Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   70 / 82

207K to 210K   out of 244.2K words

samu nutsuwa…

Sai suka ji ƙara daga cikin dajin da suka baro, wanda iyakarsu sai an ratsa ta cikin manyan duwatsu..

“Babu inda za ku je… zamu sake haɗuwa.”

Daga dajin da suka tsere, suka koma wani daji daban, ba duhu sai nau’in tsoro daban...
A nan, akwai ƙaramin gari a cikin daji, ba a gani daga nesa saboda bishiyoyi sun rufe shi.
Mutanen garin kuwa… mafarauta ne masu ƙarfi, masu jini a jikinsu, masu kamannin daji.

Suna amfani da wuƙaƙe, kibiyoyi, gatura, da makaman gargajiya.
Jikinsu ba kaya sai ganyayyaki da ƙugiya ɗin da sahon farautarsu ke rataye a wuyansu.

Da suka shigo cikin dajin, kafin su fahimci komai sai suka ji “Ffff! Ffff! Ffff!”
Wuƙaƙe suna miko musu hari daga kowane ƙarshen bishiya..

Maleekh yana riƙe da hannunta haka suke sunsunkuya.
Kafin su yi magana, mutane goma sha biyu suka fito suka kewaye su.
Dukkansu babu kaya, sai ganyayyaki da ke rufe da ƙugunansu..

Ganin mutane kewaye dasu yasa suka durƙusa cikin tsoro, domin fuskokin mutanen sun sha baƙin fenti..

Suka karɓe su da wuƙaƙe a hannu, sannan suka ɗauke machine ɗin..

Shugaban su, Babban Mafarauci, ya yi gaba..
Idonsa jajir, kan sa yana rufe da fatar bauna..

Ya kalle su sama da ƙasa ya ce da muryar da ta cika daji:

“Me ke tafe da ku? Wa ya ce ku shigo dajinmu?”

Maleekh ya yi saurin ɗago wa yana kallonsa, saboda jin tsananin muryarsa.
Amal ta riƙe hannunsa tana kuka..

Ya ce cikin tsananin tsoro:

“Hanya ce ta kawo mu nan… mun tsere… wallahi ba mu zo cutar da kowa ba.”

Mafarautan ne suka fara magana ta tsawa:

“Ƙarya ne! Duk wanda ya shigo dajinmu sai an yanka shi! An ci naman sa! Wannan dokar kakanninmu ce!”

Amal ta fashe da kuka, tana rawar jiki.
Ta durƙusa gaba ɗaya, ta ɗago kai, tana roƙonsu.

“Dan Allah… kada ku kashe mu… ba mu da laifi…
Ni da shi masoya ne… aure za a ɗaura min da wani wanda bana so…
Shine muka gudu… don mu tsira…”

Dajin ya yi shiru.
Mafarautan suka kalli juna.
Wasu suka yi shewa:

“Ahhh! Masoya!!”
“Aure! Aure!!”
“A yayanka su! A ci naman su tun kafin su yi aure!”...

Matar shugaban mafarautan ce ta fito.
Babbar mace ce, mai taushi fiye da mijinta.
Ta duba Amal sosai ta hango tsoron gaske a idanunta.

Ta ce da muryar mace mai hangen zuciya.

“Kada a yanka su.
Masoya da suka gudu don juna ba a kashe su.
Wannan al'ada ce ta tsohuwar mahaifiyata…
A bar su… a kula da su.”

Mafarautan suka yi shewar daji..

Shugaban mafarautan ya ɗaga hannu, ya ce:

“To! Idan wannan ne hukuncin mata…”
Ya juya ya kalle su, idonsa na haske.
“Za mu ɗaura muku aure a nan… yanzun nan… domin wannan shi ne tsawon zaman dajinmu.”..

Duk mutanen suka fara tsalle!
Suna shewa!
Suna rawa!
Suka fara busa ƙaho da ƙarfi domin shugaba ya yi magana..

A nan cikin dajin, a tsakanin ganyayyaki da wutar da aka kunna da rassan itatuwa, aka kafa da'ira.
Mutanen gari sun yi tsaf, suna tsatstsaye.

An sa Amal a tsakiyar da'irar.
Maleekh kuma a gefe.
An ɗaure su da igiyar reshe.

Shugaban ya yi rantsuwa cikin harshen daji, ya ɗaga wuƙa sama, ya ce:

“An ɗaura aurenku da dokar daji, da dokar ruwa, da dokar mafarauta.
Daga yau… ku biyu miji da mata ne.”

Mafarautan duk suka yi ihu:

“Auuuuuuuuuuuuuuuuuuu!!!!”

Amal tana kuka.
Ba kukan farin ciki ba sai na tsantsar razana...

Maleekh ya riƙe hannunta, ya ji hannayenta sunyi sanyi kamar kankara..

Ya ce cikin ƙasa da murya:

“Ki da kiji tsoro… ki sani… ina nan tare da ke.”

Mafarautan suka fara rawa.
Suna ɗaga wuta sama.
Ganyayyaki suna kaɗawa...

Auren da ba su taɓa mafarki ba yau an ɗaura musu...

A cikin daji.
A tsakanin mutane marasa kaya.
A ƙarƙashin hukuncin daji.

Akwai wata tsattsauran al'ada da dole su bi.

Shine zasu zauna anan.
An kafa wa Maleekh doka cewa dole ta samu ciki a cikin kwana uku.
Idan ba haka ba zasu jefa shi cikin babban tekun su.
Ita kuma Amal su aura mata maza biyu daga cikin mazan su.
Kuma a dokar su, maza biyu ne suke auran mace ɗaya domin mazansu sun ninka mata yawa...

Amal ta tsorata sosai.
An basu wani ɗaki wanda aka gina da itace.. wanda aka rufe da ganyayyaki..
Yana ta tunanin to kenam taya zai mata ciki a cikin kwana uku al'halin ba shine mai bada ciki ba..

Haka aka ajiye wannan dokar.
Idan kwana uku yayi akwai abinda suke gwadawa ya nuna musu mace ta samu ciki...


Da daddare, aka tura su cikin ƙaramin ɗakin da aka yi da itatuwa. Wurin yana ɗauke da ƙamshin ƙasa da ɗaci na hayaƙin wuta...

Amal ta zauna a kusurwar ɗakin tana rawar sanyi da tsoro, idanuwanta sun kumbura saboda kuka.

“Me zamu yi?” ta ce cikin murya mai rauni, tana kallon Maleekh da ya kasa zaune saboda damuwa.

Shima ya nufe ta ya durƙusa a gabanta.
“Ki saurare ni… ba zan bari su cutar dake ba. Wallahi ba zan bari ki shiga wannan muguwar al’ada ba.”

Sai kawai ta fashe da wani sabon kuka mai ƙarfi, tana tunanin yadda aka kakaba musu aure na dole, kuma yanzu ga wannan tsattsauran hukunci da ba zata iya tsallakewa ba.

A waje kuwa, ana ta busa wutar al’ada. Mazan mafarautan suna ta shirya manyan takubansu, kamar suna jiran ranar uku ta cika su aikata hukuncinsu. Matan kuma suna ta yi wa Amal siyayya ba don tausayi ba, sai don ta zama amarya ga mazansu idan saurayin ya gaza...

Maleekh yana ta tafiya a cikin ɗakin kamar zai haukace.

“Ya za mu yi ciki cikin kwanaki uku? Ni abun ya ɗaure mun kai… ba ni da damar…” ya tsaya, saboda ba zai iya faɗi gaba ɗaya ba...

Amal ta share hawaye ta ce,
“Suna cewa idan ban samu ciki ba… za su aurar da ni ga wani har biyu.. Kai kuma za su jefa ka cikin tekunansu. Kasan me hakan yake nufi?”

Shiru ya cika ɗakin.
A waje kuwa an kunna wuta suna rawar al’adarsu ta dare. Sautin ganguna ya ɗauki dajin da ihu na murna..

Duk suna ɗaki sun rasa abun yi, ya riƙe ta tare da zaunar da ita.

“Ni dai abu ɗaya nake so ki sani…” ya ce cikin muryar da ke rawa.
“Ko me ya faru, sai dai su kashe ni, amma ba zan bari su aurar ki ga wani ba.”

Ta kalle shi wannan maganar ta ƙara mata tsoro, amma kuma tanajin wani nau’in kwanciyar hankali a zuciya.

A wannan lokacin, matar shugaban mafarautan ta shigo ta ɗaga bargon ganyen.
“Ku shirya. Gobe da safe zamu fara bibiyar al’amuranku.”

Suka fita.

Amal ta kwanta a jikin Maleekh ta rungume shi saboda tsoro...

Da daren sun kwanta amma barci ya ƙi zuwa.
Gaskiya kawai ɗaya ce:

A cikin kwanaki uku ko dai su tsira…
ko kuma su rasa rayuwarsu.

Amal tana zaune tana murza yatsunta saboda tsoro da rashin tabbas. Maleekh kuwa ya tsaya a tsaye yana kallon ta, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi saboda nauyin abin da ake expects daga gare su.

“A yau ne daren farko…” ta faɗa cikin murya mai sanyi, tana kau da kai.
“Idan muka yi addu’a, ko Allah zai ba mu sa’a? Mu samu ciki kafin kwanaki uku?”

Ya zauna a gabanta a hankali,

“Ni ma haka nake fatan,” ya ce.
“Ba wai saboda dokarsu ba, don kawai saboda mu tsira. Kuma… saboda ina matuƙar jin ki a raina.”

Ta yi murmushi mai raɗaɗin tsoro.
“Ni ma ina sonka. Idan Allah ya rubuta a yau ne… toh shi kenan.”

Ya kamo hannunta, hannun yana rawa, nashi ma yana rawa. Babu wani wasa a al'amarin, sai zallar tsoro da soyayya, da fatan nasara a wurin Allah..

Suka durƙusa su biyun, suka ɗaga hannaye sama,

“Ya Allah, ka ba mu mafita.
Ka sanya mu samu abin da zai ceci rayuwarmu.
Ka kare mu daga wannan sharrin al’ada.
Ka sanya mu samu albarka a wannan daren.”

Hawaye ya zubo daga idon Amal saboda tashin hankali da addu’a a lokaci ɗaya.

Maleekh ya matsa kusa da ita.
“Ko da muna cikin tsoro… ni zan yi iya ƙoƙarina. Allah ya gani.”

Ta ɗaga kai, idonta cike da hawaye ta ce,
“Ni ma zan yi iya nawa. Ka tuna… muna da aure yanzu shine babban farin ciki, ba wai zina zamu aikata ba.”

Suka lumshe ido sannan suka rungumi juna, cikin nutsuwa da jin kunya da kulawa...
Babu hayaniya, babu rawar kai kawai nutsuwa, addu’a, da fatan cewa Allah zai basu ikon da zai ceci rayuwarsu..

Haka numfashinsu yake haɗuwa suna shakar ƙamshin jikinsu..
Cikin lokaci ƙanƙani suka haɗe bakinsu.... A hankali suke sumbatar juna, cike da ƙaunar juna da sha'awa lokaci guda..
Sun daɗe suna foreplay kafin a hau aiki 😅.
Haka take razana saboda tsananin zafi da raɗaɗi, a hankali ya furta mata a kunne.

"Sorry! Kar ki ji tsoro zafin na lokaci kaɗan ne......Zai shiga yanzu.....Zai shiga....Ki nutsu please..."

Haka take daure wa saboda kar mutanen waje su ji...


A waje ana ta busa ƙaho, alamar cewa mafarautan suna jiran sakamakon kwanaki uku....

☆☆☆☆☆

Bayan sun gama, suka rungume juna cikin shiru.
Ba wanda ya ce wani abu.
Kawai jin numfashin juna da fatan cewa Allah ya amsa addu’arsu.

Maleekh ya ce a hankali:

“Ina fatan wannan dare ya yi mana albarka.”

Ta jingina kanta a kirjinsa.

“Ni ma haka… gobe safe saura kwana biyu.”

Haka suka cigaba da zama, suna zaune rungume da juna cikin tsantsar gajiya da fargaba, sun sanya kayan jikinsu. Wurin ɗakin ya yi duhu, hasken fitilar wuta ta waje kawai ke shiga ta gefen ganyen da aka rufe..

Sai kawai suka ji ƙarar takun ƙafa, kafin ma su yi wani motsi, ɗan mafarauci ya bankaɗo kofar ɗakin da ƙarfi.

Ya shigo ba sallama, ba neman izini. Da wuƙa a hannunsa...

“Oh! Har yanzu kuna nan zaune? Baku yi komai ba kenan!” ya faɗi cikin tsawa yana huci...

Maleekh yana kallonsa cike da mamakin jahilci irin na wannan al'ada, ya ce.

“Yanzu muka gama...”

Mafaraucin ya zaro ido, yana matsowa kusa..

“Munafukai! Sai kun cire kayanku! Na rantse da dokar mu, sai na ga da idona.”

Maleekh ya girgiza kai ya ce,

“Yanzu muka gama fa. Kazo ka taɓa tabarmar nan zaka ji a jiƙe yake…”

Mafaraucin ya durƙusa ya taɓa tsakiyar tabarmar.
Sai kuma ya ɗaga kai ya yi ihu yana cewa.

“Ƙarya ne, ruwa kuka zuba! Kuna wasa dani ne? Sai kun cire kayan ku!”

Maleekh ya ce,

“Ta wahala sosai… ta gaji… ka bari—”

Kafin ya rufe baki, mafaraucin ya ɗago wuƙa sama, idonsa ya kaɗa da ja.

“Ƙarya kuke! Zaku yi yanzu! Ko sai nayi masa yankan damo..?”

Amal ta fashe da kuka, ta tashi a rikice tana marairaicewa:

“Dan Allah ka saurare mu! Zamu yi! Zamu yi! Amma ka fita. Bazai yu mu cire kayan mu a gabanka ba…”

Ta durƙusa tana roƙonsa, muryarta na rawa.
Amma mutumin ya girgiza kai:

“A'a! Sai an fara kafin na fita. Sai na tabbatar da gaskiya, domin turo ni akayi domin na duba.”

Haka ya tilasta su yin abin da yake so, sun tilasta kansu cire rigunansu bisa kunya, zuciya na rawa.

Sai da suka fara kusantar juna ba don sha’awa ba, sai don su tsiratar da kansu.
Sannan mafaraucin ya tintsire da dariya, ya juya ya fita.

Amma kafin ya tafi ya ce:

“Ku tabbatar na ji ihunta. Ko ba haka ba, gobe akwai hukunci.”

Ƙofar ta rufe da ƙarfi, ya bar su cikin yanayi, zafi, tsoro, da bugun zuciya.

Lokacin da su ka rage su kaɗai…

Amal ta fashe da kuka, hannunta na rawa kamar wacce aka jefa cikin wuta.

“Wallahi bana jin ƙarfin jikina… amma idan muka ƙi… za su kashe ka.”

Maleekh ya matso ya rungumeta a hankali:

“Ki yi haƙuri. Ba zan taɓa cutar da ke ba. Amma dole mu tsira. Ki bari mu yi abin da ya kamata, sannan mu yi abinda Allah ya sa a bisa aure.”

Suka yi addu’a cikin hawaye, sannan suka kusanci juna a hankali, cikin kwarin gwiwar auren da suke da shi...

Maleekh ya mara mata baya cikin sassauci, yana kwantar mata da hankali.
Ya zamar da rigarsa, tana jin bugun zuciyarsa kamar nata.

Sannan… suka shiga second round..

Na bar wannan bangaren cikin mutunci 🤭🙈

Amma a wannan karon Amal ta yi ihu...
Ihun

tsoro

raɗaɗi

nutsuwa

da kuma dalilin da za su tsira...

Ihun nata ya fita har wajen dajin.
Mafarautan suka ji.
Har an fara busa ƙaho, alamar sun gamsu da cewa “aikin daren” ya tabbata.

Wani dattijo a waje ya yi ihu yana faɗin.

“Sun yi! Sun yi! A gobe mu haɗa musu kayan ciye-ciye!”
Dajin ya cika da kiɗe-kiɗe da buge-buge..

A ciki kuma…

Amal na kwance a jikinsa tana kuka, shi kuwa yana shafa kanta:

“Ki yi haƙuri… ki yi haƙuri… duk da tsananin tsoro, Allah ya ga abinda ya faru.
Allah ya sani ba da son ranmu ba.”

Ta ce cikin rawar murya:

“Gobe sauran kwana biyu… idan ba ciki ba… zasu kashe ka…”

Shiru ya ratsa ɗakin.

Su biyun kawai, cikin duhu, cike da addu’a da fatan gobe zata kawo sabon numfashi ko kuma sabon bala’i…

💥

Asubar fari ya fara haskowa ta cikin ganyen da ke rufe rufin ɗakin itacen da aka basu.

Amal ta farka cikin firgici, tana rungume da jikinta kamar mai jin sanyi. Idonta ya kumbura saboda kuka..

Babu kaya a jikinta, haka ta lalumi kayan ta saka..Tana rawar sanyi..

Maleekh yana kwance sai baccin yake ta sha. Baccin gajiya..

A hankali ta tatta6a shi. Ya farga yana addu'a tare da lumshe ido..

Wani ƙaramin yaro ne ya leƙo cikin ɗakin, yana cewa:

“Shugaba ya ce ku fito. Akwai abubuwan da za a gwada yau.”

Dukkansu suka kalli juna da tsoro.
“Wane irin gwaji kuma?” Maleekh ya tambaya.

“Ba ni da ikon faɗi,” in ji yaron, ya gudu.

A Wajen Gari

Sun fito. Mafarauta suna tsaye a layi, tsirara daga sama zuwa ƙasa, sai ganyayyaki a jikin su. Da makamansu wuƙa, baka, kibau, sanda mai karan ƙarfe..

Mutanen gari sun yi shiru.

Shugabansu, dattijo mai dogon gemu da tabo a fuskarsa, ya ce:

“Yau kwana na biyu kenan. Dole mu tabbatar idan akwai ‘alamar ciki’ ko babu.”

Maleekh ya ji jikinsa ya sake, tsoro ya daki zuciyarsa.

“Wace alama kuke nema?” ya tambaya a hankali.

Shugaban ya ɗauko wani ƙaramin kwandon itace da ganye kore da farar laka a ciki.

“Zamu yi gwajin ganyen Takur-shi.
Idan matar nan ta zauna a kai, ganyen ya yi fari to ciki na nan.
Idan ya koma baƙi, to babu komai.
Idan babu komai kafin kwana uku, sai dai hukuncinmu.”

Amal ta jijjiga kai tana kuka:
“Don Allah, na gaji! Wannan abu ya yi min yawa…”

Sun ba ta ganyen.
Sai suka tafi su biyun zuwa wani yanki na dajin da babu mutane.
Sai wasu mata masu rakiya..

Suka isa wani wuri mai sanyi da bishiyoyi.
Suka zauna a ƙasa...
Amal na kuka kamar ranta zai fita.

Maleekh ya riƙe hannunta, yana jin zafin duniya a kansa.
“Ki yi haƙuri. Ki zauna a kai. Allah zai yi mana mafita…”

Ta zauna a hankali kan ganyen da ke cikin kwandon.
Suka jira. Shiru. Sai kukan tsuntsaye.

Mintuna suka wuce.

Maleekh ya ɗaga ta sannan ya duba ganyen a sannu…

Ya yi fari.

Amal ta yi ajiyar zuciya.
Amma shi ya gane wani abu…

Ba fari sosai ba ne, daidai tsakanin fari da launin baƙi yake..

“Wannan ba alamar fari bane.” ya faɗa a ransa.
Amma bai faɗa mata ba saboda tsoron ya ƙara rikita ta.

Ta yi murmushi kaɗan, cikin hawaye:
“Alhamdulillah… ka gani?”

Ya yi mata murmushin ƙarya:
“Na gani.”

Amma hankalinsa ya cika da tambaya:

“Idan suka ga ba fari sosai ba fa?”

Sai suka miƙe suka koma gari..

A GABAN MAFARAUTA
Shugaban ya karɓi ganyen ya kalla da kyau.
Mafarautan suka kange su a kewayen wuri gaba ɗaya.

Dattijon ya ce cikin murya mai nauyi:

“Ganyen ya nuna… ba cikakkiyar alama ba ce.
Wato… wataƙila ta fara, ko kuma babu komai.”

Wani matashi daga cikin mafarauta ya yi ihu:

“To mu jefa shi cikin tekun! Dokarmu ba wasa bane!”

Amal ta fashe da kuka tana riƙe da Maleekh sosai:
“Dan Allah ku ba mu zuwa gobe! Don Allah! Gobe ne kwana na uku! Don Allah!”

Matar shugaban wacce ta cece su jiya ta shiga tsakani:

“Ku bar su. Ba ku ga fari ba? A ajiye hukunci zuwa gobe.
Gobe ne rana na uku..."

Mafarautan suka yi gurnani da jin haushi, amma babu wanda ya ƙi umarnin matar shugaba.

Shugaban ya yi magana a tsawa ce:

“Kwana na uku zai yanke hukunci.
Ko ciki ko teku...!”

Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa na bugawa.

Amal ta riƙe hannunsa tana kuka...

“Ba za su kashe ka ba… ba zan bari ba…”

Amsar da ta fito daga bakinsa cikin muryar da ya yi ƙoƙarin ɓoye rawar kuka ita ce:

“Idan Allah bai kawo mu’ujiza ba… gobe zan ga ƙarshena.”

Daren ya gangaro da sauri a dajin. Ga wutar da mafarautan suka kunna a tsakiyar ƙauyen...

An mayar da su cikin ɗakin su na ganye da itace.
Kamar jiya, babu kofar rufe wa...

Sai da suka shiga suka zauna sannan suka ji zuciyoyinsu biyu suna bugawa da sauri.

Amal ta jingina da bango, hannunta na riƙe da ƙirji.
Maleekh ya zauna a gabanta cikin nutsuwa.

“Gobe shine ƙarshe… idan ba a samu cikakkiyar alama ba…”
Ya kasa finishing kalmar.

Ta ɗago kai cikin hawaye:
“Dan Allah kada ka faɗi hakan. Ka tuna da addu’a.”

Sai ta matso kusa da shi, ta jingina kanta a kafaɗarsa.
Zuciyarsa ta lafa kaɗan.

Saɓanin Jiya, A Yau Dajin Ya Yi Shiru

Babu sautin komai.
Kamar an dakatar da dukkan halittu saboda wani abu da zai faru.

Sai dai daga can nesa, suna iya jin:

Takk! Takk!
Kamar ana yanka itace.

Maleekh ya ɗaga kai da sauri.
“Ina jin kamar suna shirya wani abu…”

Amal ta matso kusa da shi sosai, muryarta na rawa:
“Ka riƙe ni… ban jin daɗi.”

Ya riƙe hannunta, yana shafa bayanta a hankali...

Daga can suka ji shigowar mutum yana matsowa cikin ganyen da ke rufe su.

Amal ta sa hannu ta rufe bakinta saboda tsoro kar ya ji motsi.

Maleekh ya riƙe ta sosai yana whispering:
“Shhh… ki zauna a baya… bari in wuce gaba.”

Ganin dajin babu wani abu da zai kare su sai Allah, ya matsa kusa da ƙofar itacen da aka ɗaure.

Wani irin bakanen mutum ne ya leƙo
gashinsa a ɗaure da igiya,

kuma ganyen da ya rufe jikinsa ya fi na sauran nauyi...


Ya yi magana a hankali kamar ba ya son wani ya ji:

“Ku kwana lafiya… amma ku sani akwai wasu da ba su yarda da ku ba.”

Maleekh ya tsaya daram:
“Wa ye kai? Ka zo ka cutar da mu ne?

Mutumin ya ce:
“Ba don cuta ba. Don gargaɗi.
Wasu maza sun ce gobe ba za su jira gwaji ko alama ba suna so su ɗauki matar nan.”

Amal ta fashe da kuka.

“Sun ce idan ba ka ba ta ciki ba, to zasu yi mata ‘tubani’ wato su raba ta gida biyu su bayar ga wasu...”

Maleekh ya ji jikinsa ya yi sanyi gaba ɗaya.
“Wannan ba adalci bane!”

Mutumin ya yi shiru na daƙiƙu kuma ya ce:

“Ni ɗin ba ni da iko. Na zo ne in sanar da ku.
Ku kwana a farke… ku yi addu’a.
Gobe ba zai yi sauƙi ba.”

Ya ɓace kafin su ce wani abu.


70 / 82