Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
ji.
Alkali ya yanke hukunci:
“Duba da laifukan da aka tabbatar na mamacin Alh. Gusau, da kuma hujjojin taɓin hankali da aka kawo na Amal, wannan kotu ba za ta yanke mata hukuncin ɗauri ba...
Amma dole a yi hukunci saboda an aikata kisan kai a fili. Wannan kotu ta umarci Amal ta shiga cikin kulawar likita (psychological rehabilitation) na tsawon shekara biyu..."
Maleekh ya yi murna sosai. Ya ceto matarsa daga shiga kurkuku. An daskare dukiyar Wadata, kuma an tabbatar da cewa Wadata zai rayu a gidan yari har abada.
An kammala shari’a! An gyara wa Alhaji Abdul-majeed sunan sa, an dawo da kadarorin Amal gaba ɗaya, kuma Hajiya Sa’adatu ta yi nadama ta cigaba da zama a gidan Abbah har Allah ya fito mata da miji nagari tunda ba wuce aure tayi ba..
Bayan shekara biyu na kulawa da likitoci, Amal ta warke gaba ɗaya daga raunin zuciya.
Maleekh da Amal sun ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da soyayya. Suna kula da yaran su. Suna yawaita ziyartar kabarin Farha don girmama sadaukarwar ta.
Yanzu shekaru sun shuɗe. Maleekh da Amal da yaransu Arhaan da Lihaam sun koma gidansu na Maleekh na kansa. Yara sun girma suna da shekara uku-uku yanzu, suna zuwa makaranta cikin gata da kuɗin uba da na uwa...
Zayd da Islam su ma suna can gidansu, soyayya iya soyayya suna shanta. Islam ma ta haihu, ta haifi mace kyakkyawa a inda ta samu sunan Ammy wato Maryam Inkiya Ummul Khair..
A yau an sha hidimar bikin Arfat itama, ta auri Manager Maleekh. Sun sha hidima sosai. A yayinda ita da angonta suka fita Honeymoon can ƙasar Indian. Zayd da Islam da yarinyarsu su ma sun fita yawon shakatawa ƙasar London...
Maleekh da Amal suna fita aikinsu a tare bayan sun sauƙe yaransu a School, su kuma sai su wuce babban kamfaninsu wanda ya haɓaka sosai... Suna shan soyayya na gaske, kuma babu wani damuwar komai a rayuwarsu.
❤️
Kamar yau da ya kasance ranar weekend, an kai twins can gidan Abbah ziyara. Iya su biyu suka kasance a gida, lokacin bawa soyayya muhimmanci.
Suna kwance akan gado (King size bed) a babban ɗakin su mai cike da tsarin zamani da kayan alatu da kuma hasken rana mai launi da ke shiga ta madubin ɗakin.
Maleekh yana kwance yana rungume da Amal ta bayan ta. Ta sanya kanta a kan hannunsa tana jin numfashinsa mai ɗumi.
Cikin muryar shagala da kasala ta ce,
“Hubby na... na gode wa Allah da ya sanya ni cikin rayuwar farin cikinka… bayan dukkanin abin da ya faru…”
Ya sumbaci gashinta a hankali “Ni ne ya kamata inyi godiya! Ke ce jarumar rayuwata! Kin yi haƙuri da ni lokacin da ba ki san gaskiya ba! Kuma kin yarda dani a lokacin da kowa ya juyamin baya… Ina sonki Amal! Karshen soyayyar ki shine Farin Cikina.”
Maleekh ya juyar da ita a kan gadon tana fuskantarsa. Ya sanya hannunsa yana shafa fuskarta da siraran leɓenta masu kyau.
Ya furta a hankali
“Har yanzu ina son ki fiye da yadda nake yi tun farko! Soyayyarki ta ƙare mun damuwa! Ki rufe idon ki…”
Ta rufe idonta cikin gamsuwa da yarda. Ya sunkuya ya fara sumbatar ta a hankali, yana watsa mata kalmomin soyayya a kunnenta.
“You are my Queen, my salvation! I Love You... I Love You... I Love You…”
Ta kankame shi da ƙarfi, tana mayar masa da martani na soyayya mai zafi da take ji a zuciyarta ga wanda ya kare ta daga dukkanin mugunta kuma ya kawo mata gaskiya.
Bayan sun kammala lokacin soyayyarsu a kan gado, Maleekh ya rungume ta a jikinsa, yana shafa mata bayanta a hankali.
Cikin muryar soyayya da sha'awa ya furta
“My Queen, yanzu da rayuwa ta dawo daidai, kuma an yiwa kowa hisabi. Wace ƙasa kike so mu fara kaiwa ziyara da ƴaƴanmu kafin su fara dogon hutu na makaranta? Ina son cikakken farin cikinku!”
Amal ta lumshe idonta cikin gamsuwa da kwanciyar hankali.
Ta ɗan matsa jikin shi sannan ta furta.
“Hubby, daga cikin dukkanin ƙasashe da za mu iya zuwa, Saudiyya nake so mu fara zuwa. Shine fatana kuma ina so nayiwa iyayena addu'a ta musamman acan, da kuma mu kanmu gaba ɗaya da musulman dake faɗin duniya. Muje mu yi Umrah tare da ƴaƴanmu.”
Maleekh ya yi murmushin jin daɗi da girmamawa saboda sha’awar Amal na ibada da tausayi. Ya sani cewa yin addu’a a ƙasa mai tsarki zai wanke mata duk wani zafi da ta sha a baya.
YA furta
“Masha Allah! Mafi kyawun zaɓi! Sai anjima zan kira jami’anmu su shirya takardar izinin shiga ƙasa (visa) da kuma jirgin mu na kanmu nan da sati biyu! Duk abin da kike so, za a cika miki!”
Suka rungumi juna cikin soyayya mai zurfi, suna tunanin tafiya da iyali zuwa ƙasa mai tsarki.
Bayan sati biyu da shiri mai zurfi, sun hallara a filin jirgin sama (Airport). Dukkanin iyalan su sun zo rakiya zuwa Airport: Ammy da Abbah da Inna.
Abbah yana tsokanar twins da farin ciki game da tafiyar su.
“Ku je kuyi addu’a ku dawo! Iyayenku sun cika ku da gata! Ku kula da Juna kuma ku yiwa kowa addu’a!”
A ƙarshe, Maleekh ya riƙe hannun Amal da ƴaƴansu suka shiga jirginsu na kansa. Jirgi ya tashi!
A cikin jirgin da ke ɗaga su zuwa Saudiyya, Maleekh da Amal sun zauna a sashe mai zaman kansa na jirgin, bayan an kwantar da twins suna bacci.
Maleekh ya kalli cikin idon Amal, inda ya ga alamun farin ciki da tsantsar soyayya suna fito mata daga zuciya.
YA furta “Gani nan zaune kusa da ke a cikin jirgi, ke da ƴaƴana, muna tafiya ƙasa mai tsarki... Babu abin da ya fi wannan dadi! Komai ya zama daidai!”
Amal ta rungume shi ta sa kanta a ƙirjinsa cikin kwanciyar hankali.
TA furta
“Wannan duka saboda kai ne! Kai ne jarumin mu!! Na gode da soyayyarka da kariyarka!”
Maleekh ya ɗago fuskarta ya sumbace ta cikin ƙauna. Ya sanya hannunsa a wuyanta, yana shafa ta a hankali.
Sannan ya furta
“Babu godiya a tsakanin masoya! Ke ce zuciyata! Gaskiya da soyayya sun yi nasara a kan ƙarya da ƙiyayya! Mu more rayuwarmu da yardar Allah!”
Sun ci gaba da shan soyayya da hira mai daɗi a cikin jirgin har sai da suka isa Saudiyya lafiya, inda suka cika burinsu na yin ibada tare da iyalan su da kuma yiwa iyayensu addu'a ta musamman.
Suna gode wa Allah da ya sanya soyayyarsu ta zama ta gaskiya kuma ta ci nasara a kan dukkannin ƙiyayya.
Anan ne labarin Soyayyar Maleekh da Amal ya ƙare lafiya da zaman lafiya....
✨ ƘARSHEN LITTAFI ✨
Da sunan Allah Maɗaukakin Sarki.
Ina gode wa Allah SWT da Ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai suna AMALEEKH.
Ina neman yafiyarSa idan akwai kuskure, rashin dacewa ko laifi a cikin wannan rubutu, domin ni ɗan Adam ce mai kuskure.
Ina miƙa godiya ta musamman ga dukkan masu karatu da suka bani goyon baya, addu’a da ƙarfafawa tun daga farkon wannan labari har zuwa ƙarshe.
Musamman wannan littafi na sadaukar da shi ga manyan fans ɗina na cikin WhatsApp Group:
Aunty Habiba
Aunty Khadija
Aunty Binta Muhammad
Naman Zakiyya
Aunty Hajjajo
Ummu Nihal
Allah Ya saka muku da alheri, Ya albarkaci soyayyarku da goyon bayanku.
— Asmeetah Writer ✍🏽