Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Lokaci Ne Soyayyar da Ta Zo Bayan Jinkiri BY ZUWAIRA UMMU MARYAM

Author :  ZUWAIRA UMMU MARYAM Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 75

45K to 48K   out of 224.1K words

opening the gate for her, murmushi kawai mami tayi because she never get tire of saya mashi nama,
"Zan sayo maka yau Dana jiya..." Ta amsa mashi, idanuwa Maigadi ya zaro yana cewa
"Wayyo dadi...Allah ya Kara girma ya kawo miji na gari mu gwangwnje.?.?." Ya amsa mata, bata Kara cewa komai a zahiri ba but deep inside Ta amsa da ameen, Tana zuwa office co workers dinta suka dinga yi mata. Sanna duk  sun San hardly tayi missing wajen aiki sai if Important abune ya faru. Bayan ta shiga office dinta that is neatly arranged ta ajiye bag dinta Sannan ta fita zuwa ward din patients, daman it's in her, in tazo office zata bi dukan gadajen Mara lafiya taji ya suka kwana, sai ta Kai kusan hour Tana haka kafin ta fara aiki, while she was still there suhail ya shigo hospital din, direct office dinta ya wuce daman kafin ya bar Nigeria ta fara aiki a nan so he knows her office,  budewa ya shiga tare da lumshe Ido saboda yanda koina ke kamshi kaman she's inside, tsayawa yayi yana kallon office din da hannunshi cikin aljihu, bayan kaman minti goma ya koma wani resting chair dake nan ya zauna amma Allah kadai yasan yanda heart dinshi ke beating saboda fargaba, now he knows better about her, he have never seen her so angry kaman jiya, he really pushed her button yesterday because he sees the anger he never sees in her, before, adua kawai yake Allah yasa kar ya Kara marinshi Sannan on the other side Allah yasa kar mom dinshi tayi wani abu da zaiyi ruining relationships dinsu da su Yazid, yasan if Yazid yaji he almost make a move at mami he will hate him with passion, bayan minti biyu da shigowanshi aka bude kofa mami ta shigo sani na biye daita,
"Kar ka dade pls..ka amso kudin sai ja biya Mai waazi pharmacy ka sayo mashi magannin..." Tafada walking straight into her bag, Tana shiga tasan he's there sabida itama taji kamshin perfume dinshi, amma kaman babu kowa haka tayi behaving, saidai face dinta kaman bata Taba dariya ba, bag dinta ta bude suhail na zaune yana kallonta, purse ta dauko ta bude Tana cewa
"Wane bank né kusa damu nan?.." Ta tambayeshi Tana Dan juyawa ga inda Wanda ke biye daita ke tsaye,
"Da akwai stanbic..." Ya amsa mata, atm ta zaro na stanbic Tana cewa
"Dan Allah musa Kayi sauri...kaga condition dinta..she needs it fast..." Tafada cikin damuwa, mika mashi tayi Sannan ta zagaya ta zauna, ahankali Suhail ya Mike ya dawo gaban chair dinta, Kai ta kauda gefe guda Tana murza yatsunta na hagu Da yatsunta na dama,
"Anty good morning..." Ya gaisheta cikin sanyinmurya kaman zaiyi kuka, kanta na nan gefe guda tace
"Morning..." Ta amsa mashi not even looking at he's direction,
"Anty..." Ya kirata, shuru tayi bata amsa mashi ba, kallonta kawai yake especially gaban goshinta da kananun gashi ke kwance, ahankali ya koma side da take kallo yayi kneeling yana cewa
"Anty am sorry..,kindai San I will never make any dirty move at you...kawai sharrin shaidan né...kiyi hakuri Dan Allah.." Yafada kaman baison magana,
"Ba komai ..ya wuce..." Ta amsa mashi kanta kasa, da sauri ya Mike yana tsalle tare dacewa
"Anty I love you so much...anty thank you for your understanding...Allah ya saka da alkhairi...at least Yanzu Ina iya bacci cikin kwanciyar hankali...anty Wallahi rabona da abinci tun wnda kika bani jiya da safe...anty sai Yanzu na fara Jin yunwa.." Ya jero maganar barkatai kawai because he's so excited and out of what to say, shuru mami tayi bata amsa mashi ba,
"Anty yunwa..." Ya fada yana Shafa flat tommy dinshi,
"Suhail..." Ta kirashi, ji yayi tsigan jikinshi na tashi saboda yanda ta Kira suna shi with some slant,
"Naam..." Ya amsa mata cikin sanyinmurya, ahankali ta daga eyes dinta da suka ciko da kwalla tace
"Hade you think of what' will happen if wannan maganar yaje kunnen kaka?.." Tafada trying not to burst into tears saboda yanda take ji a cikin zuciyar ta, ahankali ya zame ya zauna kan seat dake gabanta yace
"Anty nasan it will be a blast...and it's all my fault,,,kiyi hakuri..." Yafada cikin sanyinmurya, ahankali ta girgiza mashi Kai
"Nima Ina da nawa laifin...ya kamata in rike girma na..Bai kamata..." Sai kuma ya dafa goshinta not knowing what to say,
"Anty it's all my fault,,,insha kaka bazata ji ba..." Ya amsa mata, Kai ta girgiza tace
"Nasan zata ji...dole humaira zata fada...and your mom will never let go until she sees me and my mom begging for mercy in the hands of kaka...kasan sani..." Tadata tears na rolling, idanuwa ya lumshe not knowing what to say because she says exactly what he's mother is capable of doing,
"Anty let's assume humaira bata fada mata ba" Bai karasa ba tace
"She will..."Ta  amsa mashi atakaice. Shuru né ya biyo baya for a moment mami na zubar hawaye amma Tana gogewa  kar wani ya shiga ya ganta Tana kuka, tissue ta dauka ta goge hawayen Sannan ta dauki waya ta Kira wata number, word daya kawai tayi ta ajiye wayar, bayan kaman minti biyu wani ya shiga da gani he's  a messenger, kallon suhail daya hada Kai da table tayi tace
"Cutest what will he buy for you..." Tafada kaman she's not the angry person that gives him a dirty slap jiya, ahankali ya daga Kai ya kalleta amma one thing he noticed is bata kallonshi kaman yanda takeyi da, ya gane Tana Jin kunyar shi, already ya gano ta with unique quality of forgiveness,
"Anty ban cin komai..I lost my appetite..?" Yafada yana maida Kai kan table din,"
"Suhail am not joking with you,,,if you're not eating then go." Tafada atakaice,
"Zanci...anty ya kawomin anything it's ok by me..." Yafada da sauri, yar takarda ta dauka ta rubuta abubuwan da zaa sayo Sannan ya bude bag dinta ya dauki 3k ta mika mashi ya fita, files aka shigo mata da su suhail ya tashi daga kan chair dayake ya koma kan resting chair amma the most surprising thing is bai second goma bai kalleta ba, the more he looks at her the more he sees something he never see before, beauty dinta kawai yake gani fiye da da, yana na wasu patients suka shiga, yanda take magana dasu da bayani da komai makes goes crazy, her words and the way she brings them out is something he never see in anyone, ita kam ko inda yake bata Kara kallo ba sai attending mutane kawai take looking gorgeous and brilliant, ahankali ya dafa goshinshi yana sakin ajiyan zuciya,
"Ya Allah what's wrong with me.?." Shine tambayan da yake wa kanshi cikin zuciyar shi, he's becoming so confused, sake kallon ta yayi yana kallon yanda take dariya da wata mata dake fada mata magana cikin zolaya, her dimples is so perfect, he can stand on the street and shout anty is more than a woman, tunawa yayi da ta fidda miji sai yaji gabanshi ya mugun fadi, bayan kaman hour daya messenger ya shigo da abincin daya sayo masu, sai lokacin ta kalleshi Tana cewa
"Ka dauki daya ka bar min daya .." Tafada mashi Tare da yi mashi one second look ta dauke kanta, ahankali ya Mike not knowing if he can eat Don shi kadai ya San how he's feeling inside inshort ya ji haushi zuwan dayayi because he's getting in to more trouble.

Hajiya Hassana na barin gidanta taje gidan hajiya habiba daman tun asuba tayiwa mijinta karyar hajiya habiba bata da lafiya so she's going to see her, Alhaji Muhammad is not that strict but baya daukan rainin hankali. Humaira hajiya ta Kira ta shigo dakin da suke
"Yanzu kina jina zaki shiga ciki ki shirya zamuje gidan kaka..ki fada mata kinga mami Tana lalata da suhail..kinji kou..." Ahankali humaira ta daga wa mahaifiyar ta Kai,
"Maza ki shirya muna jiranki..." Babu musu ta Mike ta  bar dakin, bayan kaman minti biyar ta dawo, mikewa hajiya habiba da hajiya Hassana sukayi suka fita suka saka humaira cikin mota suka bar gidan suna cikin mota hajiya Hassana tace
"Ki ce zindir kika gansu suna aikata alfasha...kina jina?.." Ta fadawa humaira, ahankali humaira ta daga mata Kai,
"Wallahi rukkaya it's me and you a wannan garin yau...lets see yanda zaayi kaka ta goyi bayanki...shegiya kilibabba..." Tafada out of hatred, you know in life you don't have to be bad to have enemies, kawai your good attitude ma zai jama ka makiya that have opposite character like yours, tunda suke a wannan family na Mai waazi hajiya Hassana bata da burin daya wuce taga hajiya rukkaya suffering for no cause, kawai she hates her with passion because she's so perfect, ko abinci suka Kai gidan Mai waazi loKukan uban me kike..." Tafada cikin matsanacin masifakacin kafin kowa yayi nashi gidan ya tashi sai ance na hajiya rukkaya yafi dadi, hajiya Hassana na iya kawo abinci a bar shi nan amma hajiya rukkaya na kawo nata zaa cinye nan take Ana sati lokacin ba kaka kadai bace duk sauran iyayen mijin suna nan, suna nuna kaunar su ga hajiya rukkaya face to face babu munafurci Sannan har yabbing hajiya Hassana suke poor cooking habit dinta, wannan shine sanadiyar data ji ko kadan bata kaunar hajiya rukkaya Don gani take ita har da asiri ta Kama family din miji, Sannan ita hajiya Hassana bata fito daga babban family kaman na hajiya rukkaya ba, hajiya rukkaya yar gidan manyan mutane sai ya kasance Tana yawa yiwa iyayen mijinta kyauta dukda suma babu abinda suka rasa but they love her gifts so much, duk family din kaka bata da wacce takeso kaman rukkaya. Ita kam hajiya Hassana it hurts her so much that kaka and the rest of the family loves her with passion. But finally she have something to rejoice about shine mami da Allah bai bata miji da wuri ba, kullum it makes her happy if ta tuna dole hajiya rukkaya zata shiga damuwa sabida mami. Rayuwa kenan, Yanzu irin su hajiya Hassana suna da yawa cikin alumma, kawai you don't hurt or hate them but seeing you sad gives them total pleasure. Allah ya raba mu da bakin Hali Amin.

Suna isa gidan kaka suka shiga, kaka dake zaune a falo na ganinsu ta fara balai Tana cewa
"Wallahi in ma Don wannan maganar né munafukai kuka taho Wallahi ku koma...babu dole..." Tafada atakaice, humaira fashewa tayi da kuka as instructed by her mother, kallon banza kaka ta watsa mata Tana cewa
"Wallahi kika koyi halin wannan banzayen iyayen naki na kilibibi kin shiga uku." Ta fada hankalinta kwance, zama hajiyas sukayi kaka ta kalle su Tana cewa
"Wai baku jine?.. Ku bani waje kafin in Kira mazajenku suyi sake ku mu huta da masu bakin Hali....In ba Don tsabagin munafurci ba yara sun nuna basu so.ku kuma dayake kun hada Kai kun like kaman dole.,tou Maza ku bar min gida..." Tafada cikin fada,
"Kaka mu ba wannan ya kawo mu ba...wata magana ce Mai tsananin tashin hankali..." Baki kaka ta bude Tana kallon face dinsu kaman wata police officer,
"Ku fadamin abun tashin hankalin Inji..." Tafada atakaice, Tana Dora kafa daya kan daya, hajiya kallon Humaira tayi tace
"Kiyi shuru ki fada mata Abunda kika gano." Hajiya Hassana ta fada mata.
Ahankali humaira ta goge face dinta Sannan ta fada mata Abunda ya faru which is 98% lies, baki kaka ta bude ta kasa magana sabida danyan labarin da takeji, 
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun." Shine Abunda ta fada cikin tsananin tashin hankali, hajiya Hassana da hajiya habiba signaling junan su sukayi suna Mai Jin dadin yanda face din kaka ya sauya alaman maganar ya shige ta,
"Wai kike ce rukkayatu Tana falo kuma?.. Anya dai..gaskiya da wuya in ita kika gani...Don ance wannan Dan tsohuwar Tana aikata hakan babu musu..daman yanda wannan yaron ya zama fitsararre nasan da akwai magana...Kai Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Kaka ta fada Tana kare hajiya rukkaya, hajiya Hassana tabe baki tayi sabida Jin ta kareta
"Wallahi kaka Tana falo...ita tacemin in shiga dakin." Humaira Ta amsa mata cikin kuka dukda she's asked to cry Don kaka ta fi yarda da maganar she wants to cry on her own sabida ko bacci batayi ba sabida tunanin abinda ta gani, kawai tasan suhail na son mami ya yaudareta da yana sonta
"Tou  dai bata San suna hakan ba?.don da ta sani da batace ta shiga ciki ba .." Kaka ta fada masu,
"Tou Nidai na fada maki kar in dauki mataki da Kaina kice na Raina ki...Don haka a bima Dana hakkinshi.?.Ai wannan cin mutuncin yayi yawa..." Hajiya Hassana ta fada, kallon banza kaka tayi mata taja tsoki Sannan ya dauki wayarta ta mikawa Humaira Tana cewa
"Bincikomin lambar yunusa" Ta fada mata, humaira searching lambar tayi tare da dailing Sannan ta mikawa kaka, kafawa kaka tayi a kunne Tana jiran mahaifin mami yayi piçking, yana dauka da sallama ya gaidata amma ko amsawa batayi ba tace
"Inason ganinka da wannan tsohuwar diyar taka Yanzun nan." Tafada atakaice bata jira yayi magana ba ta katse wayar ta. Kara mikawa humaira tayi tace
"Bincikomin lambar Muhammadu..." Ta fada Tana karkada kafa ahankali, kallon mamaki hajiya Hassana tayi mata Sannan tace
"Yo kaka shima sai ya zone...ai nayi tunanin shi ba sai yazo ba?.." Ta fada cikin fargaba, kallon banza kaka ya watsa mata Sannan tace
"Lallai ma..shi dan naki bazaa yi mashi fada ba kenan.shi ba dadin ya sani ba har ya Bari wannan tsohuwar Tana tarayya dashi...ke Dalla fiddo in lambar shi..." Tafada atakaice, humaira fiddo wa tayi ta mika mata, hajiya Hassana sadda Kai kasa tayi Tana fargaban Abunda zai biyo baya Don cewa zaiyi ta tsallakashi ta kawo magana wajen kaka, shima yana piçking kaka, tace
"Ka kawo wannan Mara kunyar Yanzun nan..Ina jira..." Ta fada Sannan ta ajiye wayar. Both side da sukayi receiving wayar kaka sun San da akwai matsala ance in kaji Kira samu né amma Banda kiran kaka,

"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Mahaifiyar mami ta fada lokacin da kiran yazo, kasancewan suna tare lokacin,
"Alhaji me mami tayi kuma?.. Na shiga uku..." Tafada Tana dafa chest dinta sabida tashin hankali,
"Yanzu wannan yarinyar bata samun kwanciyar hankali kenan?.. Jiya yini kuka tayi and yau kuma nasan dole ba abun arziki bane..." Hajiya rukkaya ta fada kaman zatayi kuka,
"Ya isa haka nan..Bari inje office dinta in dauketa sai mu wuce since its closer..." Alhaji ya fada yana mikewa sai sweating yake sabida one single drop of tears na mami na damunshi amma shi irin matured people masu danne problem dinsu né.
"Alhaj Ai Nima zani..." Ta fada Tana mikewa itama, alhaji baice komai ba ta shiga ciki ta dauko hijab ta saka suka fito sukayi hanyar hospital din mami,

Suhail kam spoon biyar yayi yaji ya koshi da abincin, gefe daya ya tura ya Mike yana cewa
"Anty Bari in tafi gida kar in dameki,,.i will see you tomorrow..." Yafada idonshi kanta,
,"ok..." Ta amsa mashi looking into a file, ahankali ya juya har zai fita tace
"Cutest..." Da sauri ya  juyo kaman he's waiting
"Pls Kayi resuming aiki...kaji..." Ta fada mashi
"Ok anty..I will tomorrow Insha Allah...but it's because of you..." Ya fada mata,
"Nagode...if wata ya kare sai ka bani account number in dinga tura maka wani Abu tunda kaka tace you don't have salary for 3 months..."
"Aa anty.,you don't have to worry about that...if am broke zan fada maki..." Tadaaa cikin sanyinmurya,
"Ok shikenan...thanks for coming..." Tafada kaman he's a patient, idanuwa kawai ya lumshe ya fita tare da rufe mata office din, ko inda motarshi ke tsaye bai Kai ba before yayi receiving call din dad dinshi,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Yafada cikin fargaba.

17💚💛💜💙❤️
Lokacine
💙💜💚💛❤️



® zuwairat (ummumaryam)



1️⃣7️⃣



Free page



Ahankali ya Kai wajen motar shi ya Dora kanshi saboda yanda numfashinshi ke fitowa not normal,
"Kai...mommy..." Yafada ahankali tare da sakin wani irin nishi kaman Mai Jin wani ciwo cikin zuciyar shi, mota ya bude ya shiga yana tunanin Yanzu mummy dinshi yaje gidan kaka ya fada mata abinda bai kamata ya fita ba, wannan ya Kamata duk uwa ta boyewa danta such issues amma shine ta kaita wajen kaka Don ta yayashi da mami, staring ya buga da karfi yana cewa
"Humaira...humaira..Wallahi ranki in ya Kai dubu sai ya baci...gobe in gulma abinyi né sai ki Kara,..." Yafada yana tunanin abinda zaiyiwa humaira muddin hannunshi ya kamata. Ahankali ta tada mota ya bar hospital premises din ya Kama hanyar gidan kaka trying to drive safe saboda yanda gabanshi ke faduwa, kawai ba Wai yana tsoron matsifsr kaka ba, kawai he's afraid kar mami ya Kara fushi dashi, bayan kaman minti sha biyar da suhail ya bar hospital hajiya da alhaji suka Iso hospital din, hajiya kawai ce ta fita ta nufi ciki while alhaji na bayan da driver a gaba yana jiran su fito, sanda hajiya ta shiga office din mami na zaune da wani suna magana, Tana daga Kai taga mahaifiyar ta gabanta yayi mugun faduwa, da sauri ta Mike Tana Dan squeezing face sabida yanda taji wani Abu ya tokare mata zuciya, sai da ta lumshe Ido ta hadiye wani Abu Sannan ta Dan samu sakin face din, mahaifiyar ta na tsaye Tana kallon ta, murmushin karfin Hali ta saki Tana cewa
"Mommy..kece da kanki...lafiya dai .." Tafada maganar  fita daban daban, Sannan tsoro na kwance kan face dinta, murmushi mom dinta ta saki tace
"Dad dinki ke kiranki..." Ta amsa mata, kura mata Ido mami tayi Tana kokarin gano reaction dinta but nothing, kallon patients din tayi mashi magana Sannan ta Kira wani a waya ta fada mashi fita ya kamata ga patient ya dubashi, Tana magana jikinta sai rawa yake sabida tasan it's about yesterday, bag dinta ta dauka ta kalli mum dinta tare dacewa
"Mum Ina zamu?.." Ta tambayeta
"Wai kaka tace a kawo ki...Dan Allah kinyi wani Abu?.." Hajiya ta tambayeta cikin damuwa, ahankali mami ta koma ta zauna tare da dafa goshinta saboda tashin hankali
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...mummy am sorry..." Tafada Tana kokarin fashewa da kuka, da sauri hajiya ta kamata Tana cewa
"Jewel tell me what's the problem...pls

16 / 75