Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Lokaci Ne Soyayyar da Ta Zo Bayan Jinkiri BY ZUWAIRA UMMU MARYAM

Author :  ZUWAIRA UMMU MARYAM Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 75

15K to 18K   out of 224.1K words

daya Kai ni gidan wannan matar ba..." Kai alhaji ya daga ya watsa mashi harara, yace
"Wato halin ka nan...Kai bazaka fadamin ba sai na tambayeka?.. You're not serious..." Yafada not too harsh,
"Naji dadi but ask me tou..." Yafada cikin shagwaba, banza yayi dashi ya Mike ya shiga one of he's bedroom, kafa suhail ya Dora kan juna yana jiran fitowanshi, mum dinshi ce ta shigo da food of basket ta jera kan dining, ko kallon inda suhail yake bata kalla ha balle tayi mashi magana, shigewa tayi bedroom din alhaji suhail yace
"Muma dai zamuyi auren..ehe.." Ya fada yana kar kada kafa.

Thanks

6💛💙💚💜❤️
Lokacine
💙💚💜💛❤️

® zuwairat (ummumaryam)




6️⃣



Free page



Yana nan zaune har dad dinshi ya fito cikin jallabiya mom dinshi na biye dashi, ko inda yake basu kalla ba suka zauna kan dining tayi serving dinshi ya fara ci, suhail kallon su kawai yake yana imagining shi da humaira at this age, but the fact is he can't picture themselves a haka, it looks so blank, ganin babu Wanda ya tanka mashi yaga sun maida shi invisible yasa ya yace
"Duk family in yaransu sun dawo daga abroad suna nuna mashi so da Kauna amma dayake ni ba'a sona ko damuwa Dani ba'a yi " Yafada kaman zaiyi kuka, dad dinshi kallon shi yayi ya tabe baki yacigaba da cin Abincin shi mom dinshi itama ko kallon shi batayi ba, suhail ji yayi ranshi ya mugun baci kawai sai ya tale baki ya fashe da kuka, both parents kallon mamaki suka dingayi mashi without word Don suna ganin kaman he's joking, shima suhail yasan it's a Joke but he tried by all means har saida yayi forcing hawaye down kaman wani Dan film, baki suka saki suna kallon ikon Allah,  cikin kuka yace
"I hate my life...you all hate me..." Yafada yana Mikewa yana kuka,
"Kai !.." Dad disnhi ya kirashi, ahankali ya juyo ya rufe idanuwa gam sai kuka yake Dan hawaye is coming out,
"Meye haka?.. " Inji dad dinshi,
,"dad Baku damu Dani ba...you don't care how I feel anymore...kaman kun mance Dani Wallahi.." Yafada cikin kuka,
"Sit down..." Dad dinshi ya umarceshi, ahankali ya koma ya zauna ita kam hajiya Hassana rasa inda zata saka kanta tayi ganin danta na kuka,
"Now tell me meye damuwanka..." Alhaji ya tambayeshi yana kallon junior him, Don daga behavior har kaman duk nashi né, haka nan yake rufe Ido ya dinga yi mashi fada in yayi ba daidai ba amma yasan shima he was more stubborn than him when he was younger sai dai shi yayi aure da wurin Don at 25 akayi masu aure kusan 4 bayan aure kuma komai sai ya lafa, yasan duk yanda suhail ke rashin ji dayayi aure shikenan,
"Dad Baka tambayeni how is everything...dad Baka sona Yanzu..." Yafada yana Kara volume din kukan shi, idanuwa dad dinshi yayi rolling Sannan yace
"Now tell me how is everything?.."
"Fine daddy..." Ya amsa mashi, abinci bawan Allah zai koma ci suhail ya sake cewa
"Dad Baka tambayeni why naje gidan kaka ba..." Yafada cikin shagwaba,
,"tou why kaje gidan kaka?.." Dad dinshi ya biye mashi, idanuwanshi ya bude ya goge tears dinshi Sannan yace
"Dad naje né inyiwa kaka maganar mu da humaira..,shine.." Idanuwa  alhaji ya zaro yana dafa goshinshi tare dacewa
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...suhail Don Baka da kunya Yanzu maganar aure kaje fadawa kaka da kanka?.."  Alhaji ya tambayeshi cike da mamaki, shuru. Suhail yayi yana mazurai
"Yanzu Don Baka da kunya sai kaje gidan kaka the same day you come back into the country just to tell her Kai ka girma?.."
"Dad Wai meye laifina?.. Ita fa ta Haba auren mu kafin in tafi..."
"Kai dalla rufemin baki...Mara kunya kawai...ai Allah ya taimakeka Baka fada mata abinda yasa kazo ba...da Kai da auren sai bayan shekara goma....sai muga ta zumudi..in Banda abinda duk family din nan kaf da akwai Wanda ya taba zuwa wajen kaka yi mata such issues da kansu?.." Alhaji ya fada mashi sounding so angry, suhail sadda Kai yayi yaja sauraron shi maganar da shiga ta left ya fita ta right, ko gobe yana da niyyar komawa gidan kaka kan same issue,
"Nidai dad yaushe zakayi mata magana tou...nidai gaskiya I can't wait anymore in ba sai so kake in lalace ba..." Yafada Kai tsaye, hajiya ji tayi ta rasa inda zata saka kanta saboda kunya, ahankali ta kauda kanta gefe guda,
"Tashi ka bani waje..."Alhaji ya fada mashi,
"Nidai dad in bazaka ba..I ..."
"Kai ka bani waje nace..." Alhaji ya daka mashi tsawa mikewa yayi ya fice daga dakin yana dariya , yana fita shima Alhaji ya fashe da dariya yana cewa
"Wannan yaron bai da kunya ko kadan...  Ajiyan zuciya hajiya ta saki Sannan tace
"Ai gado yayi ..like father like son..." Tafada wearing a smile, shima dariya yayi yana cin Abincin shi. Suhail na fitowa ya shiga part din mom dinshi, inda take ajiye bag dinta yaje yana dubawa one by one har ya tarda abinda yake nema wato the car keys,
"Mom will never change.." YafadA yana daukan keys din,  fita yayi ya nufi gidan su humaira, yana isa Ana kiran sallah magrub,  sallah yayi Sannan ya shiga gidan, falo ya tarda mom dinta da sauran families dinta amma Banda ita, gaisawa sukayi yace
"Mommy maira na nan kuwa her number is not going..." Ya tambayeta
"Oh bata fada maka ba?.."
"No...any problems?.."
"Aa ba matsala..kawai dai ta tafi kaduna for wedding din wata cousin dinta..from my side...Ashe bata fada maka ba?.." Mom dinta ta fada mashi, shuru yayi ya kasa magana, he can't believe humaira su traveling yau amma jiya bata fada mashi ba, he was so angry, Yanzu he's feeling he's loosing her,
"Yaushe zata dawo?.." Ya tambayeta
"Zuwa ranar Sunday da yana because Tana da lectures ranar Monday da safe..." Ta amsa mashi, ahankali ya Mike yana cewa
"Tou shikenan...amma her line is not going...hope she's alright..." Ya fada sounding so broken,
"Eh dazun ma munyi wAya da second line dinta..." Kallonta yayi yace
"Pls bani line din...Wanda nake dashi is not going..." Ya fada cikin sanyinmurya,
"Ok..." Tafada Tana daukan phone dinta dake gefenta ta bude mashi number ya rubuta Sannan ya juya ya fice, cikin mota ya koma thinking about what is happening, Kai ya hada da staring yana Jin he can't even drive, wannan number da aka bashi yayi dailing yaji it's ringing, sai da ta kusa tsinkewa ta daga
"Maira.." Ya kirata cikin sanyinmurya,
"Naam yaya is that you?.." Ta tambayeshi, Sannan tambayan ya bata mashi rai amma he's a man with control,
"Yes..maira nayi laifi né?.."
"Aa yaya...me ka gani?.."
"Naga yesterday we make called amma baki fadamin zakiyi tafiya ba...I was at home waiting for you to come to family home Sannan nazo gidanku ance kina kd...pls maira if anyi abinda ya bata maki rai kiyi hakuri kar..." Bai karasa ba tace
"Haba yaya me yayi zafi haka?... Wallahi babu abinda kayi min...kawai dai muna hiran kaka sai na mance in fada maka am traveling today...pls kayi hakuri kaji yayana..." Tafada mashi calmly,
"Hmmm Maira...I have a bad feeling someone is taking you away from me..." Ya fada kaman zaiyi kuka,(hmmm rayuwa kenan..while wasu suna chan suna yiwa mazan yanda sukeso wasu suna chan suna néman mazan, when you have someone that kpcares for you so much pls pay attention to the person) nobody will know hot guy like suhail zai mutu kan yarinya amma unfortunately nor matter how hot a guy is da akwai wacce ya mutu kanta sai indai ita tayi wasa da damanta,  Jin tayi shuru batayi reply ba yasa ya sake cewa
"Maira pls tell me wani ya katse ni?.. Wani ya dauke zuciyarki daga gareni?." Ya tambayeta voice dinta na rawa,
"Pls yaya ka bar wannan maganar mana..Don naje biki sai ace wani ya dauke ni daga gareka?.. Haba Dan Allah..." Tafada kaman she's angry
"Maira dole in yi wannan tunanin...your attitude is scaring me..."
"Nidai yaya sai anjuma tunda abinda zaka ce mun kenan..." Ta fada Tana kokarin katse wAyarta,
"No maira...pls wait don't go off...pls kindai San I love you..Ina kaunar ki sosai...Wallahi duk abinda kike so zanyi maki...just don't leave me...ni tunda na dawo ko I love you you baki fadamin ba..." Yafada cikin sanyinmurya,
"Yaya I love you...shikenan?.." Ta fada irin bai dameta ba, idanuwa ya lumshe yana imagining da class dinshi yar yarinya take yi mashi hakan,  yanda ta furta I love you din sound so annoying
"Am not forcing you to say it...kawai basai kin fada in a forceful way ba...sai anjuma..." Ya fada cikin sanyinmurya, Sannan ya katse wayar, yafi minti goma nan wajen not knowing what to do with himself, he feels so bad, gani yake in har yayi kokarin driving he will get into trouble Don yana ya buge wani ko wata, number Yazid yayi dailing ya fada mashi yana gidan su humaira yazo ya dauke shi, bai tsaya ya ji abinda Yazid zaice ba ya katse wayar tare da da hada Kai da staring.

Maryam ma har 12 na dare she was thinking about Alhaji Ahmed proposal, kawai she wished batasan matarshi ba da zata amince, ko ba komai  zata samu kwanciya hankali a  wannan meeting da zaayi Don zata fada ma kaka tayi miji amma bazata iya yiwa matarshi haka ba, she will not find happiness at the expense of another's sadness.

Yau weekend so daga sallah asuba bata sauko falo ba, komawa tayi bacci saboda daman batayi bacci sosai ba, all family din are present amma Banda dad dinsu da yayi tafiya, suhail na dakin Yazid just from Daren jiya zuwa safiyar yau ya rame sosai, he's just imagining life without humaira,
"Wallahi in har na rasa humaira sai na kashe wannan tsohuwar..." Yafada out of anger, Dan dariya Yazid yayi yace
"Haba why would you say that.,,bakasan duk abinda Allah ya hana mutum ba alkhairi bane a gareshi ba?.. In har ka rasa humaira Wallahi it's destined to be...Allah zai Baka wacce tafi humaira da komai.." Yazid ya fada mashi,
"Kai daman Baka soyayya..so you won't understand how am feeling..wacce zata fimin humaira?..ni Wallahi ka bar wannan maganar da kake..,bazai taba yuwa na rasa humaira ba..."
"Yes you won't loose her,..just have a positive mind..everything will be alright..." Inji Yazid dake mikewa zaune,
"Hmm Nidai am having a bad feeling...na dawo humaira bata damu ba..kuma Wai she went to kd without informing me..ai am not stupid..something is wrong...kawai dai if anything happens to my relationship da humaira kaka is in deep trouble Wallahi..,I mean it..." Yafada atakaice,
"Naji .,ka tashi muyi breakfast..." Yazid ya fada mashi, suhail kwanciya yayi ya rufe kanshi da blanket yana cewa
"Ba'a ci.." Yafada mashi atakaice, kwace blanket din Yazid yayi yace
"It almost 11 ..ka tashi muci abinci pls..Haka nan sai ka damu kanka unnecessarily..." Sake maida blanket din yayi yana Jan tsoki,
"Suit yourself..." Yazid ya fada yana ficewa daga dakin ,falo ya fita ya tarda mom da Aisha, gaidasu yayi ya umarci Aisha ta dauko mashi breakfast dinshi,
"Mom kinga suhail na daki yaki cin abinci..."
"Oh nan ya kwana né?.." Hajiya Ta tambayeshi
"Eh jiya na dauko shi .." Ya amsa mashi yana hada tea, kallon Aisha tayi tace
"Je ki kirawoshi..." Da sauri Aisha ta Mike ta nufi dakin Yazid, daidai lokacin ita kuma mami ta sauko cikn Jean da riga kanta babu dankwali sai gashinta dake salki, face dinta babu makeup but she looks so breathtaking, kusa da mom dinta tazo ta zauna hajiya tace
"Jewel yau ansha bacci..." Ta fada mata,
"Wallahi mom I slept like a baby..." Tafada Tana relaxing Sannan tace
"Mommy Ina Aisha zata?.." Ta fada Sannan Yazid ya gaisheta tare da fada mata suhail né yaki cin abinci.
"Tou meke damunshi?." Ta tambayi Yazid,
"Oho mashi..." Ya amsa mata, Aisha na shiga dakin da sallama suhail ya daga Kai ya amsa mata, gaisheshi tayi ya amsa Sannan tace mom na kiranshi, baiyi musu ba ya fito, ahankali ya taka ya gaida mom tare da mami, tsaye yayi yana kalle kalle kaman he's looking for a place to sit kawai sai ya zauna kusa da mami har da Dora kafa kan legs dinta, da sauri ta tureshi Tana cewa
"Mommy kiyiwa wannan yaron magana kar ranshi Ya baci Wallahi..." Ta fada Tana sake ture kafarshi daya Dora for the second time, dariya mom tayi shima yayi yana cewa
," anty pet me ..am in a bad mood.." Yafada yana Kara dora leg dinshi kan kafarta,
"What's wrong with you?.." Mommy Ta tambayeshi tamkar she's asking Yazid saboda kulawa,
"Nothing..." Ya amsa mata kanshi kasa, da karfi mami ta ture legs dinshi Tana cewa
,"Tunda nothing remove your legs..." Tafada mashi, sake maida leg din yayi yace
"Wallahi anty zan fada...humaira ce..." Yafada yana kallon faces dinsu, dariya mom tayi tace
"Me humaira tayi..."
"Kawai she's about dumbing me..., " ya fada mata, dariya mami da Yazid sukayi mami tace
,"me kayi mata tou?.." Ta tambayeshi Tana kallon gefen kunnenshi dake kwance da dark thick hair,
"Nifa anty ban sani ba...kawai am feeling she's leaving me... " ya fada idanuwanshi cikin nata,, itama Dan kura mashi Ido tayi for a second or two Sannan tace
," kadai have hope..what will be will always be..." Ta fada mashi calmly
"Kaji abinda antynka tace...ka kwantar da hankalinka.." Mommy Ta fada mashi, Sannan ta juya ga Aisha tace
,"give your yaya abinci..." Ta fada mata, zata Mike itama mami tace
"Nima Bari in nemi abinda zanci..yau I want something international..." Tafada Tana ture kafar suhail dake kan leg dinta don ta Mike,
"Anty Nima naki zanci...I don't want to eat but if you're cooking am eating..." Yafada yana relaxing, Aisha dawowa tayi ta zauna while mami ta shige kitchen, Yazid kam maida hankali yayi ya ci ya koshi ya maida plate kitchen da kanshi Sannan dawo falo, hira suka dinga taba har wayar mami dake kusa da inda ta tashi ya fara ringing suhail ya Mike cikin kasala ya nufi kitchen, daga screen din yayi yaga alhaji Ahmed, mami na Jin karar phone dinta tayi saurin tahowa har suna cin karo dashi, da sauri ta amshi wayar saboda amatsayinta na Doctor she don't ignore calls, suhail karasawa cikin kitchen din yayi yana duba pot dake kan gas, ita kuma Tana ganin alhaji Ahmed ta Dan bata face Sannan tayi piçking, cikin respect ta gaisheshi while shi kuma suhail yana karanbanin juya tomatoes dake soyuwa kan wuta, kawai San Mai ya fallasa a hannunshi ya saki Kara, da sauri Maryam dake waya ta bashi baya tayi saurin juyowa, mancewa tayi da Tana waya ganin suhail na ihu kaman wani serious Abu ya same shi tayi saurin ajiye wayar ta kama hannunshi ta Kai sink sai wayyo yake cikin shagwaba, ruwa ta bude ma hannu daidai lokacin da Yazid ya shiga kitchen din, shi kam alhaji Ahmed sai hello yake, Yazid tsayawa yayi yana kallon mami dake rike da hannun suhail under running water, suhail sai tale  baki yake kaman zaiyi kuka,
"Wai me ya faru?.." Yazid ya tambayesu yana karasawa inda suke tsaye,
"Rabu dashi..oil spill yake wa wannan ihun haka..." Mami ta fadawa Yazid,
"Pls ka rike mashi hannu I was on call.." Ta fada Tana sakinshi, sai turo baki yake yana cewa
"Anty dawo ki bani first aid treatment..my hand hurt like hell..." Yafada kaman zaiyi uku, banza mami tayi dashi ta dawo ta dauki wayar sannan tacigaba dayiwa Ahmed magana, suhail kallonta yayi ya sake cewa
"Dan Allah anty ki ajiye wannan wayar ki zo ki bani first aid treatment, Wallahi da zafi sosai.." Yafada mata kaman zaiy kuka, idanuwa mami tayi rolling ta bawa Ahmed hakuri kan she will call him later, kallon Yazid tayi tace
"Daukomin first aid box..." Ta fada mashi, harara Yazid ya watsawa ma suhail yana cewa
"Kai dai kaji haushi Wallahi..." Yafada yana barin kitchen din don dauko kit din, mami sake Kama mashi hannu tayi Tana kallon hannun, sai kallon bayan kanta yake not knowing what he's thinking about, Kai ta daga ta kalleshi tace
"Gaskiya raki kawai kake...ni banga wani ciwo ba..." Tafada mashi still looking at the hand,
"Aa Wallahi anty zafi ke da akwai...nidai duba sosai..." Yafada cikin. Shagwaba, haka dai ya dinga  yi mata shagwaba kaman yanda yakeyi a gidansu, he's so close to her that if he's with her he don't think of anything but how to get closer to her, box Yazid ya dauko ta bashi magani tare da shafa mashi jb Sannan ya fita daga kitchen din ita kuma ta cigaba da aikinta.

Yau Monday da yamma suhail ya tafi gidansu humaira, yana shiga street dinsu ya hangi wata makeken jeep tsaye with tinted glasses,  motar na tsaye Kofar gidansu humaira, ko kadan baiyi tunanin humaira ce cikin motar da wani ba, yana zuwa yayi horn aka bude mashi gate ya shiga, bayan yayi parking ya shiga ciki suka gaisa da mahaifiyar humaira, wata yarinya da bazata wuce 10 years ba ya kalla yace
"Zainab anty ta dawo?.." Ya tambayeta, gani yayi mahaifiyar humaira Tana kame kame,
"Eh...Yanzu ta fita..da alhaji Ismail..." Yarinyar Ta amsa mashi hankali kwance, San murmushin karfin Hali ya saki yana Jin zuciyar shi na beating da karfi kaman heart dinshi zai fito,
"Unguwa suka je?.." Ya tambayeta pretending to be calm,
"Aa...rakashi tayi..." Yarinya Ta sake amsa mashi, gani yayi mahaifiyar humaira ta Mike ta bar wajen, sai lokacin ya tuna da jeep din daya gani   A waje, ahankali ya Mike ya Kama hanyar waje, yana bude gate yayi daidai da lokacin da humaira ta fito daga cikin motar alhaji Ismail wearing wasu sexy and expensive clothes.ji yayi numfashinshi na néman daukewa Don har sai da ya rike gate Don kar ya fadi kasa, Ahankali ya daga Idanuwa suka hada Ido da humaira da tahowa kaman munafuka.

7💙💚💜💛❤️
Lokacine
💙💜💚💛❤️

® zuwairat (ummumaryam)


7️⃣


Free page

Dedicated to my anty..


Suhail ji yayi he's finding it difficult to breathe, humaira kasa karasowa tayi saboda tasan suhail is loving and caring but he can be something else when he's angry, alhaji Ismail tafiya yayi ko kallon suhail dake rike da kofa baiyi ba,
"Yaya..." Humaira Ta fada Tana wayancewa then she's keeping her distance,ahankali ya daga red eyes dinshi yace
"Humaira why zakiyi min haka?.." Yafada kaman zaiyi

6 / 75