Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 82

27K to 30K   out of 244.2K words

“Ki daure Amal… ki tsaya mana… kin fi kowa ƙarfin hali!”

Amal bata iya magana ba, tana sauƙe numfashi, tana kallon saman sararin sama, kamar me fassara zuciyarta.


●●●


An riga an ɗauki video lokacin da Maleekh ya faɗo kan Amal yana kwance, lokacin da ta ceto rayuwarsa, lokacin da kallon idonsu ya haɗu. Duniya bata ji bayani ba tukuna, amma magana ta fara yawo.

Kwanaki biyu bidiyon Amal da Maleekh ya karkaɗe duniya, Twitter, TikTok, Instagram da dukkan kafafen labarai sun ƙone da sharhi, faɗa, jin daɗi, mamaki da ruɗani.

🌍 RA'AYIN JAMA'A:

“Wannan fa jaruma ce, ba mace ba!”

“Wata mace ce ta ceci babban attajiri kamar Maleekh?”

“Da alama akwai wani abu a zuciyar Maleekh yanzu…”

“Gaskiya Amal tayi bajinta, wannan video yafi duk hoton soyayya da na gani.”

JARIDU SUN YI RUBUTU.

Vanguard, Premium Times, The Nation da Daily Trust sun buga labarai kamar:

“Amal, Matar da ta ceci rayuwar Maleekh a harin ƴan daba”

“Ɗiyar Talakawa da ta juyar da hankali a Najeriya, Wacece Amal?”

“CashTalk FM ya shiga rikici bayan bidiyon Shugabansu da Amal”


RAYUWA FM🎤

Bayan kwana uku, Amal ta koma Rayuwa FM, cikin shiri na musamman da suka yi wa suna:

“Soft Power: Lokacin da ƴan talakawa suka dawo da iko.”

Tana sanye da doguwar riga abaya, kanta a rufe da gyalen abaya, Tana da kwarin guiwa, da nutsuwa.

Ta kunna mic ɗinta, sannan ta ce cikin murya mai ƙarfi da lumana ta fara jawabi

“Assalamu Alaikum wa rahmatullah…

Sunana Amal Abdulsamaad. Ni jika ce ga Inna, talaka ce, mace ce mai cikakken hankali da imani.

A cikin wannan bidiyon da kuka gani, ni ce a ƙasa. Na ceci rayuwar wanda yake da iko, kuɗi, suna da ƙarfafa gwamnati. Na ceci Maleekh.

Amma kafin hakan, an yi ƙoƙarin kashe ni, a tsorata ni, a siye ni, a ruɗe ni da maƙudan kuɗaɗe, An nemi in miƙa gaskiyata domin su mallaki zuciyata.

Amma ku sani, kuɗi ba gaskiya bane. Iko ba shine girmamawa ba. Gaskiya bata cika da ƙarfin tsiya. Bata jin tsoro. Kuma daga yau zan ci gaba da faɗan gaskiya a kowanne lokaci.”

Amal tayi wannan jawabin ne domin ta kawar da wannan maganar video da ake jita-jitar sanar da cewa soyayya ce..

Jama'a a kafafen sada zumunta sun ɗaura taken: #AmalVoice #JarumaAmal #TruthShines
Kuma Rayuwa FM ta samu ƙarin masu sauraro fiye da kowane lokaci....


●●●●

Maleekh yana kwance a cikin yacht ɗinsa a cikin swimmingpool dake cikin wantalelen gidan su, yana kallon bidiyon da aka ɗauka lokacin da ya faɗo akan Amal..... A cikin ransa ya furta

“Why can't I stop watching this video... Who are you, Amal?”


A lokacin ne PA ɗinsa ya shigo, ya ce masa:

“Sir… da alama gaskiya ta fara kashe ƙarya. Abinda ka yi da Amal ya fara cin riba.”


Maleekh bai ce komai ba. Ya zuba ido cikin bidiyon… ya maimaita kalmarta da murya mai sanyi...

“Kuɗi ba gaskiya bane.”



RA'AYIN JAMA'A A KAFAFEN SADA ZUMUNTA..

@RealTalkNaija:

“Maleekh na kwance akan Amal kamar drama na Nollywood 😭 Abin ya fita a rai!”



@QueenLami:

“Wannan ba ceto bane kawai. Wannan soyayya ce da basu shirya yarda da ita ba 😍”



@VoiceOfKaduna:

“Kusan shekara biyar kenan da ba a ga Maleekh da mace a dandalin jama’a ba. Amma yanzu Amal ta jawo shi da zuciya.”


#AmLeek #AmalAndMaleek #RayuwarSoyayya


A wannan ranar Amal kwana tayi tana juyi ta kasa yin bacci, jin maganganun da mutane ke faɗi tsakanin ta da Maleekh...

A ranta ta furta "daga ceto sai a fassara lamarin?..."

Inna ce ta shigo ta same ta sai faman juyi take, ta zauna a gefen katifar ta tare da furta "Amal..."

Amal ta tafi dogon tunani bata san Inna ta zaune gefenta ba, Inna jin bata cikin hayyacinta ne yasa ta buge ta a baya tare da faɗin "ke Amal..."

A ruɗe Amal ta tashi zaune tare da faɗin
"Ni ba soyayya nake da Maleekh ba ...."

Inna ta zuba mata ido ta ce "too pahh..."

Sunkuyar da kai Amal tayi...

Inna ta ce "abinda ake faɗa ashe gaskiya ne? daga ƙiyayya sai a fake da soyayya?..."

Amal ta ce "wallahi Inna ba gaskiya bane..."

Inna ta dankwale ta tana faɗin "Kan jatumarki, munafuka, har gida aka zo aka nuna mun video ke da wancan yaron, ashe bakida hankali Amal? sai yanzu na raina iliminki da tunaninki, to ki sani ke abin magana zai shafa ba shi ba, tinda shi duk abinda yayi ado ne, ki kula da irin yaran nan, tamm...."

Inna tana kammalawa ta tashi ta koma wurin kwanciyar ta...

Amal ganin ta rasa yanda zata yi ne yasa ta fara marin kanta tana faɗin "Na shiga uku! Na shiga uku!! Na shiga uku!!! Ni Amal ya zanyi..."

Itama haka ta gama shawaginta sannan ta kwanta bacci ɓarawo ya ɗauke ta....


Washegari da safe

Gidan 📺 TV PROGRAMS DA BLOGGERS sun sake fitar da wani bayani akan Amal da Maleekh...

“Gaskiyar Bidiyon Amal da Maleekh...”

Wani babban shiri a Channels TV yana nazari akan bidiyon yana ƙiran masanan zamantakewa da kwararrun masu fassarar al’amura...

“Is This Power Play or Love Story?”

Wani ɗan jarida a Arise News yana tambaya ko akwai wani ɓoyayyen abu da suka kasa faɗa...

Bloggers irin su ‘Naija Juice’ da ‘GistMe247’ suna cewa:

“Was this attack real or planned to create attention? Yanzu haka Amal ta zama celebrity.”

📻 A RAYUWA FM: Amal ta yi jawabi...

Bayan gani da jin abubuwan da ke yawo a dandalin sada zumunta, Amal ta dawo cikin studio ɗin Rayuwa FM, ta zauna tana fuskantar mic kamar yadda ta saba, sai dai wannan karon akwai ɗan fara'a da nutsuwa a fuskarta, ta fara jawabi kamar haka..

“Zan yi magana domin ku sani:
Ban san Maleekh daga baya ba har sai wata rana da ya fito da ikonsa ya shiga rayuwata. Amma faɗa ne ya haɗa mu ba soyayya ba. Kuma idan faɗa ne zai haifar da jituwa, toh wannan Allah masani....”

Sauraren wannan kalmarta ya sanya mutane sun sake tofa albarkacin baki. Wasu na ganin tayi hikima, wasu kuma sun ɗauka zata iya faɗar gaskiyar zuciyarta...


❤️

A gidan mahaifinsa, Maleekh yana kallon wani ƙaramin talabijin a ɗakinsa ana kan dawo da bidiyon nan akai akai. PA ɗinsa ne ya shigo yace masa:

“Sir, Nigeria ta riga ta ɗauka kuna soyayya. Koda ba haka bane, yanzu labarin yana raye.”

Maleekh cikin ɗan murmushi mara kwari ya ce

“Soyayya? Suna tunanin zuciyata ta buɗe… Amma shin ta karɓe ni kuwa?”

Sai ya ɗauki wayarsa, yana kallon hoton Amal da aka ɗauka lokacin da take faɗa, fuskar jarumta da ƙarfi a idonta. Bai ce komai ba, sai kawai yace:

“This girl... is ruining me gently.”



Bayan sati biyu...

Rayuwa FM ta shiga labaran duniya da sabbin jita-jita bayan an sanar da cewa an dakatar da Amal daga aiki ba tare da cikakken bayani ba. Jama’a ne suke tambaya
"me ya faru?",
"wace laifi ta aikata?", amma duk da tambayoyin da ke ci gaba da yawo, hukumar rediyon ta yi gum da baki.



Wani babban rikici ya ɓarke ne daga bayan fage, wasu gurɓatattun 'yan siyasa da suka ji tsoron shaharar Amal da yadda kalamanta ke wayar da kan talakawa, sun haɗu suka ba shugaban gidan rediyo Rayuwa FM maƙudan kuɗaɗe kimanin ₦100 Billions domin kawai a kori Amal daga aikin ta.

An hana ta dawowa ofis. Bayan mako guda da aka dakatar da ita, wani ƙaramin rubutu kawai aka turo mata:

“Rayuwa FM regrets to inform you that your services are no longer required.”

Amal ta karanta saƙon da idanuwan da suka saba da jarumta, amma a cikin zuciyarta ta ɗan firgita. Ba saboda aikin ba, sai dai saboda yaudara da cin hanci ya kashe gaskiya a gaban idonta.


Yanzu Amal ta dawo gida. Ta cigaba da kula da hidimomin gida, ta watsar da komai, ta ɗauka yanzu komai ba komai bane...

Inna ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba, domin bata son aikin Amal, kullum a cikin tashin hankali da faɗa da masu kuɗi da ƴan siyasa.

Amal ta share hawaye cikin nutsuwa. Tana son kwantar wa Inna da hankali amma zuciyarta ta cika da wata irin murɗaɗɗiyar baƙin ciki da rashin gaskiya da ta gani a duniya. Ta fahimta: gaskiya bata da matsuguni a cikin tsarin da suka sayar da komai.

Amal tana zaune da Inna cikin raunanniyar murya ta ce

“Inna... na san da yawa za su ce na yi rashin nasara. Amma gaskiya ba ta ƙarewa da aiki. Ta fi haka girma.”


Inna ganin yanda Amal take cikin damuwa ne yasa ta fara rarrashinta tare da ƙarfafa mata gwiwa akan haƙuri...


A DANDALIN SADA ZUMUNTA...

Mutane da yawa sun fara fahimtar cewa dakatar da Amal ba bisa ƙa'ida ba ne. An ƙirƙiri hashtags masu ƙarfi:

#JusticeForAmal

#RayuwaFMHasFallen

#TruthVsBillions


Wani shahararren marubuci ya wallafa:

“Sun koreta daga Rayuwa FM amma sun kasa koreta daga zukatan talakawa.”


💥

Amal ba zata zauna ba haka nan ba, domin zuciyarta na tafarfasa. Kuma tana da sabbin matakai da zata ɗauka domin cigaba da yaƙi da ƙazantar tsari. Ta yanke hukuncin za ta ƙirƙiri shafinta mai zaman kansa (YouTube ko Podcast) don ci gaba da faɗin gaskiya da wayar da kai....

Amma sai dai dakatarwar da aka mata ba iya wurin aiki ba, har da huld'a da social media gaba ɗaya an hanata..

Tana ƙara fuskantar ƙarin barazana daga ƴan siyasa, domin za su ga cewa ba a iya tsayar da ita da kuɗi ko tsoro.

Amal ta fuskanci tozarta daga gwamnatin da ta sayar da hankali da hange da biliyoyi. Amma ita ba ta sayar da murya ba...

Amal tana kuka ita kaɗai sai surutai take a ɗaki kamar wacce ta fara haukacewa, tana faɗin


“Na rasa aiki. Na rasa tallafi. Amma ban rasa murya ba. Kuma murya ɗaya idan ta faɗi gaskiya na fi biliyan da suka saye shiru.”

Kullum a cikin maimaita wannan kalmar take, domin sai da ta kwanta rashin lafiya sosai...

Ba ci ba sha kullum a cikin kuka, ga ba kuɗin tafiya hospital, sai dai Inna ta lalla6a zuwa chemist ta siyo mata magani, amma ciwo ƙaruwa yake, Inna har ta rasa kuɗin zuwa chemist ma...

Suka cigaba da jinyar gida, sai da Amal ta ɗau sati biyu a kwance, gaba ɗaya ta lalace...

A wannan rana Inna tana zaune a tabarma sai Amal dake kwance akan cinyar ta sai faman juye-juye take...

Wasu zafafan motoci ne manya baƙaƙe masu tayoyi ta baya kusan guda goma suka Parker a ƙofar gidan su Amal..

Mutanen unguwa kuwa kafin kace me wuri ya cika da mutane, yara da manya yanda kasan a ƙauye tsabar rashin wayewa irin mutanen unguwar...dake unguwar talakawa ne.

Wasu manya-manyan bodyguards ne suka fiffito daga cikin motar suna riƙe da manyan bindigu, sun sha black glass gasu baƙaƙe wuluk, yanda kasan sojojin Amurkawa....

Ɗaya daga cikin security ne ya buɗe murfin motar da babu wanda ya fito daga cikinsa, bayan mintuna wanda yake ciki ne ya wurgo da kafarsa ɗaya, kana ganin sawun kasan ɗan manyan mutane ne, shi ɗin ba abin rainawa bane sai wanda bai san shi waye ba, in ba Amal ba babu wanda zai nuna masa yatsa ya zauna lafiya...

Lokaci guda Makeekh ya miƙo daga cikin motar yana sanye da baƙin glass, ko kallon mutanen wurin bai tsaya yi ba kai tsaye ya kutsa cikin gidan, domin yau ya kudurta cewa sai yayi maganin Amal, tasa mutuncinsa ya zube a gari, kowa yana masa dariyar cewa ya fara soyayya da ƴar talakawa....

Maleekh da wasu bodyguard biyu ne suka shiga gidan, sauran kuma duk a waje suka tsaya...

Inna na ganinsu ta zabga uwar salati tana faɗin
"Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, sojoji kuma a gidan nan? dan Allah ku rufa mana asiri wallahi Amatu ta daina aikin jarida, gata nan rai a hannun Allah, babu lafiya..."

Maleekh saida ya bari Inna ta kammala magana kafin ya ce
"Assalamu Alaikum warahmatullah..."

Inna ta amsa cike da mamaki...

Maleekh zare glass ɗin kan dara-daran idanuwansa yayi ganin halin da Amal take ciki, a ruɗe ya ƙarasa wurin da take kwance akan cinyar Inna, shima zama yayi akan taburmar tare da ɗago ta akan cinyar Inna ya kwantar da ita akan tasa cinyar yana faɗin

"Amal ce ta dawo haka? me me me meya faru da ita?..."

Ganin yanda ya ruɗe ne ya bawa kowa mamaki, haka security suke kallon juna domin tin kafin su taho Ogan nasun ya sanar cewa "zai zo ne akan ya wulakanta Amal, ganin yanda video sa yake yawo tare da ita..." yanzu kuwa labari ya sauya....

Maleekh bai tsaya jiran komai ba ya miƙe da Amal, cikin gaggawa yake faɗin

"Please Mama ki sako hijab hospital zan kaita..."

Inna da saurin ta jin zasu tafi asibiti, haka Maleekh yayi mata ɗaukan lud'a ya fita da ita. A motarsa ya kwantar da ita sannan ya shige suka miƙe asibiti, ita kuma Inna daga baya aka taho da ita...

A babban asibitin Kaduna aka kwantar da Amal, sai da Maleekh yayi jinyar ta na kwana uku kafin yayi sallama da Inna ya koma Abuja, already ya gama biyan kuɗin komai na asibitin, da abinda za'a buƙata duk ya gama biya...

Sannan ya sanar wa doctor cewa 'idan da damuwa ya sanar masa a waya' ..

Inna tayi matuƙar farin ciki sosai da bajintar da Maleekh yayi musu...

Maleekh yana tafiya washegari Amal ta farka, ta samu sauƙi sosai, duk wata damuwa ya yaye mata, domin ba ƙaramin kulawa ta samu a asibitin ba...

Bayan an sallame su ne, suna gida Amal take tambayar Inna

"Inna! Aina aka samu kuɗin kaini asibiti? bayan bamu da sauran kuɗi, kuma naga babban asibiti muka je..."

Inna tayi murmushi sannan ta ce "Ɗan Albarka ne.."

Cikin rashin fahimta Amal ta ce "wa kenam?..."

Inna ta ce "Maleekh mana..."

A zabure Amal ta ce
"Wani Maleekh wai?..."

Inna ta ce "ke bana son shegen tambaya, Maleekh nawa kika sani..."

Amal cike da mamaki take jinjina batun...

Har aka ƙare makon nan Maleekh bai ƙira Amal ba sannan Amal bata ƙira shi ba, Inna tayi da ita akan ta ƙira shi tayi masa godiya amma sam Amal ta ƙi, wai ita sai idan shine ya fara ƙira tukun....

Da haka har aka sharar da zancen Maleekh....

♡♡♡
○○○

Amal ta shafe wata guda a cikin gida tana juyawa da rayuwa cikin tawali’u da haƙuri. Ta zamo abokiyar tafiya ta Inna daga girki zuwa gyaran gida, sannan kuma ta buɗe ƙaramin kasuwanci na siye da siyarwa a cikin gida. Tana saida kayan kwalliya, kayan miya, da snacks da ta ke sarrafa da kanta. A kullum ana jin dariyarta da sautin walwalarta da Inna..

Amal tayi alkawari wa kanta cewa

"Na riga na bar aikin rediyo. Babu komawa. Gaskiya zata rinƙa faɗuwa idan na dawo gurin da aka hana ni murya."..


Wata rana Amal tana zaune kusa da Kakarta, suna shan hira, tare da tura kayan kasuwa cikin leda, sai ga muryar sallama daga bakin ƙofar.

"Assalamu Alaikum..."

Amal ta ɗago kai tana sakar murmushi cikin mamaki ta ce

"A’isha?! Kece a nan gidan mu??"

A’isha ta nufo ta da murmushi, suka rungumi juna. Kawarta ta makaranta tin secondary..

A’isha ‘yar gidan wani Minister ce, wacce ta taso cikin alatu, amma bata taɓa manta ƙawarta Amal ba. Bayan sun gaisa da Inna, ta zaro wata ƙaramar takarda mai kyalli daga jaka, ta miƙawa Amal tana faɗin

“Katin bikin aurena ne! Na ce bazan bari wani ya kawo miki ba, domin sai da wannan katin ake shiga. Kuma bana so a hanaki shigowa...”

Amal ta tsaya daidai. Ta kalli katin tare da murmushin da ke haɗe da dakiya.

Amal cikin jin nauyi ta ce

“Hmm A’isha, anya kuwa zasu bari na shiga? Na san irin mutanen da zasu taru. Ƴaƴan masu kuɗi ne ke can... kuma ni yanzu dai bana da matsayi...”

A’isha ta katse ta da cewa

“Kinga Amal, ki manta da komai. Yanzu kowa yana kallonki a social media, kin dai sani, kinyi fice. Kin zama celebrity ba tare da kin nemi hakan ba. Kuma mutane da yawa ciki har da ni muna alfahari da ke. Wannan bikin kuwa, bana so kije a hanaki. Ni da kaina zan karɓe ki a ƙofa.”

Amal ta riƙe katin kamar kuɗi, tana kallon shi da ƙwarin gwiwa.....

Inna ta yi gyaran murya tare da faɗin

“Amal, Allah ne ke kawo mutum da wadata ta hanyoyin da ba ya zato. Ƙila wannan katin ba kawai na biki bane... wataƙila ƙofar sabon fata ne.”

Bayan tafiyar A’isha, Amal ta zauna da katin a hannunta tana kallonsa kamar tana karanta sirrin duniya a jikin sa. A gefe kuma Inna ta na harhada kayan miya, amma tana kallonta da ido ɗaya, ta ce

"Ke dai Amal... Allah na tare dake. Ki tafi ki je biki, amma da addu’a. Ki sani ba kowanne gayyata ce da nufin sharri ba, wasu ana kawo ta ne don alkhairi."

Amal ta kada kai tana murmushi, amma daga ciki zuciyarta tana cike da tunanin tsaro, tsoro da kuma ciwon da zuciya ta sha kwanan nan. Duk da haka, akwai wani saƙo da ya fara janyo hankalinta, zuciyar ta tana ce mata wannan ba biki kaɗai bane… wata alama ce daga sama...



Bayan kwana biyu

Amal tana zaune tana kallon kayanta cikin akwati, Ba komai mai tsada a ciki, amma akwai wani ƙaton atamfa da ta fi so. Tuni ta zaɓe shi domin tafiye-tafiye na girmamawa...

Ta wanke gashin kanta da man shafawa...

Ta yi kwalliya sosai, ba ƙaramin kyau tayi ba, ga ta fara ce tass ko bata yi kwalliya sosai ba farin ta zai ƙara mata kyau, ga gashin giran nan ya kwanta luff, komai ya tsaru a jikinta. Yanda kasan ƴar India, amma ita ɗin fulani ce ta asali..

Bayan ta kammala shirinta ta fito tana faɗin

"Inna, nayi kyau?.."

Inna ta yaba sosai tare da yi mata fatan alkhairi....

Bayan sallar la’asar, motar da A’isha ta turo ta iso a bakin titi. Amal ta fito cikin riga mai launin sky blue, riga da sket sun matse ta sosai, ga ta sha takalmi mai tudu, asalin surar ta ya fito sosai, ba abun rainawa a jikinta masha Allah, fuskar ta kamar ba mutum ba, powder da ta shafa yasa farinta yayi

10 / 82