Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   72 / 82

213K to 216K   out of 244.2K words

da Maleekh a wurin mafarauta. Sun sadu da juna har kwana biyu, a rana ta uku ne suka gudu. A yanzu, tana ɗauke da ciki na tsawon watanni shida.
​Wannan ciki ya zama shaidar soyayyarsu da kuma sadaukarwarsu a ƙarƙashin barazanar rayuwa.
​Amal ta tattara ƙarfin hali ta gaya wa Fulani gaskiyar labarinta daga soyayyarta da Maleekh, zuwa ga sace ta, zuwa ga auren da aka ɗaura musu a daji, har zuwa ga gudun tsira.
​Mutanen Fulani, da yake mutane ne masu tausayi da mutunta rayuwa, sun karɓe ta da hannu biyu. Sun ɗauke ta a matsayin ɗiyarsu ta gaskiya kuma suka yi alkawarin kare ta har sai ta haihu. Cikinta ya zama alamar bege a cikin wannan ruga mai nisa...

Duk da a yanzu mutanen rugar basu zauna ba, suna nema mata hanyar da zata bi don ta koma gida..

​Shi kuwa Maleekh, bayan tsawon wata ɗaya a kwance a cikin ramin da ya faɗa, wasu Sojoji sun tsince shi. Sojojin sun shigo yankin ne domin gudanar da aiki na yaƙi (military operation), kuma sun same shi cikin jini, sumamme a cikin rami mai zurfi.
​Sojojin sun ɗauke shi, sun fara bashi kulawa ta musamman (medical treatment) a sansanin su na ɗan lokaci.
​Bayan wata ɗaya da ya yi a hannun su, ya farfaɗo. Sai dai mamaki da firgici suka lulluɓe Sojojin.
​Maleekh bai san inda yake ba. Ba ya gane fuskarsa ko hannuwansa. Saboda tsananin buguwar da ya yi a kansa lokacin da ya faɗi a cikin rami ya bugu da dutse, kwakwalwarsa ta juye. Ya shiga cikin cikakken mantuwa (Amnesia).

​ Bai san sunansa ba. Ya manta da wata Amal. Sannan a yanzu ya manta da Mahaifinsa. Bai san yadda ya fito daga cikin wayewar gari ba.

​Sojoji sun riƙe shi, suna bashi kulawa sosai har tsawon watanni shida suna jiran farfaɗowar ƙwaƙwalwarsa. Amma shiru. Babu wanda ya sanshi a wurin, kuma Maleekh bai iya bayar da ko wani bayani game da kansa ba. Sun sanya masa wani suna na wucin gadi a cikin sansanin....
_NEXT NEXT NEXT_

asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 85 to 86

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹



​A cikin ruga, kwatsam, wani matashi ɗan Fulani wanda ya shiga birnin Suleja don kasuwanci ya dawo da wani labari mai zafi. Ya samo wata jarida wadda ke nuna hotunan Amal da Maleekh, kuma ana neman su.
​Labarin ya nuna cewa:
Ana neman Amal da Maleekh waɗanda suka ɓata. Akwai kyauta mai tsoka wadda za ta wadata mai ba da labari har karshen rayuwarsa. Haka kuma, an saka lambar waya don tuntuɓa.

​Nan da nan, matashin ya koma rugar da wata ƙaramar waya (torchlight phone). Ya sanar da mutanen rugarsu abin da ke wakana. Duk da cewa watanni shida sun shige, wannan wata dama ce ta zinare don bayyana Amal ga iyayenta.
​Amal ta ji labarin, sai farin ciki da tashin hankali suka shige ta lokaci guda. Ta matsu da ta je ta ga Innanta. Amma sai mutumin ya sanar mata da cewa tsakaninsu da Suleja da kuma Abuja nesa ce sosai.
​Sai dai, basu yi ƙasa a gwiwa ba. Suka ƙira lambar wayar da ke jikin jaridar. Lambar jami'in tsaro ce mai kula da binciken tun farko. Mutumin Fulani ya gaya masa duk abin da ya faru.

​Jami'in ya ƙira Abbah a waya, yana sanar masa cewa: "An samu Amal, a wani yankin ƙauye mai nisa."
​Abbah ya kasance tare da Inna a lokacin. Inna ta yi farin ciki sosai har ta miƙe, tana godiya ga Allah tana kuka.
​A wannan ranar, an tayar da jirgi mai saukar ungulu (Helicopter). Abbah da wasu jami’ai suka shiga cikin jirgin. Sun riga sun yi amfani da fasaha (tracking) don gano wurin da aka ƙira su, saboda haka basu buƙaci wani ƙarin bayani ba.
​Nan da nan, sai ga su a sararin rugar Fulani. Mutanen ruga sun yi mamaki sosai sai ganin Elekwabta sukayi yana shirin saukowa a tsakiyar daji!
​Abbah da Jami'an suka sauƙo.
​Jami'i Yana magana da ƙaramar waya "Mun iso. Muna kan bakin rugarku."

​Matashin Fulani Yana duban jirgin sama da mamaki ya je yanda suke yana faɗin, "Na ganku! Ga ni nan! Ku biyo ni!"

​Anan matashin Fulani ya sanar musu wurinda Amal take. Suka fara tafiya da sauri, sai ga su a gidan Fulani inda Amal take zaune.
​Amal tana zaune a ƙasa, da tsohon ciki, wata mata Fulani tana bata nono don ta sha.
​Abbah muryarsa cike da tausayi, ya kusan fashewa da kuka ganin Amal.

“Daughter?… My daughter?”

​Amal ta ɗago da sauri a zabure. Ta kalli mutumin da ya zama uba a gareta.
​Amal cikin kuka, muryarta a raunane ta ce
“Abbah!…”
​Ta miƙe da gudu duk da nauyin cikinta, ta nufe shi, ta rungume shi da ƙarfi. Shima Abbah ya kasa riƙe hawayensa, ya fara kuka.

Abbah ya rungume ta, yana shafa bayan ta,

“Alhamdu Lillah! Ƴata, na gode wa Allah! Na gode wa Allah da ya nuna min ke. Na yi zaton na rasa ki har abada!...”

Amal tana kuka ta ce, “Abbah, na shiga wahala! Na yi kewar ku! Na yi kewar Inna! Allah ya ceci rayuwata, Abbah!”

Jami'i yana motsa Abbah a hankali ya ce

“Ranka ya daɗe, ya kamata mu rage kukan nan. Muna buƙatar mu tafi nan da nan. Tana buƙatar kulawa ta musamman.”

Abbah ya saki Amal, yana riƙe da hannunta, ya kalli cikin nata ya ce “Wannan… me ya faru? Wannan… Maleekh ne?”

Amal ta sunkuyar da kai cike da kunya ta ce,
“Eh, Abbah. Auren da suka ɗaura mana ne a dajin… Amma Abbah, Maleekh ya ceci rayuwata. Bai bar ni ba. Muna son juna.”

Abbah ya numfasa da wani dogon numfashi, ya shafa cikinta ya ce, “Allah ya muku albarka, rayuwarku tafi komai muhimmanci … Ba komai, ƴata. Wannan tsari ne na Allah. Yanzu dai mu tafi.”

Bayan haɗuwar, Abbah bai manta da kyautatawa da mutuntawa ba. Ya yi wa dukkan mutanen ruga babban alkhairi. An raba musu makudan kuɗaɗe, amma gidan da Amal ta zauna da kuma matashin da ya sanar musu sun fi samun alheri da arziki sosai. An cika musu alkawarin kyauta.
​Ba a jira wani abu ba. Suka ɗauki Amal.
​Amal tana kuka tana yi wa matan Fulani da suka riƙe ta bankwana. Sun shaku sosai, kuma sun yi mata alkawarin addu'a da kuma fatan samun lafiya.

​A lokacin da suka shiga cikin Helicopter, Abbah ya tambayi Amal: “Ina Maleekh? Ba ku tare ne?”

​Amal cikin hawaye ta ce,
“Na barshi ne a bakin ruwa… An harbe shi, Abbah, ya yi ta jini. Ya bani tayar na gudu… Ban san yanzu yana ina ba.”

​Ganin cewa babu wanda ya san inda Maleekh yake kuma yana cikin matsanancin haɗari, suka yanke shawarar wucewa gida tare da Amal don a ba ta kulawa ta musamman..

Bayan Jirgin Helikwafta ya sauƙa a Abuja, gidauniyarsu ta cika da mutane. Kowa yana cikin mamaki da tsananin alhini.

​Abu na farko da kowa ya lura da shi shine cikin Amal. Sai dai, abin da ya fi muhimmanci a idon kowa shine tambaya ɗaya: “Ina Maleekh? Yana ina shi?”

​Ammy ta rungumi Amal cike da kewa da tausayi. Amma hankalinta ya tashi, ganin cewa ba a samu Maleekh ba, kuma Amal ta tabbatar da cewa an harbe shi a gaban idonta.
​Nan take, Ammy ta durƙusa, ta fara kuka sosai. Muryarta na fita da ƙarfi, tana nuna tsantsar ciwon zuciya da rashin bege na rasa ɗanta.

​Abbah ya numfasa, cike da damuwa, amma yana ƙoƙarin nuna ƙarfin hali:

“Ban ga amfanin ihun ba, Maryam. Tunda har aka samu Amatu shima Maleekh za a same shi. Ku kwantar da hankalinku, ina da yakini.”

​Ƙannen Maleekh, Islam da Arfat, suma haka suke kuka na rashin ɗan uwansu. Gidan ya kasance ba annuri tun watanni shida.

​Inna da Amal suka rungumi juna sosai, suna kuka..

​Inna cikin kuka take cewa,
“Duk laifinki ne, Amatu! Da a lokacin kin amince da Maliku, da hakan bata faru ba! Ya baki haƙuri a lokacin! Da kin amince da an fasa aurenki da wancan, an ɗaura da Maliku, da yanzu kuna zaman farin ciki!”

​Amal tana kuka tana shafa cikinta ta ce,
“Inna, kaddararmu ce haka. Allah ya nufa hakan zai faru. Ga wannan cikin na Maleekh ne, amma ba ta hanyar alfasha ba. An ɗaura mana aure ne bisa dokar Musulunci… a cikin dajin.”

​Amal ta basu labarin abin da Mafarauta suka yanke musu: Cewa idan Maleekh bai yi mata ciki ba a cikin kwana uku, za su kashe shi su jefa shi cikin tekunsu mai zurfi, sannan kuma ita za su aura mata maza biyu a cikin mafarautan.
​Wannan labari ya sanya tausayi ya lulluɓe kowa. Sun fahimci cewa gudunsu ba wai don sha’awa ba ne, gudun tsira ne. An yi alhini sosai a cikin gidan.

​Nan take, aka ƙira likita aka duba lafiyar Amal da kuma ɗan da ke cikinta.

​Likita yana murmushi ya ce,
“Dukkan su suna lafiya, amma dole ne ki rage yawan damuwa. Ki ci abinci mai gina jiki. Ki manta da abin da ya faru. Yanzu kin dawo gida lafiya.”
​Daga nan, aka fara ba Amal kulawa ta musamman, tare da abincin ƙara jini da na lafiya.
​Tana zaune a gidan Abbah don ta fi samun kulawa sosai daga Ammy da Inna. An ma buƙaci Inna ta ci gaba da zama a gidan, yayin da aka kulle gidansu na can.

​Yanzu Amal ta zama cibiyar tausayi ga kowa. ’Yan uwa da abokan arziki sun dinga zuwa duba ta.

​Farha, wacce yanzu ta ɗauki Amal a matsayin ƙawa, kullum sai tazo duba ta.
​Hatta Zayd shima ya zo ya ganta. Ya shigo cikin falo da fuska cike da fushi saboda kunya..

​Zayd ya goya hannayensa, yana dubanta sama da ƙasa a yayin da babu kowa a falon sai su kaɗai.

“Daman kun shirya guduwa ne? In ba haka ba, me zai kawo ciki? Ko ba komai, kun zubar da mutuncinku. Da farko kowa yana tunanin Maleekh sace ki yayi, amma yanzu ganin ciki ya sa kowa ya yarda guduwa kuka yi.”

​Amal, ta dube shi da kyau, ta yi wani murmushi na izgilanci fiye da nasa.
​muryarta a sanyaye ta ce,

**“Daman na taɓa cewa ina sonka ne, Zayd? Dalilin da yasa zan aureka, saboda na musguna wa Maleekh ne. Amma kowa ya san cewa Amal da Maleekh su suka fi dacewa da juna. Kuma ga babyn Maleekh a jikina. Kaga kuwa soyayya tayi rana!”
​Zayd yana huci. Ya harare ta da wani mugun kallo sannan ya fita da sauri. Domin ba shi da ta cewa.

​Ammy tana ci gaba da ba Amal kulawa ta musamman har ta shiga watan haihuwarta.
​Kowa yana cikin farin ciki da jiran haihuwar, amma kuma cikin alhini na rashin Maleekh.
​Har zuwa yanzu, babu wani labarin Maleekh.

Cikin dare, duk da cewa an rage mata damuwa, cikin Amal ya fara murɗa wa. Ta riƙe cikinta sosai, tana juyawa a kan gado. Ita kaɗai ce a cikin babban ɗakin kwananta da aka tanadar mata don kada a takura mata.
​Ta fara jin zafin nakuda mai tsanani. Ga kuma jini da ruwa suna bin ƙafarta. Ta fahimci cewa lokacin zuwan jaririn Maleekh ya yi.
​Ganin cewa ba za ta iya jurewa ba, kuma tana tsananin wahala, sai ta yi wani ihu mai rauni wanda ya ratsa cikin gidan.
​Ammy da Abbah suna ɗakinsu a upstairs suka ji ihun. Nan da nan suka sauƙo cikin tsananin firgici da gaggawa. A falon ƙasa, suka tarar da Inna da Islam da Arfat duk sun tashi daga barci.
​Dukansu suka nufi ɗakin Amal. Suka sameta a ƙasa, tana kuka riƙe da ciki. Nan da nan aka ɗauke ta da gaggawa zuwa Asibiti domin ba ta taimako.

​An garzaya da Amal zuwa asibitin masu kuɗi kuma mai daraja a Abuja. Asibiti ne da aka gina shi da kayatattun kayan gini, inda nutsuwa da tsafta suka mamaye kowane lungu da sako.

​An shigar da Amal cikin ɗakin aji Biyu (VIP Room) wanda ya yi kama da ƙaramin gida mai cin kansa, maimakon ɗakin asibiti.

Bango ne da aka yi da launin zinare da creamy white, tare da fitilu masu laushi da ke ƙara annuri ga wurin.

Gadon Amal tsararren gado ne, mai girma, tare da farin zannuwan gado masu taushi.

Babban talabijin ne rataye a jikin bango, kuma akwai sofa masu taushi don waɗanda suka zo duba ta.

Akwai ƙaramin falo a cikin ɗakin inda Abbah da Ammy suke zaune, yana nuna tsararren rayuwa da kuɗi suke bayarwa..

​A cikin wannan ɗaki ne Amal ta sha wahalar nakuda har na tsawon dare. An mata allurai don rage mata zafi, amma ta ƙi, tana son ta ji tsananin zafi na haihuwar ɗan Maleekh...

​Da asubar farko, bayan tsananin wahala da jajircewa, Amal ta haifi ɗan namiji. Kafin a gama shirya jaririn, ta sake nakuɗa ta biyu cikin sauri, kuma ta haifi kyakkyawar yarinya mace.
​Amal ta samu Tagwaye (Twins) kyawawa!

​Jariran sun ɗauko kyawun gaskiya daga iyayensu, Maleekh da Amal, waɗanda tun asali kyawawa ne.

Jariran manyan-manya ne, kuma fatar jikinsu fari tas mai haske, kamar farar fata ta Indian.

​Dukansu suna da suma mai kauri da dogon gashi a kansu, wanda ya yi kama da gashin al’adun Indiya.

Ga ​idanuwansu farare, kuma suna da wani tsantsar annuri a fuskarsu wanda yake nuna cewa sun zo duniya da sa’a.

​Duk ma’aikatan asibitin sun yi mamakin kyawun jariran.

​Bayan an gama shirya jariran, ma’aikaciyar asibitin ta fito cikin farin ciki ta sanar da su Abbah da Ammy da suke jira a Compound (babban falon jira na asibiti).
​Ma’aikaciyar Asibiti tana murmushi ta ce da su,
“Alhamdu Lillah! Muna taya ku murna! Allah ya sauƙe ta lafiya! Ba ɗaya ba, ba biyu ba… An samu Tagwaye! Namiji da Mace!”

​Dukansu sun cika da farin ciki sosai har suka yi sallama mai ƙarfi, suka gode wa Allah.
​An basu damar shiga ɗakin Amal domin ganin jariran.
​Suka shiga cikin tsananin farin ciki da kuma tausayi..

Uwar kuwa ta tafi dogon bacci sakamakon wahalar da ta sha da kuma alluran da aka mata don ta huta.
​Suna tsaye kowa ya kasa zama, suna kallon tagwayen da suka zama alama ta Maleekh a duniya..

​Ammy tana kuka da murna, tana shafa kan jikokinta ta ce,

“Maleekh… Maleekh na. Ga ‘ya’yanka sun zo duniya. Ina muku addu’a, Allah ya dawo da Abbansu!”


《》《》《》《》《》《》《》《》《》

Maleekh ya manta da komai a rayuwarsa, amma hakan bai hana shi saba da sabuwar rayuwarsa ba. Ya saba da Sojoji masu kula da shi, kuma kullum suna cikin wasa da dariya.
​Sojojin sun ba shi suna na musamman 'Lion'.

Wannan sunan ya biyo bayan wata rana da suka shiga daji don motsa jiki, suka ci karo da wani zaki mai tsananin haɗari. Sojojin sun gudu, domin babu wanda ya taho da bindiga. Sai Maleekh da ya yi nasarar tinkarar zaki da tsananin ƙarfi har ya raunana masa ƙafa, wanda hakan ya sa zaki ya kasa ci gaba da binsu. Anan ne suka fara ƙiran shi 'Lion Man'.

​Sojojin sun fahimci cewa Maleekh yana da zafin rai (intensity), kuma babban mutum ne mai tsananin jarumta da basira.

​Maleekh ya zama cikakken Soja a cikin sansanin, domin aikin training ya ƙara masa jiki da ƙarfi. Ya zama masanin dabarun yaƙi duk da mantuwar da ya yi.

​ Daman yana da tsayi, kuma karfafan jikinsa ya cika da tsoka (muscle-bound), wanda yake nuna cewa mutum ne da yake aiki tuƙuru a harkar motsa jiki.

​ Hasken fatarsa mai laushi ya ƙaru, kuma kwantaccen sumar kansa mai baƙin gaske ya ƙara masa kyau.

​Ya ƙara kyau mai tsanani, wanda ya yi kama da tsararren Balarabe mai ƙarfi da kwarjini....

​Yana zaune da Sojojin, yana basu training.

​Kwatsam, a yayin da suke tsaka da wani wasan dariya, Maleekh ya ji jikinsa ya yi sanyi sosai. Wani abu ne ya cije shi a zuciyarsa, wani jin daɗi da kuma firgici sun shige shi a lokaci guda. Ya riƙe ƙirjinsa, yana mamakin me ke faruwa da shi. Ya ji kamar yana buƙatar wani abu da yake da nutsuwa..

​“Akwai buƙatar a ba ni madara in sha, nan take. Wani abu ne nake ji a jikina, amma ban san menene ba.”

​Wani soja ya dube shi da mamaki: “What? Lion! Ko ka fara tuna wani abu ne?”

​Maleekh ya girgiza kai cike da tausasawa ya ce,

“Har yanzu dai, ban tuna ba. Amma jikina ya yi sanyi, da alamun akwai abinda ya faru. Kar ku damu, ina kan yin addu’a domin shine kaɗai ban manta ba. Wata rana, haske zai zo mun kuma zan gano kaina.”

​Sojojin sun fahimci cewa Lion yana da haɗin gwiwa na ruhi da wani abu mai mahimmanci a waje. Sun san cewa wannan jin sanyin na iya zama alamar farfaɗowa. Sun tafi da gaggawa domin su samo masa madarar da ya buƙata.


《》《》《》《》《》《》《》《》《》

​A ɗakin asibiti mai tsada, Amal ta farka daga bacci mai zurfi. Ta ji ƙarfi da nutsuwa sun maye gurbin wahala.
​Ta fara buɗe idanunta a hankali, taci karo da kyawawan jariranta guda biyu. Wata nurse ce ke kula da su a gefen gadonta.
​Amal ta shiga farin ciki sosai. Ta yi kukan murna da godiya ga Allah. Nan da nan ta miƙa hannu, ta ɗauki ɗanta namiji wanda ya yi mata kama da ƙaramin Maleekh.
​Sai dai, duk da murnar, Maleekh yana cikin ranta da kuma zuciyarta. Ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa dena kewarsa ba.

​🌟

​Duk abokan arziki da ’yan uwa sun cika asibitin, domin sai ta samu hutu na musamman kafin su koma gida. Suna ta jiran ganin jariran.
​Amal tana kallon jariran ta yi tunani na musamman

72 / 82