Author : Asmeetah writer Category : African Stories & Novels
tsaya cak, idonsa na kan Amal, zuciyarsa na bugawa da karfi kamar ana danna ganguna.
Ya ja numfashi mai nauyi, ya furta da kyar:
“Fansa kuma?... Wannan yaron ya haukace ne?...”
Inna ta share hawayenta, Farha kuwa ta zame gefe tana jin tsoron abin da zai biyo baya.
Amal ta lumshe idanu ta yi shiru, bacci ya lullube ta gaba ɗaya.
Abbah ya jinjina kai, ya furta cikin takaici:
“Dole Maleekh ya mata wani abu… amma me ya mata?... Wani irin fansa zai ɗauka akan macen da ta baka ƙauna?”
Ya miƙe tsaye da hanzari, ya fita ba tare da ya kalli kowa ba...
Kai tsaye Abbah gida ya nufa..
A lokacin da Abbah ya shiga falonsa, ya tarar da Islam, "Ke je ki ƙira mun Maleekh. .."
Islam ta ga yanayinsa gaba ɗaya ya sanja, ta zaro ido.
Ba tare da wata tambaya ba, ta hau sama domin ƙiransa..
Knocking ɗaya biyu ya buɗe...
“Yaya Maleekh… Abbah yana ƙiran ka, amma… da fushi!”
Maleekh wanda yake tsaye a bakin ƙofa yana zukar shisha, ya yi murmushin rainin hankali.
“Abbah da fushi? To wannan ai ba sabon abu bane.”
Ba tare da ya koma ciki ba, ya sauƙo sanye da gajeren wando da singlet, yana ɗauke da shisha a hannu.
Yana shiga falon, ya zauna kan kujera yana shan shishar sa cikin nutsuwa.
Abbah na zaune a gefe yana kallonsa da wani irin yanayi mai nauyi.
Cikin tsawa ya ce:
“Zaka ajiye wannan banzar abin ko sai na ci maka mutunci yanzu?! Shashashan yaro marar tunani!”
Maleekh ya tsaya, yana kallon gefe, shishar na fitar da ƙamshi mai daɗi...Ya ajiye a gefen ƙaramin table.
Ammy ta fito da gaggawa tana tambayar,
“Subhanallah! Me ke faruwa haka?!”
Abbah ya miƙe tsaye da hanzari, yana nuna Maleekh da yatsa:
“Me ka aikata wa Amal? Me ka mata? Ka bani amsa kafin na ɗauki mataki!”
Maleekh ya ɗan yi shiru, yana mai duba gefe kamar wanda ya gama komai a zuciya.
Sai ya ce da murya ƙasa-ƙasa
“Na gaya mata gaskiya ne.”
Abbah cikin fushi ya ce,
“Gaskiyar me, Maleekh?!”
Maleekh yana kallonsa kai tsaye: “Gaskiyar ɗaukan fansa da nayi akanta.”
Da sauri Abbah ya miƙe ya zo yanda yake zaune yasa hannu ya ɗauki sumar kansa da ƙarfi, yana ɗaga murya cikin fushi kamar zai fashe.
“Fansa! Fansa! Fansa!! Wani irin fansa ne haka, kai wani irin mutum ne? Marar mutunci kawai! Da kanka kake lalata rayuwar macen da kace kana so? Kuma marainiyar Allah? Ka sani sai Allah ya saka mata..”
Ya ƙare maganar tare da fincikar gashin kansa da ƙarfi, Maleekh ya ɗan yi ƙara yana riƙe da kansa.
Ammy ta ruga ta riƙe Abbah, tana faɗin:
“Don Allah ka sassauta murya! Me yasa zaka ɗauki irin wannan zafi akan soyayyar su?!”
Abbah ya nuna su da yatsa, idonsa na cike da hawayen takaici:
“Idan wani abu ya faru da yarinyar nan, wallahi tallahi, saina saka a ɗaure ka! Kayi shekaru a prison kafin ka sake ganin rana!”
Ya juyo ya ficewa daga falon, ƙafafunsa na dukan tiles cikin ƙarfi.
Ammy ta zauna kusa da Maleekh tana rarrashinsa, tana share hawayen da suka zubo masa...
Ba komai ne ya sa shi yin hawaye ba sai don Amal tasa mahaifinsa yana ɗaga masa murya kuma har da hawaye, ya rasa meyasa haka..
Ammy ta ce,
“Kai ne ka jawo wannan, Maleekh … kasan sun riga da sun asirce mahaifinka. Bazai taɓa ganin laifin Amal ba. Kuma me ka mata ne?..”
Maleekh ya dauƙi shishar a gefe, idonsa ya cika da hawaye, amma bakin ya ƙi furta komai.
Sai kawai ya ce cikin sanyi:
“Ba zaku taɓa gane menene fansa ba… sai na gama...”
Shima ya miƙe ya bar falon, kai tsaye part ɗinsa ya nufa..
🌹🌹🌹🌹
Kwana biyu kenan da dawowar Amal cikin hayyacinta, amma dai ta kasa furta komai tinda ta farka, kamar wacce tayi mutuwar zaune...
Idonta kawai ke buɗewa, amma kalmarta ta ɓace tamkar zuciyarta.
Inna ta zauna a gefenta tana magana, tana kuka, tana dariya don ta motsa ta amma Amal kamar mutum-mutumi.
Inna tana hawaye ta ce:
“Amatu, ki ce kalma ɗaya kawai… ki ce ‘Inna’, ko ‘ruwa’ ma! Me yasa haka! Me yasa kike yi min haka, Amatu?”
Shiru.
Hawaye kawai ke sauƙa daga gefen idon Amal, amma baki ko motsawa bai yi.
Abbah ma ya zo ya zauna gefenta, ya yi mata maganar duniya, amma bata ko ɗago kanta ba.
Har sai da ya lumshe ido, ya ce cikin tausayawa:
“Duk irin laifin da kika aikata, ki yafe wa kanki. Rayuwa ba haka take ƙarewa ba, daughter…”
Shiru.
Kamar da gwinki ake magana...
Farha ta zo ta zauna, ta riƙe hannunta tana mata magana amma Amal bata ma kallonta ba.
🕯️ Sati Guda tana cikin Shiru, ko sau ɗaya Amal ta kasa furta kalma ɗaya..
Kowa yana cikin tsoro da fargana har sati guda.
Amal bata yi magana ba, bata cin abinci, bata shan ruwa.
Kowa cikin gidan hankalinsa ya tashi.
Likita ya zo, ya duba ta sannan ya ce:
“Babu wata matsalar jiki. Amma zuciyarta ta ƙone. Wannan shiru ba rashin lafiya bane, kin magana ne saboda raunin zuciya. Idan har ba a samu wanda take ji ya motsa ta ba… zata iya faɗa cikin haɗari.”
Wannan maganar ya bugi zuciyar Abbah sosai.
Da hanzari ya miƙe daga kujerar, yana faɗin cikin tsawa:
“To tunda kai likita baka da mafita, ni zan nema da kaina! Wanda ya jefa ta cikin wannan halin, shi zai fito ya gyara!”
A wannan ranar Abbah ya ƙira Maleekh akan yazo cikin ƴan mintuna...
Maleekh kwata-kwata baya ƙaunar zuwa gidansu Amal amma ba yanda ya iya..
Da daren, gidan yayi shiru.
Sai hayaniyar zuciyar kowa ke yawo.
Sai ga Maleekh ya shigo cikin gidan yana shan shishar sa kamar ba komai ya faru ba.
Kallon raini da ɗan murmushin mugunta na yawo a fuskarsa.
Abbah da Inna suna zaune a falo, Abbah ya nuna masa hanya da murya mai nauyi:
“Je ka shiga ɗakin Amal. Sai ta yi magana yau. Tunda kai ka jefa ta cikin wannan mummunan halin, sai ka fitar da ita!”
Maleekh ya ɗan kalli gefe, yana yatsina fuska cikin ƙasƙantacciyar murya ya ce:
“To ni meye haɗina da rashin maganarta? In ta ga dama kar tayi mana, ban ce ta yi ba har duniya ta nad'e.”
Abbah ya tashi da sauri, cikin fusata ya ce.
“Kar ka raina min hankali, Maleekh! Idan baka shiga ka yi abin kirki ba, wallahi saina rufe ka da duka!”
Maleekh ya ɗan ja hayaƙi daga shisha yana murmushi cikin nutsuwa, sannan ya haura sama.
💔
Ya tura ƙofar ɗakin a hankali.
Ƙamshin turaren lavender ya cika ɗakin domin koda yaushe ɗakin a cikin ƙamshi yake, dake akwai masu gyaran gidan...
Amal tana zaune a tsakiyar gado, kai a jingine da bango, idonta jawur, hawaye na sauƙa a hankali.
Bata ko motsa ba lokacin da ƙofar ta buɗe.
Maleekh ya shigo a hankali, ya zauna a bakin gado kusa da ita.
Ya zu'ko hayaƙin shisha ya busa akan fuskarta kamar yana gwada ta da gangan.
Amal ko motsi babu.
“Oh, a wancan lokacin ke baki ga abinda kika min ba? Kin tuna ranar da kika mare ni a bainar jama’a a Kaduna?... Hm, da nine a matsayinki na mace marar juriya da nima haka zan shiga halin da yafi wanda kike ciki yanzu, da yau ni ne a halin da kike yanzu…Amal voice...”
Ya ɗan matsa kusa, ya kalli idonta kai tsaye, amma bata ko lumshe ido ba.
Sai kawai ya ƙara da murya mai kaifi:
“Ki sani, fansa ta a gareki itace maslaha.
Da kin san ciwon raini kamar yadda na sani, da kin san dalilin da yasa na shiga soyayya dake. Da ba'a zo wannan ga6ar ba..... Amal yanzu da kika zauna haka shiru, kin fi kyau fiye da lokacin da kike ta ihu da surutan banzaa...”
Ya saki ƙaramar dariya mai cike da ɗacin zuciya.
“Kin san me Amal? Fansa tana da daɗi. Amma a lokacin da na ɗanɗana naki... sai na gane ba farin ciki bane, azaba ce mai baƙar wuya...”
Ya ɗan ja numfashi, ya ɗaga kansa sama yana kallon fan da take juyawa, sannan ya ce a hankali:
“Ina son ganin yadda zaki sake tashi daga wannan karyewar, saboda sai kin sake ɗanɗanar fansa ta mai sanya maye a titi....”
Ya miƙe, ya juya yana shirin tafiya, amma kafin ya kai ƙofa, Amal ta motsa hannu ɗaya ba tare da ta furta komai ba..
Maleekh ya tsaya a bakin ƙofa, ya juyo kaɗan, yana kallon ta.
Idonsa ya ɗan sauya launi,
Ya juyawa zai fita daga ɗakin sai kawai wata ƙaramar murya, mai rauni mai cike da iko ta fito daga bayan sa:
“Dakata…”
Kamar iska ta tsaya a cikin ɗakin.
Murya ce mai sanyi amma mai tsinke zuciya.
Maleekh ya tsaya cak, ya juyo a hankali, yana kallonta da mamaki.
Idonsa ya faɗa cikin nata, wanda ke cike da hawaye amma kuma akwai wani sabon haske a ciki kamar wacce ta dawo daga duhu..
Murmushi yayi sannan ya ce,
“Oh, ashe ba haukacewa kika yi ba? Iskanci ne kawai...?”
Amal bata amsa ba.
Kawai ta tashi a hankali daga kan gadon, ƙafafunta suna danna ƙasan tiles a hankali, tana takowa gare shi kamar mai zuwa wajen ƙaddara.
Hawaye na bin kuncinta, amma fuskarta ta nuna nutsuwa da ɗan murmushi mai sa tsoro.
Ta tsaya gabansa, sun tsaya fuskantar juna.
Hannuwanta suka tafi kai tsaye ga wuyansa... kafin ya yi wani tunani, ta haɗe bakinta da nasa...
Da farko Maleekh ya tsaya kamar an dasa shi.
Idonsa ya zaro, zuciyarsa ta tsaya.
Sai dai sannu a hankali jikin sa ya fara yin sanyi, ya fara narkewa a hannunta...
Amal ta riƙe kansa sosai, ta zurfafa sumbatar.
Ba sumbatar ƙauna bace kawai, sumbatar azaba ce, sumbatar ramuwar rai, sumbatar mace da zuciyarta ta kone.
Hawayenta na gauraye da numfashinsa, tana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, kamar wacce ke sakin wani zafi da ta ɗauka shekaru.
Mintuna suka shuɗe suna a haka.
Kamar wanda aka tsayar da lokacin domin ya tsaya ne cakk.
Numfashin Maleekh ya canza, hannunsa ya zame a hankali daga jikinta, jikin sa ya ɗau rauni, kamar wanda aka tsaga masa zuciya da yatsa.
Amal ta dakata.
Ta ja numfashi mai zurfi, ta ɗan matsa baya kaɗan tana kallonsa cikin ido.
Sai ta saki wani murmushi mai taushi da ke ɓoye ciwo.
“Na baka raunanniyar zuciyata…”
ta ɗan numfasa
“Na karɓi taka lafiyayya.”
Ta ɗan jinjina kai, ta ƙara da murya mai ƙarfi kaɗan:
“Je ka.
Ka jira… abin da zai faru.”
Kamar an soka masa wuƙa a cikin zuciya, Maleekh ya tsaya yana kallonta.
Zare baƙin glass ɗinsa daga idonsa yayi, ya jingina kai, yana kallonta da idon da ke bayyana abu biyu lokaci guda, mamaki da ƙiyayya...
Ya ɗan ja numfashi, ya juya ba tare da ya furta komai ba.
Ƙarar takalminsa ta ɓace daga ɗakin a hankali...
A lokacin, Amal ta faɗa kan gado, ta rufe fuska da hannaye tana numfashi cikin zafi, hawaye na sauƙa kamar ana wanke zuciya da jini.
Bayan Maleekh ya fita daga gidan, sai Abbah da Inna suka shigo ɗakin da sauri, zuciyarsu cike da fargaba.
Amal tana zaune a gefen gado, idonta na kallon ƙasa kamar wacce ke jiyo muryar zuciyarta.
Abbah ya matsa kusa, ya furta cikin tausayi:
“Daughter…”
Amal ta ɗago a hankali, ta kalli Abbah da Inna, murya a sanyaye kamar wacce ta fito daga ƙasa ta ce:
“Ina son ganin Zayd…”
Kallon juna suka yi da mamaki, Inna ta dafa kafaɗarta cikin farin ciki da jin sauƙin zuciya ganin yanzu Amal tayi magana.
Abbah ya murmusa, yana faɗin:
“Alhamdulillah…! Yanzu kin yi magana kenan. To shikenan, kar ki damu, zan ƙira shi.”
Ya miƙe ya fita da sauri, zuciyarsa cike da godiya ga Allah...
☀️ Washegari da safe.
Zayd yana zaune a falo, cikin nutsuwa da ɗan damuwa. Ƙiran Abbah ne ya kawo shi, bai san me Amal zata gaya masa ba.
A zuciyarsa, yana jin ƙaunar Amal kamar da gaske amma har yanzu yana jin kunyar abinda suka aikata tare da Maleekh.
Sai ga Amal ta sauƙo daga beni.
Takalminta na yin ƙaramar ƙara, kowane mataki yana jawo hankalin Zayd ya kasa motsawa.
Ta tsaya a gaban kujera, ta zauna cikin kwanciyar hankali amma idonta na cike da nutsuwar da ke ɓoye wuta.
“Duk nasan komai, Zayd.
Duk shirye-shiryen da aka yi mun, daga photona har zuwa zubar da mutuncina duk shirin Maleekh ne.”
Zayd ya yi shiru, ya kasa ɗago kai.
ta ci gaba. “Kaima nasan baka da bambanci da shi, tinda duk ɗaya kuke wurin ɗaukar fansa. Amma ban tsaneka ba…”
Zayd ya ɗago, ya ce cikin raunannen murya
“Amal… kiyi haƙuri. Wallahi ba da niyyar cutarki nayi ba.
Na biye masa ne saboda ina son ganin farin cikinsa amma daga baya, na gane…
Na gane ke ce matar da nake so da gaske.”
Amal ta ɗan saki murmushi sannan ta furta
“Da gaske kake?”
Zayd ya jinjina kai da sauri, idonsa cike da tabbaci:
“Na rantse da Allah, ina sonki da gaske, kuma zan so ki har karshen raina.”
Ta ɗan juyo gefe tana murmushi, ta ce cikin sanyin murya:
“To in har da gaske kana sona to sai an tabbatar.”
Ya kalleta cikin tambaya.
“Ta yaya?”
Amal ta ɗago idonta kai tsaye cikin nasa, ta ce da murya mai daɗin sauraro:
“Ina so nan da sati ɗaya a ɗaura mana aure.”
Zayd ya yi firgigit, amma murmushin farin ciki ya bayyana a fuskarsa.
“Aure? Amal... kina nufin... muyi aure?”
A taƙaice ta ce: “Eh. Auren gaskiya.
Na riga na sanar da Abbah cewa kai nake so, kuma na tabbata ba zaka ƙi ni ba.”
Zayd ya kasa boye farin cikinsa, zuciyarsa ta ɗau haske kamar ɗan ƙaramin yaro.
“Insha Allahu! In har kin amince, ko gobe kika ce, zan ɗauka da hannu bibbiyu.”
Amal ta ɗan kalli gefe,
“To, next week ɗaurin aure, kai dai ka sanar da iyayenka, su zo su samu Abbah.
Ni kuma zan fara shiri tun yau.”
Zayd ya miƙe da murmushi yana faɗin:
“Nagode Amal. Na rantse bazan taɓa cutar da ke ba.”
Amal ta ɗan saki murmushi, “Na sani. Ka tafi lafiya.”
Da farin ciki Zayd ya fita daga falon, yana jin kamar mafarki.
Amal kuwa ta jingina kanta da kujera, ta lumshe ido, numfashinta ya yi nauyi.
Sai ta ce a ranta, cikin zafi da ƙuduri:
“Zaka sha mamaki Maleekh…
Zan ga yadda zuciyarka zata yi lokacin da ka ji cewa zan auri Zayd.”
Ta saki murmushi mai cike da zafi, murmushin mace da aka karya wa zuciya, amma yanzu ta zama wuta. 🔥
Washegari
Mahaifin Zayd ya samu Abbah, suka yi magana akan auren Amal.
An fara shirye-shiryen aure cikin gaggawa, ana ta walwala da cike da murna a gida, amma Amal dai kamar inuwar kanta bata runtsa ba, bata fara gyaran amare ba. Lokaci kawai take jira, ba saboda son aure ba, sai don burin zuciyarta...
A gidansu Zayd.
Farha ta riƙe hannun Zayd da murmushi ta ce,
“Dan Allah Yaya, ka riƙe Amal da amana. Ta sha wahala sosai, kar ka ƙara mata ciwo.”
Zayd ya jinjina kai cike da niyyar gaskiya.
“Farha, wallahi zan kare ta. Zan ba ta farin cikin da ta rasa. Zan zama murya a lokacin da wani ya kasa jin nata.”
Sai dai cikin zuciyarsa yasan, ƙaryewar zuciya ce kawai ta sa Amal ta amince da shi...
A can wajen Maleekh, lokacin da labarin auren Amal da Zayd ya riske shi, sai kawai yayi murmushi, murmushin ƙarfin zuciya..
Sai kawai ya buge da cewa.
“To tunda ta ce tana so, ai sai tayi. Ni kuma ban damu ba...”
Ya faɗa yana shan shisharsa, amma a ransa akwai rikici da tambayoyi marasa amsa.
🌹🌹🌹
Ana saura kwana uku a ɗaura auren Amal da Zayd, Abbah ya ƙira iyalansa gaba ɗaya a babban falo.
Yana zaune a kujerar tsakiyar falo, kowa yana kallonsa. Ammy, Maleekh, Islam, Arfat, da Zayd wanda zai auri Amal.
A cikin nutsuwa Abbah ya gyara murya, yana murmushi.
“Na tara ku saboda wani abu mai muhimmanci. Kuma maganar akan Maleekh ne.”
Maleekh ya ɗago kai yana kallon mahaifinsa cikin rashin fahimta.
“Ni kuma? Me ya faru, Abbah?”
Abbah ya ɗan murmusa, sannan ya ce da ƙarfi mai nauyin gaskiya:
“Saboda ina tausaya maka, Maleekh. Na san baka tausayin kanka, Ka ji auren Amal, ko? Toh, yanzu zaka ji sirrin da muka ɓoye a cikin wannan shekarar...”
Ammy ta ɗan matsa kusa da shi ta ce,
“Wani sirri ne haka Alhaji?”
Abbah ya ɗaga mata hannu alamar ta dakata.
“Zan gaya muku duka. Maleekh... waccan Amatu da ka bari a shekarun baya, wadda ka ɗauka ta mutu a gobarar gidan su... to itace Amal!”
Falonsu ya ɗauki shiru na ɗan lokaci.
Maleekh ya ɗago da sauri, yana kallon Abbah, zuciyarsa ta tsaya.
“Me... me kake faɗa Abbah?”
Abbah ya daure ya cigaba.
“Ita ce fiancée ɗinka tun yarinta. Na faɗa maka labarin, ko? Gobarar gidan iyayenta? To, iyayenta ne suka mutu, ba ita ba. Kakarta Inna ce ta gudu da ita kafin gobarar ta ci gaba. Wannan dalilin yasa bata da wani a duniya face Inna.”
Maleekh a rikice yake kallon Abbah yana girgiza kai tare da faɗin,
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un... na wulakanta ta... ni na ci amanar wadda ta kasance fiancée ɗina tun yarinta...!?”
Ammy ta riƙe kirjinta tana kallon Abbah da mamaki.
“Kace Amal ɗiyar Hajiya Khadija ce? Ƴar gidan Babban Governor Alhaji Abdulsamaad Cash Maker?!”
Abbah ya ce da karfi,
“Itace! Itace ‘yar Alhaji Abdulsamaad babban abokina, wanda aka kashe da gobara a lokacin siyasarsa! Amma ga ɗiyarsa ka zalunce ta!”
Maleekh yana riƙe da kansa yana faɗin,
“Me yasa... me yasa ban gane ba? Me yasa ban bincika wacece ba? Sunanta ma Amal Abdulsamaad... ya kamata nayi tunani... amma na makance da ƙiyayyar fansa!”
Zayd ya yi shiru yana kallon ƙasa, zuciyarsa na bugawa jin wannan al'amarin...
Maleekh ya ɗago idonsa cikin hawaye ya kalli Abbah.
“Abbah, me yasa baku gaya mun da wuri ba? Meyasa Amal ta ɓoye min alhalin tasan nine Leekh ɗinta?”
Abbah ya ce da murya mai