Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   71 / 82

210K to 213K   out of 244.2K words

Bayan ya tafi

Suka zauna su biyun kamar kurame.
Maleekh ya zura ta cikin jikinsa ya rungume ta sosai, zuciyarsa tana bugawa kamar tambari.

Amal ta ce cikin kuka mai sanyi:
“In ba mu tsira ba fa? In gobe ta yi fa?”

Ya goge mata hawaye,

“To ki saurare ni. Idan suka zo gobe, ko me zai faru, ba zan bar ki ba.
Idan ni za su kashe to ki tabbatar kin gudu. Ki gudu ki kuɓuce...”

Ta girgiza kai da sauri:
“A’a! Ba zan bar ka ba!”

Ya kalli idonta cikin duhun ɗaki, ya shafi kumatunta:
“Kin riga kin zama matata. Kuma zan kare ki da rayuwata...”

Ta matsa jikin sa sosai, tana jin numfashinsa yana tafiya da sauri.
Daren ya yi tsawo, suna jin bugun zuciyar juna kawai.

Yau babu wani wanda ya kusanci su cikin ɗaki, amma tsoron gobe ya fi duk wani abu tsanani..

Amal ta yi magana cikin rauni:
“Ka yi addu’a ka sake rungumata… zuciyata na tsalle.”

Ya sake matseta a hankali, suna kallon fitilar daji ta waje tana ɗaukar ido.

Cikin sanyi da matsanancin tsoro, suka kwana suna rungume da juna har gari ya fara haske...

Gobe… gobe… ita ce ranar hukunci....
_NEXT NEXT NEXT_

asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 83 to 84

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹


Da asuba, hasken farko ya shiga cikin dajin. Amal da Maleekh sun buƙaci a kaisu bakin ruwa domin wankan tsarki na janaba, kamar yadda addinin Musulunci ya tsara, duk da cewa mutanen dajin ba sa bin wannan dokar..
​Maza biyu ne suka rakosu, masu gadinsu.
​Bayan sun yi wankan tsarki, kusa da wurin ruwan, suka yi sallah. Domin wurin shine wurin da suke ganin yafi tsarki.
​A lokacin da masu gadin suka juya bayansu don gudun ganin tsaraicinsu yayin da suke wanka, Maleekh ya fahimci cewa wannan ce damarsu ta ƙarshe. Ya riƙe hannun Amal da ƙarfi.
​A hankali, ya furta ciki-ciki, “Mu gudu… ki riƙe hannuna, mu gudu…”

​Amal ta dube shi cikin tsoro ta ce, “Machine ɗin yana hannunsu. Ba zamu iya tafiya ba!”

​Ya ce, “In sha Allah zamu tsira, ba tare da machine ba. Allah yana tare da mu, zo mu tafi!”
​Basu jira wani tunani ba. Suka ratsa wani wuri da masu gadin ba sa nan. Suka yi amfani da juyawar bayansu a matsayin kariya kuma suka fara gudu cikin dajin.
​Can aka ji shiru. Masu gadin suka leƙa, sai suka ga ba su nan. Nan da nan aka hura ƙaho, kuma dukkan mutanen dajin suka bazama, suna neman su.

​Suna gudu cikin dajin ba ji ba gani. Ba takalmi a ƙafafunsu, suna taka kwalabai da itace masu kaifi, amma basu tsayar da gudun ba.
​Daga nesa, aka fara harbo kibiyoyi.
​Cikin sa’a marar kyau, wata kibiya ta samu nasarar harba ƙafar Maleekh. Wata kuma ta shige shi a baya. Amma bai saki hannun Amal ba. Ya ci gaba da gudu, yana jan ƙafarsa da ƙyar.
​Sun kai bakin wani babban ruwa wanda shi ne iyakar dajin da kuma mafarautar suke. Idan suka tsallaka, sun tsira.
​Cikin sa’a, suka tarar da wani ƙaton taya a wurin. Maleekh ya ɗauko shi da sauri, domin mutanen sun kusan iso wa.
​Ruwan yana da matuƙar zurfi.
​Ya ɗora tayar a wuyan Amal, sannan ya jefa ta cikin ruwan, yana faɗin, “Ki riƙe tayar sosai. Kiyi ƙoƙarin tsallakewa. Ba zan bari a cutar da ke ba!”

​Amal tana kuka tana faɗin, “Babu yanda zanje na barka! Kazo mu tafi tare!”
​Tayar ce ke ta tafiya da ita, kamar jirgin ruwa.
​Shi kuwa Maleekh, jini sai zuba yake a jikinsa. Kibiyar da ya ji a baya ta yi masa rauni, amma da saninsa ya yi ƙoƙarin tare kibiyoyin don kada su same ta. Dafin kibiyar ya fara ratsa shi.
​Yana tsaye, sai da ya tabbatar da ta yi nisa, sannan shima ya juya, ya bi wata hanya daban, yana jan ƙafa da gudu da ƙyar...

​Bayan Maleekh ya bar wurin, sai ga mafarautan dajin sun iso, suna ihu.
​Suka tsaya a bakin ruwan, suna hango Amal ita kaɗai a tsakiyar ruwan, cikin tayar. Har ta kai tsakiya, ta bar yankinsu, ta shiga wani yanki daban.
​Mutanen dajin suka firgita, da cewa

“Wannan yarinyar ce ita kaɗai ta tsere mana! Shin ina yaron? Duk yanda akayi yana cikin yankin nan!”

​Suka ga yadda jinin Maleekh ya zuzzuba, ya zama kamar wani rubutu a ƙasa. “Ba zai yi nisa ba. Yana kusa…”
​Suka durƙusa, suna laluben ƙasa. Suna biye da tabon jinin, wanda ya yi layi kamar zane. Suna binsa, kamar karnukan farauta.
​Maleekh yana ci gaba da gudu, numfashinsa na fita. Kibiyar bayansa ta yi masa nauyi, dafin kibiyar yana ci gaba da cin jikinsa kamar wuta marar hayaƙi. Ya ji jikinsa yana sanyi, hannayensa suna rawa.
​Ya ji ƙasa ta juya masa. Yayi tuntuɓe ya faɗi amma da haka ya miƙe da ƙyar, yana jan ƙafa ɗaya kamar gurgu.
​Kamar daga sama ya ji muryar su daga bayan daji,

“Ga shi nan! Ga jinin nan yana tafe!” “Kada ku bari ya tsere! Ku kama shi kafin ya tsallake yankin mu!”
​Hankalin Maleekh ya ƙara tashi. Gumi ne ke ta kwaranya a jikinsa, zuciyarsa tana bugawa kamar ƙaho “Kar na mutu kafin in tabbatar ta tsira… kar su kama ni domin bana so na hallaka a hannunsu.”

Da ƙyar ya rarrafa. Ya kama jikin wata bishiya mai kaifi, yana jan kansa gaba.
​Har sai da ya ji ƙafarsa ta zame, ya faɗi ƙasa da ƙarfi. Kibiyar da ke bayansa ta makale sosai, ba ƙaramin shigarsa tayi ba..
Ya yi ihu kaɗan yana cije haƙoransa..
​A lokacin ya ji ƙafafunsu sun kusanto.
​“Ga shi nan!” ɗaya ya yi ihu. “Kada ku bari ya mutu nan! Ya kamata mu jefa shi cikin babban tekun nan, yadda doka ta ce!”
​Ya kalli gaba, sai ya ga ƙaramin kwazazzabo a cikin ƙasa, ramin da ruwa ya tone...
​“Wannan ce damar da ya rage…”
​Maleekh ya tattara ƙarfin da bai san yana da shi ba. Ya nannarke jikinsa cikin ramin, yana ɓoye kansa da ƙasa..

​A dai dai lokacin da suka iso, sai jinin da ya zuba ya tsaya a bakin ramin, amma babu alamun sa.

​“Sai dai idan ƙasa ta haɗiye shi!”
"Amma babu yadda za'ayi ya shige ƙasa, dole yayi wani hanya daban..."

Suka ƙareshi maganarsu daga bisani suka ci gaba da bi, suna bazama cikin daji, suna ta ihu.

​Maleekh kuwa yana ɓoye a ciki, kamar gawa. Numfashinsa na fita a hankali. Jikin sa yana rawa.
​A hankali, ya furta cikin zafi.

“Allah… ka kare ta… ka kare ni…”

​Ruwan rami ya fara cika wurin da yake kwance, saboda ruwan yana zuba daga sama. Yana jin jikinsa yana nutsewa.
​Sai duhu ya mamaye shi.
​Daga nesa, muryar mafarautan ta sake tashi da ƙarfi, “Mun rasa shi! Amma dole sai an same shi kafin dare! Mai cin dokar mu ba ya rayuwa!”

​Maleekh ya shiga cikin duhu mai sanyi. Ruwan ramin yana ci gaba da cika, yana shigar masa hanci da baki. Dafin kibiyar yana aiki tukuru, yana kashe masa jijiyoyi, kuma zafin kibiyar da ta shige shi ya sanya jikinsa ya yi nauyi kamar guba. Ya ji kamar ruwan ya rufe shi gabaki ɗaya.
​Amma a cikin wannan nutsuwar, wani ƙaramin abu ya haskaka a cikin zuciyarsa wato Amal.

​“Kada in mutu kafin in tabbatar ta tsira…”

​Wannan tunani ya zama ikon numfashinsa. Ko da yake numfashinsa yana raguwa, tunanin cewa idan ya mutu mutanen dajin za su dawo su nemo ta ya ba shi ƙarfin da ya tilasta masa buɗe idanunsa da suka rufe da ƙasa.
​A hankali, Maleekh ya fito da yatsunsa daga cikin laka. Ya ɗaga kansa daƙyar, ruwan ramin ya kusan cikowa, ya zama kamar wani ƙaramin kogi mai ruwan laka. Ya ji motsi sama da shi, sautin tattaunawar mafarautan sun fara raguwa, alamun suna ta nisa. Suna ci gaba da bin sawun da basu samu ba.
​Ya jira har sai da shiru ya sake mamaye daji. Dajin ya koma wurin tsoro.
​Daƙyar ya fito daga cikin ramin. Jikinsa ya yi sanyi, ga zafi, ga zufa. Kibiyar ta shige shi sosai, kuma ya san cewa dole ne ya cire ta ko ya mutu..

Jikinsa duk taɓon ƙasa, haka ya rarrafa ya je ya wanke fuskarsa sannan ya jingina da wata bishiya mai kauri, ya tattara duk wani ƙarfi na ƙarshe.

Cire kibiya mai dafi na iya zama haɗari, amma Maleekh ya san cewa barin ta ma zai kashe shi.

​Haka ya riƙe jikin kibiyar da ƙarfi, ya yi ihu marar sauti saboda zafin da bai taɓa ji irinsa ba, kuma ya ja ta da sauri. Jini ya sake ɓarkewa daga jikinsa, amma tare da shi wani nauyi da zafi ya ɗan ragu. Ya faɗi ƙasa yana huci, amma ya yi nasara.
​Ya tattara wasu ganye waɗanda ya san suna da magani ya ɗaura su a kan rauninsa da rigansa da ya yage.
​Maleekh ya fito da kansa gabaɗaya daga dajin, ya fara tafiya zuwa bakin ruwa da ya bari, yana jan ƙafarsa da take ciwo. Burinsa shine ya tarar da wata hanyar da zai iya ƙetare ruwan. Ya san cewa idan har Amal ta tsira, dole ne ya yi haka...

A wannan ranar a bakin ruwa ya kwana.. Yana shan iska da sanyin wurin..
Asubar fari duk da bai san lokacin sallah ba a wurin haka ya yi alwala da ruwan sannan ya tsaida sallah.
Yana cikin sallah sai ga wasu daga cikin mutanen sun afko masa.

Yana jin yanda suke ta ihu suna ɗaga makamansu sama amma haka ya ci gaba da sallah.

Wasu ne suka fara kwaɗa masa sanda a baya ga raunin kibiya.
Haka yake daure wa sai da ya kammala sallarsa yayi sallama sannan ya ɗaga hannu sama yana addu'a..

Wani ne ya kwaɗa masa a tsakiyar kai sai a lokacin ne ya riƙe kansa tare da sakin ihu...

Wani irin ƙarfi ne ya ziyarce shi a take ya riƙe ya riƙe hannun wani daga ciki wanda ya kawo masa sara da adda.
Wani irin zulluya yayi ya miƙe ya murɗe addar, cikin fusata yake kai musu sara da addar..
​Maleekh, duk da raunukan da ya ke fama da su amma jarumtarsa ta ƙaru. Kuma haka ya ci gaba da sararsu, har sai da ya kashe su duk yawansu.
​Bayan ya gama da su, ya fara jin ihun wasu mutane da suke tahowa da gudu, kuma suna da yawa. Maleekh ya jefar da addar, jini na zuba daga raunukan da ya ji. Yana jin ihun sababbin mafarauta suna tahowa. Ya san cewa duk da nasarar da ya samu a kan waɗannan mutanen, ba zai iya sake fuskantar taron mutane ba tare da ya mutu ba. Dafin kibiyar da kuma raunin faɗa sun yi masa nauyi..
​Ya tattara ragowar ƙarfin da ya rage, ya juya, ya fara gudu cikin zurfin daji inda duhu ya mamaye ko'ina, duk da yanzu ba dare bane.

​ Maleekh yana gudu ne da ƙafa ɗaya mai rauni, raunukan da ya ji a faɗan suna ci gaba da buɗewa, yana zubar da jini a kowane mataki.
​Ya yi ta tuntuɓe a kan kwalabai da sassanyan bishiyoyi, duk yana roƙon Allah ya ba shi ƙarfin da zai ci gaba. Amma ganinsa ya fara rufe wa.
​ Ya tsallake wani rami mai zurfi da duhu. Bai gane ba, saboda duhun ya yi masa katanga.
​Ya faɗa cikin ramin da ƙarfi mai ban tsoro.
amma sa'ar ta juya lokacin da kansa ya bugu da wani ƙaton dutse mai kaifi. A take, ya sume a cikin ramin...

Mutanen dajin sun isa wurin faɗan. Sun ga gawarwakin 'yan'uwansu a warwatse. Fushin su ya ƙaru.
​“Ya kashe su! Wannan yaron ba mutum ba ne! Ruhu ne na daji!” wani ya yi ihu cikin mamaki da tsoro.
​Suka bi sawun jinin Maleekh. Suna ta ihu, suna ta nemansa, amma duhun ya ba shi kariya.
​Sun zo bakin ramin, amma rami ne mai zurfi da duhu ya rufe shi. Jininsa ya tsaya a bakin ramin, amma ba su ga faɗuwar tasa ba.

​“Babu shi! Ya gudu! Ko kuma duniya ta haɗiye shi! Ku cigaba da nema! Ba za mu koma ba tare da shi ba!”

Sun ci gaba da nemansa har tsawon dare, ganin basu same shi ba yasa suka koma yanda suke da safe ba tare da nasara ba. Doka ta ce dole ne a rama mutuwar 'yan'uwansu, kuma sun sanya farashin duk wanda ya nemo Maleekh....



​Ita kuwa Amal bayan ta tsallake ruwa, tana tafiya a can gefen ruwa, ta fara jin wani irin hajijiya saboda ƙaton ruwan tekun da ta shiga. Anan ta faɗi itama ta suma.
​Sai da ta kwana a wurin. Da sassafe, wasu matasa Fulani suka tsince ta. Mutanen Fulani ne, da matansu da yara. Suka kaita wata ruga. Anan aka fara mata jinya.


Amal ta farka daga sumewar wahala da hargitsin jiki da ta samu sakamakon tafiya mai tsawo a ruwa. Ta fara jin ƙamshin madara da hayaƙi.
​Tana buɗe idanunta, ta ga wata mata Fulani tana sanye da kayan fillo farare, tana gauraya wani abu a cikin ƙaramin tukunya..

​“Sannu da zuwa, 'yar gida,” matar ta furta
“Mun same ki a bakin ruwa. Jikinki duk ya yi sanyi.”

​Amal ta yi ƙoƙarin tashi, amma rauninta da hajijiyar da ta shiga sun hana ta. Ta ji kamar ta shiga wata sabuwar duniya.

​Matan Fulani sun yi mata jinya ta gargajiya. Sun yi amfani da ganyen magani da man shanu don shafa mata a jiki. Sun ba ta madara mai zafi da nono don dawo da ƙarfinta.
​A rugarsu akwai zaman lafiya da tsafi.
​Amal ta kwashe kwanaki tana murmurewa. Ta ƙudurce cewa ba za ta faɗa musu cikakken labarinta ba tukuna, don tsoron kada su gane ta kuma su mayar da ita. Ta dai faɗi musu cewa ta rasa iyayenta ne a cikin ruwa.

Amal ta koyi zaman gida da kuma yadda Fulani suke mu’amala.

​A cikin zuciyarta, Maleekh shine burinta.. Tunaninta kullum akan Maleekh.


《》《》《》《》《》《》

Tashin hankalin a ya mamaye Abuja. Mutane ba su san inda Amal da Maleekh suka shiga ba tun bayan sace Amal da Maleekh ya yi ta hanyar Superbike a wurin walimar aure..

​Inna ta shiga cikin tsananin tashin hankali da baƙin ciki. Tana zaune a cikin falonta mai tsada, amma babu wani abu da yake da daraja a idonta face Amal.

​Inna tana kuka tana faɗin “Na rasa Ɗana (mahaifin Amal), yanzu kuma ga Amal ta shiga cikin haɗari! Ina Maleekh ya kaita? Me yasa zai raba ta da mutuncinta har haka?”


​Abbah shima ya shiga gigicewa. Yana jin laifin rashin kulawa, da kuma laifin ɗansa da ya kawo masa ci da baƙin ciki a idon abokinsa (mahaifin Amal) da ya mutu.

Abbah ya yi amfani da dukkan hanyoyin jami'an tsaro da kuɗi da yake da su don neman yaran. Ya san cewa idan ba a gansu ba, za a iya zargin Maleekh da sace mutum (kidnapping), duk da cewa an san suna soyayya.

​‘Yan sanda sun fara bincike a duk manyan hanyoyin fita daga Abuja, suna neman motosar Superbike ɗin Maleekh..

​Hotunansu sun bazama a shafukan sada zumunta da kuma gidajen rediyo, amma babu wani shaida mai ƙarfi da aka samu.

Zayd kuwa daman yasan aurensa da Amal ba mai yu wa bane kawai ya amince ne... Domin yasan Maleekh bazai taɓa bari ba..

​Babban Sufeto mai kula da case ɗin neman yaran, wanda ke da hankali da gogewa, ya gano wasu bayanai masu mahimmanci:

​ Binciken Sufeto ya sanar cewa “Wannan ba sace mutum ba ne na tashin hankali. Wannan guduwa ce ta masoya. Amma gudunsu ya yi nisa sosai har muka rasa sawun su. Ga alama, sun shiga wani wuri ne da ba shi da hanyoyin sadarwa.”

​Ya gano cewa Abbah ya riga ya ajiye wasu tsare-tsare na gano su, ta hanyar satellites da kuma wasu ƙwararrun masu binciken sirri. Ana zargin cewa sun shiga yankin daji ne saboda Motosar Superbike ba za ta iya tafiya nesa a kan hanya ba tare da shan mai ba.

​Bayan kwanaki da yawa na bincike mai tsanani, wata ƙwararriya a fannin fasahar sadarwa ta gano wata yar ƙaramar siginar waya da ta fito daga wani wurin da ba a sani ba a wani wuri mai nisa da Abuja, kusa da wani babban dajin da aka sani da haɗari.
​Sifeto ya fahimci cewa wannan siginar na iya zama wayar Amal ko ta Maleekh, ko kuma wani tsarin sadarwa da suka yi amfani da shi kafin a gano su.
​Ya ƙira Abbah ya sanar da shi cewa,

“Muna da wani wuri. Ga alama sun shiga cikin wani babban daji mai haɗari. Dole mu tura ƙwararrun mutane su shiga nan da nan.”

Duk da irin bincike mai tsanani da jami’an tsaro da masu neman sirri na Abbah suka yi, binciken ya kasance a banza. An shiga dukkan kwa-kwa da rassa na dajin, amma babu wanda ya ga ko wani alamar Amal ko Maleekh.
​Hakan ya faru ne saboda basu da wata wayar hannu da za a iya bin sawunta (tracking), Maleekh kuma yana kwance sumamme a cikin rami mai duhu, ita kuma Amal tana cikin ruga mai nisa inda hatta mutanen rugar gaba ɗaya basu da wayoyin sadarwa..

《》《》《》《》《》《》《》《》

​Bayan tsawon watanni shida na neman da aka yi ba dare ba rana, an haƙura da neman. An ba da sanarwar cewa watakila yaran sun shiga tekun haɗari ko kuma sun rasa rayukansu a cikin daji. Inna ta fita daga hayyacinta, shima Abbah ya shiga cikin baƙin ciki da nadama mai tsanani. Ga an rufe shari’ar...

​Amal ta samu kulawa ta musamman a cikin Rugar Fulani. Ta yi amfani da nutsuwar wurin da magungunan gargajiya don warkewa daga wahalar da ta sha a dajin.
​Bayan tsawon watanni, Amal ta fahimci cewa ikon Allah ya ɗaura mata juna biyu a cikin ɗan kankanin lokacin da suka yi tare

71 / 82