Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
dukkan al'amurransu, sannan yakoma Daura.
Faruk shi kanshi wani irin dad'i yaji a ranshi a yanzu ji yayi kamar an cire mashi wata k'aya a jikinshi hankalinshi ya kwanta akan ku'butar jawahir saidai chan k'asan zuciyarshi kuma akwai abinda yake damunshi wanda yake da muhimmanci a rayuwarshi, kwance yayi d'akinshi yana tunani chan kuma yamaida idanunshi yalumshe.
Washe gari wajen k'arfe goma jawahir tafarka daga baccin da takoma bayan ta yi sallar asuba, Mom ce tahad'a mata ruwan wanka taje tayi bayan ta fito tasamu riga gown saman gadonta an ajiye mata, murmushi tayi tad'auki rigar taduba ta yi mata kyau sosai wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata tana cikin kallon rigar Mom taturo k'ofa tashigo hannunta rik'e da tray, ganin Jawahir tana hawaye yasa tayi saurin ajiye tray d'in ta iso wajen tana cewa jawahir lafiya? Me yafaru?
Batare da ta janye idanunta akan rigar ba tace akowane lokaci Ammi taje kasuwa tana siya min irin wad'annan rigunan saboda ta san d'iyarta tana sonsu sosai bazan ta'ba sanin ta siyo min ba saidai da na fito daga wanka inga ta d'aura min a saman gado wannan ne natuna a lokacin da naga rigar nan, a yanzu babu Ammi na rasa komai.
Matsowa Mom tayi tace duk uwa tana sanin abinda d'iyarta take so tabbas Amminki tana nan baki rasataba, saurin juyowa takalli mom tayi, Mom tace nice Amminki jawahir d'ana guda d'aya a duniya ko zaki iya kirana da Mummy.
Cikin sauri jawahir tafad'a jikin Mom tare da fashewa da kuka tace nagode sosai Mom nagode tabbas ke Mom d'ina ce nagode da wannan matsayin da kika bani zan cigaba da kiranki da mom har k'arshen rayuwata.
Wani irin sanyi Mom taji a cikin ranta cikin jin dad'i tace nagoe sosai Jawahir.
Faruk da yake tsaye a k'ofar d'akin zai shigo dan yasanar da Jawahir fitar da zasuyi jin abinda suke tattaunawa yasa yatsaya yana saurarensu, jingine kanshi yayi da bango yana murmushi sai kuma chan yawuce yabar wajen.
Mom taimaka mata tayi tashirya sannan tasata taci abinci bayan ta gama taruk'ota suka fito parlour takunna mata kallo tana yi suna d'an ta'ba hira
Faruk da Dad ne suka shigo suka gansu Dad yace lallai uwa da 'yarta suna nan suna ta kallo mu sunma mance da mu.
Murmushi Mom tayi tace to ya kuka iya kunsan dai babu me shiga tsakanin uwa da 'ya.
Faruk ya ji dad'in furucin Mom sosai yace toh tsakanin uwa da d'a fa?
Su dukansu dariya sukayi Mom tace kana kishi ne?
Jawahir zamowa tayi daga saman kujerar tagaishesu cikin girmamawa suka amsa mata nan su ma suka zauna suna ta hira ita dai murmushi kawai take yanayin family d'in yana burgeta.
Faruk ne yace to ke d'iyar Mom bazakice komai ba sai murmushi kawai kike yi.
Mom tace ina ruwanka sarkin sa ido.
Kallon Dad yayi yace kana ji ko Dad yanzu Mom ta daina ji dani ashe daman duk jin da ake da ni na rashin d'iyartane yanzu tunda ta zo ni anjefani a kwandon shara.
Yanayin yadda yayi maganar har Jawahir saida tayi dariya.
Mik'ewa yayi yace bari ma inyi tafiyata tunda abun haka yake tun kan Dad ma yajuya min ba, Dad yace a'a Son kayi hak'uri wa ne ni injuya maka baya.
Kallon agogon hannunshi yayi yace Allah Dad su Barr Nas suna jirana bari inje, kallon jawahir yayi yace da anjima idan nadawo zamu fita.
Amsawa tayi da toh.
Nan iyayen nashi sukayi mashi Allah yakiyaye.
Jawahir dai saidai kallonshi tayi batace komai ba.
Wajen k'arfe ukku suka fita da Jawahir sukajr kotu aka mallaka mata komai da yake hak'k'inta na hannunsu Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan sannan na wajen marigayi Abba ma da aka tattara aka mallaka mata matarshi bata tashi da komai ba saboda mallakin jawahir ne.
Filaye kusan biyar da gidaje hud'u sai motoci biyar tatashi da su sai mak'udan kud'in da aka saka mata a account d'inta aka bata takardun kamfaninta da komai, banda kuma gidansu da suke zaune da a yanzu yazama shima mallakinta.
Nan tayi godiya suka shiga mota suna cikin tafiya kallon Faruk tayi tace dan Allah ko zaka rakani gidan da su Nasiba suke zaune?
Shuru yayi kamar baiji abinda taceba saida tasake maimaita mashi sannan ya amince suka je daga nesa da gidan yayi parking yace taje kar tadad'e, yana kallo tad'ibi wasu file tafita da su baice mata komai ba dan baisan abinda zatayiba, da idanu yabita har tashiga cikin gidan.
Tana shiga tasamesu zaune a parlor su dukansu Mummy da yaranta ukku sunyi jugum dan mutane d'aid'aiya ne suke zuwan masu jaje basu ganetaba saboda sau d'aya suka ta'ba ganinta, yanayin yadda suka tarbeta ne yasa tagane haka.
Gaishesu tayi tace sunana Jawahir mekud'i.
Su dukansu jikinsu sanyi yayi dan a yanzu sun ganeta.
File d'in hannunta tamik'a masu tace ga wannan takardun gidanku ne namaido maku kukoma kuzauna kucigaba da rayuwa na mallaka maku shi halak malak, domin ko bakomai baku cancanci hakan daga gareniba bakuda laifi a ciki baidace arabaku da gidanku ba.
Hajiya maijidda ce kayi k'arfin halin cewa a'a jawahir ai mallakinki ne.
Biro tafiddo cikin jakkarta tayi signing tamik'a mata tace gashinan kusa hannu wallahi na baku halak malak kukoma kucigaba da rayuwarku bazan ta'ba amsa ba bai dace inkasance me son kainaba ku ma mutane ne kuna buk'atar raayuwar 'yanci na tabbata zakufi jin dad'in zaman chan dan Allah na rok'eku ku amsa, kuyi hak'uri da abinda yafaru na tabbata kunji babu dad'i a ranku.
Yaya sadiya ce tayi k'arfin halin amsa nan taduba su dukansu kuka suka fashe da shi sunayi mata godiya.
Nasiba da idanunta suke kumbure tace tabbas ke d'iyar mutinci ce jawahir baki dace ace iyayenki aka ci ma mutunci hakaba nayi nadamar kasancewar Dad a matsayin uba agareni domin shi mutum ne meson kanshi da yawa, na yi ma kaina alk'awali bazan ta'ba taka inda Daddy yakeba saboda abinda ya aikata me muni wanda yaja mana mutane suke kallonmu da abin, ya ja munrasa komai har da k'imarmu da ace ya hak'ura baibi son zuciya ba koda ace acikin k'aramin gida muke rayuwa zamu hak'ura muzauna domin ubangiji shi yanufemu da haka, kibar gidanki jawahir hak'k'inki ne kece kad'ai yadace kigajeshi.
Jawahir da tafara hawaye saboda tausayi girgiza kai tayi tace a'a Nasiba wallahi bazan amsaba na baku kyauta kuje kucigaba da zama kawai domin na tabbata da ace a lokacin ya nuna yanaso Abbu zai bashi kuma da ace Abbu yana raye bazai ta'ba bari kubar gidan ba, dan Allah na rok'eku kuzauna.
Su duka shuru sukayi suna mamakin irin halin jawahir ita aka zalunta ammah ita take binsu tana rok'onsu sukoma gidan.
Su duka har da mahaifiyarsu suka safko k'asa sunayi mata godiya bataji dad'in hakan ba tace sudaina nan tasa Nasiba tabata account number d'inta tayi mata transfer d'in 2millions, bayin Allahn nan suna kuka suna mata godiya ganin haka yasa tayi masu sallama su duka suka tashi dan su rakata tace a'a subarshi dan ta san Faruk bayaso suhad'u haka tafito tana goge k'wallah ta isa wajen motar Faruk da yake zaune yana waya ganinta yasa yakashe wayar tare da cewa wani abu sukayi maki?
Saida tashigo tarufe motar sannan tace a'a basuyi min komai ba.
Ammah me kikayi a gidan?.
Juyawa tayi takalli taga sannan tace na yi abinda yadace ne, sannan tajuyo tace dan Allah saura gidan Alhaji Mansur.
Da mamki yake kallonta yace wai me kike aikatawa mi kikayi da file d'in da kika fita da shi?.
Hawaye ne suka gangaro mata tace Yaya Umar sai kuma tayi shuru na d'an lokaci a karo na biyu tace Barrister tun ina k'arama Abbu yana kwatanta min akan taimakon nak'asa da kai musamman wanda yashiga cikin wani hali, ya sha yace min kar inbari wani yayi kuka a dalilina kar inbari wani yayi kuka ni kuma inyi dariya inkasance mutum me adalci a rayuwata.
Ajiyar zuciya yasafke dan tabbas ya gane file d'in mallaka ma su Nasiba shi tayi, rok'onshi tasake yi akan yataimaka yakaita gidan Alhaji Mansur yakaita kud'i da fili taba iyalanshi tare da maida masu motar da kotu ta amsa tashi nan suma sukayi ta mata godiya.
Faruk mamakin halayyar jawahir kawai yake tabbas a yanzu ya fahimci ita mutum ce me adalci wadda abun duniya bai rufe mata idanu ba inko hakane to tabbas halin iyayenta ne tagado
Koda suka koma gida Mom da Dad suka samu zaune a parlor suna jiransu, bayan sun zauna ne Jwahir tatattaro duka files d'in tamik'a ma Faruk banda guda d'aya daga ciki amsa yayi yana tambayar me zai mata da su, zataje ganin gidajen da filayen ne?
Batare da ta bashi amsaba taje tamik'a ma Dad gudan tare da zama k'asa gefen k'afarshi tace Dad wannan na kamfani ne na mallaka maka shi a hannunka domin nasan kaine kad'ai zaka iya kula da shi kamar yadda zaka kula da naka.
Jinjina kai Dad yayi yace shikenan jawahir na amshi wannan amanar zan kular maki da shi yadda yadace insha Allahu zan maido maki darajar kamfaninki kamar lokacin da mahaifinki yana raye.
Fashewa tayi da kuka tace nagode sosai Dad sai kuma kud'in da ke account d'ina zan turo maka sai ayi amfani da su wajen ha'b'bako kamfanin.
A'a jawahir banason kud'inki ni zanyi maki komai da aljihuna domin ko bakomai akwai amana tsakanina da mahaifinki.
Duk da haka Dad na fi so ayi da dukiyar nan domin hankalina zaifi kwanciya,.
Katseta Dad yayi yace dangin mahaifiyarki suna buk'atar wani abu daga gareki.
Dad zan basu zan raba dukiyar ukku inbasu kashi guda sauran sai ayi amfani da ita.
A'a jawahir tunda dai kin nace zan amshi kashi d'aya kibasu d'aya, sauran kuma kiyi amfani da ita.
Ganin bataso tacigaba da yi mashi gardama amatsinyishi na babba yasa ta amince da hakan.
Kallonta tamaida ga Faruk da yake jiran jin abinda zatace akan files d'in da tabashi, murmushi tayi tace wannan kuma kaza'bi gida d'aya da fili guda duk na mallaka maka sannan Dad yad'auki mota guda Mom kuma abata fili d'aya, na san kunfi k'arfin hakan ammah nima na baku ne saboda Allah dan ni kaina na san banda abinda zan iya biyanku da shi saidai addu'a
Su duka sukace a'a bazasu d'auki komai ba tayi amfani da abunta duk yadda taso sud'auka ammah suka k'i dan haka tafitar da gida da mota tace zata mallaka su ga Ummah dan ko bakomai uwace gareta.
Nan suka amince da hakan indai har ita zata ba babu matsala saboda ta cancanta saboda matsayinta.
Bayan sun gama tattaunawane take sanar da su gobe takeso tawuce Kebbi nan suka nuna basu yarda ba, nacewa tayi da hakan saboda garin ji take duk ya gundureta komai ji take babu dad'i tunda tafito daga gidan yarin ba dan komai ba sai dan rashin wani makusancinta a cikin garin, wannan dalilin ne yasa tanace.
daga k'arshe dai suka amince ba dan sun so ba sukace Allah yakaimu, sai kowa yakasance cikin shiri gobe sai muje Kebbi ammah ta flight zamu bi, inyaso sai insa driver yatafi da motar da kikeso atafin maki da ita chan, kai kuma Faruk a yau kaje kayi mana booking d'in jirgi.
Toh Dad insha Allahu.
Jawahir godiya tayi masu sosai har da k'wallarta nan Mom talallasheta sukace tadaina kuka.
Da marece tare da Mom suka shiga kitchen tatayata girkin dare, Mom jin son yarinyar take a cikin ranta ji take ina ma ace d'iyarta ce dan a rayuwarta tana son 'ya'ya mata saidai ubangiji bai bataba sai d'a d'aya tilo.
Wajen k'arfe tara Jawahir tana kwance a chan part d'in mummy kallon agogo tayi nan tamik'e tad'auko hijab d'inta tasaka tafito a main parlor, tana safkowa tasamu Faruk zaune yana dannar waya, Murmushi tayi tataka ta isa wajen da yake tayi sallama.
Sai a lokacin yalura da ita nan ya amsa yace daman bakiyi bacci ba?
Zama tayi tace Eh na kasa baccin ne.
Idanu yazuba mata yace meyasa kika kasa?
ina tunani sai zuwa anjima,,, tabashi amsa.
Ajiyar zuciya yasafke yace ammah Jawahir bazaki hak'ura da tafiyar nan ba sai zuwa jibi, kinga gobe na so kije kiga filayenki da gidajen sannan gidanku ya kamata afitar da duk kayan da suke ciki.
Duk'ar da kanta tayi k'asa tace ba damuwa Yaya Umar kai zaka iya.....saurin d'ago kai tayi tace am yi hak'uri wlh na saba cewa yaya umar ne.
Murmushi yayi yace ba damuwa nima ai Umar d'inne ko kin mance?
Murmushin itama tayi tace kaima yayanane ammah saidai ince Yaya Faruk.
A karo na biyu yayi murmushi yace nagode sosai jawahir da wannan matsayin da kika bani daman kinga ban da kowa ni kad'ai ne wajen iyayena sai 'ya'yan k'anwar iyayena.
Jawahir tace Allah sarki, ashe bakasan dad'in k'anneba.
Tarar numfashinta yayi yace au ke kin sani ashe?
Dariya tayi har saida hak'oranta suka bayyana tace ina fa nasani, ni dai gobe zan tafi Kebbi.
Hmmm kedai kin k'agara kitafi kamar wani abu muke maki to wai ma kin san inda suke zaune?
Eh Man a cikin garin Fanah a lantarki, ko da ba lallaine ingane gidan ba ammah gidan ba wani me wuyar ganewa bane da ance gidan Malam me salati duk an sanshi acikin lantarki.
Toh shikenan goben sai muje ammah naso kije kigano gidajen, ko zaki shirya tun da wuri mufara zuwa.
Girgiza kai tayi tace a'a Yaya Faruk bazan iyaba ni fa duk sun fita raina banason ganin gidajen da filayen,
K'wallar da yaga sun cika mata idanu ne yasa yace shikenan Jawahir ya kikeso ayi maki da su a aje maki har sai ranar da kikazo katsina?.
Shuru tayi sai chan tace cikin gidajen aba Ummah guda sannan duk kayan da suke cikin gidanmu na mallaka mata su tasa akwashe sannan abata mota guda sai kuma kud'i zan turo a account wanda za'a basu na maganinta.
Faruk jinjina ma jawahir yayi sosai irin tausayinta da son taimako tabbas ba kowa ne zai iya irin haka ba, yace toh shikenan jawahir zanyi duk yadda kikeso.
Nan yafiddo wayarshi yace bari kiga wani abu, gidaje ne guda hud'u da filaye ukku sai motoci ukku duk yagwada mata taduba tace wad'annan fa?.
Kallonta yayi yace d'azu naje nagano su shine nad'auko maki su hoto dan na san wannam zumud'in na son zuwa kebbi bazai barki kije ganosuba kuma sai gashi hakan.
Dariya tayi tace kai dai ko Barrister.
Idanu yazuba mata yace nidai me?
Girgiza kai tayi tace bakomai sannan takalli agogo tace bari inje inkwanta dare ya yi fa.
Faruk yace toh shikenan sai Allah ya kaimu nima yanzu zanje inkwanta.
Har ta juya zata tafi yace am baki ji ba.
Juyowa tayi tace na'am.
Murmushi yayi yace kije kawai ba komai.
Itama murmushin tayi tajuya takoma part d'in Mom cike da farin cikin gobe zata je Kebbi.....
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 23*
Washe gari tun da safe suka tashi suka fara shirin tafiya dan jirgin k'arfe goma zasu bi, tun wajen k'arfe tara driver yakama hanyar kebbi da mota inda aka zuba duk wata tsaraba da akwatin kayan jawahir da aka saka wanda bata san da shi ba, dan mamaki ma taba Faruk sam bata yi tunanin tatanadi kayan sawa ba.
Wajen k'arfe goma saura Barr Nas yakaisu airport, goma daidai tana yi jirginsu yad'aga zuwa KEBBI STATE tunda suka baro gida jawahir shuru tayi duk kuma sai taji wani iri sai a lokacin tayi tunanin shin ko har yanzu dangin mahaifiyartata suna a nan cikin garin Kebbi, gabanta saida yafad'i tace Allah yasa dai suna nan.
Suna safka suka samu mota suka yi shata suka kama hanyar FANAH jawahir dai titi kawai take kallo yanayin garin yana burgeta dan zata iya tunawa tun tana k'arama rabonta da garin a lokacin da Amminta taci burin k'ara zuwa da ita a lokacin tarasu, saurin goge jawayen da suka gangaro mata tayi Faruk ne kawai yalura da su ammah bai ce komai.
Sun d'an d'auki lokaci suna tafiya har suka isa garin a lantarki wani dattijo suka tambaya gidan Malam me salati dan ita bazata iya ganewaba saboda da jimawa rabonta da garin nan yayi masu kwatance me mota ya ida isa da su har k'ofar gidan suka biyashi kud'inshi suka fita.
Wani gida ne babba wanda da kagani ka san family house ne, daga gaban gidan akwai icce a k'ark'ashin iccen wani tsoho ne da wasu manya biyu zaune hannun tsohon rik'e da carbi yana masu magana, ganinshi yasa Jawahir taganeshi tace tabbas wanchan ne kakana na ganeshi, cikin sauri tanufi wajen da yake tace Baba Malam, daga shi har mutanen d'ago kai sukayi suka kalleta lokaci guda sukace Jawahir yau kece a garin namu?
Jikin tsohon tafad'a tare da fashewa da kuka tace Baba Malam meyasa kukayi min haka kuka daina sona.
Su dukansu jikinsu yayi sanyi dan basuda bakin magana, tsohon ne yayi k'arfin halin cewa bamu daina sonki ba jawahir muna k'aunarki wallahi ba laifinmu ba.
'Dagowa tayi cikin muryar kuka tace koma menene Baba malam baidace laifin wasu yashafeni ba ku duka dangin mahaifiyata kun yadani babu me k'aunata sai wad'anchan, tanuna su Faruk da suke tsaye.
Juyawa su duka sukayi suka kalli su Faruk sukace bismillah sannunku da zuwa.
Amsawa sukayi da yauwa nan suka zo zasu zauna d'aya daga cikin mutanen ne yace a'a kuzo mushiga gida ya za'ayi mubarku waje bismillah mushiga ciki.
Gabad'aya suka mik'e suka nufi cikin gidan inda suka nufi 'bangaren Baba Malam dan gidan irin family house d'innan ne suna shiga da sallama wata 'yar dattijuya tafito daga cikin wani d'aki tana gyara zane, Baba Malam ne yace Mairo kawo mana tabarma muna da manyan bak'i yau.
Cikin fara'a tace masha Allah marhabanbikum bak'inmu muna maku barka da zuwa, amsawa sukayi da yauwa.
Babbar tabarma tad'auko tashimfid'a nan duk suka zauna suka fara gaisawa tsohuwar ce tazuba ma Jawahir idanu tace oh ni Mairo wannan d'iya kamar 'yar wajen khausar.
Baba Malam yace itace man baki ganeta ba.
Saurin rik'o jawahir tayi tace oh ni 'yar nan kece?