Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
ake son haɗa wa...
A lokacin kuwa, wani ne daga cikin masu bibiyanta ya ke ɗaukar hotonta daga mota mai tinted da ke tsaye a nesa.
Sai da ya ɗauki hotuna sannan ya kunna wayarsa ya tura su cikin group ɗin sirri da ke da suna Operation Cash Maker..
Duk kissing da hugs da sock and lick duk an ɗauki hotunan like da saninta akayi, irin ba tilastata akayi ba...
A cikin group ɗin kuma mutanen da suke ciki basu fi mutum biyar ba...
Alhaji Wadata da Zayd da kuma Alhaji Gusau da kuma Maleekh da akayi joining ɗinsa a ciki...But sun cancanza numbobi yanda Maleekh bazai gani ko mutum ɗaya a ciki ba, da zaran an fito da shi daga international cell...domin sun san cewa tin da mahaifinsa ya je to bazai dawo ba sai da Maleekh...
Wanda yake kissing Amal kuwa baza'a taɓa gane ko waye ba domin yana sanye da bakaken kaya ne sai kuma black fenti da yayi a fuskarsa... ga kuma haske dadau dadau...
Amal tana ta ƙoƙarin kwace kanta, bayan ya gama ya hankad’a ta, ta faɗi ƙasi har sai da ta buga gwiwar ta sosai...
Kafin ta ɗago kuwa mutumin ya ruga da gudun gaske ya nufi motar, yana zuwa ya shige suka ja suka tafi...
Bayan ta gama koke-kokenta da shan kuka ta tashi da ƙyar tana ɗingishi ta shige gida..
Tana shiga ta fara buga wa mai gadi ƙofa, can ya fito da torch ɗinsa mai uban haske duk da hasken fitullun gidan.. ga ƴar sandarsa a hannu..
Yana fito wa ya ci karo da Amal, cike da mamaki yake binta da kallo sannan ya ce.
"Hajiya lafiya kuwa?..."
A fusace ta ce. "Meye aikinka a gidan nan? Shin an kawo ka saboda ka bar get a buɗe kayi ta bacci?..."
Maigadi cike da mamaki ya ce. "A buɗe kuma Hajiya? ..."
Idonsa ya kar wurin get ya ga a wangale, ya sake baki tare da faɗin.
"Ah!Ah!Ahhh, to wallahi sai da na kulle get ɗin nan har da bida, ya akayi a buɗe haka?..."
Amal tana kuka ta ce "To wa ya buɗe get ta waje kuma?..."
Maigadi ya haska ƙasi yanda aka fasa kwad'on a yayin da za'a fita amma ba'a san ta yanda aka shigo ba, abun ya bada mamaki sosai...
A zabure Maigadi ya yi waje da gudu yana faɗin
"Yau sai na kamo ɓarawon da ya shigo mana wallahi..."
Ita dai ta tsaya tana kallon waje gaba ɗaya jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba...
Haka kawai take jin tsinkar jikinta yana zuba wa, gabanta yana faɗuwa, da gudu ta zabura tayi ciki tana dingishi... Tana shiga falo ta kulle tare da sa key, sannan ta haura saman upstairs nan ma ta kulle bedroom, ta zauna a tsakiyar saman gado tana kuka....
《》《》《》《》《》《》《》《》《》
A gefe guda kuwa, a London, Abbah da Ammy suna cikin tashin hankali...
Suna ta tunanin sanar musu cewa an kama ɗansu Maleekh Abdul-Majeed a filin jirgi saboda samun kwayoyi masu haɗari a jakarsa...
Tin lokacin da suka baro wurin Maleekh da kuma halin da yake ciki gaba ɗaya sun rasa sukuninsu..
Suna zaune a wani gidansu dake nan London..
Abbah yana zaune ya riƙe kansa, ya ce da murya mai rauni:
“Na san ɗana ba zai taɓa yin hakan ba… akwai makirci a nan.”
Ammy tana zaune a gefensa tana kuka, ta ce:
“Alhaji, wannan makirci ne! Amma waye zai iya yin haka? Me ya ja wannan makircin?”
Abbah ya dube ta cike da damuwa.
“Sai na gano asalin komai. Kuma zan rantse da Allah, duk wanda ya sa hannu a cikin wannan sharrin, sai gaskiya ta fallasa shi, akwai lauyoyina da suke nam zasu tsaya masa gobe, domin daga yau insha Allahu bazai ƙara kwana cell ba.”...
_Washegari_
A ɓangaren Maleekh kuwa..
Wani sanyi na fluorescent ne yake dukan saman ɗakin ƙaramin cell ɗin, ƙaramin taga da ke da reja a kai ya nuna ƙaramin layin haske mai ƙarfi kamar sanda. Maleekh ya farka da sabon rikicin zuciya, ba bacci mai annashuwa, sai gajiyar damuwa da rashin sanin makoma. Hannayensa na rawar sanyi, ya leƙa gefensa ya ga babu komai a tattare da shi. Ba wayoyinsa, babu passport, babu komai... Jakarsa na ƙarƙashin kulawar hukumomi...
Ya dafa kansa da hannu, yana ƙoƙarin tunawa...
Barinsa gidansu, zuwa gidansu Amal, ganin Amal da Zayd a gado ɗaya...
Zuwansa filin jirgi, da sauƙarsa anan ƙasar london, jin muryar wani jami'in da ya ce “we have an issue here.” Sai kuma lokacin da aka ɗaure masa hannu, an ɗauke masa komai. Cikin zuciyarsa akwai tambaya ɗaya mai ƙwazo:
“Ta yaya abubuwa suka kai ga haka? Wanene zai yi mun haka? Amal? Ko Zayd?..”
Sai murmushi marar daɗi ya bayyana a leɓensa. Tunanin Amal ya dawo masa kamar an ƙwanƙwasa masa ƙirji...
A lokacin aka buɗe ƙofar cell ɗin, wani jami’in interrogations ne ya shigo da fuska mai tsanani, yana riƙe da wani babban fayil. Ya zauna a gaban Maleekh tare da ajiye takardun a teburin gefensa.. ya kallesa kamar wanda yake auna abu.. kafin daga bisani ya ce:
“Mr. Maleekh,” sannan ya fara da harshen Ingilishi mai sautin hukunci, “you are being charged with possession and intent to distribute controlled substances under UK law. We discovered illegal substances in your luggage upon arrival. Do you understand the charges?”
Maleekh ya tashi a hankali, idonsa sun yi ja, zuciyarsa na duka kamar za ta fashe.
A hankali ya furta.
“No... no, I don’t understand. This is not mine. I swear wallahi ba na da hannu a ciki. Someone planted it. Ask my family. Ask my lawyers!”
Jami'in yana girgiza kai ya ce
“We will try to engage a local counsel, Mr. Maleekh. The Embassy can assist with consular visits, but legal representation is a matter you must fund or your family must arrange. The process here is strict possession with intent can lead to very severe penalties if convicted.”
(Zamu yi ƙoƙarin neman lauya daga cikin mutanen garin nan, Mr Maleekh.
Ofishin jakadanci zai iya taimakawa wajen ziyarar diflomasiyya, amma batun lauya wanda zai kare ka dole ne kai ko iyalinka ku biya kuɗin sa ko ku shirya hakan da kanku.
Tsarin shari’a a nan yana da tsauri, kama mutum da kayan da ake zargi yana da niyyar amfani da su na iya haifar da hukunci mai tsanani idan aka same shi da laifi...)
Cikin ƙaryewar murya Maleekh ya furta:
“Ina Abbah?... ina Ammy... Ina fatan sun yi wani abu. Don Allah ka taimaka.”
Lauyan ya dinga rubutu. Cikin akwai rashin tabbaci. Wannan hukuma ce mai tsauri, ba kamar wajen zaman gida can Nigeria ba inda magana za ta warware cikin husuma. A nan, takarda, hujjoji, signatures, da scanning ne suke magana.
Washegari da safe an shigar da Maleekh kotu..
Ga lauyoyin da Abbah ya kawo domin kare Maleekh, Abbah da Ammy su ma duk suna zaune cike da tausayawa yaronsu...
Maleekh yana tsaye a gaban kotu, a can ne ya ga idanuwan mutane daban-daban: wasu suna kallonsa da tausayawa, wasu suna ganin shi kamar wanda ya yi kuskure mai muni. an umurce shi ya zauna a gefen matsayi. Alkali ya duba takardu, ganin babu wasu hujjoji ne yasa shi faɗin:
“The court hereby remands Mr. Maleekh in custody pending further investigation and trial. He is to remain in custody.”
(Kotun nan ta bayar da umarni cewa a tsare Mr Maleekh a gidan yari har sai an kammala bincike da shari’a.
Za a ci gaba da tsare shi a halin yanzu...)
Wannan hukunci ya sauƙa a cikin zuciyarsa kamar dutse. Duk mafarkinsu da tsarinsu na rayuwa a cikin kunnuwa abbah da yake zuba fata ga shi yanzu ya koma ruwa...
Bayan zaman kotu, an mayar da shi cell, inda ya zauna.
A wannan dare Maleekh yana zaune sai tunani yake. Tare da maganar zuci.
“Idan suna so in faɗi, to kuwa za su faɗi tare da ni. Zan yi yaƙi da wannan, zan nemi wakilcin lauya. I will not die as someone’s pawn.”
《》《》《》《》《》《》《》《》
A can Abuja
A yau Amal tayi dare a wurin aikinta ga ana ruwan sama.
Ta fita zatayi gida. Sai taga wasu black cars guda biyu na binta A baya..
Haka ta ƙara gudun mota suma suka ƙara gudu.
Tana gudu da mota su ma suna binta da gudu..
Har tayi kusan accident sauran kaɗan motarta ta faɗa cikin wani rami.
Sai ga wani mota ya sha gaban motarta sai motarta ya daki motar da yasha gabanta...
Da karfi ta buga kanta da sitiyarin motar...
A gigice ta buɗe ta fito, a lokacin motar da yasha gabanta Zayd ya fito a ciki yana ƙiran sunanta pretty...
Amal tayi gudu ta nufi wurinsa tana faɗin "Zayd dan Allah ka taimaka mun wasu ne suke bina da gudu.."
Bata san Zayd fuska biyu yake nuna mata ba, da sa hannunsa a cikin waɗanda ake bibiyanta, amma a gaban idonta sai ya nuna tausayawa, ya riƙe ta tare da rarrashinta yana faɗin
"Kar ki damu ina tare da ke, ba abunda zai same ki..ina sonki sosai har yanzu..."
Sauran motocin kuwa juyawa sukayi suka tafi...
Zayd ya rakata har gida kafin ya tafi yana murmushin mugunta. A ransa yake faɗin
"Haka zaki cigaba da zaman tsoro da firgita yarinya, wanda zai kare ki bayanan ya tafi...kuma ba dawowa..."
Bayan tafiyarsa ta shiga gida tana tunanin mafarkin da tayi a office ɗinta akan Zayd.. Sai ta ƙara tsorata da shi, amma wani zuciyan ya sanar mata cewa
"Ai mafarki ba gaskiya bane..."
Rana ya ta yau ne za'ayi zama na ƙarshe a kotu.. an kawo shi gaban kotu a tsare, hannayensa a jikin sarkar da ke ɗaure. Idanuwansa sun yi ja. A katu mutane sun hallara: lauya, ‘yan jarida, ma’aikatan jakadanci, 'yan uwa, da sauran masu sha’ani. Kowa ya mayar da hankali ga taron zama na uku, za a gabatar da sababbin shaidu...
Alkali ya yi shiru, ya duba takardun da ke gabansa, ya ce cikin murya mai nauyi:
“An kawo shaidar da zata buƙaci sauraro. Prosecution, ku gabatar.”
Wani jami’in ofishin tsaron filin jirgi daga Najeriya ya hau gaban kotu. A nutsuwa ya na ɗauke da wani fayil na hotuna da video. An kunna allon domin a nuna wasu frames na CCTV.
A cikin video ɗin da aka kunna, an ga hoton tashar jirgin Najeriya, hoton check-in counter. Jakar guda biyu sun bayyana, ɗaya tana da tambarin kamfanin jirgin, ɗayan kuma jakar Maleekh wanda ya kasance iri ɗaya ne. Sai kuma an ga mutanen biyu daga cikin su wani ya ɗauko jakar, ya maida ta a kan trolley, tare da musayar sa da wani mutum da ya yi kama da ma’aikacin tashar. A frame ɗaya kuma an nuna wani mutumi ya ɗago jakar da sauri, ya tura ta cikin wani trolley daban.
Lauyan Maleekh ya tashi tsaye, fuskarsa ta cika da bege. Ya miƙa hannu ya ce:
“My Lord, wannan hoton ne zai nuna muhimmin abu: an maye jakar ƙasa a filin jirgi kafin tafiyar zuwa London. Wannan bayanin yana tabbatar da cewa jakar da aka tsare a Heathrow ba ta da alaƙa da abun da Mr. Maleekh ya shigo da shi.”
Prosecution ya yi ƙoƙarin tada tambayoyi, amma mai gabatar da bincike daga Nigeria ya ci gaba da bayanin:
“Mun gano ta hanyar passport da address an yi scanning a tasha. Jakar da aka samu a London ta fito ce sakamakon bayanan da muka samu a check-in. An duba signatures, an kwatanta lambar tag da passport kuma mun gano cewa jakar an sauya ta a Abuja, kafin jirgin ya tashi.”
An kawo shaidun da suka nuna ticket number, boarding pass da hoton wanda ya aika da jakar, an gano sunan wani mai aiki a kamfanin tafiye-tafiye da ya shiga da wani ɓangare na aikin amintacce. An kuma gabatar da labarin forensic, analysis ya nuna cewa abubuwan da aka samu cikin jakar sun bambanta da abubuwan da ke cikin irinsa a Nigeria, hakan ya nuna maye gurbi ne...
An yi tir da shaidu na prosecution waɗanda suka riƙe cewa an samu abubuwa masu haɗari a cikin jakar Maleekh. Amma bayan ganin hoton musayar jakar a Nigeria, da bayanan check-in, da kuma sakamakon forensic da ya nuna ana samun bambanci a cikin jaka ɗaya da ɗayan, alkali ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya yi magana.
A wannan lokaci, lauyan Maleekh ya tashi ya gabatar da jawabi:
“My Lord, abun da Allah ya nuna a bidiyon nan ya bayyana gaskiyar cewa an maye jakar. Abun da aka samu a London ba shi ne abin da Mr. Maleekh ya ɗauka daga Nigeria ba. A cikin wannan hali, akwai shakku mai zurfi. Babu cikakken hujja da za ta tabbatar da laifin wanda aka zarga. Mun roƙa a saki Mr. Maleekh domin babu hujjar da ta gamsar.”
Prosecution ya yi ƙoƙarin ɗaga murya, ya nunawa kotu wasu bayanai amma dukan bayanan sun rushe ta hanyar hoton musayar jaka. Alkali ya ɗago idonsa, ya kalli lauyan da ke tsaye, sannan ya yi jawabi cikin murya mai tsanani:
“Bisa ga abin da muka gani a gaban kotu, an samu cikakkiyar shaidar musayar jaka a tashar jirgin Nigeria. Hakan ya kawo shakku mai zurfi a kan sahihancin hujjojin da ake amfani da su a wannan shari’a. A saboda haka, kotu tana yanke hukunci cewa babu isasshen hujja da za ta tabbatar da laifin Mr. Maleekh Abdul-Majeed.”
A nan ne ɗakin shari’a ya yi wani irin murna da farin ciki. Wadansu suka yi shiru. Maleekh ya ji kamar wani nauyi ya faɗi daga kansa, hawaye na zubo daga idonsa. Abbah ya miƙe tsaye cikin zaune, ya kalli ɗansa, idanunsa cike da hawayen murna. Ammy kuwa ta faɗi ƙasa cikin kuka ta rungumi Abbah.
Jami’in ofishin jakadanci ya tashi ya tafi kusa da Maleekh ya ce cikin rarrashi:
“Mr. Maleekh, your release is granted. We will assist with your travel documentation and liaise with authorities in Nigeria to investigate further the persons responsible.”
Maleekh ya juya ya kalli alkali, ya yi godiya da karyayyen muryarsa:
“Allah ya saka da alkhairi. Na gode. Na gode sosai.”
Lauyoyi kusan huɗu ne waɗanda sukayi fice da shige wurin kwato Maleekh domin duk mutanen Abbah, wasu daga Nigeria wasu kuma daga nan ƙasar...
A waje kuma ‘yan jarida da ke jiran fitar da sakamako sun yi ta dropawa da tambayoyi, Ammy da Abbah sun ɗauki lokaci suna rungumar ɗan su.. hawayensu na haɗuwa da godiya da jin daɗi. Amal dake can Niger ta ji labarin a wayarta ta hanyar wani abokin aiki ya ƙira ta:
“Wallahi an wanke shi.” Ta ji kamar zuciyarta ta yi tsalle da daɗi sai kuma fargaba ta dawo: “Amma me zai faru gaba?” Ta rungumi kanta, tana addu’a a hankali...
Ammy ta yi ta godiya, tana ta furta:
“Allah mun gode maka! Waɗanda suka yi wannan sharrin ba zasu yi nasara ba.”
Acan ɓangaren Alhaji Wadata da Alhaji Gusau da shi kanshi Zayd da mahaifiyarsa sun yi baƙin cikin fitowar Maleekh...
Bisa tsaron jami'ai aka shigar da Maleekh mota tare da iyayensa suka nufi gida dake nan London..
Sai dai kuma, a ƙarshen wannan rana, akwai wani abu da ya rage: tambayar wanene ya maye jakar? Kuma wa zai amsa saboda irin wannan sharrin? Wannan tambaya ce da zata jefa labarin cikin sabon babi, bincike mai zurfi, haɗin gwiwar lauyoyi, da faɗakarwa ga wanda ya yi shirin.
A babban falo duk suka hallaru..
Komai ya lafa sai nutsuwa, amma zuciyoyin su na ɗauke da abubuwan da suka sha wahala akan sa..
Maleekh ya zauna ya jingina da kujera, yana riƙe da wayarsa. Idanunsa sun yi ja saboda rashin bacci da damuwa.
A hankali ya kunna wayar, sai ga jerin saƙonni daga Amal guda sama da ɗari!
“Maleekh please ka yarda da ni…”
“Wallahi ban san da komai ba…”
“Don Allah ka amsa wayata…”
“Ina cikin fargaba…”
"Naji labarin kana cell sakamakon abin da aka samu a jakar ka, shin gaskiya ne?..."
"Allah ya fitar mun da kai Maleekh..."
Saƙonni suna ta shigo wa a jere, kamar ruwa da aka buɗe masa hanya.
Ya runtse idonsa da ƙarfi. Zuciyarsa na bugawa. Duk da ciwon da yake ji a cikin ransa, har yanzu yana sonta amma hoton da ya gani ita da Zayd a ɗaki yana bin kwakwalwarsa kamar wuta.
Wayar ta sake yin ƙara, “Amal Calling…”
Sai dai ya tsaya kawai yana kallo, bai ɗaga ba.
Ya rufe idonsa, yana sauƙe numfashi mai nauyi.
A gefe kuwa, Abbah da Ammy suna zaune suna kallonsa cikin tausayi da godiyar Allah.
Haka abokansa suka rinƙa ƙira suna masa fatan alkhairi, duk ƙiran da ya shigo sai ya ɗauka amma banda ta Amal, tana kiransa akai akai amma sam ya ƙi ɗaukan kiranta...
Abbah ya murmusa kaɗan, yana cewa cikin murya mai nutsuwa,
“Alhamdulillah, Allah ya tabbatar mana da gaskiya. Na gode da irin juriyar da kayi, ɗana. Wannan komai ya zama tarihi yanzu.”
Ammy ta ɗan share hawaye, ta ce,
“Ni har yanzu jikina yana rawa idan na tuna da wancan ranar… amma Alhamdulillah ka fito lafiya.”
Maleekh ya ɗan sunkuyar da kai, yana cewa cikin murya mai sanyi,
“Ni ma haka nake ji, Ammy. Amma har yanzu kamar mafarki nake kallon abun, ban taɓa zato cewa zan shiga irin wannan masifa ba.”
Sai Abbah ya gyara zama, yana ɗan murmushi da girmamawa:
“Maleekh, yanzu dai lokaci ne na farin ciki. Da zarar mun koma gida, zan so mu fara shirye-shiryen auranka da Amal.”
Ammy ta zabura da sauri, tana kallon mijinta da fuskarta cike da mamaki:
“Haba Alhaji! Daga fitowarsa a cell sai aure? Ai yaron nan har yanzu yana cikin tashin hankali, bai da cikakkiyar nutsuwa.”
Abbah ya jinjina kai, yana dariya kadan.
“Maryam, aure ma wani hutu ne. Kuma ya dace mu gyara kuskuren da ya faru. Maleekh da Amal sun jima da haɗuwa da soyayya, babu dalilin da zai sa mu jinkirta.”
Maleekh ya ɗan motsa, yana kallon iyayen nasa. Zuciyarsa na bugawa da sauri.
Sai dai ya ƙudura a ransa ya gama da soyayya.
Ya ce da murya mai natsuwa da kuma cike da rauni,
“Abbah... ta mun laifi sosai. Don haka a barni in huce tukun kafin a kai batun aure.”
Abbah ya kalle shi da ƙarfi, yana murza agogon hannunsa.
“Wannan ba mai yuyuwa bane, domin bazaka lalata wa yarinya Aure ita da ɗan uwanta ba kuma kai ka ƙi aurenta, wannan kuskure ne da kuma yaudara,