Author : ZUWAIRA UMMU MARYAM Category : African Stories & Novels
he has never noticed before, the unique thing about her when ever he stares at her for a very long time dole zaiga Abunda ya Kara burgeshi dangane daita, she's so beautiful and alluring, from he full lips to her full chest is something he never took a second to admire before sai Yanzu,
"My cutest in Allah ya yarda zanyi maka adua..I will pray for the best for you...Insha Allah you will stand boldly before her and tell her how much you love her...ka kwantar da hankalinka..." Tafada mashi,
"It's you that i love...am carving to have you my anty...am dying to tell you how much I feel for you...bansan haka zuciya ke tafiya ga Abu lokaci guda ba sai a kanki...anty I love you so much.?" Yafada cikin ranshi while staring at her like mirror, itama she looks at him for about a second Sannan ta dauke kanta sabida kallonshi is some how,
"Anty ki yi min aduar Allah ya zabamin wacce bazan sha wuya ba..." Yafada ahankali, Dan dariya mami tayi tace
"What's love without battle..ai so da yaki is sweet..according to professionals..." Dan dariya yayi Sannan yace
"Wai anty in tambayeki pls...but kar kice na rainaki..." Ya fad cikin manner,
"Hmmm indai ba rashin kunya zakayi ba..."
"Hmmm anty Wai ni Ina rashin kunya né?.. Nifa ban rashin kunya..." Yafada yana turo mata baki., ajiyan zuciya mami ta saki Tana tunanin ranar da baiga girmanta ko darajnta ba ya Kai bakinshi saitin nata,
"Bakayi alaji..now tell me..." Tafada Tana gyara zamanta,
"Wai anty Kin taba soyayya.." Ya tambayeta kaman yana wani Jin kunyar tambayan dariya tayi Sannan tace
"Maganar gaskiya nifa ban taba ba?..kawai nasan I do like people...amma har yau am not so crazy about anyone..." Ta amsa mashi sounding so truthful,
"Tou anty Yanzu Wanda zaki aura ma is just likeness?.." Ya tambayeta, shuru tayi with out saying a word
"Nidai Allah na gani Wallahi I don't think marriage will work out base on like..ai da so ake aure...ya fi dadi Wallahi..." Yafada cikin sanyinmurya, ajiyan zuciya mami ya saki Sannan tace
"Yanzu at my age sai in tsaya jiran love kafin inyi aure?.. Baka ganin age Dina?.. Am 32 for crying out loud Sannan ni macece ba namiji ba..bazan iya rayuwar sa ku zakuyi ba...kawai dai Yanzu am praying Allah yasa wannan auran should work out." Tafada atakaice, goshi ya dafa dayaji tayi maganar age,
"Anty pls nunamin age dinki..Wai Abu kadan sai kice age,,,Wai anty nifa ban ganin age dinki..Wallahi assuming ba family daga muke ba I will think you're 24 haka..in short Ina iya ganinki a hanya in tsaida ki Wallahi...kawai ki bar daukar age dinki as a big deal.?.age is just a number fa...you shouldn't concentrate on your age...," Yafada kaman zaiyi kuka, Kai mami ta girgiza mashi Sannan tace
"My dear you're just a child...,"wannan maganar ya Dan batawa suhail rai, Wai he's just a child, yanda tayi maganar irin ta rajnashi sosai ko kuma ita ta haifeshi,
"Yanzu my age should be my number one concentration...nifa macece...did you know that if am not lucky Yanzu at age 40 to 45 zan isa monopause?.. I might not have one child of my own..kasan dole in damu...dole inso inyi aure ko I will be lucky...I need to feel like a woman...and ga kaka gefe daya..She will just make life a living hell for me indai ban fiddo miji ba...so alhamdulillah Allah ya rufamin asiri...."
"Yanzu dai anty kedai babu maganar so..,kawai you're getting married...hmmm nikam Wallahi I can't come close to the person o don't love har in kwanta kan gado daya daita har ince I will be itimate with her...." Yafada kanshi kasa, mami juyawa tayi Sannan tace
"Wai Kai Baka komawa office?.." Ta tambayeshi forgetting about the discussion,
"Aa kawai zan jira in kaiki airport sai in tafi gida kawai..Wallahi ban Jin dadin jikina..." Yafada yana kara kwantawa nan kasa, tare da kallon bayanta,
"nidai babu ruwana if. Kaka ta gano... So you better go back to work..." Tafada mashi,
"Nidai ban zuwa koina....kawai if da akwai abinci ki bani..." Yafada idanuwanshi kan bayanta, rufe system dinta tayi Tana cewa
"Bari in Baka abinci sai inje inyi wanka in shirya..." Tafada Tana mikewa, yanda tayi bending makes something in him rise, kawai he's imagining what will happen if suna tare alone in same house as couple, ajiyan zuciya ya saki tare da lumshe
"What is happening to me....!" Ya fada under he's breath, juyowa mami tayi tace
"Kayimin magana?.." Ta tambayeshi, ahankali ya girgiza mata Kai with he's two eyes closed, kitchen ta shiga ta jero mashi abinci ta kawo ta ajiye kan dining sai binta yake da kallo har ta gama tace
"Zo kaci...zanje inyi wanka in shiryo..." Ta fada mashi, ahankali ya Mike ya koma kan dining while ita kuma ta hau sama, abincin bai wani ci sosai ba, wasa ya dingayi da abincinshi kaman yanda yakeyi this days, ita kuma mami bathroom ta shiga tayi wanka ta shirya, kafin ta gama shiryawa it was kusan 12:45 her flight is two amma dole taje kafin lokacin saboda hold up, Dan bag dinta ta dauko dressing in jallabiya Mai tsada sai kamshi take looking so breathtaking, dakin mom dinta ta shiga tayi mata bankwana, rakota hajiya tayi downstairs taga suhail, nan suhail ya gaidata cikin girmamawa Sannan ya amshi bag din hannunta suka fita looking so good together, hajiya na biye dasu suka isa waje, part din alhaji mami taje suka fito tare nan sukayi mata adawo lafiya Suhail ya bude mata mota ta shiga shima ya shiga suka bar gidan, yana tuki yana Dan janta da hira har suka isa airport, hannunshi rike da bag dinta har suka shiga ciki, atakaice dai suhail na tsaye har jirginsu ya tashi, he feels so sad and lonely, shi already yasan he's In love with her, amma how zai bude baki yace yana sonta, if he says that the whole family will explode sabida abubuwan da zai biyo baya,
"She's getting married..." Yafada ahankali yana tuki ya koma gida.
Bayan kwana uku
Mami ce a Saudi Tana adua, daman point of prayer dinta is Allah ya bata miji na gari, inda zata zauna lafiya,
"Ya rabbi..if alhaji Ahmed mijine a gareni Allah ka bamu zaman lafiya...ka samin sonshi cikin Raina,..,Allah indai bazan zauna dashi lafiya dashi ba Allah ka watse wannan maganar...ya rabbi indai hankalina bazai kwanta a tare dashi ba Allah ka zabamin wani..ya rabbi indai driver kaka alkairi né gareni I won't argue,,,ya rabbi indai alhaji Ahmed ba alkairi bane gareni rabbi ka kawomin wani...ko kuturu né bazanyi gardama ba...ya rabbi ka tausaya min...ya rabbi ka Rufamin asiri Kaman yanda kake rufawa sauran bayinka...ya rabbi indai aure alkairi né gareni let my time be now...in kuma ba alkairi bane gare Allah ka zaba min abinda yafi alkhairi..." Wannan shine prayer point din mami tunda ya shiga the pure and holy land, tunda tazo batayi magana da yan gida ba, kawai adua take babu dare babu rana, she's always in the mosque praying to Allah, wannan Karin tayi adua sosai ba kasan ba, at time sai tayi Dana suhail, shima Tana roka mashi Abunda yafi alkairi gareshi. Ahaka ta Kai 5 days a kasan Saudi, haka nan she feels so happy because Tana Ji a jikinta her prayers have been answered,
Suhail kam tunda yake bai taba shiga damuwa irin wannan ba, the more mami na adua a Saudi the more Ana hura mashi wutan sonta cikin zuciyar shi, he can't believe wannan is him, babu maganar da yake sai mami, in yana office sai ya tambayi Yazid I'd sunyi magana da mami.
Manage.
Lokacine 19💚❤💛🧡Kawai bashi da maganar da yake sonyi sai na mami, he will be like mami this mami that, sai ya tambayi Yazid mami kaman sau biyar kafin su bar office, yau ma office disnhi ya Bari ya dawo na Yazid ya zauna face dinshi duk babu walwala he looks so dull and pale abinka da farin mutum,
"Pls for the last time ka bani number da mami ke amfani dashi a Saudi...there's no way I will believe you're not communicating with her..." Suhail ya fada cikin damuwa, Yazid dake duba wasu files ya kalleshi kaman zaiyi magana Sai kuma ya dauke Kai ya cigaba da aikin da yake, tsoki suhail yaja yana cewa
"wato bani da amsa kenan kou...ga mahaukci yana magana abi?.." Yafada sounding angry, idanuwa Yazid ya sake dagawa ya kalleshi tare Dacewa
"Kai din né da abun haushi...I told tun tuni cewa bani da number da Mami take amfani dashi..inshort she's not using any line because bamuyi magana ba...amma Kai sani gaba sai damuna kake..salon kaja kaka ta tsigeni..." Yafada yana maida hankali kan abinda yake, mikewa suhail yayi ya dafa goshinshi da one hand Sai kuma ya rike waist disnhi daya sha belt da Dayan hannun, steps ya dauka kaman biyu zuwa gaba sai kuma ya sake daukan biyu zuwa baya, kawai he looks so confused and disturbed, Kai Yazid ya daga ya kalleshi tare dacewa
"hope dai ba Don anty mami kake Wannan through and fro din ba?.." Ya tambayeshi sounding weird Don baki ya saki yana kallon yanda suhail ke gaba yana baya, suhail baiyi magana ba ya saki Ajiyan zuciya tare da komawa ya zauna, mikewa yayi sai kuma ya sake komawa ya zauna tare da Dora kanshi kan table din Yazid,
"tou fa..." Shine abinda Yazid ya fada yana kallon suhail, ahankali suhail ya dinga sakin ajiyan zuciya while turning he's head from side to side,
"Wai meye haka?.." Yazid ya tambayeshi sounding so disturbed saboda yanayin shi abinda tambaya né, ji ya daga ya kalli Yazid tare dacewa
"Kawai am having a feeling né..." Yafada atakaice, gira daya Yazid ya daga tare dacewa
"What sort of feeling?..bad?..good?.. Which one?.." Ya tambayeshi, suhail sakin ajiyan zuciya yayi tare dacewa
"Nidai kawai gani nan..I don't really know..." Yafada yana ware mashi hannuwa tare da mikewa tsaye, kura mashi Ido Yazid yayi for a moment sai ya saki dariya yana cewa
"da gani Kai da anty mami kun fini shakuwa Yanzu tunda Kai you're having a feeling and am having nothing..anyway relax anty mami is alright..nasan kawai batasan Ana damunta da calls né shiyasa ta kashe wayarta...after all is a week trip..Yanzu nan da kwana biyu kou uku zata dawo..." Yafada mashi, Don ko kadan bai San feeling da suhail ya fada means he's falling for mami ba, shi kanshi he's not sure what exactly is happening to him ba, kawai he's feeling he's heart is attached to her that he can spend 10 whole minutes without thinking about her,
"Allah yasa she's alright..." Suhail ya fada mashi cikin sanyinmurya yana komawa ya zauna,
"she is..." Yazid ya amsa mashi. Shuru yayi ya kurawa waje daya Ido kaman he's thinking, Yazid bai Kara bin ta kanshi ba sai kusan bayan minti biyar ya daga ki ya kalleshi tare dacewa
"Wai Kai Baka komawa office Dinka?.." Yazid ya tambayeshi, idanuwa suhail ya lumshe tare dacewa
"inajin fever na néman rufeni...feel my temperature kaji..." Yafada mashi, ahankali Yazid ya Mike ya zauna kan desk dinshi ya taba gaban goshinshi yaji it's getting hot,
"Yes you are...hope dai ba Don anty mami kake running wannan fever ba?.." Ya tambayeshi,
"Dan Allah ka kyaleni...Nidai kawai gani nan..." Yafada mashi yana maida kanshi kan table din,
"Kaje company clinic ka kwanta...daman your face looks pale..kilan su gano abinda ke damunka.." Yazid ya fada mashi, suhail saka hannu yayi cikin aljihu ya fiddo wayar shi, galary ya shiga yana searching ko yana da picture din mami amma sai yaga bai da ko daya, babu picture din mace cikin wayrshi sai ta humaira itama tun ranar da ya ganta da wani yayi clearing, wayar Yazid dake kan table dinshi ya saka hannu ya dauka,
"What?.." Ya tambayeshi,
"I want to check if kana da complete Quran...nawa babu..." Yafada yana kokarin mikewa, Yazid bai ce komai ba ya maida hankali kan aikin da yake,
"Zanje clinic..if am through transferring it zan bawa messenger ya kawo maka..." Yafada atakaice bai jira abinda zai ce ba ya fice daga office din. Nashi office ya koma ya bude wayar Yazid ya shiga gallery dinshi yana duba pictures dinshi, he was lucky he found almost 20 pictures din mami cikin wayar, bai tsaya bata lokaci ba ya fara marking duk picture da take ciki yana turawa cikin wayrshi, yana gamawa ya mikawa messenger ya kaiwa Yazid, zama yayi yana analyzing duk picture dinta, da akwai Wanda take kan hospital bed hannunta Mai cannula cikin hannun Yazid sukayi wannan picture, she looks so young and beautiful, idanuwa ya lumshe yana cewa
"Anty mami na shiga uku...my heart is taking me to place am not suppose to go..." Yafada yana kallon picture din , da akwai Wanda Tana falonsu Tana tafiya Yazid ya dauketa, da gani batasan ya dauka ba, kanta babu dankwali, she looked tired a cikin picture din, kallonta yayi from her head to toe, she har yau yana ganin kilan mistakes din age dinta akeyi amma ko da wasa bai yarda ta Kai wannan age din ba, da ake cewa yara suna auran manya sai Yanzu ya gane dalilin hakan, if Allah ya dora maka sonsu zakaga Allah ya dauke maka ganin girman age dinsu da kuma duk wani aibu dake tare dasu, shi Yanzu kallon yar karamar yarinya that he can hold to himself yakewa mami. Kawai abinda yake bashi mamaki is yanda akayi duk wannan feeling din babu sai Yanzu suke rushing into him Kaman zasu kasheshi,
"Now that she's getting married..." Yafada cike da damuwa,
"rabbi you know best..but pls don't let me suffer ya rabbi..." Yafada yana kallon picture din, ahankali ya koma clinic Don ya samu daman kallon picture dinta da kyau.
Mami kam kullum her prayers are the same, kawai maganar ta Allah ya kawo Wanda yafi alkairi in kuma alhaji Ahmed ne mafi alkairi Allah yasa ayi dashi, she prays a lot har ranar dawowanta yayi, ko pin bata sayo daga Saudi ba, asalima ko fita batayi iyakanta masjid Sai kuma masaukin mai waazi Wanda ke saudia Wanda duk family dinsu dayaje nan yake sauka.
Kafin mami ta dawo Nigeria suhail ya mugun fita hayyacinshi, ya rame ya damu, dad disnhi na tambayan shi abinda ke damunshi, shi kanshi bai iya cewa ga Abunda ke damunshi kawai dai yasan bai samun bacci Sai kuma yawan tunani, mom disnhi ma Tana tambayanshi why bai cin abinci like before sai yace he's not having much appetite né. Wajen karfe 12 yana zaune a office din Yazid sai wasa yake da kan pen dake hannunshi but he's so lost in thoughts,
"Kaidai Yanzu na gane ka fara boyemin abu...duk ka rame amma kaki ka fadamin exactly what is happening to you..." Yazid ya fada mashi cikin damuwa, suhail daga idanuwa da suka koma kaman yana Jin bacci yayi ya kalli Yazid tare dacewa
"Hmmm kawai I can't say exactly Abunda ke damuna...but I will give anything to be normal again..." Yafada cikin Sanyinmurya, ajiyan zuciya Yazid ya saki before saying
"I know it's about humaira...duk sannan heartbreaks din né ke néman ja maka..." Bai karasa ba yaji anyi mashi message, shuru yayi ya dauki phone disnhi ya bude message din, Dan murmushi ya saki tare da turawa suhail wayar gabanshi without saying a word,
"Menene?.." Suhail ya tambayeshi yana daga wayar, Yazid bai amsa mashi ba, suhail duba message din yayi yaga an rubuta
"Pls little bro if you're not too busy pick me up from the airport by 1:30..reply.." Ya karanta sai ya duba sunan sender yaga anty mami, da sauri suhail ya ajiye wayar ya Mike yana cewa
"Let me pick her..." Yafada yana barin office din, dariya Yazid yayi yana cewa
"You're mad internationally..." Bai karasa ba suhail ya dawo ya dauki wayar daya ajiye ya rubuta mata
"Am sending suhail..am a bit busy today.,he's on he's way..he said zai jiraki har ki sauka..." Ya rubuta sai ya tura mata Sannan ya ajiye wayar ya fita daga office din,nashi office din ya koma ya dauki car keys disnhi ya fice kaman lokacin yayi. Kawai sai yaji duk wannan damuwa is gone, at least zai samu ganinta,yasan duk wannan damuwa is as a result bai ganinta né, amma today zai ganta, daya saura ya iso airport yayi parking ya shiga ciki yana jiran jirginsu ya sauka, daya da minti goma suka iso, suna landing ya fito yana jiran saukowanta, after like 5 minutes ya hango ta, what he experienced is somethings he never experienced in he's whole life, babu abinda yake gani a face dinta sau wani irin haske da annuri, tamkar an Dora wni florescent light a gaban goshinta haka ya gani, her faces bright more than daylight it's self, kawai he's looking kaman bai taba ganin ya mace ba, yau he thought zai iya controlling kallon amma ko kadan ya kasa, ji yayi Ana saka maki hannu cikin Ido yayi saurin blinking, murmushi ya saki itama ta saki murmushi Tana cewa
"Cutest how far?... " tafada Tana dariya, shima dariya yayi ya lumshe idanuwa tare da sakin ajiyan zuciya Sannan yace
"Alhamdulillah anty mami..and you?.."
"Fine lil bro...ya aiki." Ta tambayeshi Tana tsaye gabanshi Tana daga Kai ta kalleshi saboda daman height dinshi yafi nata sosai,
"Fine antyna na Kaina..." Yafada yana bending Don amsar bag din hannunta, intensionally ya taba hannunta tayi saurin sakin bag dinta tare da yarfa hannu Tana cewa
"You're full of electricity..." Tafada cikin zolaya, baki ya tale kaman zaiyi mata kuka yace
"anty meye electricity kuma?.." Dariya tayi sosai cikin zolaya tace
"Baka ganin hannu ka zaiyi electrifying Dina?..." Ta fada mashi Tana kallon hannunta,
"Anty nayi missing dinki like crazy...kuma Dan wulakanci ba'a Kira mutum..." Ya fada idanuwa cikin nata,
"Wayyo Allah my bro..sorry kawai banason damuwa né...I want to concentrate on abinda ya kaini chan..shiyasa...sorry pls..." Tafada mashi, ahankali ya juya Tana biye dashi, Dan juyowa yayi yace
"Am angry..ko you miss me too bazaki fada ba..." Ya fada yana turo baki yana tafiya,
"Haba in Banda abinka da akwai Wanda nayi missing kaman Kai?.. I miss you a zillion