Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   42 / 82

123K to 126K   out of 244.2K words

Ammy ta hankad’a ta gaba tana faɗin.

"Je ki! Je ki!!..."

Islam ba yanda ta iya haka ta sa Zayd a gaba zata kai shi part ɗin Maleekh....

Farha cikin shagwaɓa ta ce.

"Ammy nima dai ina son ganin Ya Maleekh ne dai..."

Ammy ta ce
"Ki bari daga baya kya gan shi, tin da kuna tare yanzu..."

☆☆☆☆

Abbah yana zaune a bakin gadon da Maleekh yake zaune shima, sun jeru kamar masu hira...

Abba ne yake ta bashi haƙuri akan ya daina sa damuwa a ransa yanzu, sannan ya daina gaggawar ɗaukan hukunci....

Abbah ya ce

"Maleekh na ga tsantsar soyayya a idon wannan yarinya, dan Allah ka tsaya kayi bincike sosai kafin ka yanke hukunci, kallo ɗaya nayi wa wannan yarinyar na fahimci cewa bazata taɓa aikata abinda ake zarginta akai ba, naga nutsuwa a tattare da ita..."

Maleekh ya ce

"Abbah please ni yanzu bana son jin maganarta, zan yi abin da ya kamata idan na nutsu..."

Su na cikin wannan halin sai suka ji knocking...

Abbah ne ya bata izinin shigo wa..

A falon ɗakin suka ji sallamar Islam..

Abbah ne ya yi magana da cewa:

"Ya akayi ne shigo ciki mana.."

Islam ta ƙara yin sallama sannan ta buɗe ƙofar bedroom ta shigo, a bayanta kuwa Zayd ne yake biye da ita...

Abbah ganin Zayd yasa shi faɗin.

"Ha'a yau babban ba'ko muka yi ne?.."

Zayd yana dariya ya durƙusa yana gaishe da Abbah..

Abbah ya amsa cikin nutsuwa sannan ya tashi ya yabar musu ɗakin...domin yasan Maleekh da Zayd manyan abokai ne...

Maleekh miƙe wa yayi yana murmushi suka rungumi juna....Zayd ya bubbuga bayansa tare da faɗin:

"Man ya jikin nakan, naji ance ka haɗu da break heart..."

Maleekh jin haka yasa ya harare shi ya zauna a bakin gadon..

Islam kuwa sallama tayi musu sannan itama ta fita...

Idon Zayd ne ya sauƙa akan wani glass pictures na yara biyu suna rungume da juna..

Murmushi ya yi tare da ɗauka yana duba wa...

"Har yanzu ka kasa cire Baby a ranka..."

Maleekh ya ce yana kallon hoton hannun Zayd.

"Da ba dan rasata da nayi ba, da babu wani heart break da zan fiskanta...A yanzu zan ci gaba da jiran fiance ɗina..."

Zayd ya ce

"Idan kuma ta mutu fa?.."

A zabure Maleekh ya kalle shi tare da girgiza kai yana faɗin
"Kar ka sake faɗin haka..."

Zayd ya ce. "Kana hauka ne? amma kowa yasan cewa ita da iyayenta sun mutu sakamakon gobarar wuta da aka dasa musu.."

Maleekh a hankali ya furta.

"Idan iyayenta sun mutu to ita tana raye kuma zan ci gaba da jiranta.."...


☆☆☆☆


Da ƙyar Amal take tuƙi, hawaye na zuba kamar ruwan sama. Gaba ɗaya titin da take bi sai ya rikice mata a ido. Sau biyu tana kusan yin karo da mota saboda tsananin tunanin da ya mamaye ta.

“Ya Allah… me yasa rayuwata ta zama haka? Na rasa wanda zuciyata take so… Na rasa farin cikina gaba ɗaya…”

Ta dafe kirjinta, tana jin kamar zuciyarta ta tsinke gida biyu. Duk inda ta dubi gilashin mota, a madubin gaba sai ta hango fuskar Maleekh. Idanunsa masu ƙarfi, muryarsa mai dukan zuciya, da kalmomin da suka fi kowane makami ciwo:

_*“Bana sonki, Amal… bana sonki.”*_


“Ya Maleekh…” ta furta da rawar murya.
“Wallahi ban aikata laifin da ake zargina ba. Na rantse da Allah kai kaɗai nake so. Na rantse da Allah kai ne numfashina. Ka yarda da ni, My Bee… kada ka ƙi ni haka.”

Sai hawaye suka sake zuba sosai. Ta tsaya gefe da hanya ta jingina kanta da sitiyari tana kuka kamar wata ƙaramar yarinya...

A zuciyarta tana addu’a:
“Ya Allah, idan ina tare da gaskiya, idan ina son shi da zuciya ɗaya, ka dawo min da shi. Kada ka bar soyayyarmu ta mutu haka kawai. Ka tsare shi da cuta, ka tsare shi da mugunta… ka shiryar da zuciyarsa gare ni.”

Numfashinta ya yi nauyi, amma har yanzu zuciyarta na ambaton sunansa:

_“Maleekh… Ya Maleekh…”_


______________________________________

Maleekh yana zaune a gadon sa yana jingine da pillow, idanunsa na kallon Zayd wanda ke zaune a gefen gado da murmushin nishaɗi a fuska.

Zayd ya gyara zama ya ce:

“Bros, wallahi yau a zuwana gidan nan na haɗu da wata pretty yarinya… gaskiya ta kwanto min a rai sosai. Amma fa tana da ɗan jiji da kai, duk da haka babu matsala, soyayyata zata sauƙe mata wannan girman kan.”

Maleekh ya ɗan ɗago ido ya kalle shi, sai kawai ya yi murmushi mai rauni sannan ya ce:

“So cute, na tayaka murna.”

Zayd ya girgiza kai yana dariya:

“Hmm, Bros, kai da kanka ka san idan Zayd ya fara, to babu gudu babu ja da baya.”

Maleekh ya ce cikin dariyar dole:

“Ni dai ina fatan kada ta kawo maka wahala.”

Zayd ya lumshe ido ya ce cikin salo:

“Amma ka san wani abu? Na yi big mistake wallahi. Ban tambayi sunanta ba, ban kuma karɓi address ɗinta ba. Kuma a lokacin ma she is so weak… kamar mai ciwo.”

Maleekh ya yi dariya kaɗan, yana kallon shi da murmushin tausayi:

“To sai ka yi searching ɗinta a zuciya, ko? In ka ci gaba da yi mata addu’a za ku haɗu da ita in Allah ya so.”

Suka yi dariya duka.

Sai Zayd ya matsa kusa da shi ya ce:

“Amma fa Bros, sai ka daure. Na san kana da wani abu a zuciya, amma ina maka addu’a zaka samu nutsuwa. Kai fa ba kawai yayana ba ne kai ne abokin rayuwata. Duk ciwonka, duk damuwarka, ina tare da kai har ƙarshe.”

Maleekh ya ɗan rufe ido, zuciyarsa ta yi nauyi. Amma saboda ƙoƙarin kada ya nuna raɗaɗinsa, ya ce cikin murmushi:

“Na gode, Zayd. Allah ya saka da alheri. Kai kaɗai ne kake bani nishaɗi a wannan lokacin.”

Zayd ya bubbuga kafaɗarsa yana dariya:

“To ai ba komai ba. Ni dai na ce maka ka shirya, very soon zan zo maka da labarin soyayya irin ta film. Ka ga na fi ka nasara kenan.”

Duka suka sa dariya.... dariya mai saurin yankewa daga gefen zuciyar Maleekh saboda ciwon da yake boyewa.


Bayan dariyar ta ɗan lafa, Zayd ya tashi daga gefen gadon ya ce:

“Ni dai zan je in huta. Amma Bros, ka kwanta ka cire damuwa daga ranka. Komai zai daidaita da izinin Allah.”

Maleekh ya yi ƙoƙarin mayar da murmushi:

“Na gode sosai, Zayd. Allah ya sa ka samu farin cikin da kake nema.”

Zayd ya yi masa _thumbs up_ ya fice daga ɗakin cikin nishaɗi.

Maleekh ya zauna a gefen gadon na ɗan lokaci, hannunsa yana shafa hoton da yake a gefen bedside table. Wani irin numfashi ya sauƙe, ya kwanta da baya ya rufe idanunsa.

Amma duk da ƙoƙarinsa, hoton Amal ya bayyana cikin zuciyarsa kamar tana tsaye a gabansa. Kukan da ya ji daga gare ta a falon gida, hawaye a fuskarta, da muryarta tana ƙiran sunansa duk suka sake dawo masa.

Ya rufe fuska da hannayensa yana ambaton:
“Ya Allah… me yasa har yanzu zuciyata ta kasa daina ji da ita?..”

Wani irin raɗaɗi ya shige shi, amma duk da haka ya danne shi, yana son ya nuna ƙarfin hali gaban kowa. Sai dai a zuciya, ya san ciwon Amal ba zai bace masa da sauƙi ba.

____________________________________

A wannan daren...

Amal tana kwance kan gadonta, ƙwance cikin duhu, idanunta suna kallo ceiling ɗin ɗakin amma zuciyarta ta kasa samun nutsuwa.

Ta juyo gefe tana riƙe da pillow kamar zata matse shi. Hawaye suka zubo a kuncinta tana faɗin cikin rauni:

“Maleekh… duk duniya babu wanda na so kamar kai. Ko da baka yarda dani ba, ni nasan gaskiya zata bayyana wata rana…”

Ta runtse idanu tana ƙoƙarin yin bacci, amma duk lokacin da ta lumshe ido, hoton Maleekh ne yake bayyana, yana mata tsawa da maganarsa mai ciwo.

Sai kawai ta yi shahada a hankali, tana roƙon Allah ya ba ta ƙarfin zuciya:

“Allah ka bani haƙuri da ƙarfin zuciya akan wannan jarabawa…”

Ta zauna bakin gado tana kallon taga, tana jin wani irin ƙarfi a zuciyarta cewa ko da Maleekh ya ƙi ta, ta tabbata ba haka zuciyarsa take ji ba.


_WASHEGARI_

Da safe suna zaune tare a dining area, an shirya breakfast.

Zayd yana cin toast yana kallon Maleekh cikin annashuwa ya ce:

“Bros, shin wani matsayi za’a bani a cikin company ɗinka?..”

Maleekh ya ɗan ɗaga kai daga coffee cup ɗinsa, ya girgiza kai tare da faɗin:

“Zan iya faɗa maka Zayd, amma ka bari mu je muji daga bakin board kafin a sanar maka matsayi.”

Zayd ya lumshe idanu yana murmushi ya ce:

“Gaskiya fa, ina so ace an bani matsayin assistant ɗinka. Ka san muna tare a koda yaushe.”

Ƙaramin murmushi ya bayyana saman fuskar Maleekh sannan ya ce:

“Akwai wacce take kan wannan matsayi. Ban yarda da cire wanda yake kan mukaminsa kawai don wani ya shigo ba. Abin da ya dace shine, zan baka matsayin da ya yi daidai da kwarewarka. Duk wanda yake matsayin assistant burinsa shine ya haura gaba, ba ya tsaya nan ba.”

Zayd ya ɗan saki baki cikin rashin fahimta ya ce:

“Oh, kenan ban dace da matsayin ba?..”

Maleekh ya ɗago idonsa ya kalle shi da nutsuwa ya ce:

“Ba haka nake nufi ba. Zayd, adalci ne yafi komai. Idan na sauƙe wacce take assistant ɗina kawai saboda kai, ai na zalunce ta. Ina fatan zaka fahimce ni.”

Zayd ya lumshe ido cikin murmushi ya ce:

“Shikenan, no problem. Na yarda da kai.”

A haka suka gama breakfast ɗin suka nufi company ɗin tare...


_Campany_

Yayin da suka shigo cikin babban reception ɗin, ma’aikata suka fara gaishe da Maleekh da girmamawa.
A nan suka tsaya kafin su nufi sama, sai kawai ƙofar glass ta buɗe.

Amal ce ta shigo cikin tsararren kaya, tayi dressing cikin class, high heels ɗinta na danna tiles ɗin ƙasa tana tafiya cikin ƙasaita. Duk wajen ya ɗan tsaya cak.

Zayd ne ya fara hangen ta, ya yi ido huɗu da ita.
Ya buɗe baki yana cewa cikin farin ciki:

“Wowww… Allah ya sake haɗa mu, my beautiful pretty!”

Duk reception suka juyo da kallon mamaki, suna kallon Amal da Zayd.

A hankali Maleekh ya juya kansa saboda jin yanda Zayd ya ƙira pretty.
Idonsa ya sauƙa kan Amal, zuciyarsa ta buga da ƙarfi! Ya dunƙule hannunsa da ƙarfi tare da haɗiyar yawu...

Amal ta tsaya cak, idonta akan Maleekh, jikinta yana rawa da tsoro.

Maleekh ya ɗan jinjina kai da ƙarfi, yana murza yatsansa cikin tafin hannu, sannan cikin nutsuwa ya ce da karfin zuciya:

“Fatan alkhairi…”

Ya nufi escalator..Yana zuwa ya ɗaga ƙafarsa ya hau escalator, amma idanunsa suna kan Amal har sai da ya haura.
Amal itama idonta akan sa har sai da ya ɓacewa gani.

Zayd yana nan tsaye kamar wanda ya ci jackpot, yana murmushi ya ce da Amal:

“Pretty, ke ma a nan company kike aiki? Alhamdulillah! Wannan babban alheri ne. Ni ma yau zan fara aiki anan. Kinga yanzu za mu zama ɗaya kullum…”

Amal bata ko kalleshi ba, kawai ta ratsa gefensa cikin isa, ta nufi elevator.

PA ɗin Maleekh dake tsaye a reception ya yi murmushi ya ce wa Zayd:

“Your welcome sir. Waccan ce assistant CEO ɗin company.”

Idon Zayd ya buɗe da mamaki ya ce:

“What! Assistant CEO? She?…”

Kafin ya gama, Amal ta shige elevator.
Da sauri Zayd ya nufi wurin yana cewa:

“Wait, pretty! Ki jira mana please!”

Amma elevator ɗin ya rufe a gabansa, Amal ta tafi sama ta barshi tsaye a ƙasa yana ƙoƙarin numfasawa da murmushi marar dalili...


A wannan rana haka Zayd yake ta shishshige wa Amal.
Zayd ya ci gaba da zagaye Amal a cikin company...

Ko da break-time sai ka ganshi ya shigo office ɗinta da excuse: “Pretty, kin ci lunch kuwa?..."

Anjuma kaɗan sai ya dawo ya ce "Pretty, kin huta kuwa?.."

Bayan wasu ƴan mintuna sai ya sake dawowa Ya ce "Pretty, kin sha ruwa kuwa?”..

Duk da Amal tana ƙoƙarin sharar da shi da kakkaucewa, Zayd ya kasa nisanta daga gare ta...

Ba yanda ta iya haka take biye shi suna fita tare da sauran staff, yana yi mata hira da dariya. Duk wanda ya gansu zai ce soyayya ce mai tasowa...

Amma Amal a ranta tana jin nauyi, tana jin ba komai bane idan ba da Maleekh ba….

A gefe kuwa, Maleekh shiru yake. Duk lokacin da ya hango Zayd yana yi wa Amal hira, idonsa na canzawa. Yana jin zafi a zuciyarsa amma baya nuna komai. Kishi na cin ransa, amma sai ya dake, yana bawa kansa hujja:

“Ba ni da masoyiya, na sallame ta, so… me yasa kike jin zafi Maleekh?”


☆☆☆☆☆

Two days after Zayd started working at the company….

Wata rana, bayan aiki, Amal ce ta ɗauki babban fayil ɗin takardu. Su ne takardun da Maleekh bai samu damar dubawa ba lokacin da yake jinya. Ita ce assistant, dole ta kai masa domin ya sanya hannu kafin ranar ƙarshe.

Tana shiga cikin office ɗin sa.
Ƙamshin turarensa ya buga mata kai.
Maleekh yana zaune shi kaɗai, ya jingina a kujerarsa, hannunsa riƙe da pen yana rubuce-rubuce.

“Excuse me, sir…” Amal ta furta a hankali, zuciyarta na tsalle-tsalle.

Ya ɗago idonsa, suka yi ido huɗu. Zuciyarsa ta buga, amma bai nuna ba.
“Zo,” kawai ya ce da muryar kasaita.

Ta matsa kusa da desk ɗinsa, ta aje fayil ɗin.

“Wannan su ne takardun da ba a duba ba lokacin da kake jinya. Na yi reviewing, sai ka sanya hannu.”

Ya ɗauki pen ɗinsa, ya fara dubawa.
Amal ta tsaya a tsaye tana kallon gefe, zuciyarta na rawa. Duk da ita ce assistant ɗinsa yanzu, ba zai taɓa sauƙin kasancewa da shi cikin ɗaki guda ba.

Shiru ya mamaye office ɗin, sai ƙarar bugun zuciyoyinsu da suke jin shi su kaɗai.

Bayan ɗan lokaci ya ɗago ya ce da muryar nutsuwa:

“Na gode da kula da company lokacin da ban samu dama ba.”

Amal ta ɗan runtse ido, ta ce cikin sanyin murya:

“It’s my duty, sir.”

Suka yi shiru.
Takardun suka koma magana tsakanin su.
Babu wata hirar soyayya. Babu wata rigima.
Sai dai ƙirji biyu suna bugawa cikin ciwo da sha’awar da suke ɓoyewa.


Amal tana tsaye a gaban desk, tana nuna wa Maleekh inda zai sanya hannu a cikin fayil.
Shi kuma yana kallon takardu, sai lokaci-lokaci idanunsa su kai kanta, sannan ya ɗan janye kai kamar bai kula ba.

Shiru ya rufe office ɗin, bugun zuciyoyinsu na ci gaba da daɗa karfi.

Kawai aka buɗe ƙofa, Zayd ya shigo da murmushi a fuskarsa..

“Prettyyy! Ashe kina nan…”

ya faɗa yana matsowa cikin sanyi.

Amal ta juyo da sauri, idanunta suka firgita.

“Zayd… kai fa…”

Maleekh kuwa ya ɗago daga rubutunsa, ya kalle shi da idon da ba a iya fassara ba. Idonsa cike da kishi da takaici, amma fuskarsa na ɗauke da ɗan murmushin da ya fi zafi fiye da faɗa.

Zayd bai damu ba, ya ƙarasa gaban Amal, har yana ƙoƙarin kai hannu zai ɗauki fayil daga hannunta..Yana cewa

“Kin wahala fa Pretty. Ina gaya miki, idan kin gaji da yawa sai ki bar sauran a hannuna.”

Amal ta janye hannunta da sauri, ta ɗan ɗaure fuska sannan ta ce:

“Ba sai haka ba, Zayd. Ina yi ne saboda aikin company.”

Maleekh ya jingina da kujerarsa baya, ya ɗau pen ya fara jujjuyawa a yatsansa..
Da wata muryar ƙasaita mai sanyi amma mai tsanani, ya ce:

“Mr. Zayd… wannan office ba wajen hira bane. Idan akwai aikin da ya shafe ka, zaka iya aiko da secretary ɗinka.”

Shiru ya ɗan ɗauki ɗakin.
Zayd ya murmusa, yana son nuna bai damu da tsawar ba ya ce:

“Sorry, sir. Ni dai kawai na zo in ga Pretty—ehm… Amal ko ta gama da waɗannan takardu.”

Amal ta ji kunya sosai, zuciyarta na buga wa...

Maleekh kuwa idanunsa sun ƙanƙance, ya dafa desk ɗin da hannu ɗaya.
Cikin natsuwa amma muryarsa ta sauya, ya ce:

“From now on… babu wanda zai ƙira assistant ɗina da wani suna daban a nan cikin office.”

Zayd ya ji an kulle masa baki.
Amal ta kasa ɗaga kai saboda kunya da bugun zuciya.

Amal jan jikinta tayi ta bar Office, Zayd ganin haka yasa shi bin bayanta yana faɗin

"Ya za ki tafi ki bar ni ehhh pretty tsaya manaa..."


Bayan antashi daga wurin aiki..

Amal ta fito daga building tana riƙe da jaka a hannu. Zayd ya biyo bayanta da sauri, yana ɗan tafiya da wani irin sanyi da yanga.

“Pretty,” ya ƙira ta da fara’a, “nasani kin gaji sosai yau. Ki bari ni na kai ki gida da kaina a mota.”

Amal ta tsaya, ta kalle shi da ɗan murmushin ladabi, sannan ta girgiza kai.

“A’a, ka barshi. Zan tafi da motata. Sai gobe ka fito da wuri kar ka makara.”

Zayd ya yi dariya yana jingina da jikinsa kamar wanda ya ci nasara...

“To my pretty, ai ko ba komai … saboda naga wannan kyakkyawan fuskar taki zan fito da safe.”

Amal ta yi shiru kawai, ta buɗe motarta ta shiga. Ta ja motarta ta tafi cikin nutsuwa.

A gefe kuma…
Maleekh yana cikin motarsa, hannunsa yana ta matsa sitiyarin kamar yana son ya murƙushe shi. Fuskar tasa ɗauke da murmushi marar annuri, idanunsa sun cika da wani irin haske na kishi da haushi.
Ya kalli hanyar da motar Amal ta bi, zuciyarsa na karyewa da tunanin:

“Tana iya yin dariya da shi… ta kyale shi yana ƙiran ta da suna da ni kaɗai na san darajarsa… amma ni na rasa komai. Na bar komai.”

Bayan mintuna kaɗan, Zayd ya ƙaraso motar Maleekh da murmushi a fuskarsa. Ya buɗe ƙofar ya shiga cikin nishaɗi tare da faɗin.

“Bros Maleekh! Wallahi wannan assistant ɗinka…ehm sorry—Amal—she’s so wonderful! Ka ga irin yadda take da nutsuwa? Kuma gaskiya she’s different, ba kamar sauran mata ba…”

Maleekh ya ɗauke kansa daga kallonsa, ya mayar da hankalinsa kan hanya.
Zayd yana ta zuba maganganu yana yaba Amal kamar wanda ya gano wani abu na musamman.
Shi kuma Maleekh ba ya cewa komai.
Sai dai idanunsa suna ƙara yin ja saboda haushin maganganun Zayd, zuciyarsa na ƙonewa cikin silent fire.

Sai kawai ya murɗa accelerator, motar ta yi wani irin gudu kamar yana zubar da ɓacin rai cikin gudun...

Zayd ya ɗan tsaya yana kallonsa, ya ce da dariya:

“Bros… wai kai ba ka ganin irin yadda Amal take kyakkyawa ne? Ai ba a barta haka kawai ba.”

Maleekh ya ɗan yi murmushi mai sanyi, wanda bai nuna farin ciki ba.
Ya ce cikin wata murya mai sanyi da raɗa:

“Ka cigaba da yaba ta, Zayd… kai dai ka tabbatar baka makara a aiki gobe ba.”

Shiru ya rufe motar. Zayd bai fahimci nauyin kalaman ba, ya cigaba da hira, yayin da Maleekh zuciyarsa ke tafasa cikin silent jealousy...


_AMAL_

Ta riƙe sitiyarin da hannayenta biyu kamar mai gudun kada zuciyarta ta tsinke.
Tun lokacin da ta hango Maleekh a reception, har lokacin da ya haura saman escalator ba tare da ya yi mata magana ba, zuciyarta ta kasa natsuwa.

“Ya kalle ni… amma ya ɗauke kai. Ya jinjina kai kamar wanda ya gama da ni. Amma shin da gaske ya gama da ni? Har yanzu idanunsa sun

42 / 82