Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
*FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 22*
Yana barin gidan chan gidan da yasafke buzu megadi lokacin da yad'akkoshi daga Marad'i dan yazo yabada sheda yawuce ya yi sa'a daidai lokacin yafito daga cikin gidan, ganin motar Faruk yasa yanufo wajen cikin hausar shi da bata fita sosai yace hannu da zuwa Alhaji hannu.
Murmushi Faruk yayi yace yauwa buzu megadi ashe na yi sa'a da fita ma zakayi.
Washe baki yayi yace eh na d'an fitone zanga gari kafin gobe inkoma garinmu.
Allah sarki, yanzu shigo mota inmaka wata tambaya.
Bai musaba yabud'e motar yashiga yace toh Alhaji ai dun yanda kashe haka za'ayi.
Yanayin maganarshi tana ba Faruk dariya har saida yayi murmushi sannan yace yauwa tambayar da zanyi maka itace: dan Allah kana iya tuna mak'abartar da aka binne Hajiya Khausar bayan ta rasu?
Yatsa yasa yadafe kanshi irin yana tunanin nan sai chan yace Eh aradu har k'abarinta na sani kusa da wani iccen giginyane akwai tudu a wajen ban mancewa har lokacin nayi tuntu'be a wajen nafad'i bayan mun rufota har yanzu akwai tabon gurjewar da nayi a gwiwata bari ma kaganshi.
A'a kabarshi ba sai na ganiba yanzu fad'a min mak'abartar muje dan inason ganin k'abarinta.
Angama oga nan yafad'a mashi Faruk yaja motar dagudu yanufi anguwar da mak'abartar take suna zuwa suka samu waje daga chan k'etare sukayi parking d'in motarsu suka tsallako, megadin mak'abartar suka samu suka gaisa nan Faruk yafayyace mashi komai akan abinda yakawoshi, da fari megadin be yarda ba dan ya yi tunani wani abu sukeson yi ne kawai.
Ganin haka yasa Faruk yace na san baka yarda da maganataba saboda duniyar nan ta yanzu ta 'baci matsafa sunyi yawa suna amfani da wani sashe na jikin gawa suna tsafi da shi, wallahi ni ba wannan yakawoni ba idan baka yarda ba muje tare ayi komai a gabanka.
Jin haka yasa megadin ya amince suka je tare buzu megadi tsaye yayi yana tunanin inda zai gane k'abarin saboda tsawon shekaru ukku kenan da binneta, gefe gefen mak'abarta yafara bi dan ya san tabbas daga gefe yake, megadi ganin haka yasa yace da hak'ura kukayi dan kusan shekara ukku ai babu abinda zaku samu saboda bayan ita mutum dubu nawa aka binne a wajen.
Jikin Faruk sanyi yayi dan ya san gaskiya megadi yafad'a.
Daidai wani iccen giginya dake kusa da wani d'an rami buzu megadi yatsaya yace alk'ur'an nan ne wajen ga ma k'abarin nan kusa da giginyar nan.
Megadin mak'abartar ne yace ka tabbata nan ne dan gaskiya an kwana biyu ba'a binne mutane a wajen ba dan duk gawar da aka binne saidai washe gari azo atadda k'abarin a bud'e ko ansake rufewa haka yake faruwa wannan dalilin ne yasa gabad'aya aka daina binne gawa a wajen.
Sake kallon wajen yayi yace wallahi nan ne ban manceba.
Jin haka yasa Faruk yace tunda ya tabbata da nan d'inne toh mutone wajen mugani ta yuwu aga gawar.
Megadin mak'abartar amincewa yayi nan suka duk'a suka fara tonen k'abarin babu komai a cikinshi sai k'asa haka sukaita tonawa daga k'arshe ma sai farin yashi suka fara gani, ganin haka yasa Faruk yaduk'a yasaka hannunshi yafara lalubawa cikin yashin yana cewa indai har wajen nan ne toh tabbas zamuga layar, cigaba yayi da lalube ganin baiji komai yasa yasa suka cigaba da tone ramin har said sukayi mashi zurfi sosai sannan suka kwashe k'asar ciki, suna cikin kwasar k'asar ne buzu megadi yakwaso da wani abu bak'i nan yanuna ma su faruk.
Me gadin mak'abarta ne yad'auko abun yana dubawa nannad'e yake da zare yace to menene wannan ko dai layar ce?
Buzu yace anya kuwa ai laya ba bak'a bace.
Wurgi yayi da shi yace wani dai abun ne daban kunga ahak'ura kawai k'ila ma ba nan bane tunda kusan shekara ukku ai ya isa amance.
Faruk ne yayi saurin zuwa yad'auko abun yace tabbas raina ya bani wannan ce layar bakuga an nad'e da zare ba, bari inbud'a muga abinda yake ciki, nan yafara warware zaren saida yawarware tas yaga da fata aka had'a an d'inketa nan suka warware d'inkin sai ga wani siririn gashi guda d'aya a ciki, cire gashin sukayi suka bud'e layar nan wani bak'in hayak'i yafito daga ciki, sunan Khausar ne tun daga sama har k'asan layar, faruk yace kungani ko wallahi itace aljihunshi yafara lalube zai d'auko ashana nan sukaga wata irin isaka ta taso me k'arfi wadda tasa gabad'aya iccinan da suke cikin mak'abartar suka fara kad'awa su kansu iskar saida taso tayi masu yawa.
Faruk saurin fiddo ashanar yayi yafara kyastawa saidai saboda iska da ya kyasta sai tamutu, saida yakyasta ashana kusan guda goma tana mutuwa ganin haka yasa megadi yace saidai muhad'e waje guda mukare yadda iska bazata shigaba da wannan shawarar sukayi amfani nan suka had'e wata irin k'ara suka dinga ji tana tashi a wajen ahaka suka kyasta ashanar, muryace suka juyo ana cewa kar kak'ona kabari zan tafi bazan sake dawowa ba kabarni ina gargad'inka kar kak'onata!!!
Saurin cinna wutar yayi a jikin layar tafara ci, k'abarin khausar saida yad'an girgiza nan wani bak'in hayak'i yafito daga ciki, layar na kusa cinyewa a hannunshi yayardata a k'asa daidai lokacin iskar da take wajen tadaina kad'awa komai yatsaya chak, jinjina kai megadin mak'abarta yayi yace lallai Annabi ya yi gaskiya tsafi gaskiya ne yana kama mutum yanzu daman da abinda aka k'ulla ma wannan baiwar Allah saisa tun bayan ita babu wanda aka sake rufewa a cikin k'abarin nan dan ko anrufe mutum wahala za'asha sai ma ancanza mashi waje.
Buzu megadi yace wallahi da gaskiyarka haka abun yake, kallon faruk yayi yace yanzu shikenan bazata sake kashe kowaba Jawahir ta dawo daidai
Hamdala faruk yayi nan suka maida k'asar ramin suka rufe sannan suka wuce godiya sukayi ma megadi sosai sannan suka tafi.
Biyawa yayi yasafke buzu megadi gidan da yake nan yatambayeshi gobe da k'arfe nawa zai wuce yace da asuba, kud'i yafiddo sosai yabashi yace yayi kud'in mota da tsaraba nan buzu yayi ta mashi godiya har da fita daga cikin mota yaduk'a yana godiya.
Faruk yace bakomai shine da godiya da yayarda yabiyoshi suka zo katsina.
A chan 'bangaren Jawahir Malam addu'o'i kawai yake yi mata, har a lokacin bata motsi sai wata irin zufa da take kwarara daga fuskarta jikinta zafi yayi sosai kamar me zazza'bi dan hucin zafin har su suna jinshi, daidai lokacin da Faruk ya k'ona layar taja dogon numfashi nan tafara atishawa, saida tayi ta fi goma.
Dawowar Faruk gidan ne tafarka tatashi zaune tana binsu da kallo daga k'arshe tasafke idanunta akan faruk da yashigo a daidai lokacin ahankali tabud'e baki tace me yake faruwa da ni? Kun rabani da Ammina ko?
A'a Jawahir ba rabaki mukayi da ita ba.
'Dan guntun murmushi ne tayi sannan tamik'e dak'yar tafito tsakar gidan duk su ma suka fito, wani part ne taje tabud'e tashiga taja tatsaya a tsakiyar parlorn lokaci guda tafara hawaye tajuyo takalli Faruk tace nan shine part d'inmu ni da Yaya Umar d'ina a nan muke rayuwarmu ammah Ammi tazo tarabamu wannan dalilin ne yasa nakasa cigaba da sonta, na sani kun rabani da ita bazan ta'ba damuwaba, kallonta tamaida ga Malam tace nagode sosai Malam.
Faruk cikin sanyin jiki yace Jawahir kakana ne wannan.
Murmushi tayi ahankali tasake cewa nagode.
Saurin goge hawayen da suke kwarara a fuskarta tayi sannan tafito daga d'akin tace ya kamata inje Kebbi inason ganin dangina wad'anda su kad'ai suka rage min dangi a duniya.
Dad yace a'a jawahir kibari sai kin samu sauk'i sannan kitafi, mu zamu rakaki wajen danginki.
Malam yace tabbas hakan yakamata dan nima kaina akwai wasu magunguna da zan d'aurata akansu na tsawon kwana biyu.
Faruk yace to kinji abinda yace dan Allah kizo mukoma gidanmu na tabbata mom zata kula da ke sosai.
Ita kanta ta san jikinta yana mata ciwo dan haka ta amince, ammah saida tafara shiga part d'in Abba taduba duk wasu file babu su, kallon Faruk tayi tai murmushi tace su Abba sun mutu ni kuma antafi da ni prison ummah tana asibiti sunyi amfani da duk wannan damar sun zo sun kwashe duk wani abu me amfani, saidai wannan ba shine a gabana ba, a yanzu na fi farin ciki da natabbatar su ma zasu mutu.
Faruk yace haka ne ina tayaki murnar samun 'yancin kanki jawahir.
Murmushi tasake yi a karo na biyu tace nagode.
A cikin motar da sukazo duk suka shiga suka koma gida, nan Malam yakawo maganin da yazo da shi yabata yace tadinga sha kullum sau ukku a rana na tsawon kwana biyu ne, godiya tayi mashi tare da su Dad, nan mom tadinga nan nan da ita.
Da marece Faruk yasanar da ita neman da akeyi mata akan dukiyarta tace bazata iya zuwa ba yau saidai zuwa gobe shima d'in yayarda da hakan dan saboda batada lafiya.
Bacci tadinga yi a ranar sallah kad'ai take tadata da kuma ta yi sai takoma.
Malam yace abarta duk na gajiya ne da kuma yanayin da take ciki.
Nan yakawo tsarabar da yakawo masu yabasu yayi masu nasiha da wa'azi dan duk zuwan da zaiyi ko idan sukaje sai ya yi masu nasiha akan suji tsoron Allah ga dukkan al'amurransu, sannan yakoma Daura.
Faruk shi kanshi wani irin dad'i yaji a ranshi a yanzu ji yayi kamar an cire mashi wata k'aya a jikinshi hankalinshi ya kwanta akan ku'butar jawahir saidai chan k'asan zuciyarshi kuma akwai abinda yake damunshi wanda yake da muhimmanci a rayuwarshi, kwance yayi d'akinshi yana tunani chan kuma yamaida idanunshi yalumshe.
Washe gari wajen k'arfe goma jawahir tafarka daga baccin da takoma bayan ta yi sallar asuba, Mom ce tahad'a mata ruwan wanka taje tayi bayan ta fito tasamu riga gown saman gadonta an ajiye mata, murmushi tayi tad'auki rigar taduba ta yi mata kyau sosai wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata tana cikin kallon rigar Mom taturo k'ofa tashigo hannunta rik'e da tray, ganin Jawahir tana hawaye yasa tayi saurin ajiye tray d'in ta iso wajen tana cewa jawahir lafiya? Me yafaru?
Batare da ta janye idanunta akan rigar ba tace akowane lokaci Ammi taje kasuwa tana siya min irin wad'annan rigunan saboda ta san d'iyarta tana sonsu sosai bazan ta'ba sanin ta siyo min ba saidai da na fito daga wanka inga ta d'aura min a saman gado wannan ne natuna a lokacin da naga rigar nan, a yanzu babu Ammi na rasa komai.
Matsowa Mom tayi tace duk uwa tana sanin abinda d'iyarta take so tabbas Amminki tana nan baki rasataba, saurin juyowa takalli mom tayi, Mom tace nice Amminki jawahir d'ana guda d'aya a duniya ko zaki iya kirana da Mummy.
Cikin sauri jawahir tafad'a jikin Mom tare da fashewa da kuka tace nagode sosai Mom nagode tabbas ke Mom d'ina ce nagode da wannan matsayin da kika bani zan cigaba da kiranki da mom har k'arshen rayuwata.
Wani irin sanyi Mom taji a cikin ranta cikin jin dad'i tace nagoe sosai Jawahir.
Faruk da yake tsaye a k'ofar d'akin zai shigo dan yasanar da Jawahir fitar da zasuyi jin abinda suke tattaunawa yasa yatsaya yana saurarensu, jingine kanshi yayi da bango yana murmushi sai kuma chan yawuce yabar wajen.
Mom taimaka mata tayi tashirya sannan tasata taci abinci bayan ta gama taruk'ota suka fito parlour takunna mata kallo tana yi suna d'an ta'ba hira
Faruk da Dad ne suka shigo suka gansu Dad yace lallai uwa da 'yarta suna nan suna ta kallo mu sunma mance da mu.
Murmushi Mom tayi tace to ya kuka iya kunsan dai babu me shiga tsakanin uwa da 'ya.
Faruk ya ji dad'in furucin Mom sosai yace toh tsakanin uwa da d'a fa?
Su dukansu dariya sukayi Mom tace kana kishi ne?
Jawahir zamowa tayi daga saman kujerar tagaishesu cikin girmamawa suka amsa mata nan su ma suka zauna suna ta hira ita dai murmushi kawai take yanayin family d'in yana burgeta.
Faruk ne yace to ke d'iyar Mom bazakice komai ba sai murmushi kawai kike yi.
Mom tace ina ruwanka sarkin sa ido.
Kallon Dad yayi yace kana ji ko Dad yanzu Mom ta daina ji dani ashe daman duk jin da ake da ni na rashin d'iyartane yanzu tunda ta zo ni anjefani a kwandon shara.
Yanayin yadda yayi maganar har Jawahir saida tayi dariya.
Mik'ewa yayi yace bari ma inyi tafiyata tunda abun haka yake tun kan Dad ma yajuya min ba, Dad yace a'a Son kayi hak'uri wa ne ni injuya maka baya.
Kallon agogon hannunshi yayi yace Allah Dad su Barr Nas suna jirana bari inje, kallon jawahir yayi yace da anjima idan nadawo zamu fita.
Amsawa tayi da toh.
Nan iyayen nashi sukayi mashi Allah yakiyaye.
Jawahir dai saidai kallonshi tayi batace komai ba.
Wajen k'arfe ukku suka fita da Jawahir sukajr kotu aka mallaka mata komai da yake hak'k'inta na hannunsu Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan sannan na wajen marigayi Abba ma da aka tattara aka mallaka mata matarshi bata tashi da komai ba saboda mallakin jawahir ne.
Filaye kusan biyar da gidaje hud'u sai motoci biyar tatashi da su sai mak'udan kud'in da aka saka mata a account d'inta aka bata takardun kamfaninta da komai, banda kuma gidansu da suke zaune da a yanzu yazama shima mallakinta.
Nan tayi godiya suka shiga mota suna cikin tafiya kallon Faruk tayi tace dan Allah ko zaka rakani gidan da su Nasiba suke zaune?
Shuru yayi kamar baiji abinda taceba saida tasake maimaita mashi sannan ya amince suka je daga nesa da gidan yayi parking yace taje kar tadad'e, yana kallo tad'ibi wasu file tafita da su baice mata komai ba dan baisan abinda zatayiba, da idanu yabita har tashiga cikin gidan.
Tana shiga tasamesu zaune a parlor su dukansu Mummy da yaranta ukku sunyi jugum dan mutane d'aid'aiya ne suke zuwan masu jaje basu ganetaba saboda sau d'aya suka ta'ba ganinta, yanayin yadda suka tarbeta ne yasa tagane haka.
Gaishesu tayi tace sunana Jawahir mekud'i.
Su dukansu jikinsu sanyi yayi dan a yanzu sun ganeta.
File d'in hannunta tamik'a masu tace ga wannan takardun gidanku ne namaido maku kukoma kuzauna kucigaba da rayuwa na mallaka maku shi halak malak, domin ko bakomai baku cancanci hakan daga gareniba bakuda laifi a ciki baidace arabaku da gidanku ba.
Hajiya maijidda ce kayi k'arfin halin cewa a'a jawahir ai mallakinki ne.
Biro tafiddo cikin jakkarta tayi signing tamik'a mata tace gashinan kusa hannu wallahi na baku halak malak kukoma kucigaba da rayuwarku bazan ta'ba amsa ba bai dace inkasance me son kainaba ku ma mutane ne kuna buk'atar raayuwar 'yanci na tabbata zakufi jin dad'in zaman chan dan Allah na rok'eku ku amsa, kuyi hak'uri da abinda yafaru na tabbata kunji babu dad'i a ranku.
Yaya sadiya ce tayi k'arfin halin amsa nan taduba su dukansu kuka suka fashe da shi sunayi mata godiya.
Nasiba da idanunta suke kumbure tace tabbas ke d'iyar mutinci ce jawahir baki dace ace iyayenki aka ci ma mutunci hakaba nayi nadamar kasancewar Dad a matsayin uba agareni domin shi mutum ne meson kanshi da yawa, na yi ma kaina alk'awali bazan ta'ba taka inda Daddy yakeba saboda abinda ya aikata me muni wanda yaja mana mutane suke kallonmu da abin, ya ja munrasa komai har da k'imarmu da ace ya hak'ura baibi son zuciya ba koda ace acikin k'aramin gida muke rayuwa zamu hak'ura muzauna domin ubangiji shi yanufemu da haka, kibar gidanki jawahir hak'k'inki ne kece kad'ai yadace kigajeshi.
Jawahir da tafara hawaye saboda tausayi girgiza kai tayi tace a'a Nasiba wallahi bazan amsaba na baku kyauta kuje kucigaba da zama kawai domin na tabbata da ace a lokacin ya nuna yanaso Abbu zai bashi kuma da ace Abbu yana raye bazai ta'ba bari kubar gidan ba, dan Allah na rok'eku kuzauna.
Su duka shuru sukayi suna mamakin irin halin jawahir ita aka zalunta ammah ita take binsu tana rok'onsu sukoma gidan.
Su duka har da mahaifiyarsu suka safko k'asa sunayi mata godiya bataji dad'in hakan ba tace sudaina nan tasa Nasiba tabata account number d'inta tayi mata transfer d'in 2millions, bayin Allahn nan suna kuka suna mata godiya ganin haka yasa tayi masu sallama su duka suka tashi dan su rakata tace a'a subarshi dan ta san Faruk bayaso suhad'u haka tafito tana goge k'wallah ta isa wajen motar Faruk da yake zaune yana waya ganinta yasa yakashe wayar tare da cewa wani abu sukayi maki?
Saida tashigo tarufe motar sannan tace a'a basuyi min komai ba.
Ammah me kikayi a gidan?.
Juyawa tayi takalli taga sannan tace na yi abinda yadace ne, sannan tajuyo tace dan Allah saura gidan Alhaji Mansur.
Da mamki yake kallonta yace wai me kike aikatawa mi kikayi da file d'in da kika fita da shi?.
Hawaye ne suka gangaro mata tace Yaya Umar sai kuma tayi shuru na d'an lokaci a karo na biyu tace Barrister tun ina k'arama Abbu yana kwatanta min akan taimakon nak'asa da kai musamman wanda yashiga cikin wani hali, ya sha yace min kar inbari wani yayi kuka a dalilina kar inbari wani yayi kuka ni kuma inyi dariya inkasance mutum me adalci a rayuwata.
Ajiyar zuciya yasafke dan tabbas ya gane file d'in mallaka ma su Nasiba shi tayi, rok'onshi tasake yi akan yataimaka yakaita gidan Alhaji Mansur yakaita kud'i da fili taba iyalanshi tare da maida masu motar da kotu ta amsa tashi nan suma sukayi ta mata godiya.
Faruk mamakin halayyar jawahir kawai yake tabbas a yanzu ya fahimci ita mutum ce me adalci wadda abun duniya bai rufe mata idanu ba inko hakane to tabbas halin iyayenta ne tagado
Koda suka koma gida Mom da Dad suka samu zaune a parlor suna jiransu, bayan sun zauna ne Jwahir tatattaro duka files d'in tamik'a ma Faruk banda guda d'aya daga ciki amsa yayi yana tambayar me zai mata da su, zataje ganin gidajen da filayen ne?
Batare da ta bashi amsaba taje tamik'a ma Dad gudan tare da zama k'asa gefen k'afarshi tace Dad wannan na kamfani ne na mallaka maka shi a hannunka domin nasan kaine kad'ai zaka iya kula da shi kamar yadda zaka kula da naka.
Jinjina kai Dad yayi yace shikenan jawahir na amshi wannan amanar zan kular maki da shi yadda yadace insha Allahu zan maido maki darajar kamfaninki kamar lokacin da mahaifinki yana raye.
Fashewa tayi da kuka tace nagode sosai Dad sai kuma kud'in da ke account d'ina zan turo maka sai ayi amfani da su wajen ha'b'bako kamfanin.
A'a jawahir