matsawa tayi tatsaya gabanta tace na tabbata kowanene akayi ma irin abinda akayi maki sai ya ji ba dad'i a ranshi dan an zalunceki anci amanarki dan Allah ina neman afuwarki akan abinda mahaifina ya aikata maki.
'Dago kai jawahir tayi tana kallonta.
Ganin haka yasa Nasiba tace ba wai ina neman afuwa bane akan asaki mahaifina saidai ina neman afuwa akan kasancewata 'yarshi mukaci da hak'k'inki dan Allah kiyafe min.
'Daga mata kai kawai Jawahir tayi batare da tayi magana ba.

Nasiba kallon Faruk tayi tace dan Allah Faruk kar wannan abun da yafaru yasa kabarni dan Allah kar kakalleni da halin mahaifina inaso kacigaba da kasancewa tare da ni.

Juyawa yayi yakalli iyayenshi da aketa tayawa murnar dawowar d'ansu sannan yace Nasiba yanzu ba lokacin wannan maganar bace, kallon jawahir yayi yace muje kugaisa da iyayena.

Bata musaba tajuyo tabi bayanshi suka tafi suka bar Nasiba nan tsaye tana kuka, daidai lokacin mahaifiyarta tazo nan tafad'a jikinta tana cewa Mummy na rasa Faruk ya daina sona, meyasa?
Girgiza kai Hajiya Maijidda tayi tace a'a Nasiba kizo muje gida kawai.
Haka tabi mahaifiyartata suka tafi.

Faruk nuna ma iyayenshi Jawahir yayi nan suka gaisa suka yi mata jaje sannan suka tayata murnar ku'butar da tayi daga gidan kaso.


Mom dai tana manne da d'an nata chan tace Faruk wai ya akayi kaku'buta daga hannun wad'anchan azzaluman?
Murmushi yayi yace Mom muje gida sai insanar da ku komai.
Dad ne yace Alhamdulillah kinga zuwan da mukayi kotu ya yi amfani daman raina ya bani zamu ga Faruk saisa nace maki

31 / 74