Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   62 / 82

183K to 186K   out of 244.2K words

raye tana jira…”

Ta yi shiru, ta share hawayenta sannan ta ƙara magana da cewa.

“Yaya Zayd ya ce, a duniya babu macen da Yaya Maleekh yake so kamar fiancée ɗinsa, har ya ce ko Amal ba zata kai fiancée a wurinsa ba…”

Inna wacce ta saurare su ta girgiza kai, muryarta ta sauya cikin nutsuwa mai haɗe da tausayawa..Ta ce

“Farha… fiash (fiancée)ɗin da kike magana akanta... ita ce Amatu.”

Farha ta kalli Amal da mamaki ta ce.

“Ban gane ba…”

Inna ta soma magana cikin zafin rai da ƙarfi,

“Ai Amatu ce fiash ɗinsa tun yarinta! Maleekh da Amal sun daɗe da alkawarin soyayya, sannan sun sha bambanci na ƙaddara amma soyayyarsu ta ci gaba da numfashi har yau!..

A lokacin tana ƙarama ce sosai, shekara biyar kacal a duniya, amma ta riga ta saba da Maleekh.
Shi kuwa yana da shekara goma sha uku, ɗan saurayi mai wayo da murmushi wanda yake burge kowa.
Sun taso tare tamkar ‘yan uwa, saboda iyayensu abokai ne na ƙud da ƙud, musamman mahaifiyar Maleekh da mahaifiyar Amal kawaye ne, aminan juna da ke yin komai tare.

Ko da yake Maleekh ya girme ta da shekaru takwas, shi ne mai bata dariya, mai kora mata karnuka idan ta tsokano su, mai bata lemo da sweet idan ta yi kuka.
A gidansu Amal ake yawanci samun su suna wasa, wani lokaci kuma sukan koma gidansu Maleekh.
Har ma iyayensu suka saba da cewa,

“Ku dai idan kun girma, aure zamu muku, ku zama daya har abada.”

Wannan magana tana nan cikin zuciyar Amal kamar alƙawari mai tsarki.
Ta yi imani cewa da zarar ta girma, shi ne mijinta, shi ne abokin rayuwarta.

Sai dai rayuwa ta juyo da wata fuska.
Wata rana da dare, gidan su Amal ya kama da wuta. Gobara ta cinye komai mahaifiyarta, mahaifinta… komai ya ƙone.
Sai ni ce nazo da gudu na ɗauke ta muka tsere cikin duhu, muna kuka, muna neman mafaka.
Tun daga wannan rana Amal bata sake ganin Maleekh ba, bata sake jin labarinsa ba...

Amma a zuciyarta, tana rayuwa da hotonsa, ƙaramin yaro mai murmushi, wanda yake saka zuciyarta jin daɗi.
Hotonsa ta riƙe har zuwa yanzu, wanda ta gani cikin wani tsohon jakar makarantarta...
Irin wannan hoton ta gani cikin ɗakinsa a manne ita da shi, shi ne ya tabbatar mata wannan ne Maleekh nata…
A yau kuma, shi ne mutum ɗaya da zuciyarta ke bugawa saboda shi..."


Farha ta sake baki tana kallonsu cike da mamaki, ta ce

"Amma me yasa bai gane ta ba?
Me yasa har yanzu yake kallonta kamar ba su taɓa sanin juna ba?..."

Amal ta lumshe idanu tana sauƙe ajiyar zuciya mai raɗaɗi.
Ta ɗan murmusa cikin ɓacin rai.

“Rayuwa… tana da ban mamaki,” ta furta a hankali. “Mutumin da aka rubuta a zuciyata tun ina ƙarama, yau yana gabana amma bai san ni ba.”

Farha ta riƙe hannunta, idanu a cike da hawaye ta ce.

“Subhanallah… amma ai da kun sanar da shi da wuri!…”


Amal ta ɗago kai cikin mamaki da shiru mai cike da tsoro da farin ciki lokaci guda.
Zuciyarta ta yi wani irin nauyi.

“Maleekh…” ta maimaita a cikin zuciya, “ko da bai gane ni ba, ƙaddara ta dawo da mu.”

Ta ɗan kalli Inna sannan ta ce cikin nutsuwa..

“Inna, mu bar komai haka. Farha, ki min alkawarin kar kowa ya ji wannan magana. Iya ke kaɗai ce yanzu kika san cewa ni ce fiancée ɗin Maleekh.”

Farha ta ɗago hannayenta sama ta ɗora akan Amal sannan ta ce.

“Nayi miki alkawari Amal. Wallahi ba zan faɗa wa kowa ba. Wannan sirri ne a tsakaninmu.”

Yanayin ya sauya daga damuwa zuwa fara’a. Inna ta ɗan sake fuska, Amal ta yi murmushi...

Farha ta share hawayenta cikin dariya ta ce.

“To, yanzu bari mu koma magana ta bikin. Ya labarin anko ne? Don naga ana ta shiri sosai.”

Amal ta yi dariya cikin salo.

“Ku ai a ɓangaren maza kuke, ni kuma ban da wasu kawaye balle nayi maganar anko…”

Farha ta kwaɗaita idanu sannan ta ce.

“Da ke kawai za’a iya yin anko fa! Ni zan miki odar ankon daga Dubai, ko ya kika gani?”

Amal ta yi murmushi, ta dafa kafaɗarta ta ce.

“Ki bar wannan sai gobe, zan gaya miki irin launin da nake so. Yau dai naji daɗin ganinki.”

Farha ta ɗan miƙe da murmushi itama ta ce.

“Ni ma Amal. Na gode da yafiya, Allah ya albarkaci bikin ku.”

Ta rungumi Amal a karo na ƙarshe. Inna ta ɗan amsa mata da murmushi mai nauyi, sannan ta rakata har ƙofar get. Lokacin da Farha ta tafi, Inna ta juya ta kalli Amal da nutsuwa, tace:

“Kin ga yadda komai yake dawowa daidai. Allah yana da tafarkin sa.”

Amal ta yi shiru tana kallon ƙofar da Farha ta fita.

“Eh Inna… amma har yanzu zuciyata tana jin tsoron abinda ke tafe.”...


Farha tana cikin motarta zuwa gida..

Sai tunani take tayi akan maganar da taji iyayenta suke akai, cewar "za'a kashe Amal. Sannan su sukayi silar hatsarin Amal, to meyasa suke neman rayuwarta?..."

Wannan tambayoyin sun tsaya mata a rai..


_NEXT NEXT NEXT_


asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 71 to 72

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹


Ranar Alhamis da safe a gidansu Maleekh.

Ranar ta fara da motsin ma’aikata, sautin “sweep! sweep!” na tsabtace gidan yana tashi a ko’ina. Gaba ɗaya gidan ya canza kalar sa, ga sabon fenti ya ratsa bango.
A jikin bango an rataye hoton Maleekh da Amal, wanda aka tsara cikin kwali mai tsada, an rubuta a ƙasa:

“Forever Begins Here A&M.”

Sabbin kayan alatu daga Dubai sun cika falon. Kujeru masu launin royal blue, tagogi sun ɗauki labulen silk masu sheƙi, ƙamshin turaren oud yana yawo har ƙofar shiga.

A waje, ana gyaran lambu. Ƙamshin furanni na tashi, ga murya ta masu gyara suna dariya da raha..kowa da farin ciki akan fuskarsa.
A gefe, ana ɗora manyan fitilu masu walƙiya crystal chandeliers waɗanda zasu haskaka gidan..

A cikin babban falo, Maleekh yana tsaye a bakin window yana kallon aikin. Ya zura hannuwansa cikin aljihun wando, idanunsa a kan yanayin gidan yana tunanin Amal.
A hankali, murmushi ya suɓuce masa.

“Ko gidan ma ya fahimci farin cikin da zuciyata take ciki…”
Ya faɗa a hankali, yana shakar ƙamshin sabon fenti.


Gidansu Amal kuwa, ya koma aljanna ta mutane.
Daga ƙofar shiga har cikin tsakar gida, an yi ado da furen gwangwani, fitilun string lights suna walƙiya kamar taurari.
Ƴan uwan mahaifinta daga Borno sun iso, suna ta dariya da raha cikin ƙayatattun kaya.
Ƴan uwan mahaifiyarta daga ƙauyen Kaduna suma sun iso, wasu suna kitchen suna dafa girki, wasu suna gyara falo, wasu kuma suna saka kayan ado.

An saka sabon carpet, an canza labule zuwa pink and silver launin da Amal tafi so.
Daga sama har ƙasa gidan yana sheƙi.
Ana ta shirya turaren wuta, ga ƙamshi ta ko ina, an haɗa wa Amarya wasu arnar turaruka na jiki dana wanka dana ɗaki dana kaya dana gaban mace, su almisk da sauran su dake ƴan uwan mahaifinta daga Borno duk ƴan shuwa ne....
Ga kayan lefen da aka kawo daga gidansu Maleekh da kayan ɗaki...

A ɗaya sashen, Amal tana tsaye a gaban mirror tana kallo, tana murmushi cike da nauyin zuciya. Ta taɓa fuskar ta a hankali.

“Wannan ce ni?... fiancée ɗinsa tun yarinta...”
Ta faɗa a hankali, muryarta kamar sirri..

Sai kawai ta ji Inna daga ƙasa tana faɗin:

“Amatu! Ki sauƙo ki gani, ƴan uwan mijinki sun kawo kayan lefe ɗin Dubai!”

Da gudu Amal ta sauƙo. Kayan lefen sun cika babban falo, akwatuna masu launi, wasu gold-plated, wasu rose pink, wasu silver diamond design.
Daga cikin akwatunan akwai turaren jiki, kayan kwalliya, riguna, takalma, jewelries, hijabai, kayan sallah, kayan kwanciya. komai sabo daga Dubai. Ni kaina bazan iya misalta yawan kayan ba..

Ƴan uwa suna tafa hannu suna yaba wa kyawun kayan..
“Wallahi Maleekh yayi ƙoƙari sosai!” wata daga cikin dangin tace da dariya.
“Ai Amal ta same shi a sa’a,” wata kuma ta ƙara.
Inna ta yi murmushi kawai tana kallon jikarta, hawaye na farin ciki suna shirin zubo mata..

Abin da ba kowa ya sani ba shine gaba ɗaya Maleekh ya saka CCTV a gidansu Amal, daga ciki har waje.
Yana kallon ta a gida, yana lura da komai cikin sirri.
Yana ganin yadda take murmushi, yadda take tafiya, har yadda take gaishe da mutane.
Wani lokaci yakan tsayar da bidiyon ya ƙara kallon fuskar ta yana murmushi.

“Ni da ke mun wuce nisan duniya, Amal…”
Ya faɗa cikin lumshe ido, yana jin wani irin nutsuwa ta ratsa shi.


A wannan ranar da daddare za'a gudanar da waliman aure..
Rana ta fara faɗuwa, hasken rana ya dushe.
Gidansu Amal yana cike da hayaniya, dariya da nishadi.
Ƴan uwa suna ta ɗora shirin walima, masu kwalliya suna yi, masu saka kayan walima, Inna tana tsara jeren kayan lefe..

Amal tana tsaye a jikin tagar ɗakinta, tana kallon sararin sama, zuciyarta na bugawa da jin daɗi da shakku lokaci guda.
Ta ɗago hannunta ta murza zoben da Maleekh ya sanya mata lokacin da suka samu matsala a kaduna..

“Gobe fa za a ɗaura auren…”
Ta faɗa a hankali.
Sai murmushi ya suɓuce mata amma a cikin murmushin akwai ƙanƙanin hawaye..


Gidan da Maleekh ya kera domin Amal, ya zama abin da ake kallo kamar aljannar duniya.
Yana cikin unguwa ta manyan mutane, inda kowane gida yake da bango mai tsayi, fitilu masu sheƙi, da ƙofar wuta mai sarrafa kanta.
Gidan Amal ya fi yawancin sauran tsari da kyau sabuwar ƙira ce ta zamani, storey building mai parts uku:

Part ɗin Amarya da Ango

Part ɗin baƙi masu ziyara

Sai Garden Area da aka tanadar don walima..

Wurin da za'a gudanar da walima.
Hasken fitilu masu launin warm gold sun lulluɓe wajen, suna kyalli a cikin iska mai sanyi.
A ƙofar shiga, banner ɗin da aka tsara na rataye da rubutu:

“Welcome to the Union of Hearts Amal ❤️ Maleekh 2025”

Ƙamshin turaren oud da vanilla rose yana gauraya da ƙamshin furen da aka shuka a jikin hanyar shiga.
A gefe kuma, ana busa saxophone mai daɗi, yana haifar da nutsuwa da nishaɗi.

An kafa big white tent mai gilashin bango da fitilu masu walƙiya a ciki.
Kujeru sun jeru cikin tsari, kowace kujera da flower centerpiece a tsakiyarta.
Jerin kujerun mazan gefe ɗaya, na mata gefe ɗaya kowa cikin kwalliya da annuri.
Ƴan uwa da abokai, Kaduna, Abuja, Lagos, Borno, England, American, Dubai, da sauran manyan ’yan siyasa da ’yan kasuwa duk sun hallara.

Wani lokaci zaka ji wani daga cikin jama’a yana faɗin:

“Wallahi wannan shi ake ƙira bikin manya."

A bakin shigowa, ma’aikatan walima suna ta yin ushering cikin ladabi.
Ƙamshin abinci yana yawo fried rice, jollof, salad, grilled chicken, pepper soup, da non-alcoholic champagne da aka shigo da su daga Italy.

Fitowar Amarya

Kowa ya ɗaga kai lokaci guda!
Sai Amal ta shigo cikin long gown mai kyalli, launin champagne gold ɗauke da silver stones.
Rigar ta zagaye jikinta cikin salo da nutsuwa, ta ɗora veil ɗin light gold net da aka shafe shi da diamonds.
Ƙamshin turarenta ya cika wajen, haɗin Ajmal Amber da Mukhallat Shams...

Da kallo guda zaka fahimci ba kawai kyanta ake gani ba, ana ganin natsuwa, kunya, da hasken zuciya.
Ƴan uwa mata suka tashi suka fara shewa:

“Amarya ta fito! Amarya ta fito!!”

Sai hayaniya ta barke, ana ta tafi da waka da ihu cikin nishadi.
Wata daga cikin danginta tana dariya ta ce:

“Allah ya sa albarka cikin wannan aure.”

Amal tana murmushi, tana tafiya a hankali, hannunta a cikin hannun kawarta Aisha da ke rakiyarta zuwa kujerar amarya..

Fitowar Ango Maleekh..

Sai kuma Maleekh ya fito daga sashen sa, cikin white suit mai sheƙi, da black tie, gold wristwatch, da shoes masu glass shine.
A gefe ɗaya Abbah ne yana murmushi da alfahari, yana zaune.
Duk inda ya taka sai jama’a sun juya suna kallonsa..
Ga wasu manyan abokansa a gefe da gefensa.

Ga ƙannensa Islam da Arfat suma sun fito, sun sha kyau sosai..

Hankalinsa duk yana kan Amal.
Idanunsa sun haɗu da nata.
A lokacin, duniya ta tsaya cik a gare su.
Babu kowa a cikin ido sai su biyu...

A gefe, Ammy ba ta hallara ba.
Tana zaune a gida cikin living room ɗinta, tana kallon walimar ta hanyar TV live broadcast..
A gefe ta ajiye cup ɗin tea amma ba ta sha ba.
Tana kallon Amal a fusace.

“Yaron nan... wannan ce mace da zai ɗauka? Wannan ce har zai ce ta fi masa kowa?”
Ta lumshe ido, ta ɗaga hannu a hankali tana faɗin:
“Allah Ka kare ɗana daga halin da bai sani ba...”

A zuciyarta akwai ƙunci da kuma wani ɓangare na soyayyar ɗanta da ta kasa fitarwa...

An kunna lights show, DJ ya saka waka mai nutsuwa.
Amal da Maleekh suka zauna kusa da juna a kujerar aure, fuskokinsu cike da annuri.
Ƴan uwa suna ta ɗaukar hotuna, ana ta murna, ana dariya.
Maleekh ya juyo a hankali yana kallon Amal.

“Yau kowa yana gani… amma ba kowa yake fahimtar yadda zuciyata ke bugawa saboda ke ba.”

Amal ta yi murmushi, ta ɗaga kai ta ce:

“Daga yau ni ce matar da zaka ƙira naka… har abada.”

Sai suka kalli juna lokaci ɗaya fitilun wajen suka sauya launi zuwa gold and white.
Jama’a suka tashi da tafi da shewa:

“Auren shekaraaa!!! 🎉🎉🎉”

Daren Walimar Aure

An rufe taron da murna da nishaɗi. Wurin ya cika da farin ciki, kiɗa, da ƙamshin turaren da ke fita daga ko’ina. Kowa na faɗin,

“Allah ya kaimu gobe lafiya, Allah ya tabbatar da ɗaurin auren lafiya.”

Yamma ta wuce, dare ya sauƙa da sanyin iska mai ɗauke da ƙamshin furanni. Gidaje suna walƙiya da hasken fitullun gilashi da aka rataya a ko’ina.

Misalin ƙarfe 9 na dare
Kowa ya koma gida, Amal ta cire veil ɗinta, ta zauna gaban madubi tana duban kanta da murmushi. Cikin ranta tana jin kamar ta shiga mafarki auren da ta jima tana mafarki da shi, yanzu gobe ne.

A gefe kuma Farha, Aisha da wasu ‘yan uwanta mata suna zaune a akan gado suna ta dariya, suna tsokanar Amal:

Farha wacce yau ta kasance a wurin hidima kuma ta shiga sahun ƙawayen Amarya, yau a gidansu Amarya zata kwana cikin ƙawaye...

Farha ta ce “Ke fa Amal, kin san idan aka ɗaura auren nan gobe, gobe da dare ba zaki huta ba!”

Duk suka yi dariya.

Aisha ta ce “Ke Farha ki bari mana amarya ta huta, kin manta da walimar yau? Duk jikinta a gajiya yake, kika sanar mata wannan al'amarin ai sai ta tsorata kuma...”
Suka kwashe da dariya gaba ɗaya.

Amal ta ɗago kai daga madubi, tana murmushi cikin kunya.

“Ku dai ku bar ni in sha iska, na gaji sosai.”

Wata daga ciki ta ce
"Ji sai kace wacce kika yi wani rawar azo a gani..."

Amal ta ɗan harareta tana shirin tashi kenan, sai wayarta ta yi ƙarar message.
Ta ɗauka, zuciyarta na bugawa. Number ɗin “Amaleekh ❤️” ce, ta bayyana...

“Please Beb, ki fito waje yanzu... inason ganin kyakkyawar fuskarki kafin na wuce gida.”

Amal ta ji zuciyarta ta yi wani irin sanyi. Ta tashi, ta saka veil, ta ɗauki jakarta da wayarta ta ce da murmushi:

“Ina zuwa yanzu…”

Farha ta ce da dariya:

“Ango yayi ƙira kenan, to Ya Maleekh amarya zata fito!”

Aisha ta miƙe da sauri tana faɗin.
"Tsaya a kwaskware miki fuskar mana.."

Nan aka sake tsara mata sabon makeup..

Ta matsu ta fita saboda kar ta ɓata masa lokaci..

Farha ta ce "Dan Allah ku barta haka kar Ango ya gudu.."

Suka kwashe da dariya gaba ɗaya, Amal ta fita tana murmushi.


A Harabar Gidan

Daren ya yi shiru. Iska mai sanyi na busowa, Haske na haskaka filin gidan...

Amal ta iso bakin get, ta ce wa mai gadi cikin ladabi:

“Please ka buɗe mun ƙofa, ina dawowa yanzu.”

Mai gadi ya buɗe, yana murmushi.

“To Amarya, ki kula fa, dare yayi.”

Tana tafiya a hankali cikin doguwar gown mai ruwan milk, tana ɗauke da ƙamshi mai sanyaya zuciya. Ga takalminta mai tsini sosai, ta ɗan ɗaga rigarta kaɗan saboda kar ta taka takalmin..

A gaban get ta hango wata babbar mota baki mai taya ta baya, fitilunta a kashe. Ta ɗan yi murmushi a zuciya ta ce, “Laa, har yanzu yana nan a mota yana jirana.”

Tana kusantowa ta buɗe motar ta shiga da murmushi.
Bayan ta shiga ta rufe ƙofar, ta tsaya cak ganin wasu mutane daban a ciki..

Kafin ta yi magana, wani mutum daga bayan kujerar ya damƙeta da ƙarfi, ya sanya handkerchief mai ɗauke da turare a hancinta.
Amal ta fara ƙoƙarin yin ihu, amma muryarta ta sare. Idanunta suka fara lumshewa, numfashinta ya yi rauni.

“Ssshhh… shiru, komai zai dai-daita,”
wani murya mai sanyi ya faɗa, kafin komai ya rufe mata duhu.

A lokacin ta sume domin turaren irin mai saurin sumar da mutum ne...

Motar ta tashi da sauri cikin dare, ba kowa ya lura ba.
Sai ƙarar motar ta ɓace cikin shiru...

🕛 A cikin gidan kuwa.

Lokaci yana tafiya. 11 na dare.
12.
Har 1 na dare.

Farha ta miƙe daga inda suke zaune, tana kallon agogo cikin tashin hankali.

“Ni fa har yanzu hirar bata ƙare bane? Ko kuwa ta koma wajen Maleekh ne da kwana?”

Aisha ta ce:

“Ai ta ce ‘ina zuwa yanzu’. Ta tafi ne kamar za ta dawo nan da minti goma…”

Farha ta ɗauki wayarta ta ƙira Amal ringing... amma ba’a ɗauka ba.
Ta sake ƙira still not picking.

“Ba’a ɗauka ba. To bari na ƙira Yaya Maleekh.”

Ta ƙira. Switch off.
Farha ta kalli Aisha cikin tashin hankali.

“Wayarsa a kashe... wannan ba daidai bane.”

Aisha ta ce: “Ku tashi mu fita mu duba waje.”

Suka fita zuwa harabar gidan, suka tambayi mai gadi.

Mai gadi ya ce musu: “Ai ta fita ta ce za ta dawo

62 / 82