Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Amaleekh Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  African Stories & Novels

Chapter   56 / 82

165K to 168K   out of 244.2K words

daga wannan azaba…”

Yayinda Zayd ke ƙoƙarin cire mata rigarta, sai suka ji ƙarar ƙofa ta turo da ƙarfi...!

Zayd a zabure ya tashi daga kanta yana kallon bakin ƙofar!
Amal ta ja blanket da sauri ta rufe jikinta tana kuka.
Idanunta suka haɗu da na Maleekh, wanda ke tsaye bakin ƙofa, hannunsa riƙe da takardar da ya zo bata. Idanunsa sun kumbura, zuciyarsa na harbawa da jin zafi fiye da rauni.

Ya kalli Amal, ya kalli Zayd, sannan ya yi dariya mai ciwo.

“Toh... dalilin rabuwar kenan?.. har gida kike kawo ‘visitor’? Har cikin ɗaki? Har kan gado?”

Amal ta ɗaga murya tana kuka, tana son yin bayani amma muryarta ta kasa fita...

“Maleekh... ba haka bane wallahi...”

Zayd yana riƙe da rigarsa da yake kokarin sa, yana faɗi cikin ƙarfin murya,

“Amma kai ɗan iska ne Maleekh! Ka turo mana ƙofa ba sallama, shin kai maigidanta ne...?”

Maleekh ya yi wani murmushi mai haɗe da zafi da raini...

“Ba sai na zama maigida ba don in gane ƙazanta. Na gani da idona kuma hakan ya wadatar...”

Amal ta yi sauri katse wa da cewa,

“Wallahi Zayd bai—”

Kafin ta ƙarasa, Maleekh ya juya.
Idanunsa sun cika da hawaye, zuciyarsa ta cika da ɓacin rai da rauni. Ya matse envelope ɗin da yake riƙe da shi, sannan ya jefa shi ƙasa...Yana furta

“Kin gama da ni, Amal. Daga yau bana buƙatar ganin fuskarki. Kina da wanda yafi ni... ai kin same shi.”


Yana faɗin haka ya fice daga ɗakin.
Ƙarar rufewar ƙofa ta ƙara girgiza jikinta, ta durƙusa ƙasa tana kuka, tana faɗin:

“Ya Allah! Ina zan saka kaina? Me yasa rayuwa take min haka? Na rasa soyayya, na rasa mutunci a idon wanda nake so…”


Zayd ya tsaya bakin ƙofa yana kallonta, sai da ya gama sa rigarsa kafin ya fita yana wani irin murmushi....


Jiragen sama suna tashi da ƙarar da ke shiga kunne, amma a zuciyar Maleekh, ba ƙarar jirgi yake ji ba, ƙarar bugun zuciyarsa kawai yake ji.
Ya tsaya bakin glass window yana kallon hasken titin jirgin, fuskarsa ta kumbura da damuwa, idanunsa sun yi ja kamar wanda bai kwanta ba kwana biyu.

A hannunsa akwai boarding pass, amma a zuciyarsa akwai rashin natsuwa.
Ya furta a hankali kamar yana magana da kansa:

“Yanzu duk abinda nayi mata da abin da zata sakamun kenan? Duk da kaunar da nake mata, ta iya wannan abin? Amal?...”

Ya jinjina kai, hawayen da yake ƙoƙarin boyewa suka zubo da kansu.
Ya share da hannu, yana ƙoƙarin daurewa ya zama namiji, amma zafin ya fi ƙarfinsa...

Wani mutum ya wuce kusa da shi yana riƙe da hannun matarsa, suna dariya cikin farin ciki.
Maleekh ya bi su da kallo, sannan ya murmusa cikin ciwo.

“A lokacin da nake ganin soyayya aljannar duniya ce... ban san cewa ta fi jahannama zafi ba.”

Ya juya, ya nufi chair ya zauna.
A gefe, wayarsa ta yi ƙara, Ammy ce ke ƙira.
Ya ɗaga cikin kasala.

“Hello Son, ka tafi ne? Ina gida ina yi maka addu’a Allah ya tsare ka. Kada ka damu da waccan yarinyar nan, Allah zai baka wadda tafi ta komai.”

Maleekh da kasalalliyar murya ya ce:

“Na riga na manta da ita, Mom. Na riga na manta da ita...”

Ammy ta ce:

“Hakan nake so. Kar ka juya baya, idan jirgin ya tashi ka bar komai a nan.”

Ya kashe wayar, ya jingina da kujera, amma zuciyarsa ta ƙi yin shiru.
Duk yadda yake ƙoƙarin tuna ƙiyayya, sai tunanin so ke dawowa.

Yana tuno ranar farko da suka haɗu a office acan Kaduna, yadda Amal ta tsaya a gaban ofishinsa tana faɗin:

“Ni ba’a raina ni saboda talaucina.”

Da yadda yake kallonta yana ganin wata irin nutsuwa da bai taɓa gani a wata mace ba.

Sai zuciyarsa ta soma bugawa da sauri.
Ya matse hannunsa cikin fushi,

“Amal... me yasa kika bani dalilin tsanarki bayan na fi so in mutu saboda ke?”

Sai wani announcement ya cika hall ɗin:

“All passengers traveling to London Heathrow, please proceed to gate 6…”

Maleekh ya miƙe a hankali, ya ɗauki hand luggage ɗinsa, amma kafin ya taka ƙasa zuwa gate ɗin sai ya tsaya.
Idanunsa suna masa raɗaɗi, jikinsa ya ɗan yi sanyi.
Wata murya a zuciyarsa ta furta masa:

“Ka tafi, amma soyayyar nan zata dawo maka. Ka tafi, amma ba za ka taɓa mantawa da ita ba.”

Ya ɗan murmusa cikin raɗaɗi,

“Toh, insha Allahu zan manta da ita kafin ta manta da ni.”

Ya nufi hanyar gate, yana tafiya a hankali, kamar mai gudu daga wani abu da yake binsa a zuciya.
Jirgin ya tashi amma a ƙasan duniya, akwai Amal da ke neman rai cikin hawaye da nadama.....


NEXT NEXT NEXT...


asmeetahwriter✍️

*🎤AMALEEKH🎤*


*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.


*Writing and Storytelling By*

Asma'u Muhammad Auwal

Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*

*MARUBUCIYAR:*

*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*

Bauchi State Nigeria.

*WhatsApp 09065443871*

Follow my channel 👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


BOOK ONE page 63 to 64

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹

Bayan Amal ta gama shan kukan ta idonta ya sauƙa akan envelope dake ya she a ƙasi...

Da sauri ta sauƙa daga kan gado ta ɗauka. Ta buɗe letter hannu na rawa..

"Ban san yadda zan fara ba… sai dai kawai zan faɗa miki gaskiyar cewa zan tafi, kuma bana son ki ƙara gani na a gajeren zango.
Rayuwa ta rikice, zuciyata ta gaji da yaƙi da soyayyar da take ban wahala.

Na tafi ba don na gaji da ganinki ba, ba kuma dan na tsaneki ba, zan tafi ne don kawai na bar zuciyata ta huta daga tunaninki.
Kullum idan na rufe ido, ke nake gani amma kin kasa fahimtar halin zuciyata, baza mu taɓa kasancewa tare ba indai baki koyi zama dani ba....

Please Idan kika tuna da ni, kar ki yi kuka.
Ki yi addu’a kawai, domin duk inda nake, sunanki yana rayuwa cikin zuciyata.

Maleekh 💔..."

Tana kammala wa ta fashe da kuka, tana furta cikin rawar murya:

“Wayyo Allah, meyasa zaka tafi ka barni inda gaske kake kana sona? Meyasa na bashi dalilin tsanata?… Amma ban fa yi komai ba! Me yasa rayuwa bata bani dama in bayyana gaskiyar zuciyata ba?”

Ta share hawayen, ta miƙe a zabure.
Ta zura rigar jikinta da hanzari, ta ɗauki key ɗin motarta, tana hawaye tana furta:

“Zan same shi! Ko da kuwa a bakin jirgi ne, zan gaya masa gaskiya kafin ya bar ni.”

Tana fita daga gida sai ta ja motar cikin gudu, tayoyi na rawa tsabar gudu...
Fitilar gari ta zama hazo a idanunta saboda hawayen da suka hana ta gani sosai.

“Ya Allah ka tsare ni… kar in isa jirgin ya tashi kafin in gan shi…”

Tana isa gate na tashar jirgi, ta tsaya cak ganin motoci da mutane da yawa suna barin wurin.
Da gudu ta shige cikin tashar, tana share hawaye, tana tambayar ma’aikacin tsaro:

“Don Allah, jirgin London… jirgin London Heathrow, ya tashi ne?”

Ma’aikacin ya duba agogonsa, sannan ya ce:

“Madam, jirgin ya tashi mintuna goma da suka wuce.”

Amal ta tsaya kamar an zuba mata ruwan sanyi.
Hannunta ya saki key ɗin motar da take riƙe, ya faɗi ƙasa.
Tana kallon taga mai nuni da jiragen da ke tashi a sararin sama, sai hawayen da sake gangarowa cikin zafi..

Ta durƙusa ƙasa ta fara ihu kamar zuciyarta zata tsage:

“MALEEKH! Don Allah ka tsaya ka saurare ni! Wallahi ba haka bane, ban ci amanarka ba!!”

Wata mata dake wucewa ta tsaya tana kallonta cike da tausayi, amma Amal bata ma lura da ita ba.
Tana kuka tana faɗin:

“Na rasa shi... Na rasa shi... Allah Ya sani ban yi masa laifi ba, amma bai tsaya ya saurare ni ba…”

Ta durƙusa sosai, ta tallafi kanta da hannu guda tana kuka kamar ranta zai fita.
Jikin ta na rawa, murya na dusashe wa.
A hankali ta ɗaga idanunta ta kalli sama, tana faɗin a fili:

“Allah, idan akwai adalci a duniya, ka tabbatar gaskiyata ta bayyana... kar Maleekh ya rayu cikin ƙarya... kar ya rayu yana tsanata da abin da ban aikata ba…”

Hawayenta suna zuba gaba ɗaya ta jiƙe gaban rigar abayar ta, ta rufe fuska da tafukan hannayenta tana kuka.
Wani sanyi ya ratsa jikinta, kamar an busa iska mai ƙarfi.
Tayi shiru na ɗan lokaci, sai ta ɗaga kanta cikin tashin hankali:

“Idan soyayyata ta ƙare da Maleekh, to ni ma zan kare daga rayuwar nan…”

Sai ta tashi a hankali, ta fice daga tashar, tana tafiya kamar mai neman hanya cikin duhu, zuciyarta na bugawa...
Haka ta shiga mota ta tafi jiki ba ƙwari..


Kwana Biyar Bayan Tafiyar Maleekh...

Tunaninsa bai taɓa barin Amal ba. Tun ranar da ta dawo daga airport da kuka, babu rana da ta tashi ba tare da ta ƙira lambar sa ba.
Kowane lokaci da ta danna “call”, sai ta tsaya tana sauraron sautin “number you are calling is switched off…” sautin da ya zama kamar wuƙa a zuciyarta.

Tana zaune a gaban window, ta jingina kai a jikin gilashi, tana kallon ruwan sama da yake sauƙa cikin nutsuwa. Wayarta a hannu, idonta a kumbure, jiki duk ya rame.
Tana faɗa cikin disasshen muryar :

“Maleekh… har yanzu baka dawo ba? Ko baka ji ƙiran zuciyata ba?... Kai nake nema, Allah yasa kana lafiya.”

Sau da yawa tana duba WhatsApp, babu last seen.
Instagram shiru.
Email babu amsa.
Kamar ya ɓace daga doron ƙasa...

Amal ta kasa cin abinci. Idan ta ɗauki cokali, sai hawaye su gangaro. Inna tayi iya ƙoƙarin lallashinta, amma ita kanta ta gane cewa ciwon soyayya ya fi kowanne ciwo ciwo.

Da daddare Amal takan tashi tsakar dare, tana tunanin ko ya ci abinci, ko yana lafiya.
Ta ɗauki wayarta ta kunna voice recorder, tana magana kamar yana gabanta:

“Maleekh… ni ce Amal. Ka tuna mun yi alƙawarin cewa babu rabuwa a tsakaninmu, ko?”
“Zan jira ka, har sai lokacin da ka dawo min da murmushi ɗaya daga cikin naka.”

Ta dinga faɗin haka cikin kuka, tana maida numfashi a hankali.
Da asuba, ta tashi ta shiga bathroom, tayi brush sannan tayi wanka tare da ɗauro alwala, ta saka hijab ɗinta ta tsaida sallah...

Bayan tayi sallah tare da addu’o'i, ta tashi cikin ƙarfin hali tana faɗin.

“Uhmmm, ban isa in mutu saboda ciwon soyayya ba. Zanyi aiki, zanyi rayuwa har sai lokacin da Allah Ya dawo min da shi.”...

Da wannan niyyar, ta shirya ranar ta biyar, ta saka suit skirt da rigar office, ta ɗaure tie ɗinta a wuya, ta ɗauki handbag ta nufi falo, a wannan ranar ta dage tayi breakfast, daga nan ta shiga ɗakin Inna suka gaisa sannan ta wuce company.
Lokacin da ta shiga reception, murmushi marar zurfi ne ya bayyana a fuskarta, murmushin wacce ta sha kuka amma ta nuna ƙarfin hali...

Sai nan ne ma’aikatan suka yi mata sannu da dawowa, tare da gaisheta...

Sai kuma Zayd ya bayyana da kalmar nan “My pretty…”
Amma wannan karon, mari ya riga da ya sauƙa kan fuskarsa kafin kalmar ta gama fita daga bakinsa...

Zayd ya tsaya dafe da kuncinsa, kowa a reception ya tsaya shiru. Sai sautukan takalman Amal da take taku cikin ƙasaita.. Idonta cike da zafi da hawaye, amma ta tsaya a gabansa kamar shugabar da ya kama wani da laifi...

“Kayi farin ciki, ko? Ka rabani da mutumin da zuciyata ke numfashi dashi! Ka ɓata min suna a gabansa, kayi amfani dani wurin cimma burinka…Ba tare da nayi wani tunani ba na biye maka, wallahi ban yafe maka ba Zayd..."

Zayd ya yi ƙoƙarin murmushi, amma muryarsa ta nuna gurbatacciyar niyya.

“Eh, gaskiya ne. Ni nake sonki shiyasa nayi haka, na daɗe ina jiran wannan damar. Maleekh ya tafi, yanzu ba wanda zai tsaya tsakanina da ke. Wannan itace gaskiya, Amal.”

Ta matso kusa da shi, tana kallon sa da idanunta masu cike da hawaye da tsantsar tsana ta ce.

“Burinka bai cika ba, Zayd. Ba zaka iya maye gurbin Maleekh ba. Jininmu ya riga da ya haɗu, ba a cikin jikina kawai ba, har cikin ruhi da numfashina. Ka ji da kyau: ko ka kawar da ni, ko ka kawar da shi, ƙauna bata da kabari.”

Tana kaiwa ta juya da ɗan huci. Ma’aikatan suka ba ta hanya, babu wanda ya iya magana. Ta shiga elevator, ƙamshin turarenta ya ci gaba da yawo cikin reception...

Bayan ta hau saman bene na takwas, ta fito tare da shige office ɗinta ta rufe ƙofa.
Ta jingina da ƙofar, hawaye suka fara sauƙa kamar ruwan sama.
Ta zame a ƙasa ta durƙusa, tana riƙe da kanta tana faɗin

“Ya Allah... har yaushe zai waiwaito ni? Ko da gaske ya tafi ne har abada? Maleekh, don Allah ka amsa ƙiran da nake yi maka…”

Ta lalubo wayarta daga jaka, ta sake ƙira. number you are calling is switched off.
Ta saki wayar ta faɗi gefe, ta lumshe ido tana kuka kamar ranta zai fita.

A cikin office ɗin akwai hotonsu su biyu da Maleekh a kan tebur, lokacin da suka yi launching na sabon project ɗin CashTalk FM. Ta miƙa hannu ta ɗauka, ta kalli hoton, ta shafi fuskar sa a hankali tana faɗin.

“Ka faɗa min cewa ba zaka taɓa yin nesa dani ba… ka faɗa min cewa zaka kasance dani har abada…”

Sai ta ji kanta na sarawa. Tana numfashi da sauri, zuciyarta na bugawa da kyar.
Ta tashi ta nufi window, tana kallon sararin sama, tana jin kamar ta ƙira sunan sa cikin iska...

“Maleekh…”


Sautin sunan ya fito da ƙarfi, yana haɗuwa da hawayen da suka zubo kamar ruwan sama daga idonta.

Tana nan tsaye har sai da hasken rana ya fāɗi, sannan ta zauna a kujera, ta riƙe kai tana murmushi cikin hawaye:

“Ba zan daina jiranka ba. Ko ka bar ni, zan ci gaba da yi maka addu’a.”..

A wannan ranar Amal bata samu ƙarfin gudanar da aiki ba....




Tafiyar da aka yi shi cikin fushi, bata taɓa sa ran zama makamin hallaka kamar haka ba...

Maleekh ya bar Najeriya da zuciya mai raɗaɗi, fushi da ƙaunar Amal suka haɗu suka zama wuta a ƙirjinsa.
A hannunsa akwai jakar da ya ɗauko kai tsaye daga cikin motarsa wanda yana tunanin nashi ne domin sak irin jakarsa ce, tunani ya dabaibaye kwakwalwarsa, yana tunanin komai lafiya. Bai san cikin jakar akwai abinda zai iya ruguza rayuwarsa gaba ɗaya ba....

Yana shiga jirgin.
Ko wayar Amal da ke ta ƙira, bai amsa ba. Ya kashe komai, yana son mantawa da komai amma ba zai taɓa iya mantawa da yadda ya ga Amal cikin ɗakin nan tare da Zayd ba.

Lokacin da jirgi ya sauƙa a Heathrow, tsaftataccen iska mai sanyi ya daki fuskarsa...
Ya sauƙo cikin natsuwa, hannunsa na riƙe da pasport ɗinsa, sai kawai ya ji murya daga gefe ta ce:

“Sir, can we have your luggage, please?”

Ya miƙa musu cikin nutsuwa. Amma kafin ya ankara, sai ya ga wasu ma’aikatan tsaro biyu sun tsaya a bayansa, suka ɗauki jakar nan da suka saka a scanner.
Cikin mintuna biyu, komai ya canja, hasken da ke kan fuskar screen ya yi ja, wani ɗaya daga cikin su ya ɗago da murya mai tsanani.

“We have an issue here…”

Maleekh ya kalli fuskar su cikin mamaki.

“What? Is there any problem?”

Suka nuna masa allon: cikin jakarsa akwai ƙwayoyi masu hatsari waɗanda a ƙasar nan hukuncinsu ɗaya ne da kisa...

Cikin rawar murya, ya ce:

“That’s… impossible. That’s not mine! Wallahi I don’t know about that!”

Amma ba wanda ya saurare shi.
Nan take suka kwace wayoyinsa, suka sa masa handcuff, suka tura shi cikin wani ƙaramin ɗaki mai duhu, inda ake tsare waɗanda ake zargi da laifin safarar miyagun abubuwa...

A nan ya zauna, ba tare da kalmar da zata fito daga bakinsa ba.
Abinda ke masa yawo a zuciya shi ne “Amal… idan ta ji wannan fa?”

A can gida kuwa, kwana uku suka wuce ba labari.
Ammy tana ganin kamar ya kashe wayarsa ne don ya huce.
Abbah kuma ya ce,

“Ku barshi, zai dawo da kansa.”

Sai rana ta bakwai sati guda kenam, lokacin da Amal ta isa kamfani da safe, cikin kaya masu kyau amma idonta kumbure saboda rashin kwanciyar hankali. Ta shiga reception da sallama, ta amsa gaisuwar ma’aikata da natsuwa, tana ƙoƙarin ɓoye ɓacin ranta...

phone ɗin receptionist yana yawan ring..

Receptionist ta ga wani number da yake meta da rubutu: “International Airport Authority. URGENT CALL”. Kafin Amal ta wuce sai ta ce cikin girmamawa:

“Miss Amal. Wani ke ƙira daga Airport London. Sun ce akwai buƙatar a yi magana da dangin Maleekh.”

Amal cike da mamaki take kallon receptionist ɗin da take ƙoƙarin bata wayar:

Amal ta karɓa da faɗuwar gaba, zuciyarta na dukan kamar ana buga ganguna a ƙirjinta.
Da ƙyar ta furta,

“Hello....“Hello? …Waye ke magana?”

Sai wata murya mai sanyi ta amsa daga can ƙetaren teku:

“We’re calling from Heathrow Airport. A man named Mr. Maleekh Abdul-Majeed has been detained in our custody for drug trafficking. We need his family or representative.”

Wayar ce take ƙoƙarin faɗuwa daga hannunta, da ƙyar ta riƙo wayar da sauri ta ƙara karawa a kunne.
Cikin tsoro ta matsa kusa da receiver tana faɗin.

“A, Mr… wai… me kuke cewa? Maleekh? Amma… ya tafi ne, ya riga ya sauƙa? Ya… ya faɗa muku da abin da ya faru?”

Ma’aikata suka tsaya kallonta yanda ta firgita. Idonta ya cika da hawaye...

Officer ya kuma cewa:

“Muna neman mu tabbatar da gaskiya. An tsare shi ne lokacin da aka samu kayan miyagun kwayoyi a jakarsa. Yana nan a interrogation room yanzu. Muna buƙatar wanda zai zo a matsayin danginsa ko wakili. A halin yanzu wayoyinsa an kwace, kuma ana nazarin jakarsa. Muna bukatar lambobin danginsa: akwai yiwuwar mu yi contact da su don sanarwa….”

Amal a ruɗe ta ce

“What…? Maleekh…?”

Ƴar amsa kawai ta fito daga bakinta kafin ta durƙusa, ta dafa tebur tana huci, hawaye na zuba kamar an kunna famfo....


A wannan

56 / 82