Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Lokaci Ne Soyayyar da Ta Zo Bayan Jinkiri BY ZUWAIRA UMMU MARYAM

Author :  ZUWAIRA UMMU MARYAM Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 75

6K to 9K   out of 224.1K words

kisha..." Ta fada Tana shiga dakin, kaman bata so ya amsa ta kafa Kai, sai da ta shanye tas Sannan ta daga Kai ta mikawa mami dake tsaye Tana Shafa Bayanta cup, ruwa ta dauko mata Tasha,
"Yauwa sweetheart..yi sauri kiyi sallah..Nima Bari Inje Inyi.." Ta fada mata Tana fita daga dakin rike da cup din.


Share...
3💛💙❤💚💜
Lokacine
💙💛❤💛💚


® zuwairat (ummumaryam)


3⃣


Free page


Dedicated to my anty...love you..



Tana  shiga dakinta ta watsa ruwa Sannan tafito da alwallah tayi sallah , nan kasa ta kwanta Tana kallon sama, kawai her young life is reflecting, she's thinking about lokacin da take in her 20s, lot of people come for her hand in marriage, cikinsu har da family amma dad dinta yace tunda medicine take karanta kar tayi aure karatun ya shirirce, she remembered yanda kaka da dad dinta suka samu sabani saboda hakan, ita dai bata taba cewa komai because daman she's not in love with any specific person, Sannan she don't hate anyone among her suitors, she's always neutral, cousin dinta daya sota kaman hauka wato salim is now married with 3 beautiful children, duk sanda sukaje family meeting haka zai dinga nan nan da yaranshi da wife dinshi duk Don ya bata haushi but she never cares, juya kwanciyar ta tayi Tana tuna yau saurin kwana biyar family meeting, har fargaban karshen wata take saboda kaka, she harasses her fiye da tunanin Mai karatu, har cewa take zata nemo old man ta bada ita kyauta, duk ranar da akayi family meeting dole sai ta kwanta hospital saboda tashin hankali,
"Am tired..." Tafada under her breath saboda bakincikin rayuwa,
"Ya rabbi in bani da rabo duniya ka dauki rayuwata ka bani rabona a cha,.." Tafada hawaye na fita daga idanuwanta suna shiga kunnenta, tunawa take da friends dinta da suka gama secondary school tare wasunsu nada yara biyar wasu hudu wasu har shida, tun farko Tana zuwa gidajensu saboda zumunci amma sai wasu suka fara Chanza mata fuska wai kar tayi masu snatching miji,
"Kai rayuwa...naga rayuwa ..." Tafada cikin hawaye, ahankali ta Mike daga kan carpet da tayi sallah ta koma kan gado, zama tayi ta rafka tagumi Tana hawaye, knocking akayi a bakin Kofar dakinta tayi saurin goge face dinta, gaban Mirror taje ta dinga goge face dinta Don kar a gane tayi kuka, knocking aka sake yi taji ance
"Jewel bude mana..." Mom dinta ta fada mata,, ahankali ta Kai bakin kofa ta bude kanta kasa Tana cewa
"Sorry momma sallah Nayi..." Ta fada mata trying to hide her face, shiga mom dinta tayi ita kuma ta rufe door dinta, Tana shigowa mom dinta ta daga face dinta taga idanuwanta kaman garwashi,
"Kuka kike kou?.." Mahaifiyar Ta tambayeta cikin kulawa, da sauri ta girgiza mata Kai, zama uwar tayi bakin gado tace
"Maryam kiyi hakuri da irin wannan jarabawar...am quite sure yours will be among the best...Allah zai kawo lokacin naki..kinji kou?.." Ahankali Maryam da hawaye ya cika Idanuwanta ta daga mata Kai,
"No delay has ever been a disaster...Alhamdulillah kullum Ina godewa Allah dayasa kika zama kamilar mace..baki taba ketare umarni ba...am so happy da Allah ya bani ke...and am sure Allah will pay you with happiness...kiyi hakuri komai yayi farko definitely zaiyi karshe...ki rike destiny dinki da hannu bibbiyu Mai hakuri bai taba tabewa ba..Sannan inason ki bar zubda hawaye kar a ga gazawarki..kinji babyna.."
"Mommy nagaji..." Tafada cikin kuka, uwar goge hawayen dake néman zubo mata tayi yace
"Pls don't say that...pls " Ta fada cikin rarrashi
"Mom I want to die before end of the month..." Tafada cikin matsanacin kuka, hannun taDora  a bakinta Tana cewa
"Don't ever say that again...never..." Inji mommy dinta,
"Tou mommy pls ku bar ni in skipping next family meeting..." Bata karasa ba ta sake rufe mata baki
"Wannan is a family tradition..na wasu states ma suna zuwa sai ke ki kizuwa?.. Aa..."
"But mummy I can't bear it anymore...Wallahi maganar kaka yana kashe min  zuciya...duk sanda mukayi meeting sai na nemi numfashi na rasa...mummy pls ku bar ni wannan watan..." Tafada cikin kuka kaman small girl,
"Dan Allah ki bar wannan maganar..kinsan abu né Wanda bazai yuwu ba...ko bakije ba mussanman zata sa a dauko ki..."
"Mummy in tafi kaduna tou..." Bata karasa ba mum dinta tace
"So kike insha zagi..." Ahankali ta girgiza Kai Tana cewa
"Aa mummy..."
"Then pls ki bar wannan maganar..kawai ki dauki hakuri..everything will be alright...kinji sweetheart.."
"Ok mummy..." Tafada har lokacin bata bar hawaye ba.
"Mummy..." Ta sake kiran mamanta,
"I want to travel to Saudi..."
"Wani Abu zakiyi chan?.."  Dan goge face dinta tayi Sannan tace
"Kawai just want to pray again..." Tafadawa mom dinta
"Ok babu matsala...zanyiwa kawunki na Lagos magana sai yayi maki booking..but pls before then try and swallow your pain..."
"Insha Allah mummy..Zanyi kokarin haka..." Tafada sounding firm,
"Yauwa my sweetheart..Yanzu Bari in Barki ki huta...tunda kina rigan kowa na gidan nan tashi..." Tafada Tana mikewa good night kiss tayi mata Sannan ta fice daga dakin, ahankali Maryam ta dauki wayarta ta Kira dad dinta dake Abuja.

Suhail bai Kara cewa komai ba har suka isa Mai waazi estate, wajen babban ne sosai yana dauke da gidaje akalla guda sha biyar Wanda manyan yaran shi ke zaune da family dinsu, cikin daya daga cikin gidajen kaka take, kowannen gida is fenced da gate dinshi, Sannan a nan makeken meeting hall dinsu yake, a cikin hall din anyi family tree a cikin wata katuwar board da permanent marker Wanda duk sanda aka samu karuwa afamily zaa rubuta. Sunan abinda aka samu under he's parents name that is under nasu parent din, na farko a jikin tree din is late alhaji Mai waazi then matanshi da, Sannan a cikin gidan da akwai inda aka tanada domin yin Abincin da zaaci lokacin meeting Don hardly suci abinci waje, masu aiki aka samu da zasuyi wannan aikin a biyasu, Sannan sai kuma main estate gate Wanda zai sada ka da estate din, ba kowa ake Bari ya shiga ba sai Wanda aka sani, ba kowa ake tsaro ba sai kaka saboda sau biyu Ana attempting kidnapping dinta saboda Tana da yara masu kudi sosai, yazid na zuwa bakin main gate yayi horn, daya daga cikin security men na main gate dake zaune daga waje  ya taso ya fara haska faces din mutanen dake cikin mota wani irin tsoki suhail yaja yace
"Malam meye haka?.." Suhail Yafada looking so angry da ake haska mashi face,
"kayi hakuri aikin mu mukeyi..." Inji Mai haska su din
"aikin ka kakeyi bakasan yan gida ba zaka kashe mana idanuwa da hasken touch?.." Suhail Yafada yana kare face dinshi,security din banza yayi dashi ya gama haska cikin motar Sannan yace
"Dan bude min booth.." Yafadawa yazid that knows the law indai da dare zaka shigo, bude mash yayi ya duba Sannan security din  yayi magana da gate man ya bude masu suka shige,tsoki suhail ya sake ja yana cewa
"What was that all about?.." Ya tambayi yazid
"Ka mance na fada maka anyi attempting sace kaka har sau biyu?.." Bai karasa ba suhail ya kwace da dariya yana cewa
"Ai da an dauke ta kowa ma ya huta...she's so annoying..." Yafada hankalinshi kwance, Kai kawai yazid ya girgiza mashi Sannan yace
"Yanzu dai mu tsaya muyi sallah both magrub da ishai Sannan mu shiga wajen kaka..Don bamu San ranar fitowa ba in mun shiga..." Inji yazid, suhail bai amsa mashi ba yazid yace
"I will take that as a yes..." Ya fada yana nufan masjid dake cikin estate din. Parking yayi suka shiga wurin da aka tanada Don alwallah sukayi Sannan sukayi sallah. Sai da suka idar suka taka zuwa gidan Inna dake karshen estate din, knocking sukayi a bakin gate dinta maigadin ya leko yace
"Wa kuke nema?.." Ya tambayesu
"Mai gidan.." Suhail ya amsa mashi face dinshi kaman bai taba dariya ba,  rufe gat din Maigadi yayi yana cewa
"Bari in tambayota..." Goshi suhail ya dafa yana cewa
"Ko president Ai sai haka..." Dariya yazid yayi yace
"Indai kaka ce kadan ka gani..." Yafada mashi yana jingina da jikin gate din. Few minutes later Maigadi ya leko yace
"Tace batason ganin kowa yau kuma sai gobe..."
"Kan uban nan..." Suhail Yafada, maigadin bai tsaya sauraron shi ba ya maida gate din zai rufe suhail yayi saurin tureshi ya shiga ciki
"Cutest if you don't want to annoy her Kawai ka dawo gobe mun dawo...Wallahi that woman's problem is getting bigger by day...kawai ka fito mu tafi..." Suhail bai tsaya ya sauri abinda zaice ba ya shige abinshi, hanyar falon ya shiga ya shiga corridor dinta, sallama yayi bai karasa ba yaji ance
"Wane Dan kan ubane ya shigo min gida da wannan Daren..." Niji an fada daga ciki, idanuwa suhail yayi rolling ya shiga falon, kaka ce zaune legs dinta biyu kan pillow yanmata biyu na danne mata, matar fara ce sosai Don dukda ta tsufa shi still glows, Tana da jiki sosai Don jibge take kan kujera, Tana Jin an shigo tayi saurin daukan glasses dake kusa daita ta kifa a eyes dinta Sannan ta kalli inda suhail yake, kallon shi tayi daga head to toe tace
"Dan ubanka daga Ina?.." Ta tambayeshi kaman batasan ko waye ba, daure fuska suhail yayi ya durkusa har kasa yace
"Kaka nine..." Bai karasa ba tace
"Kaine wa?.."
"Suhail..."
"Tou ba'a fada maka banson ganin kowa da wannan Daren ba?.. "
"Ai kaka dawowa..."
"Dan uwaka tashi ka bani waje.." Baki suhail ya turo yace
"Kaka daga kasar waje nake nazo gai..." Still bata Bari ya karasa ba tace
"Allah yasa daga lahira kake tashi ka bani waje..." Suhail zai bude baki yayi magana ta nuna shi da yatsa Sannan tace
"Wallahi Ina da mabuga...daman nasan sai Kai...Wallahi in Baka tashi ba sai in sa aci ubanka..jan banza kawai..." Tafada mashi cikin fada, suhail daga idanuwa yayi ya watsa mata harara Sannan ya Mike, wata sanda dake kusa da ita ta dauka ta wulla mashi yayi saurin kaucewa yana cewa
"I wish you're dead..." Yafada kasan makoshin
"Ka zagi munafukar uwarka da munafukin ubanka...Wallahi kasa na dauki wayata sai ranka ya baci..." Tafada mashi sounding so tensed kaman they're enemies, sai Yanzu nagane abinda yasa mami ke fargabar haduwansu, tsoki suhail yaja ya bar falon,
"Allah ya hadani da Kai...Wallahi zamu hadu...kasan dai da hankalina kuma nasan kaine..." Yaji Tana fada da karfi,  tsoki yaja da karfi tare dacewa
"Kanki akeji..." Yafada da karfi yanda zataji da kyau,
"Kan ubanka akeji...allah ya Kai mu gobe...har gidan ubanka zanzo..." Tafada sounding so angry, suhail fita yayi ranshi bace, yana fitowa wajen gate yazid dake jingine da gate yace
"Hope you're satisfied that you touches the lions tail...Wallahi Yanzu sunan ka sorry indai kaka ce..." Ya fada mashi,
"Kai Wannan tsohuwar is something else...Wallahi har cewa tayi gobe zata zo gidan mu..." Suhai ya fada cikin bacin rai,
"Kuma Wallahi zuwa zatayi...kuma she will make sure tasa dad yayi maka abinda zai faranta mata...kawai shawara muje gidan mu har sai tazo ta koma sai In maidoka gida..." Yazid ya fada mashi yana bude mota ya shiga.
"Aa babu inda zani..." Suhail Yafada yana shiga mota shima,
"Hmmm I think Baka San kaka ba...indai tasan saboda humaira kazo Tana iya hanawa ayi maku aure..Kai ba hakuri ita ba hakuri..so kawai lets go home..in taje ta gama rashin mutunci sai in maida ka gida..." Yazid ya fada yana tada mota, suhail bai Kara cewa komai ba Jin an ambaci zata hanashi auren humaira and for sure yana iyawa, yazid barin gidan yayi ya Kama hanyar gidansu, suna daf da shiga unguwar suhail yace
"Wai Ina SIM card Dina Dana Baka ajiya?.."
"It's safe..." Yazid ya fada mashi yana shiga street dinsu, yana zuwa daidai saitn gidan yayi horn Maigadi ya bude mashi ya shiga yayi parking, bedroom din yazid a kasar bane yake while bed na sauran mutanen gida na upstairs sai part din dad dinsu dake waje, fitowa sukayi suka nufi falo lokacin mom bata dade da saukowa daga wajen mami ba, Tana Jin sallama Ta amsa Tana kallon Kofar, suhail né ya fara shigowa, Tana ganin shi ya saki murmushi Tana cewa
"Sannu da zuwa Dana na Kaina..." Da sauri suhail ya karasa gabanta ya durkusa kasa ya gaisheta amsawa tayi tana Shafa kanshi, yazid né ya shigo ya jefa kanshi kan sofa dake kusa da mom dinshi,
"Ya karatu?.." Ta tambayeshi
"Alhamdulillah mommy..." Ya amsa kanshi kasa
"Wai mum Ina aunty?.." Yazid ya tambayi mom dinshi,
"She's upstairs..." Ta amsa mashi, surprise look suhail yayi masu yace
"You mean anty is still in this house..." Ya tambayesu yana mikewa tsaye farin ciki na appearing a face dinshi because he's so close to her, duk sanda suka samu matsala yazid itace ke sasantasu Sannan she's like their second atm machine da duk sanda sukaji su broke or can't go to bank wurinta suke amsar kudi,
"Yes she's upstairs..." Mommy Ta amsa mashi, da gudu ya Kama hanyar upstairs deep down he's thinking wai har yau batayi aure ba? Because first year daya tafi yana kirashi then she later stopped, yasan dakinta so yana zuwa knocking yayi da karfi kaman yanda ya Saba yi mata, Sam mami batayi tunanin shine ba, she thought it's yazid,
"Go away bacci Zanyi..." Ta fada cikin sanyinmurya, ,sake knocking yayi da karfi ta saki tsoki Tana mikewa zaune cikin cotton rigar bacci dake jikinta, 
"Allah this better be good..come in..." Tafada Tana zama bakin gado, yana bude kofa taga suhail tsaye, da sauri ya shigo dakin yana dariya face dinshi dauke da farin ciki,
"I should have known tunda Allah ya maidoka lafiya..." Tafada Tana dariya, takawa yayi zuwa gabanta ya zagaya hannunshi bayan wuyanta yana cewa
"Auntyna nayi missing dinki sosai,..." Buge mashi hannu tayi tace
"Ashe Kay missing Dina and you don't bother to call me even once..ai shiyasa Nima na daina kiranka...I always ask of you a wajen yazid nasan ku kullum jone kuke, dariya ayi ya zauna bakin gado yace
"Haba anty na,,,ba student nake ba?... Kuma Ai kira daga chan zuwa nan yana cin kudi..." Yafada cikin zolaya, harara ta Balla mashi Sannan tace
"Wato daga nan zuwa chan bai cin kudi kou?..Lallai Dan rainin wayau..." Tafada cikin raha, matsawa yayi kusa daita ya Dora hannu a shoulder dinta yana cewa
"Anty what's up...how have you been?.."
"Am fine...ya kake ha karatun?.." Ta amsa mashi cikin kulawa
"Wallahi anty Alhamdulillah...karatu is over..,next week zan fara aiki .." Juyowa tayi ta zuba idanuwanta cikin nashi bakinta bude tace
"Wow kanina am so proud of you...naji dadi sosai...Allah ya taimaka..." Tafada
"Ameen antyna..." Kofa aka bude yazid ya shigo rike da bowl of salad yana ci,
"Anty Ashe bakiyi bacci ba ko wannan shegen ya tasheki?.." Yazid ya fada yana zama kan stool dake gaban mirror yana kallon suhail da hannunshi ke kan shoulder mami,
"Daman am about to naji kaman zaa ciremin kofa..I was thinking it's you...Ashe shine..." Tafada Tana lumshe idanuwa,  dariya sukayi, hira sukayi kaman minti goma Sannan tayi hamma tare da ture hannun suhail dake kan shoulder dinta tace
"Ku tashi ku tafi I want to sleep..." Tafada Masu, dariya suhail yayi ya Mike taganshi wani zankankan gabanta tace
,"wai Kai Ina zaka Kai tsawo?..ji yanda ka karayin tsawo.." Tafada mashi, dariya yayi yace
"Kai anty mami ko kafin in bar kasar nan da tsawo na Ai..."
"Yes I know..amma Yanzu kafi da...you that is very small lokacin..." Dariya duk sukayi suhail yace
"Anty wallahi kin fiya son girma..kina magana kaman yarintar mu...alhaji duk kusan tare muka taso..." Bai karasa ba ta dauki wata small pillow Mai shape din heart ta jefa mashi yayi  grapping yana dariya
"Ai gaskiya na fada..." Yafada mata yana kallon yanda take hararanshi
"Kun Raina min wayau..wai tare muka taso daku...ku da har na shiga secondary kuna yawo da majina..." Bata karasa ba yazid yayi saurin ajiye salad dake hannunshi yana cewa
"Shikenan ban Kara ci..ya fita Raina da Jin majina..." Yafada yana goge bakinshi, dariya suhail yayi yace
"Rabu da anty...kawai Tana fada né Don taji dadi..." Kai mami ta girgiza ganin zasu Raina mata hankali
"Naji ku tashi ku tafi...I want to sleep now..," mikewa yazid yayi Don daman suhail na tsaye rike da heart pillow da mami ta jefeshi dashi, takawa suhail yayi ya ajiye mata pillow din Sannan yace
"Anty sai da safe..." Shima yazid yace mata same thing, hannu ta daga masu Tana cewa
"Allah ya kaimu.." Tafada masu Tana mikewa,
"Bari in cinye tunda ka koshi...," Ta taka zuwa gaban mirror ta dauki bowl da yazid ya ajiye,
"Daman you did that on purpose..." Yazid ya fada yana ficewa daga dakin, shima suhail fita yayi yana tunanin why is he's favorite cousin sister not married yet, suna sauka suka ga mom ta bar falon, zama sukayi yazid ya kuna kallo, suhail shuru yayi yana kallon waje daya for a moment Sannan yace
"Wai besty tunda na tafi anty batayi aure ba?.." Ya tambayeshi cikin sanyinmurya, ajiyan zuciya yazid ya Saki Sannan yace
"Wallahi har Yanzu anty shuru..."
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...amma gaskiya am disturbed,,,ya zaayi ace nice woman kaman anty ta rasa mijin aure?.. Kodai something is wrong?.." Ya fadawa cikin damuwa,
"Allah kadai masani...physically nothing is wrong gaskiya....amma wayasan ikon Allah?.." Inji yazid, shuru suhail yayi damuwa na rubuce in his face
"Gaskiya am not happy...am not happy at all...inda Ana siyan miji I will use all I have got to get her the best of them all..amma sai gashi ba'a sayarwa...Allah sarki antyna...I pity her Wallahi..." Suhail Yafada kaman zaiyi kuka,  wata ajiyan zuciya yazid a sake saki Sannan yace
"The worst part is next two months auta zatayi aure...and the most annoying is kaka is on her nerves..." Inji yazid
"Pls forget about that old woman let's say something important Wai you mean auta ma getting married?.."  Suhail ya tambayeshi cikin babban tashin hankali
"yes oo...she's getting married...Yanzu anty kadai zata rage nan gidan tunda Nima bazan Kai one gaba banyi ba..."
"No,,,Insha Allah..in Allah ya yarda anty zatayi aure soon...kawai muyi mata adua..let's pray for her morning and night..." Inji suhail , Dan baki yazid ya tabe yana cewa
"Sai kace wani malami...har saudia an  biya an Kai malamai sunyi mata adua ballekai..." Tsoki suhail yaja yana cewa
"Ai adua bai yawa...kawai lets continue praying..Wallahi it hurt me so much to see her like this...Wallahi da ganin idanuwanta dazun kaman

3 / 75