Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 74

18K to 21K   out of 220.3K words

kotu tasa Barr Faruk yagyara kalamanshi dan yana nema yazargi wani na daban bayan kuma kowa ya san itace tayi kisan tun daga mark d'in da ke jikin wad'anda aka kashe.
Jinjina kai Alk'ali yayi, Barr Faruk juyawa yayi yace ina neman afuwa ya me girma me shara'a saidai ni ina ganin har yanzu basu bada kwakkwarar shaida da tanuna jawahir ce tayi kisan ba,
Alk'ali yace miye hujjarka na cewa haka?
Barr Faruk yace saboda ko lokacin da su Barr muhsin suka rasu and'aura zargi akan wannan baiwar Allahn alhali lokacin tana nan gidan yari ana tsaronta taya zata fita har tayi kisa tadawo.
Barr MB a fusace yace ammah ai kowa yasan itace tayi.
Juyawa Barr Faruk yayi wajenshi yace shin a matsayinka na lauyan masu k'ara tunda su sunkasa yin magana munaso kafad'a mana a lokacin da jawahir tashiga gidajen mamatan ance wasu da dare takashesu shin ta wace hanya tashiga gidan alhali gidan rufe yake ko su basu rufe gidajen su?
Juyawa Barr MB yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a tambayoyin Barr Faruk sunyi ma masu shigar da k'ara tsauri saisa suka kasa bashi amsa sannan jawahir ana zarginta da yin layar zana ta wannan hanyar ne take zuwa tayi kisan, ya me girma me shara'a yakamata kotu taduba bayanina da yadda akayi jawahir takasa kare kanta a lokacin da nayi mata tambaya.
Alk'ali duk'awa yayi yai yan rubuce rubuce yad'ago yakalli jawahir yace shin ko zaki iya kare kanki akan tuhumar da akeyi maki?

Barr Faruk kallon jawahir yayi da take ta hawaye ta kasa cewa komai kowa ya zuba mata idanu yana jiran tayi magana chan dai tagirgiza kai, Barr Faruk maida kallonshi yayi ga Alk'ali yace ya megirma me shara'a muna nema kotu tataimaka mana tad'age k'arar nan zuwa zama na gaba domin akwai binciken da muke wanda bamu idaba a matsayina na lauyan wadda ake k'ara kuma saboda k'arancin lokacin zuwana bai sa nasamu na ida bincike na ba ina neman wannan alfarmar kotu taduba min.
Murmushin nasara Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a yakamata kotu tayi watsi da wannan alfarmar da barristern wadda ake k'ara yanema domin baida wata kwakkwarar shaida da zai iya kare wadda ake k'ara da ita, munaso kotu ta gaggauta yanke ma wadda ake k'ara hukuncin da yadace da ita.
Shuru Kotun tayi har saida alk'ali yagama rubuce rubucenshi yad'ago yace barrister Faruk kotu ta amshi uzurinka a matsayin lauyan wadda ake k'ara wanda bai dad'eba da tsaya mata dan haka kotu ta baka dama kaje kakawo mata kwakkwaran shaidar da kace ba ita tayi kisan ba, zamu d'age wannan k'arar zuwa 2 ga wata nagaba watau wata d'aya me zuwa insha Allahu shi muke fata yakasance zama na k'arshe,,,,yana fad'in haka yabubbuga table.
Barr Faruk wani irin dad'i yaji a ranshi dan yasan wannan hanyar kawai zaibi yaku6utar da jawahir saboda baida hujjar da zai iya kareta, inda shikuma Barr MB yaji kamar yabuge kowa saboda haushi.

Jawahir fashewa tayi da kuka dan ba haka tasoba haka matan suka riketa suka tafi da ita prison.

Haka aka tashi Shari'a masu murna sunayi masu bak'in ciki suna yi.


_*Free page*_


_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_

_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_


_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_






_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/11, 21:25] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......*



_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_



*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]



*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*


*PAGE NINE*

Barr MB suna fita yanufi wajen Barr Faruk da yake shirin shiga motarshi yana zuwa murmushi yayi yace Barrister kenan wane tsotsai yakaika tsaya ma Jawahir ina ce ko ka gaji da rayuwarka ne saisa?.
Shima murmushin yayi yace kusan haka dan daman ita mutuwa akowane lokaci zuwa takeyi.
Tab'e baki yayi yace hakane daman ashe kaine lauyanta shine kazo kabugi ta cikina kaji sirrina?
Cikin rashin damuwa yace wannan ai ba wani abu bane tunda duk cikin aikinmu ne.
"Na san da haka saidai kai na san bakasan komai ba akan case d'in jawahir dan haka Kataimaka ma kanka kajanye daga tsaya mata".
Kar kadamu barrister kai shaida ne bana bayan k'arya akowane lokaci bayan gaskiya nakebi dan haka kai zan ba shawara kajanye kar kad'aure ma k'arya gindi inma kud'i aka baka kamaida masu abinsu.
Barr MB Katseshi yayi yace kai kana ganin kaine akan gaskiya nima haka nake gani dan haka muhad'e kawai wata me kamawa idan Allah ya sa rayuwarka ta kai.
Dariya Barr Faruk yayi yace toh Allah yakaimu nan yabud'e motarshi yashiga yabar Barr MB duk haushi ya cikashi.

Barr Faruk yana komawa gida wanka yayi yashirya yafita parlour dan yayi lunch momcy ce tafito tana fara'a tace Son har andawo?
Zama yayi saman cushion cike da nuna gajiya yace Eh Momcy.
Itama zama tayi gefenshi cikin nuna tausayawarta tace sannu son da alama ka gaji dayawa ina fata dai anyi nasara?
Murmushi yayi yafad'a ma momcy yadda akayi,,,ta tausaya ma jawahir sosai koda bai fad'a mata ainahin abinda akayiba ya 6oye mata dan kar tatada hankalinta tanuna bata yadda ba yasa yace mata kawai zarginta akeyi da laifin kisa kuma baya tunanin ita tayi saboda yarinya ce k'arama.
Addu'a tayi akan Allah yataimaka yaku6utar da ita idan har batada laifi aciki.
Ya amsa mata da Ameen.
Fitowar Daddy ne yasa suka gaisa shima yayi mashi sannu da dawowa sannan suka d'unguma zuwa dining area dan suyi lunch, suna cikin yi Dad yakalleshi yace Son gobe fa za'ayi baikonka da Nasiba.
Murmushi yayi me nuna jin dad'i yace toh Daddy na gode sosai, wata nawa za'a tsaida bikkin?
Shuru Daddy yayi sai chan yace ina tunanin bazai wuce wata ukku ba dan Dad d'inta ya ce bayaso aja lokaci dayawa kuma mu ma bamuda matsala mun gama shirinmu tunda hatta gida kana da shi.
Momcy tace hakane Alhaji nima kaina bansan aja lokaci dayawa saisa nanuna farin cikina da akace baza'a fi wata ukku ba.
Faruk yana jinsu saidai yayi murmushi yacigaba da cin dinner d'inshi.


Bayan sallar la'asar yana dawowa daga masallaci ko gida bai shigaba yashiga motarshi yabar gidan yakama hanyar prison.

Jawahir tunda aka maidata a cikin d'an kurkukun d'akinta bajewa tayi a k'asa tana wani irin kuka me cike da k'ara, duk tacika wajen da kuka wasu ma'aikatan gidan ne sukazo da manyan bulalai suka sameta nan suka kwatsa mata tsawa sukace tayi masu shuru dakyar ta iya danne kukan nata saidai hawaye da take idanuwanta duk suka k'ank'ance maida idanuwanta tayi tarufe bata sake bud'e suba saida Barr Faruk yazo batare da ta bud'e idanunba tana jin abud'e k'ofar anshigo cikin muryar kuka tace bance maka kar ka kuskura kashiga acikin wannan maganar ba? Sau nawa nafad'a maka mutuwata tafi rayuwata amfani, Miyasa bazaka ji maganar da mutane suke fad'a ba akaina, dakyar tabud'e idanunta tace barina in rayuwa a doron k'asa tamkar kashe d'an maciji ne ba'a sare kanshiba, shawara zan baka kabi maganar da sauran mutane suka fada maka karabu da ni gudun kar matsalata ta shafeka.
Matsowa yayi kusa da ita cikin sanyin jiki yace jawahir ban damuba kowace irin matsala tasameni dan ni na riga da nasa ma raina ina da burin taimakonki komai zan iya yi dan ganin kin fita daga gidan nan saboda zama nan baidace dakeba.
Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tace Barrister Kaine kake ganin haka ammah ni rayuwata a cikin d'akin nan ta fiye min kwanciyar hankali akan bala'in da nake ciki wanda barina gidan nan zai iya shafar kowa.
Cike da mamaki Barr Faruk yace wane irin bala'i ne kike ciki haka? Shin ko zani iya saninshi?
Tashi tayi zaune tace saninshi zai iya sa kaima yashafeka bazan gaji da fad'a makaba kanisantar da kanka daga gareni.
Jawahir nayi maki alk'awalin zan taimaka maki da dukkan k'arfina.
'Dan guntun murmushi tayi tare da janye kanta gefe.
Barr Faruk yace nasan ba lallai ne kiyarda daniba dan kina min kallon kamar halayyata iri d'aya ce da tasu barrister muhsin saidai ni ba haka nakeba kiyarda da ni.
Girgiza kai tayi tace ba na ji akwai wanda zan iya yarda da shi a wannan lokacin har zuwa k'arshen rayuwata.
Jawahir ya kamata kifahimceni banzo da niyar cuta agarekiba kitaimaka kiban had'in kai dan inwanke ki daga zargin da duniya takeyi maki.
Wani irin kallo tayi mashi tace zargi kuma? Wanene yafad'a maka zargi ne?
Koma minene Jawahir ina da burin taimaka ma rayuwarki,
shuru tayi na d'an lokaci kamar tana nazarin wani abu sai chan tayi murmushi tare da goge hawayenta kamar ba ita bace tagama kuka tace shikenan tunda ka ce zaka taimaka min saidai duk matsalar da kashiga kar kayi kuka da kowa sai kanka.
Cikin nuna rashin damuwa yace na amince da haka, dan haka inaso kiban tarihin rayuwarki.
Mik'ewa tayi tsaye tana tafiya dakyar har ta isa wajen yar k'aramar tagar da take yawan tsayawa wajenta,,ganin kamar bataji abinda yaceba yasa Barr Faruk yasake maimaita mata.
'Dan guntun murmushi tayi batare da ta juyoba tace na amince zan fad'a maka tarihin rayuwata ammah ba anan ba saidai idan zaka fitar da ni daga kurkukun nan muje wani waje dan Indai a nan ne na tabbata zamu shiga matsala daga ni har kai dan matsalata zata iya shafarka, bazata ta'ba barinkaba.
Shuru Barr Faruk yayi kamar yana nazarin maganarta sai chan yace wace irin matsala zata shafeni?
Kowace irin matsala zata iya shafarka Indai har kanason jin tarihina saidai kayi yadda nace maka.
Ajiyar zuciya yasafke yace shikenan Jawahir zan kwatanta hakan zanje in nemi amincewar shugaban gidan nan in ya amince sai mu fita muje wani wajen zuwa gobe.

Baya baya tafara ja lokaci guda muryarta tafara rawa tace kayi gaugawan barin wajen nan yanzu.
Da mamaki yake kallonta yace saboda me?
Juyowa tayi fuskarta cike da tashin hankali cikin d'aga murya tace na ce kabar wajen nan katashi kafita!
Ganin yadda lokaci guda tabirkice yasa yamik'e yawuce yafita cike da mamaki, bayanshi Jawahir tabi cikin sauri tajanyo k'ofar tarufe tare da ja da baya ahankali taje chan wajen kusurwar d'akin tatsaya jikinta gaba d'aya rawa yake nan tayi saurin zama tare da dunk'ule jikinta waje guda tadafe kanta da dukkan hannuwanta.
Barr Faruk yana tsaye yana kallonta ta 'yan hudojin k'ofar yana jiyo sautin kukanta ahankali da magana wadda bazaice ga abinda take cewaba chan kuma sai yaji ta shuru.

Ji yayi kamar yashiga d'akin dan yagane ma idanunshi abinda yake faruwa da ita sai kuma yafasa yawuce suka tafi.

Yana fita direct office d'in shugaban gidan yarin yawuce yana zuwa yashiga lokacin wasu files ne hannun Alhaji mahadi yana dubawa yana ganinshi Murmushi yayi yace ya dai abokina har ka gama?
kujera faruk yaja yazauna yace abokina dan Allah wata alfarma nazo nema a wajenka.
Alhaji Mahadi yace haba alfarma kuma? Ina jinka
Numfasa yayi yace Jawahir nakeso ataimaka a ara min ita zuwa gobe zan fita da ita saboda zan d'auko wani bayani ne wanda itace zata taimaka min wajen d'aukoshi a matsayina na lauyanta.
Zaro ido mahadi yayi yace fita fa kace zakayi da ita daga gidan yarin nan?
Cikin nuna rashin damuwa yace Eh kuma insha Allahu da nagama abinda zanyi zan maidota.
Girgiza kai mahadi yayi yace kayi hak'uri Barrister gaskiya hakan bazai yuwuba kafita da ita dan tana cikin tsaro me tsanani fita da ita laifi ne a k'a'idar aikin nan ba'a fita da me laifi indai ba asibiti ko court za'aje ba.
Na san da haka abokina taimaka min zakayi insha Allahu zan maido ta bazan dad'eba ina gama d'aukar bayanan da zan d'auka zan gurfanar da ita a wajenku, nayi maka alk'awalin haka kataimaka min ko dan amincin da ke tsakaninmu muyi abun mugama batare da sanin kowaba.
Iska yafuzgar yace gaskiya dan dai Kaine saisa zan amince ammah katabbatar ka maidota dawuri gudun kar wata matsala tafaru banaso kowa yasan kun fita.
Cikin jin dad'i Barr Faruk yace kar kadamu abokina insha Allahu zanyi k'ok'arin haka.
Toh shikenan Allah yakaimu
Cikin jin dad'i yace Ameen Nagode sosai sai goben idan na zo.
Nan yamik'a mashi hannu sukayi sallama yatafi.


Tafiya yake a cikin motarshi a hankali ba wani gudun kirki yakeba kallon mirror da zaiyi sai gani yayi kamar wannan tsohuwar ce zaune a bayan sit d'in motar saurin waigawa yayi yakalla sai baiga kowaba yak'ara kallon mirror yaga gatanan dai zaune kanta sadde a k'asa wani irin burki yaja yatsaya ba dan Allah ya taimakeshiba da ya fad'a ma motar da take gabanshi, juyowa yayi gabad'aya yakalli bayan sit din ammah baiga kowaba yak'ara kallon mirror nan ma baigantaba a wannan lokacin ajiyar zuciya yasafke tare da Jingine kanshi a jikin kujerar cikin ranshi yace idanuwanshi ne sukayi mashi gizo dan tana ranshi ne, saidai me miyasa jawahir tasan da maganar tsohuwar kodai itama jawahir ba mutum bace,,,kwankwasa mashi glass akayi yai saurin bud'e idanunshi sai gani yayi fiitt wani abu ya wuce ammah baiga ko menene ba fitowa yayi daga motarshi yana dubawa babu kowa sai yan motocin da suke wucewa jefi jefi dan haka ne yakoma cikin motar yatada yatafi ammah yana ta mamaki wanene yakwankwasa mashi glass d'in mota.

Yana cikin tuk'i Nasiba takirashi a waya yana yin picking yai sallama bayan sun gaisa ne tafara yi mashi tsegumin rashin zuwa murmushi yayi yace Sweetheart ganinan yanzu hope dai kina gida?
Cike da jin dad'i tace Eh ina gida lovely sai ka iso.
Yace ohk kiban minti biyar insha Allahu na iso.
Toh Allah yakawo min kai Allah.
Ameen sweetheart.

Yana gama wayar ya ajiyeta yacigaba da tuk'in shi a nutse har ya isa gidansu Nasiba yana yin parking a harabar wajen da ake ajiye motoci kiranta yayi a waya yace tafito gashi.

Suna gama wayar yanufi wajen wasu plastic chair yazauna chan sai ga Nasiba ta fito tana yafiyarta me jan hankali idanu yazuba mata yana kallonta cike da shauk'in sonta dan har cikin ranshi yake jin son Nasiba shi a tsarin rayuwarshi bai damu da kyakkyawar maceba shidai nutsatstsa me hankali kawai yakeso me addini ahaka har ta iso bai saniba yana ta tunani saida tahura mashi iska a fuska sannan yadawo cikin hankalinshi yasakar mata Murmushi.
Zama tayi itama tana murmushin tace Lovely tunanin me kakeyi haka?
Lumshe idanunshi yayi yabud'e sannan yace tunanin sweetheart d'ina nake.
Murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai lovely ammah sai inga kamar yanzu ka rage damuwa da ni, dan kwananka biyu bakazo mukaga junaba saidai muyi waya.

Girgiza kai yayi yace kod'aya Sweetheart a kowane lokaci kina a cikin raina kawai dai kwana biyu shara'a tasani a gaba.
Cikin sanyin jiki tace to shikenan ammah dan Allah kadinga zuwa ina ganinka ko zan samu sauk'i a raina.
Toh shikenan sweetheart zan dinga zuwa ko dan saboda nima ganinki yana sa min nutsuwa inrage yawan tunaninki.
Wata dank'areriyar mota ce tashigo a gate d'in gidan nan duk suka zuba ma motar idanu Barr Faruk yace Allah yasa ba Dad bane yadawo.
Murmushi Nasiba tayi dan ta sanshi sarai bayaso suna had'uwa da Dad wai kunyarshi yakeji tace aiko bashi bane ammah yana nan cikin gida.
Yana shirin bud'e baki yayi tambaya nan driver d'in motar yayi saurin fitowa yazo yabud'e bayan motar wanda yafito ne yasa Barr Faruk yagirgiza saida mamaki yabayyana a idanunshi, shima mutumin kallonshi yake yana murmushi har ya iso ta wajen Barr Faruk bai saniba saida yaji Nasiba tana gaisheshi sannan yadawo cikin hayyacinshi yad'an rissinar da kanshi ya gaisheshi amsawa yayi fuska a sake sannan yawuce yanufi cikin gidan Barr Faruk da kallo yabishi inda shima mutumin yajuyo yakalleshi yana mashi murmushi sannan yajuya yashige.
Yana shigewa yayi saurin juyowa yakalli Nasiba da itama take kallonshi yace Sweetheart wanene wannan?
Murmushi tayi tace aminin Dad d'ina ne nasan zuwa yayi suyi magana akan ranar aurenmu da za'a tsaida dan duk yadda yace haka za'ayi saboda Dad gabad'aya shi yamik'a ma ragamar komai.

Damuwa ce tabayya k'arara a fuskar Faruk ammah yayi k'ok'arin boyeta tabbas shine mutumin da yasameshi bayan sun fito daga kotu yana tafiya a hanya zai koma gida yazo yashigar da motarshi a gaban tashi yatare mashi hanya kan dole yatsaya yafito cike da jin haushi yajingina da motarshi yana jira yaga wanene yai mashi haka.
Anyi kusan minti ukku sannan driver d'in yabud'e mota yafito yazagaya yabud'e bayan motar wani Alhaji ne yafito yana tafiya cikin isa ya iso wajen Barr Faruk da mamakin Barr Faruk sai ji yayi ya kira sunanshi batare da ya amsaba yazuba mashi idanu yana kallonshi murmushi mutumin yayi yace nasan zakayi mamakin ganina dan baka sanniba saidai ni na sanka.
Cigaba yayi da kallonshi batare da ya ce komai ba.
Mutumin yacigaba da cewa sunana Alhaji Mansur Mai harka da dollars,
Cikin rashin damuwa Barr Faruk yace me kake buk'ata a wajena da kazo katare min hanya?
Murmushi yayi a karo nagaba yace babu abinda nake buk'ata saidai ina so inmaka gargad'i akan kajanye maganar tsayawa yarinyar nan da muke k'ara akan kisan da tayi dan muna bin jinin 'yan uwanmu munaso akasheta kamar yadda itama takashe ba wai gwaninta bane dan ka tsaya mata kaima kanka baka wuce takashekaba kamar yadda takashe sauran lauyoyin ta.
Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace nagode da shawararka nan yajuya zai tafi mutumin yace ammah naga kamar baka d'au shawarar ba ko?
Juyawa Barr Faruk yayi yace kusan haka.
Jinjina kai mutumin yayi yace haka nagani saidai ya zama dole kad'au shawarar dan babu wanda ya isa yatsaya mata kamar yadda takashesu Itama ya zama dole ad'au *FANSAR RAI* akanta.
Murmushi Barr Faruk yayi a

7 / 74