Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
ya jefa mata a gabanta.
“Wannan rahoton ne daga likita,” ya ce cikin sanyi, muryarsa na dukan kunne kamar ƙaho.
“Yana cewa kin zubar da cikin wata huɗu. Wannan rahoton ne daga club ɗin da aka sameki cikin jini.”
Zuciyar Amal ta buga.
Ta dago a hankali tana kallonsa, hawaye suka cika idonta.
“Maleekh…” ta ce da muryar da ke rawa. “Ka kasa saurara na tun lokacin… ka kasa tambayata me ya faru.”
Ya ɗan jinjina kai cikin ɓacin rai..
“To yanzu nake son jin ki. Ina sauraronki yanzu.”
Amal ta miƙe da sauri tana faɗin,
“To yanzu kake buƙatar ji na? Bayan ka riga ka yanke hukunci? Bayan ka riga ka ɗauke ni a matsayin mai laifi?”..
Amal tana surutai ta nufi ƙofa zata buɗe ta tafi taji ko ina a kulle.
Haka ta haƙura tana kuka.
Maleekh yana danna computer
Ya ce.
"Ke, bana wasa dake! Yanzu gaya mun, a kwanakin baya meya faru aka sameki a gidan club hakan ma a cikin jini sannan doctor ya ce, kin zubar da cikin wata huɗu..."
Amal tana harararsa ta ce
"Tin lokacin Meyasa ka kasa saurara ta?.."
Ya ce cikin izzah.
"Yanzu..Ina sauraronki.."
Amal ta ce.
"To nima banida lokaci yanzu.."
Wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata har sai da ta gigita. Sauran kaɗan ta fece jikinta na 6ari..."
"Gaya mun na ce.."
Muryarta ta rikice, tana girgiza kai, jikinta na rawa...Ta ce:
“Ka yi mun hukunci ba tare da shaidar gaskiya ba, Maleekh! Ba ciki na zubar ba!”
Ya ɗan miƙe daga kujerar, ya sauƙe ido daga kanta yana furta a hankali,
“To menene ya faru, Amal? Me yasa aka sameki cikin jini a club?”
Tana kallo cikin idonsa, murya ta fara karyewa,
“Na ji labarin Aurenka da Farha shine nayi ta ƙiran ka, baka ɗaga ba. Na fita saboda ina sonka na je gidanku aka sanar mun cewa kana club, hankalina ya kasa kwanciya hakan yasa naje domin dubo ka. Na samu wasu ƴan mata suka sanar mun cewa kw fita amma zaka dawo yanzu...Na sha juice da suka kawo, sai na ji duniya ta fara juyawa… daga nan ban sake sanin komai ba. Ina farkawa sai a asibiti... Bayan zargina da ake akan batun nan naje wani hospital domin tabbatar da kaina. Likita yace babu wani cikin da aka zubar, amma an zuba wani abu a cikin abin sha na.”
Ya ɗan tsaya shiru, idonsa ya ƙanƙance kamar mai son yin kuka amma ya danne cike da iko ya furta.
“Me kike nufi? An drug ɗin ki?”
Amal ta gyaɗa kai cikin kuka,
“Eh… amma baka saurare ni ba. Ka bar ni cikin rauni, ka yi min hukunci kafin ka ji gaskiya.”
Da sauri ta fara lalu6o wayarta yanda tayi snap ɗin result ɗin da doctor ɗin ta ya bata cewa babu abinda ya faru illah drugs da ta sha...
Ta ce cikin rawar murya.
"Ka ga..."
Ya karɓa ya duba da kyau sannan ya jinjina kai ya ce:
"Wa ya tura ki wurin? Ina nufin wa ya sanar miki cewa ina club?..."
Amal ta girgiza kai ta ce
"Kawai kayi haƙuri komai ya wuce.."
A tsawa ce ya ce
"Wa ya sanar miki?..."
A ruɗe ta ce:
"Fa F Far Farhaaa.."
Ya rufe ido da hannu ɗaya, yana maida numfashi cikin wahala.
Sannan cikin tsawa mai rauni ya ce,
“Me yasa baki faɗa min tun farko ba?”
Ta ɗaga kai tana kallonsa cikin hawaye,
“Saboda baka tambaye ni ba.”
Shiru mai nauyi ya sauƙa tsakanin su.
Ƙarar iska daga window kawai ake ji tana shigowa tana motsa labulen bakin gilashi.
Amal ta juyo gefe ta share hawayenta, ta ce cikin murya mai sanyi,
“Wannan shine dalilin da yasa nake son barinka. Kai ka kasa sauraro na sai lokacin da zuciyarka ta riga ta yanke hukunci.”
Maleekh ya kalleta sosai, idonsa ya canza daga fushi zuwa nadama.
Ya matso kusa da ita a hankali, amma kafin ya iya cewa komai Amal ta juya ta kama ƙofa, ta fara dukan ƙofa tana faɗin,
“Ka buɗe ƙofar, Maleekh. Ka barni in tafi.”..
Ya tsaya a gefe yana kallonta, muryarsa ta yi rauni sosai.
“Idan na buɗe, ki gaya min gaskiya bakya sona?”
Amal ta tsaya ta juyo tana kallonsa da hawaye,
“Na taɓa sonka, amma yanzu tsoranka ne kawai a zuciyata.”
Ta juya ta zauna a ƙasa tana kuka.
Maleekh ya zauna yana kallonta, zuciyarsa ta rikice gaba ɗaya....
A bangaren Zayd kuwa...
Zayd ya shigo gida da jiki gaba ɗaya a raunane. Rigar sa ta tsage, fuska ta kumbura, leɓensa ya fashe. Ya tsaya a bakin ƙofa yana riƙe da ciki da hannunsa, yana fitar da numfashi da ƙyar..
Ammy da yaranta suna zaune a babban falon suna hira da dariya, sai suka juyo da ganin yadda yake jina-jina...
Ammy a tsorace ta ce:
“Subhanallah! Zayd! Me ya same ka haka? Waye ya maka haka?”
Zayd ya zauna a kujera yana jan numfashi. Ya share jinin da ke gefen leɓensa sannan ya ce cikin muryar da ke cike da haushi:
“Maleekh ne... Maleekh ya kwace min masoyiya sannan ya dake ni kamar ɗan yaro a gaban mutane...”
Falon ya ɗauki shiru, kowa ya kalle shi da mamaki.
Ammy ta ɗaga gira ta ce:
“Masoyiya kuma? Wace yarinya ce da zata sa Maleekh yayi maka haka?”
Zayd ya ce:
“Amal... Sunanta Amal. Tana aiki a cikin campany ɗin mu.”
Daga nan kowa ya girgiza kai.
Arfat ta zabura da sauri tana faɗin:
“Tabbas ai dole ne Yaya Maleekh ya maka duka! Kai baka san yanda yake ji da Amal ba? Har sumar dani yayi saboda ita, wallahi a lokacin na ɗauka kashe ni zai yi saboda wata Amal!”
Islam ta ƙara da murmushi mai cike da raini:
“Ai ba kwace maka masoyiya yayi ba, dan tun farko ita masoyiyarsa ce. Amal ta Maleekh ce, kai dai baka san komai ba.”
Zayd ya kalli Islam da Arfat, idanunsa suka kaɗa da fushi.
“Shi yasa ke kike magana kamar kina farin ciki da hakan!? Idan masoyiyarsa ce me yasa yake rayuwa kamar wanda ya tsane ta? Me yasa baya nuna cewa yana son ta? Yake toshe mata hanya, yana tsareta kamar bai damu da ita ba?”
Arfat ta ɗaga kai tana murmushi mai ɗan raini ta ce:
“Eh to... Wannan ai shi ne irin soyayyar Maleekh, mai zafi, mai daɗi, mai ƙarfi. Kai dai baka san komai game da su ba, in taƙarƙare maka to akanta Yaya Maleekh ya kwanta jinya, ya samu matsalar zuciya...”
Farha ta harare su duka biyu cikin bacin rai ta ce:
“Dallah ku daina wannan sakarcin magana! Naga yanzu Maleekh ba ya son Amal, wallahi ba ya yinta. Dole ne ku gane hakan.”
Zayd ya miƙe tsaye a hankali, yana goge jinin da ke gefen fuskarsa.
Idonsa ya sauya, ba na zafi kawai ba, har da na ƙuduri...
Ya ce da muryar da ke cike da alƙawari:
“Ko da Maleekh yana so ko baya so... sai na mallake ta. Amal zata zama tawa ko ta halin ya ya ne.”..
Ya juya da fuskar da ta haɗa zafi, rauni da azama, sannan ya nufi ɗakinsa...
NEXT NEXT NEXT....
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 53 to 54
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Fitowar hasken safiya, rana ta fara bayyana a saman tagogin gidansu Amal. Inna tana zaune a falon ƙasa, tana sanye da hijabi tana lissafin tasbihi, amma idonta duk ya nuna damuwa. Tana tunanin dalilin da yasa Amal bata dawo gida ba tun jiya.
Ƴan aiki suna ta motsi a kusa, wata na share falo, wata na haɗa breakfast. Cikin wannan yanayi ne maigadi ya shigo yana ƙiran Inna.
Maigadi yana tsaye a ƙofar falon ya ce:
“Inna, anyi baƙi.”
Inna ta ɗago kai da mamaki ta ce:
“Baƙi kuma? Da mota ne suka zo?”
Maigadi ya ce
“A’a Inna, da ƙafa suka zo. Wani dattijo ne da matarsa, sai wani saurayi da wata ƙaramar yarinya..”
Inna ta haɗe gira ta ce
“Toh, to. Kace su shigo nan cikin falon.”
Maigadin ya juya ya fita. Ba da jimawa ba, sai ga su sun shigo cikin falon, dattijon yana da farin gashi da tsintsiya, matarsa tana sanye da hijabi mai launin toka, sannan wani saurayi da ya cika kamar ɗan gari, kyakkyawa da tsawo, sai karamar yarinya mai kimanin shekara 17 zuwa 18.
Inna tana kallonsu har suka ƙaraso. Tana ganin dattijon sai ta zabura ta miƙe tsaye da mamaki.
Inna da mamaki da farin ciki ta ce
“Yawale!? Kai malam Yawale! Ashe kai ne?”
Malam Yawale yana dariya ya ce
“Na’am Inna Delu! Kin gane ni ke nan.”
Inna tana dariya ta ce
“Wallahi na kasa gane ka, Malam Yawale! Ai shekaru sun ja fa. Ina Zainabu? Ga ita nan ko?”
Zainabu matar Yawale, tana murmushi ta ce.
“Eh ni ce, Inna. Na gode Allah da naga fuskar ki bayan shekaru.”
Inna ta ce.
“Lallai yau gida yayi albarka. Kun taho daga ina haka?”
Malam Yawale cikin farin ciki ya ce
“Daga ƙauyen Gajeren Rafi a cikin Kaduna Local Government. Ai kin san shi can bayan Rijana, hanyar zuwa Kachia. Mun daɗe muna shirin zuwa ganin ku, sai yau muka samu dama.”
Inna ta gyara zama ta ce
“Toh, ai kunzo gida. Ku zauna. Allah ya kawo ku lafiya. Yanzu ga wannan saurayin da karamar yarinyar nan fa?”
Malam Yawale yana nuna su ya ce
“Wannan ɗana ne, Kabiru. Ga matata Zainabu, kuma wannan karamar yarinyar mu ce wato auta kenan Halima. Dake yaran duk sun mutu sai iya biyun nan, Kabiru da Halima ne suka rage mana, ai Halima tunda aka gaya mata akwai ƴar uwarta Amatu a burni sai ta nace zata zo ta ganta da idonta.”
Cikin jin wannan kalma, Inna ta ɗan tsure, sai ta murmusa da ƙyar tana danne tsoro.
Inna ta share gumi a goshi ta ce:
“Eh, eh... Amatu dai tana wurin aiki yanzu. Tunda safe ta fita ba ta dawo ba. Aikin campany ne, kin san dai irin aikin birni babu sauƙi.”
Zainabu ta ce cikin kalar tausayi.
“Eh ai haka rayuwar burni take. Amma sai ta dawo fa mu ganta. Mun daɗe muna son muje mu gaisheta, tun bayan rasuwar mahaifiyarta.”
Inna tana murmushi amma idonta cike da damuwa ta ce.
“Insha Allahu zata dawo. Ku huta da gajiya. A girka muku abin ci. Ke Halimatu! Je ki ce a dafa muku tuwo da miyar taushe.”
Halima ta tashi da hanzari kamar wanda aka zabure ta..
Kabiru yana duban falon ya ce
“Ai gidan nan ya ginu sosai. Amatu kenan ke zaune a irin wannan gida? Lallai ta samu albarka a burni.”
Inna tana dariya cikin ɗan ɗoki ta ce
“Eh, ai Amatu yarinyar kirki ce. Ta dage da aiki sosai. Allah ne ya bamu arziki ta hannunta.”
Malam Yawale yana kallon Inna ya ce.
“Toh Alhamdulillah. Sai dai Inna, muna fatan komai lafiya. Na ji kamar kin damu ne tun muna shigowa.”
Inna tana ƙoƙarin boye damuwarta ta ce.
“A’a, lafiya lau. Kawai gajiya ce ta kwanan jiya.”
Suka zauna suna hira, amma Inna tana ɗan duban ƙofa lokaci-lokaci zuciyarta cike da fargaba, tana addu’ar kada Maleekh ya dawo da Amal cikin wannan yanayi, musamman yanzu da danginta daga ƙauye suka iso.
Bayan an ci an sha, an jera kofin shayi a kan teburi. ƙamshin tuwo da miyar taushe ya ratsa ko ina. Kowa ya ɗan yi nishaɗi, ana hira a hankali sai Malam Yawale ya tashi ya gyara zama, fuskar sa cike da murya mai nauyi...
Malam Yawale yana kallon Inna ya ce:
“Inna Delu, daman ina so mu yi wata magana mai muhimmanci.”
Inna ta gyara zama, tana miƙewa a hankali ta ce:
“To malam yawale, ina jinka. Me ke ranka? Me kake so mu tattauna?”
Malam Yawale ya ɗago kai yana kallon duk wanda ke falon, ya dubi Kabiru da Halima a gefe sannan ya koma kan Inna.
Malam ya ce
"Kin dai san ni Yayan Mahaifiyar yarinyar nan ne wato Amatu, kuma iyayenta mahaifiyarta da mahaifinta sun juma da rasuwa tin tana ƙarama, yanzu abinda na yanke shine, me zai hana zumuncin mu yayi karko, mu haɗa zumunci sosai, inaso zan haɗa ɗana kabiru da Amatu Aure.."
Kabiru yana gefe yana farin ciki...
Inna taji batun baiyi mata daɗi ba ta ce
"Wai malam yawale taya ma kuka san muna nan Abuja?"
Malam ya ce
"Ai mun shiga Kaduna can gidan da kuke akace kun daɗe da barin Kaduna kun dawo Abuja. Shine muka zo Abuja munata nema saida muka yi sati guda anan Abuja kafin muka samu gidan ku.."
Inna ta ce
"Aww saboda kun ji munyi arziki shine zaku wanko ƙafa kuzo wai akan a haɗa aure ko? To sannu masu son zuciya.."
Malam ya ce
"Me kike faɗa haka Inna Delu?.."
Inna ta ce
"Lokacin da iyayen Amatu suka rasu tin tana yarinya ba ƙin kula da ita kukayi ba? Saboda babu dukiyar iyayenta duk sun ƙone a gobara shine kuka guji ɗiyarsu, kuma alhalin lokacin da iyayenta suke da rai babu abinda kuke rasawa daga wurinsu, kullum a cikin maula kuke, ni mahaifiyar mahaifin Amatu ce inada iko akansa amma ban hanashi taimaka muku ba, shi kaɗai na haifa a duniya bashi da wa bashi da qani...Na tabbata da inada wasu ƴaƴa bayan shi nasan zasu taimaka mun...amma dake babu kowa, ku da kuke ƴan uwan mahaifiyarta sai kuka kama gabanku, wai bakwa so a ɗaura muku dawainiya, saboda iya Amatu kawai, amma ai kuna riƙe da ƴaƴanku ko? Marasa imani kawai, badan zuciyar musulunci ba ai bazan kalli yanda kuke ba tinda kuka kasa riƙe ɗiyar ƴar uwarku saboda bata da rai, kun ji kunya, yanzu kuma ko kunya babu kunzo wai batun auren zumunci, to baza'ayi baaa...."
Malam yawale ya ce
"To bamuda halin taimaka muku ya zamuyi? Shiyasa muka daina zuwa yanda kuke...ba gashi yanzu tayi arziki ba, nima dai inada iko akan Amatu, don haka sai anyi auren nan..."
Zainabu ta tsoma baki cikin maganar ta ce:
“Inna Delu, ba mu zo ne don mu tayar da hayaniya ba. Mun zo ne saboda mu gyara kuskuren da muka aikata a baya, mu tayar da zumunci, mu ba wa Amatu gida na gaskiya. Mun zo ne da niyyar taimako, ba da tada faɗa ba.”
Malam Yawale yana jin zafi amma cikin nutsuwa ya ce:
“Inna, gaskiya ba mu zo don mu yi ruɗu ba. Na san abin da kuka ji lokacin da iyayen Amal suka rasu, amma ni da matata, duk lokacin da muka yi tunani, zuciyarmu ta cewa mu taimaka. Ina son Amatu tun tana ƙarama. Yanzu da akwai damar a gyara, me ya hana mu haɗa Kabiru da ita? Zan riƙa kula da ita, in ba haka ba za ta ci gaba da zama a burni ita kaɗai a yayin da babu ranki..."
Inna ta dafe goshi, idanuwanta sun cika da hawaye. Ta kalli Kabiru, ta ji raɗaɗi a ranta. Sai ta miƙe hannu ta ɗaga ƙofin shayin ta karɓa..
Inna ta yi sanyi sosai, ta tsinke muryarta da cewa.
“Kun bar ta lokacin buƙata, kun guje ta saboda rashin dukiya yanzu kawai kun dawo saboda nufin ku ɗaura mata aure da ɗanku? Ai ni mahaifiya ne, na san halin da ƙasa take; Ba da sauri zan yarda ba, Malam Yawale. Zumunci abu ne mai tsarki; amma gina zumunci ya danganta da niyya, tausayin juna da gaskiya ba don abun duniya ba.”
Malam Yawale ya kusanci Inna, ya yi magana da murya mai laushi da ƙarfin gwiwa ya ce
“Inna, ina roƙon ki da zuciya ɗaya: ki yi la’akari da abin da zai faru da Amatu idan ta ci gaba ita kaɗai, ko da Aure zata yi dole fa sai an nemo ƴan uwanta, shin waye madaurin auren ta?. Ni ba zuzzurfan arziki nake nema ba; ina neman ‘yar uwa, ina neman wurin da za ta samu gida. Kabiru ba ɗan son duniya ba ne; yana da niyyar gaskiya. Inna, ki kalla zuciyarta ki nuna karamci. In ba mu yi ba, me zai faru da ita? Zamu haɗa zumunci ne domin ta samu gida, ba domin mu mallaki dukiya ba.”
Inna ta rufe baki, idanuwanta sun yi ja. A gefen, Zainabu ta kalli mijinta ta ɗan matsa masa hannu: suna ƙoƙarin nuna jituwa. Kabiru ya yi ƙasa ya yi murmushi, sai ya tashi ya yi jinjina kai ya ce
“Inna, ina roƙonki. Zan riƙa kula da ita saboda gaskiya ce a raina. Ba ni da wata buri sai kula da Amatu, mu gina mata gida mai cike da nutsuwa.”
Halima ta ɗago itama ta ce
“Inna, don Allah, ki ba mu dama. Mu za mu yi mata biyayya, mu kula da ita kamar matar gida.”
Inna ta ɗan yi shiru, ta duba fuskokin su duka, ganin kyakkyawan niyya a idonsu ya sa zuciyarta ta ɗan sassauta, amma tana riƙe da ƙarfin magana ta ce:
“Zan yi tunani, Malam Yawale. Ba zan ɗauka a sauƙaƙe ba. Ku ba ni lokaci nayi tunani. Kuma ku sani: idan kuka yi niyya na gaskiya, zan yi marhaba amma idan niyyarku ta sha alamar biyan buri ne kawai, to ku bar ni kawai. Kada ku yi tsammani na yarda da gaggawa.”
Malam Yawale ya yi godiya, ya yi jinjina, Zainabu ta yi murmushi, Kabiru ya sunkuyar da kansa cikin godiya. Suka gyara zama, an dawo da yanayin hira amma a hankali, Inna kuwa ta nufi ɗaki ta zauna tana tunani...
Anan ne bayan Inna ta zauna a ɗaki tana dogon tunani, tana ta kai komo tsakanin abin da zuciyarta ke so da abin da al’adun rayuwa ke ɗora mata. Bayan ta yi tunani, ta tashi ta fito falo cikin sanyin jiki. Dukkan su Malam Yawale suna zaune suna hira a hankali, Halima na wasa da ƙaramar wayarta, Kabiru kuma yana ta kallon ƙasa yana murmushi lokaci zuwa lokaci.
Da suka ga Inna ta fito, duk suka gyara zama.
Inna Delu ta zauna a kujera, ta kalli Malam Yawale sannan ta ce
“To malam Yawale, bayan tunani mai zurfi da nayi… na yanke shawarar cewa babu laifi idan zumunci ya tabbata. Na amince da auren nan.”
Malam Yawale ya ɗaga kai cikin farin ciki, ya saki murmushi mai nuna godiya.
Malam Yawale ya ce
“Alhamdulillah! Wallahi Inna Delu, kin faranta mana rai sosai. Wannan zumunci