Author : ZUWAIRA UMMU MARYAM Category : African Stories & Novels
nayi kar ya sake wannan naganar amna shine yayi son zuciyar shi.. Pls don't see my fault... "yafadawa alhaji yunusa while both of them are heading towards their cars
"haba Dan uwa wallahi ba Komai..ka tuna ba yau muka San junanmu ba... Nasan baka magana biyu... Kuma wallahi ko kadan ban gan laifinka ba... Allah yasa hakan shi yafi alkhairi.. Komai Lokacine.. Haka Allah ya kaddara auren mami... Kar kaji komai.. Saidai ina hango Babban matsala... "tsayawa alhaji Muhammad yayi shima alhaji yunusa ya tsaya, ahanakli alhaji yunusa ya cigaba dacewa
"ina tsoron abinda zai biyo baya ta wajen mahaifiyar suhail..."da sauri alhaji Muhammad ya daga mashi hannu tare dacewa
"wannan ba matsala bane... AI nine mijin kuma in har tana son zaman lafiya dole ta natsu... Aure dai an daura...don haka ko kadan kar ka dauki wannan as matsala... "yafada mashi calmly with confidence,
"shikenan yaya... Yaya yanzu yaushe zamu samu lokaci muyiwa yab uwa da abokan arziki godiya kan abubuwan da sukayi?..don yanzu wannan bikin bamu da sauran abinda zamuyi.. Iyaka mu Nada hannu muyi kallo... "alhaji yunusa yafada in a funny way, murmushi alhaji Muhammad yayi cikin ranshi yana jin dadin da danuwanshi baiyi misunderstanding dinshi ba, ajiyan zuciya ya saki sannan yace
"AI bamu sukayiwa VA yaransu sukayiwa don haka su zasu je yi masu godiya... "ya amsa mashi, hirar su suka cigaba dayi kaman nothing happened sannan suka rabu.
Karfe biyu hajiya rukkaya ta dawo gida bisa umarnin yayarta, har lokacin bata bar hawaye ba, her heart is boiling, ita ba wai age different din ne problem dinta ba, kawai tana bakincikin her beloved daughter is now married to the sun of a woman who hates her more than death it self, yazid ne ya fara dawowa gidan ya wuce dakin mom dinsu, nan GA ya ganta kwance tana hawaye, zama yayi bakin gadon ya fara mata magana cikin tattausar lafazi kaman he's not the son, kawai yana nuna mata haka Allah yaso tayi hakuri tayi masu adua, sai da ya gama magana tace
"daman you're happy about it... It's what you always wanted. Ina kallon yanda ka rike mashi hannu kafin yayi wannan maganar... It's me and you a gidan nan... "tafada still crying,
"wayyo Allah mummy.. Ni har na isa in sa a daura auren anty mami... It's kaddara... "
"dalla rufe min baki... "ta ha hantareshi tare dacewa
"ina mami take... "ta tambayeshi cikin jin haushinshi,
"dazun kaka tace suhail yaje ya kaita hospital..." surprise look hajiya tayi mashi sanna tace
"and you're here saying long story ...better call him ya fad'a maka inda ya kaita... " tafad'a mashi sounding so Angry, babu musu yazid ya saka hannu cikin aljihunshi ya fiddo wayarshi yana searching number suhail.
Suhail kam ko Minti goma baiyi cikin mota ba ya fita har lokacin inda mami ta shaka mashi allura b'ata bar zafi ba, he feels the pain deep inside, kaman ta taba mashi wani abu a ciki haka yake ji, bakin kofar inda take yaje ya tsaya yana sauraron yanda take kuka, sai nishi kawai take alaman Shes tired of crying but don't want to stop, jingina yayi da bango wity he's two eyes close, yafi minti biyar tsaye sannan ya bude kofa ya shiga ciki, swollen eyes dinta ta daga ta kalleshi ta nuna. Mashi hanyar waje without saying a word, ahankali ya samu kan kujerar dake wajen ya zauna
"out... "ta fad'a cikin matsanacin kuka
"sorry... "yafada cikin sanyimurya, cikin shessheka tace
"suhail I loved you more than duk cousins dina... I cherished you... I adore you... Amma kaine Kaja min zagi da kunya... I begged you... What did you want from me... "tafad'a sounding so tired, kura mata ido yayi yana kallon yanda take magana da kyar
"pls stop talking.. Ki huta... "yafada cikin sanyimurya, kai ta girgiza mashi tare dacewa
"suhail tell me menayi maka to deserve what you did to me... "tafada cikin shessheka
"bakiyimin komai ba... "b'ata Bari ya karasa ba tace
"then why... "ta sake tambayar shi babu wasa,
"because I Mean everything..."still ta sake katse shi dacewa
"what did you mean suhail... What could it be suhail... "ta tambayeshi in an intimidating way, hannu ya dora a goshi tare da lumshe idanuwa,
"ina sauraron ka... "ta sake tambayar shi,
"mami i love you... " yafada mata kai tsaye, idanuwan ta lumshe hawaye na sake gangaro mata, wannan love word is just like hot water kan heart dinta, yana mata ciwo sosai in taji yace he loves her, sai yanzu ta gane namiji bashi da kunya, tana mamakin yanda akayi suhail zai kalleta ya dinga furta mata I love you, hawaye kawai take
"mami... "ya kirata ckin sanyimurya, da sauri tace
"wai baka jin wani abu calling me by my name ?..pls baka jin wani iri?.." ta tambayeshi cikin takaici
"haba ai ba maryam nace ba... " Yafada calmly
"suhail Allah yaisa tsakanina da kai... Wallahi sai ka sakeni... I will transfer your sadaki back to you... " tafada out of anger
"hmmm antyna kenan... Wai baki tunanin Allah ne ya kaddara?..nasan you never prayed for a husband like me but nasan you prayed for the best and Allah ya baki ni..baki ganin if you do otherwise zaki batawa Allah rai... " kai mami ta kauda tana jin bakin ciki na ratsa zuciyar ta, wayarshi ne yafara ringing yaga yazid, picking yayi ya fad'a mashi inda suke ya kashe sannan ya kalli mami da idanuwanta lumshe but hawaye na fitowa yayi yace
"pls me zansamo maki kici?. "ya tambayeta, wannan ya kara b'ata mata rai, the most annoying part is yanda shi yake ganin everything will work, ita kam tasan it's not possible at all, there's no chance in hell kawai take tunani. Har wajen minti arbain b'ata Kara bude ido ba balle yayi mata magana ta amsa mashi, kawai she's thinking of how to get out of this mess, takaici da bakinciki sun hanata sukuni, bude ido tayi ta kalli kanta, she don't even know why She's here while she's alright,
"sister... "tafada da karfi Wanda yasa suhail that is deep in thought dawowa hayyancinshi, sake kira tayi sannan wata ta shigo,
thanks
biya kudin karatu ba kika karanta Allah yaisa37
For those that suna son biya amma har yau basusan ta yanda zasu biya ba, you don't have to call pls, kawai send 300 to 0024878383 stanbic ibtc Zuwairat haladu sai ki turo screenshot zuwa 08106102727 via whatsapp kou kuma ki tura mtn card na 300 to 08106102727 shima ta whatsapp bata message ba, kou kuma kiyi transfer na Kati shima mtn na 300 ga number sama sai ki turo screenshot dinki zuwa ga same number ta whatsapp, remember it's kudin karatu not kudin mallaka. Nagode
labewa yayi gabanshi na mugun faduwa like never before, he's so scare to death, wani irin mugun tashin hankali yakeji, tamkar ana drum a kirjinshi haka yake ji, hajiya hassana sai nishi kawai take tana kwance kan gadonta, duk tashin hankali duniya ta dorawa kanta saboda bakin halinta, just imagine someone thinking you don't deserve something saboda nasu son zuciya ko wata bukata tasu, kaman ya koma yake ji because he knows it's definitely a bad time, but he knows it's now or never, yasan dole yayi facing dinta, adua ya dingayi a zuciyar shi Allah ya huci zuciyar ta, sai da ya kai kusan minti goma nan bakin kofar sannan ya lumshe cute eyes dinshi ya dora hannu kan knob din ya murda ahankali tare da sallama, aikam hajkya najin sallamarshi ta Mike da sauri ta shakumoshi tana cewa
"suhail.. Ni?.."tafada sounding so bitter tana nuna kanta,
"ni zaka tozarta suhail?..ni zaka maida abun dariya... " tafada sounding very harsh tana girgiza shi alhalin shi kuma ya dora hannunshi biyu kan nata in a tender way idanuwanshi cike da kwalla saboda yanda take kuka tanacewa
" suhail yau zaka fadamin abinda nayi maka kakeson ganin bayana... Yau sai ka fadamib abinda nayi maka da ban chanchanci in baka umarni kabi ba... You must tell me... " tafada tana rike da wuyar rigarshi da hannu bibbiyu kaman she wants to box him,
"mummy sorry... " AI bai k'arasa ba ta daukeshi da wani irin giggitaccen Mari, yayi saurin dafe inda ta mareshi because it hurt like crazy,
" wallahi ba hakuri zaka bani ba... Fadamin laifina zakayi... " tafada still crying very loud kaman itace aka mara,
"bakiyi komai b... " still the other side of he's cheek ta sake Mari da karfi, kuka suhail ya farayi Don she's slapping him with all her strength, tamkar Babba ya Kama Dan karamin yaro yana hukuntawa haka take mashi despite he's taller than her amma marinshi kawai take kaman he's just a boy who have committed an artrocities, he's crying like a baby yana cewa
"mummy ki kashe ni if That will make you happy but wallahi I love her... " yafada cikin matsanacin kuka, wani irin matured Mari hajiya hassana ta sake daukeshi dashi tana cewa
"wallahi saidai ka mutu... I will strange you myself... Wallahi it's better in saka maka guba ka mutu da ka auro wannan yarinyar... "tafada tana shakeshi sosai
"do it.... Kill Me... " yafada yana kuka, cikin kuka tace
"suhail me nayi maka?..why won't you make me happy for once?... Why bazaka saka ni proud as a mother ba?.. Me nayi maka... " tafada tana girgiza shi da dukkan karfin da Allah yayi mata, shi kuma ya sakar mata duk jikinshi tana yanda ta gandama dashi, kuka ya dingayi hannunshi biyu kan cheek dinshi.
suhail bai dade da fita daga part din mahaifin shi ba shima ya fita daga nashi part din, part din hajiya hassana ya nufa because he wants to know how everything is going, yana kallon shi ya ciki, ahankali ya taka yaje bakin kofar yana jin duk abinda hajiya take cewa, he want her to take her anger out ko zata ji sauki cikin ranta tunda ita ta dorawa kanta wannan balain.
"mummy I love you... Wallahi ban taba yin wani abu don in munana maki ba... Amma wannan is above me... Pls kiyi hakuri... " yafada cikin kuka kaman ranshi zai fita,
" then do the right thing... Ka saketa this instant.... " ta daka mashi tsawa, sabon kuka ya farayi yana cewa
"momma... laifinki zai shafeki... You hated them for no reason... Now I love her for no reason...wallahi mummy without her mutu.... " wani irin mahaukaciyar Mari ta daukeshi dashi ya saki sabon kuka sosai yana cewa
"yes... mutuwa zanyi... " yafada kaman ranshi zai fita,
"wallahi ka saketa saidai ka mutu... Nidai kake fadawa hakan kou... Wato ni kake fadawa laifina zai shafeka?..wallahi sai ka saketa... " tafada tana turashi da karfi ya fadi kasa, kuka ya cigaba dayi yana zaune kasan tiles, tana kuka ta dinga neman takarda da Biro,
"wallahi sai ja saketa... Ko kuma ka zaba tsakanin ni daita... Wallahi ban yarda... "tafada crying very loud, duk alhaji Muhammad na sauraron su, da sauri hajiya ta dauko pen da takarda tana mika mashi
"Dan ubanka rubuta mata.. Saki uku... Be fast about it. " tafada cikin matsanacin tsawa, suhail kin amsa yayi yana kuka yana cewa
"mummy kiyi hakuri.. Wallahi Inason mami... " yafada yana ja baya saboda yanda takeyi kaman zata harbeshi da kafarta,
"wallahi sai ka rubuta mata yanzun nan... Right now take it... Ko Kuma in tsine maka yanzun nan... Now take it..." ta daka mashi tsawa tana hawaye, kin amsa yayi yana ja baya,
"wallahi zan tsine maka.. Wallahi I will curse you da ruwan nonona daka sha...nothing in this world will make me accept her..so Write it now..." yafada babu wasa, suhail na kuka ya amshi paper daga hannunta, hannunshi na rawa ya amshi pen da second hand dinshi, alhaji Muhammad dake labe bude kofa yayi ganin haukan nata bai karewa, cikin kuka sosai suhail ya kalli mahaifinshi da swollen face dinshi yace
"daddy tace in saketa... Tace should divorce her ko ta tsine min... I have no choice... " yafada cikin matsanacin kuka, wani irin disgusting look alhaji yayi mata sannan yace
"write..and ki sani kome ya rubuta mata also applies to you too...in uku ya rubuta kema na baki uku... Naga haukanki bai karewa...i have given so much liberty that I have no single respect a idonki.... Wallahi in suhail ya saki mami babu ni babu ke... I mean it this time around... " yafada sounding so bitter, suhail susucewa yayi, hajiya hassana dake kuka tace
"wato abun har ya kai haka?... Ya kai ka hada aurena da auren wannan yar gidan munafukar matar... Muguwar matar... " ta fad'a Tana kuka
" tell me one thing da tayi da kike ganin b'ata chanchanci suhail ya aureta ba... Tell me only one... " yafada yana kwace paper da pen daga hannun suhail ya nuna mashi hanyar waje alaman ya fita da sauri suhail ya fita, kaman na kwace shi daga hannun terrorist haka yaji,
" you know uwarta b'ata sona... " tafada cikin kuka, bai Bari ta k'arasa ba yace
"kece dai bakisonta... Kowa na family din nan yasan you're the evil one.... Kowa yasan kece mara mutuncin...auren suhail da mami will serve as a punishment to you... You will sit and watch her zaune da suhail da yaransu... Kilan ya zama ajalinki.. Amma wallahi kika kuskura ya sake ta ke na saka... " ya fad'a mata sounding so frank, abunka da Dan Adam Wanda idonsu ya rufe, ko kadan b'ata ganin laifin kanta, idanuwanta sub rufe ruf da b'ata ganin komai sai wannan kiyayya da take ji, ko ana nuna mata gaskiya b'ata gani balle ta dauki gyara,
"wato kaima an asirceka... In ba asiri ba yazaayi dana Dan matashi sardidi dashi ya auri wannan tsohuwar da baa San bakin jinin daya hanata aure ba... "
"danki yafi manzon Allah S. A. W daya auri macen that is far more older than him?..." hannu ta daga mashi tana cewa
"ni kar ka kaini inda ban kai ba... Maganata daban maganr ka daban... Bai yuwa dana ya aureta... " shoulder alhaji ya daga yace
" wannan ya rage naki... Suhail kam yayi aure... Any attempt to stop it will affect you too... " yafada atakaice tare da juyawa,
"wallahi sai dai in bar gidanka...wallahi it won't happen... "
"it already happen... Do your worst... " yafada atakaice ya bar dakin, hajiya wulla kanta tayi kan gado tana bude sabon babin kuka kaman wacce akayiwa mutuwa, mutuwar ma na important person.
Suhail na shiga part dinshi ya tsaya a gaban mirror yana kallon yanda hannu mahaifiyar shi ke kwance kan face disnhi on both sides, kuka ya dingayi yana kallon face dinshi, ya san mum dinshi sosai, she don't give up easily on things, kome ta saka agaba sai ta GA bayan wannnan abun, yasan in har yana gidan nan she won't leave him har sai ta sa ya rubuta sakin ko da kuwa hakan zaisa ta rasa nata igiyan auren, she's a determine person, she don't care about the results of her action, kome takeso shi zatayi, bag ya dauko daga saman closet dinshi ya bude bag din sannan ya bude closet ya dauki kaya kaman kala biyar ya saka ciki, zipping bag din yayi ya dauki ATM dinshi ya fito, daidai lokacin da dad dinshi ya fito daga part din hajiya, yana ganin shi da bag yace
"ina zaka?. " ya daka mashi tsawa,
"daddy... Gidansu... " bai k'arasa ba yqce
"go back and return the bag.... Kar ka Bari in maimaita maka... " ya fad'a atakaice yana shigewa nashi part din. Jiki ba kwari suhail ya koma ciki ya ajiye bag din kan gado sannan ya shiga bathroom yayi wanka har lokacin bai bar hawaye, dayake love is a powerful thing yana zaune cikin bathtub sai yasaki murmushi tare da biting lips dinshi.
Mami na isa gida tun a falo ta fara sabon kuka tana hawayen upstairs, babu kowa falon, tana hawa ta shiga dakin mahaifiyar ta, hajjya dake kwance tayi saurin daga kai, tana ganin mami ta Mike zaune, kaman anyi mutuwa mami ta rungume mahaifiyar ta ta dinga kuka itama hajiya tana tayata
"mummy... Yanzu duk jiran danayi... Suhail ne mijina?. " tafada tana kuka sosai, shafa kanta hajiya tayi tace
"jewel... Tunda nake.. Ban taba tsintar kaina cikin bakin ciki mara misaltuwa ba kaman yau.... Amma. Ya na iya... Ya muka iya da ikon Allah... " ta fad'a tana hawaye,
"mummy... Na gaji.... Da rayuwar bakin ciki... Kilan mutuwa zai fimin sauki... " tafada sounding so fed up With life, wani gajiya kawai takeji da rayuwa, ahankali hajiya ta girgiza mata kai
"aa... Bazakice hakan ba... Komai na da lokacin.... "
"mummy am tired.. I want go rest... Kilan bana cikin Wanda Allah ya kaddarawa hutu a duniya... Maybe if I die I will rest.." tafada cikin kuka sosai, hugging dinta hajiya tayi sosai tana cewa
"jewel.... Kilan hutun ki na gaba.." kai mami ta girgiza mata face dinta sharkaf da hawaye tace
"mummy happiness with suhail as my husband?... Mutumin da mahaifiyar shi ka slaughter me without a second thought?... Kanin bayana?.. Mummy inason suhail amma not as husband at all... I can never see him as my husband... " tafada Tana kuka, shafa kanta kawai hajiya take, tana jin kukan mami har cikin zuciyarta, her daughter have suffered a rayuwa, ba wai suffer na rashin wani abu na rayuwa ba, suffer Wanda yafi rashib wani abu ciwo, rashin mijin aure is some thing that ko billionaire can give up her wealth for, duk yanda mace take yau in b'ata da miji kallon da ake mata daban,