Author : ZUWAIRA UMMU MARYAM Category : African Stories & Novels
nayi mata kaman an ajiye dutse a Kai, sai nishi take hannunta kan chest dinta, few minutes later hajiya ta shigo da cup of tea hannunta, begging dinta tayi ta amsa tasha Sannan Tasha magani ta koma ta kwanta. Yazid na shiga yaga suhail kwance rungume da pillow ya bawa kofa baya,
"Ashe nan ka yo..." Yazid ya fada mashi yana rage kayan jikinshi, shuru suhail yayi bai amsa mashi ba
"Cutest Kayi bacci né?.." Ya sake tambayan shi, still shuru yayi, Dan lekawa Yazid yayi yaga face disnhi cike da hawaye, ajiyan zuciya Yazid ya saki ya dawo gabanshi ya zauna, hannu ya Dora kanshi Sannan yace
,"nasan dukda wannan ihun da kake na bazaka aureta ba you will still get yourself hurt...now gashi...." Yafada cikin sanyinmurya, suhail baice komai ha sai hawaye kawai yake,
"Dan Allah stop crying..kawai abinda zaayi zamu koma wajen kaka..." Bai karasa ba suhail yace
"No..." Yafada yana mikewa zaune, face dinshi ya goge Sannan yace
"Kawai am shedding few tears for being disappointed...kasan yanda nake ji kuwa?.. It hurts ka sa rai ga abu and be fucked up at the end of the day...na Sa ran auren humaira...all I ever dreamed of is me and her in our holy matrimony...kawai just in a blink of an eye dream Dina has been chattered...dole inyi kuka...na sa raina...na kwallafa Raina...saboda humaira naki bawa wata yarinya chance...saboda ita ko kallon wasu banyi amma she publicly rejected me...me suhail was rejected publicly..." Yafada cikin matsanacin kuka, face dinshi yayi ja sosai, Yazid dafa goshinshi yayi trying not to cry amma yanda the whole suhail ke kuka is going to make him shed some tears,
"Wai ni ake cewa zaa hada aurena da maira take kukan bataso...my heart hurts...it hurts so much...bansan humaira zatayi min haka ba...bansan zaa samu ya mace da zata nunamin total rejection ba...kaico..." Yafada crying like a baby, shima Yazid hawaye ya farayi amma yana controlling kanshi, rungume juna sukayi da suhail har saida ya gaji da kuka Sannan ya kwanta, mikewa Yazid yayi ya shiga bathroom ya hada mashi ruwan wanka ya fito, suhail shiga yayi shi kuma ya fita ya shiga kitchen yasa Mai aiki ta zuba mashi abinci, dakinshi ya koma ya ajiye Abincin yana jiran fitowan suhail, sai bayan kaman minti goma ya fito daure da towel, da kyar Yazid ya shawo kanshi yaci Abincin Sannan ha kwanta, bai dade sa kwanciya ba bacci yayi gaba dashi. Sai da magrub Yazid ya tadashi sukayi sallah, falo suka dawo idanuwa suhail sun mugu kumbura sosai, babu kowa falo sai su biyu, mikewa suhail yayi yana cewa
"Let me check on anty..." Yafada bai jira abinda zaice ba ya bar wajen. Itama Mami bacci tayi har sai lokacin magrub ta watsa ruwa tayi sallah ta koma ya kwanta, knocking akayi bakin kofar tace
,"come in...." Kasancewan she's decent wearing long light gown, ahankali suhail ya bude Kofar ya shiga wearing Yazids jallabiya, Tana ganinshi ta Dan Mike zaune amma legs dinta na kan gadon, stool ya dauko ya zauna gabanta, yana kallon face dinta, itama kallon shi tayi taga he's eyes are so swollen tace
"Cutest kuka Kayi kou?.." Ta tambayeshi cikin damuwa, ahankali ya girgiza mata Kai tare dacewa
"Am just having headache..antyna sorry about today..." Yafada mata, ajiyan zuciya ta saki tare da komawa ta kwanta,
"Nagode cutest...you really make me feel better today..but pls ka auri humaira since tace ta amince..." Tafada mashi calmly.gani tayi ya daure face Sannan yace
"Anty pls mu bar wannan maganar...its. Pass tense...." Yafada atakaice, mikewa tayi ya zauna ta fuskanceshi Sannan tace
"If you do that Kai zaka wahala...kowa yasan you love her so much...pls don't do this to yourself..." Tafada mashi cikin whisper.
"I loved her before she rejected me publicly...anty ko humaira ce autar mata ban aurenta...nobody will make me..." Yafada mata atakaice, shuru tayi bata Kara cewa komai ba, ahankali ta koma ta kwanta hannunta kan cikinta, legs dinta ya Dan kurawa Ido yaga her feet is so shaped, he remembers lokacin a school sai ace mace Mai shape din kafa suna da juria da kuma dadin harka, kawai sai ya saki murmushi, kallonshi mami tayi tare dacewa
"What..." Da sauri ya dauke idonshi yana murmushi yace
"Nothing anty..."
"Ko dai we should get you check up..." Tafada cikin zolaya,
"Aa nidai anty ki bani maganin ciwon Kai....my head hurts..." Ya fada mata, ahankali ta Mike ta taka zuwa inda box dinta yake, shi kam har juyawa yayi yana kallon bayan kafarta, this days ya lura he stairs at her a lot, he don't really know why but it's fun watching her, yana kallon ta tayi bending ta dauko box dinta, kawai sai yayi tunanin ace Yazid ya ganshi yana wa anty such look yasan ba karamar tashin Hankali zaa yi ba, zaice raini né, magani ta dauko ta hado mashi da ruwa ya amsa yasha. Relaxing yayi kan stools in yace
"Yanzu anty kin samu sauki kou?.."
"Yes..." Ta amsa mashi while lying down again,
"Anty ki Mike zaune mana...it's not good lying between magrub and ishai..." Yafada mata, babu musu ta Mike, shima mikewa yayi tare dacewa
"Let's go downstairs..."
"anya I can't walk long distance..har Yanzu my feets are cold..." Gabanta ya dawo ya tsaya yana cewa
"Let me carry you..." Yafada yana Jan hannunta, for the second time today ya jawota jikinshi, ji yayi wani Abu na yawo from he's toes to he's head,
"Bari pls..." Tafada sounding angry, da sauri ya hadiye wani Abu ya ce
"Anty why...ni banso kina zama lonely..it will make you think worst..." Idanuwa tayi rolling tare dacewa
"I have been managing..." Ta fada mashi, har lokacin hannunta na cikin nashi, zarewa tazo yi taji ya riketa sosai, yana kallonta,
"Pls ka sake ni pls..." Tafada face dinta babu wasa Sannan voice dinta na rawa, ahankali ya saki hannunta yana cewa
"Sorry..." Yafada mata ahankali, hannu ta daga mashi alaman its ok. Komawa tayi ta zauna kanta kasa,
"Tou muje falo tou?.." Ya fada mata cikin sanyinmurya kaman zaiyi kuka
"Kaje am coming..." Tafada kanta kasa, bai Kara cewa komai ba ya fice, yana ficewa ta koma ta kwanta. Suhail na gani ta Kai minti goma bata sauko ba ya Mike ya shige daki.
The following day mami bataje office ba kasancewan she's not still feeling good, bayan sallah asuba ta koma ta kwanta sai bacci. Shikam suhail kwanciya yayi yana tunanin abinda yasa if he touches anty mami yake Jin wani iri, before ba haka yake ba, they play a lot amma Yanzu despite he's so sad he feels something, yasan yana da saurin Jin feeling but not like this, he don't feel anything if he's angry, amma jiya a wajen meeting dukda yana ji kaman ya kashe kanshi sai da yaji wannan abun then a dakinta, Kai ya girgiza trying to forget he's thought Don if anyone finds out zaayi tunanin he's trying to mock her because batayi aure da wuri ba.sai daf da asuba ya samu bacci. He's suppose ya fara zuwa office yau amma tunda kaka tace bai da salary babu inda zaije, karfe 8 Yazid ya gama shiri ya fita yayi breakfast ya hau upstairs ya gaida hajiya tare da fada mata Suhail na nan Dan Allah ta Lura dashi Don kar yaki cin abinci. Karfe goma hajiya ta sauko tasa Aisha ta kawai suhail abinci amma sai yace ta maida he's not hungry, Tana maidawa itama mami na saukowa,
"Ya akayi kika maido Abincin?.." Hajiya Ta tambayi Aisha,
"Mommy yace baici..Wai he's not hungry " Ta amsa mashi, mami dake kan last stairs tace
"Hala suhail né..." Ta tambayeta looking weak,
"Eh anty...baici komai ba..." Aisha ta amsa mata, ahankali mikawa Aisha hannu Aisha ta bata plate din Abincin, dakin ta nufa, hajiya zama tayi Tana kallon ta, bataji komai Don tasan mami loves and cares for duk Wanda ta sani, caring is in her nature, halinta yana burge mahaifiyar ta sosai, it makes her feel so happy to have a child that is selfless like Maryam, tasan ko bayan ranta halin Maryam zai ja mata rahama sosai, ahankali Maryam ta bude Kofar dakin suhail dake kwance cikin blanket ya bude kanshi, mami daya gani rike da plate yasa yayi saurin mikewa zaune yana cewa
"Anty good morning..." Ya fada trying not to look at her, not after what he keep imagining in he's brain,
"Morning..." Ta amsa mashi Tana ajiye Abincin agaban shi
"Wai why kakeso wasa da cikin ka??.. Bakasan hakan na iya janyo maka wasu problems din ba...komai sai kace you won't eat...now seat up and eat..." Tayi commanding dinshi, kura mata Ido yayi yaga ta rame sosai yace
"Anty kema Ai ba abincin kika ci ba.. " Yafada yana Turo mata baki kaman wani karamin yaro,
"Nidai Yanzu eat..." Tafada atakaice,
"Let's eat together tou...after all we both are sad..." Yafada yana kallon reaction dinta, babu musu ta ture legs dinshi baya ta zauna ta dauko Abincin ta ajiye kan gadon ta bude ta dauki Arish daya ta saka a baki, zama yayi yana kallon yanda take taunawa kaman ba abinci ba, kawai ya gane she's doing it Don shima yaci amma ba Don Tana son cin Abincin ba,
"Caring anty..." Yafada yana dariya, daure face tayi tace
"Kaci mana..."
"Anty my hands are dirty sai dai ki bani..." Ya fada mata,
"Eat with fork..." Ta umarceshi,
"Nidai anty just give me..." Ya fada cikin shagwaba, harara ta watsa mashi tace
"Kaci Wallahi ko mu bata da kai..."
"Ki bani..." Ya sake fada mata, bata Kara cewa komai ba ta dauki guda daya ta Kai bakinshi, bude bakin yayi ya amsa tare da lumshe idanuwa, ko kunya bai ji, ya saba da sangarta, kaman wasa tayi feeding dinshi ya cinye tas har dacewa
"Anty a Karo min..." Yafada yana licking bakinshi, harara ta watsa mashi ta Mike
"Tou anty ki bani ruwa..." Yafada kaman zaiyi kuka,
"Wai Kai har Yanzu gani kake you're a child kou?...." Baki ya Turo yana cewa
"Wajen wasu nii babban né...amma wajen ki ni yaro né.." Yafada cikin shagwaba,
"Lallai ma..." Tafada Tana daukan plate din
"Ka fito falo..." Tafada Tana fita daga daki, zama yayi yana dariya tare da biting lips dinshi, he's concentrating on her sosai and she's concentrating on him and it's making him feel somehow, ahankali ya Mike ya shiga bathroom ya kuskura bakinshi ya fito, gaban mirror ya tsaya yana kallon kanshi from head to toe, murmushi ya saki yana Shafa gashin kanshi Sannan ha dauki perfume din Yazid ya fesa kan jallabiya dake jikinshi Sannan ya fita falo looking so hot as usual.
12💙💛💜❤️💜
Lokacine
💛💚💜❤️💙
® zuwairat (ummumaryam)
1️⃣2️⃣
Free page
Mami na fita falo hajiya ta kalleta da empty plate ta saki dariya tare dacewa
"Suhail rigima...ya cinye kenan...da haka zai bar kanshi da yunwa..." Tafada cikin dariya, itama mami murmushi tayi Tana cewa
"Mummy suhail rigima né fa...Wai saida nayi feeding dinshi...kaman wani yaro..." Tafada Tana mikawa Aisha plates din, baki hajiya ta bude Tana dariya sosai,
"Kai suhail Allah ya sauwake...ko yaushe zai girma Oho..." Tafada, zama mami tayi tare da relaxing sai lumshe idanuwa take,
"Baby am happy wannan month din baki kwanta hospital ba...you're becoming strong my sweetheart..." Mahaifiyar ta tafada mata cikin so da kauna, idanuwa mami ta lumshe Tana cewa
"Mom it's not my happiness inyi stressing dinku..,I don't want to stress anyone of you..." Tafada hawaye na taruwa Idonta,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...mami you will never be a burden to me...kinsan bazai taba yuwa ki zamemin wahala ba...kawai am happy wannan Karin you're strong..." Tafada cikin rarrashi,
"Mommy what will happen if ban fiddo miji ba..,har wata ukun da kaka ta babu yayi?.." Tafada tashin hankali na kwance kan face dinta,
"Insha Allah Allah zai share maki kukanki...Allah zai share mana kukanmu...your husband will come..." Mom dinta fada mata, raurau mami tayi da idanuwa tare dacewa
"In bai zo ba fa?.. What will happen to me?.." Ta tambayeta voice dinta na rawa, suhail daya fito daga daki tsayawa yayi yana sauraron abinda suke cewa, kasa shiga falon yayi ya tsaya nan yana Jinsu, mikewa hajiya tayi ta koma kusa daita tare dacewa
"Baby be positive mana..." Bata Bari ta karasa ba tace
"Mommy for how long...for how long mommy..." Tafada Tana fashewa da kuka, suhail dake ringine Jikin bango ji yayi he's legs are weak,
"Baby ki Bari mana..remember Aisha is around..suhail ma is around..Dan Allah ki daina kuka..." Mom dinta ta fada hannunta biyu kan shoulder din mami Tana rirrigata,
"No mommy..let me cry...they all know what am going through...bazan iya boyewa ba anymore..." Tafada ciin matsanacin kuka,
"Pls baby ki Bari..." Hajiya tafada kaman zatayi kuka,
"Mommy my heart feels so heavy..mummy na gaji...am so tired..why am I different..."
"Because you're special..." Mom dinta ta amsa mata Tana kokarin maida tears dinta,
"Special people don't suffer the way am suffering...mommy am not special..mommy let me die before next three months..." Tafada cikin kuka sosai,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...mami why are you saying this..." Hajiya ta fada Tana fashewa da kuka, ahankali suhail ya zame ya zauna nan wajen babu Wanda yasan he's there, ji yayi hawaye na fito mashi, he wish there's something he can do for her, he wish zai iya sayo mata miji
"I wish I can marry..." Sai kuma ya dakatar da heart disnhi daga karasa maganar,
"Mommy na gaji..the husband issue bai hurting zuciya na kaman humiliation din kaka.,,, mom one more of it will kill me,..na gaji..." Tafada cikin matsanacin kuka, Aisha ce ta fito saga kitchen taga both mom da mami na kuka, bata nemi Jin komai ba itama ta fara kuka, hannu mami ta mika mata ta taka ahankali ta zo wajensu ta fada jikin mami ta cigaba da kuka, duk Wanda Bai sani ba sai yayi tunanin mutuwa akayi masu sabida yanda su uku suka hada Kai waje waya suna kuka, shima suhail yana chan gefe daya yana tayasu hawaye, he's heart is so broken,
"Anty Dan Allah ki daina kuka..." Aisha ta fada mata,
"Aa baby..let me cry maybe Allah will answer my prayers..." Tafada crying loud, Kai baby ta girgiza mata Tana cewa
"Dan Allah aa,,,kar kiyi kuka pls..." Aisha ta sake fada mata, amma bata daina kuka ba, sai kuka kawai take, Kofar falo aka bude alhaji ya shigo, ganin abinda ke faruwa yasa yayi saurin shigowa yana cewa
"Lafiya?." Ya tambayesu cikin tashin hankali, goge face hajiya da baby sukayi while mami ya cigaba da kuka, ahankali Aisha ta Mike ya bar su wajen ta hau upstairs, kallon su alhaji ya tsaya yayi for a moment Sannan ya gane it's because of mami
"Amma rukkaya kin bani mamaki..ke da zaki rareaheta sai ki tisata gaba kuna kuka?.. Kin taimaka kenan..." Ya fada sounding so angry, shuru hajiya tayi while mami was still crying loud,
"Taso kiji my sweetheart..." Alhaji ya fada mata mika mata hannu kaman wata karamar yarinya, ahankali ta Mike ta mika mashi hannu tare da bin bayanshi har part dinshi, nan ya dinga bata advice kan komai yayi farko zaiyi karshe Sannan nothing good comes easy, Don haka kar maganar Kaka ya tada mata hankali
"Dad am afraid...she can do what she said..." Mami ta sake fada mashi
"Don't worry..bazan Bari ba...Ai shuru hauka bane...kawai nothing will happen..." Ya fada mata, ahankali ta lumshe idanuwa Sannan tace
"Daddy...inason zuwa Saudia for the last time...kawai I want to go again..I feel this time my prayers will be answered..., ." Tafada still weeping,
"Ok babu matsala...amma after bikin Aisha kou?.."
"Daddy bikin Aisha yayi min nisa...dad if possible I want to follow next flight..." Ta fada mashi.
"Ok shikenan,,zan Kira musa...let's see when next flight zai tashi, sai kibi..." Yafada mata, dadi taji ta lumshe idanuwa tare da goge face dinta,
"Amma daughter ya maganar Wanda mom dinki Ta fada min...I think in dai bai da wani bad habit you should accept him...saboda ke da matarshi are friends shouldn't stop anything..." Shima ya fada just like the way mom dinta take fada, ajiyan zuciya ta saki Sannan tace
"Dad...am scared.,banason sunan traitor...I have seen enough and want peace now..." Tafada mashi
" yes dear...zaki samu peace of mind...accept him in kinje Saudi sai ki Kara adua kanshi...in ba blessing bane Allah zai sake maki da Wanda yafishi..but please baby don't let him go..." Dad dinta ya fada yana Kama hannunta,
"Dad Ina tsoro pls..."
"There's nothing to be afraid of,,,always am proud to have you as a child..mata da dama dake cikin situation dinki bazasuyi tunanin halin da ta gida zAta shiga ba..but ke you're compassionate and insha Allah bazaki taba Dana sani ba...Don haka accept him..." Ya fada mata atakaice
"Ok dad..." Tafada out of respect, murmushin Jin dadi dad dinta yayi Sannan yace
"Allah ya albarkaci rayuwarki..."
"Ameen dad,.," Ta amsa mashi. Ahankali ta Mike Tana cewa Bari in kwanta,
"Hope kinci abinci..." Ahankali ta daga mashi Kai, ficewa tayi daga cikin part dinshi, suhail kam tunda suka fita da dad ya koma ciki yayi ruf da ciki tare da rungume pillow, ji yayi ya rasa abinda ke damunshi, he's feeling so weird and crippy. Koda tazo straight ta wuce upstairs ta shiga dakinta, phone dinta ta dauko Sannan ya kwanta kan gado, number din alhaji Ahmed ta nemo Tana son dialing amma ta kasa, har yau bata bashi amsa ba and he's patiently waiting for her response. Mikewa tayi ta fita daga dakin ta shiga dakin mom dinta, zama tayi bakin gadon da take kwance tace
"Mom dad yace I should accept Ahmed..." Tafada sounding a little bit angry, ahankali mom dinta ta Mike tace
"Alhamdulillah..thank Allah ..am so happy..." Dan bata face mami tayi Sannan tace
"Wallahi mommy any slightest talks from he's wife na fasa..." Tafada cikin bacin rai, dariya mom dinta tayi tace
"Let's be positive jewel..," Tafada mata,
"Nidai i said my mind..at 32 I should look for peace..." Dariya hajiya ta karayi da karfi Sannan tace
,"you and this your age...kina son age dinki da yawa...wasu at your age suke ganin kansu yara..."
"Tab mommy..Lallai ma..." Ta fada Tana dariya,
"baby it's because kina yawan fadin age dinki but you look 25.." Mom dinta tayi complementing dinta, kallon kanta tayi tace
"Mom baki ganin wannan weight din?..